Free chapter · Read without an account

Page 19&20

by Ammey Laylerh · DUHU na DUKAN duhu

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.

ꨄ Ranar da aka cika ta makwanni biyu da kwamushe Sameer garin Kaduna suma suka waye da nasu tashin hankalin rasa ɗan gidan Debuty governor. Wanda cikin abinda bai wuce kasa da awa daya ba har labarin ya ƙara de media, inda kai tsaye social media ta samu abin tattaunawa har wasu na zargin cewa kodai a wannan karon din ma dai Kind Dada nada hannu a batar Zayed?.... Aikuwa kafin kace me ne sai ga wannan maganar ta zama abin tattaunawar ko a ina media, haka wannan kidnapping din yaci gaba da bazuwa yana yaduwa kamar wutar daji. Don a yanzu duk inda kabi media maganar kidnapping din ita ce very latest story dake tashe a media. Jami'ai kuwa suma cikin abinda bai wuce kiftar idon ba suke sake tsaurara tsaro. A can Abuja bangaren Dss Headquarters nasu kuwa gagarumin taro aka shirya na gaggawa sabon jami'i da tsoho, washe garin ranar dake shima cikin dare ne aka kwamushi,don haka tun cikin daren Ajmaal ya samu sakon lokacin 2:46 Am na dare. Wanda shi a lokacin ma yana zaune gaban system nashi yana zurfafa akan bincike game da Rayyern ɗin, don haka a lokacin da sakon ke fado masa tun kafin ya gama karanta sakon gaba ɗaya, abin da ya fara kawo masa a rai shi ne hoton Rayyern, aikuwa kamar Rayyern din daya furta kafin haka ta ratsawa cikin kansa kamar saukar guduma haka yaji sunan ya wani dake shi a tsakiyar ka. Idanunsa yaja yana dan lumshewa na wasu dakiku a hankali yana kallon pop na ɗakin nasa na wasu daƙiƙu, kafin ya miƙa tsaye yana nufar gaban gadonsa ya saka hannunsa ya ɗauki wani file. Wanda gaba ɗaya ya gama tattara bayanan irin yadda Rayyern ke gudanar da ire iren ayyukansa ne, wanda file na farko ke dauke da folder na Old Operation File Authorization Required. Tamkar ba shi ne yayi documentation nashi ba haka ya bude file din yana sake nazarta da kuma karantarsa, kafin ya kai zaune daga gefen gadon yana tunanin ko me ya sa wannan tsohon file ɗin ya kasance ana buƙatar izinin babban jami'i kafin a buɗe shi?. Duk da ya sani aikin DSS ba sabon abu bane a gare shi, yawanci ko wane files suna zuwa ne da matakan sirri daban-daban, amma akwai bambanci tsakanin file da aka ce CLASSIFIED ne da kuma wanda aka ce sai da izinin babban jami'i kafin a taɓa shi bayan shekaru. Wannan na biyu shi ne yake damunsa. Domin idan babu wani abu mai nauyi a ciki, me ya sa har yanzu ake tsare da shi haka?. Kai tsaye gaban wani ƙaramin shelf wanda yake kamar ababuwan sirrin sane a ciki ya nufa, kai tsaye idanunsa suka sake sauka kan hoton birthday ɗin Rayyern na ranar, ɗan jim yayi ya tsaya yana kallon hoton, tsam yai a ransa yana son sanin mai yasa hoton birthday din ke yawan fado masa? Ajje hoton kawai yayi sai dai kafin ya juya sai idonsa ya sake sauka kan wani ƙaramin abu dake gefen hotun. Wata tsohuwar lambar ce da aka rubuta a bayan wata takarda ce. Kai tsaye ya ɗauka yana dubawa ta, lambobi ne guda shida kawai, ba tare da wani suna ba. Da farko ya so ya mayar da ita, amma sai ya tsaya tamkar mai nazartar wani abu, kai tsaye wani abu na haskuwa a cikin ransa tabbas yasan wannan tsarin rubutun. Tabbas tsarin rubutun Rayyern ne shi ke amfani da irin wannan lambar kuma a duk wani lokacin aikin da suka yi shekaru da suka wuce. Ba lambar waya bace, ba kuma code ɗin ofis bane. Alama ce da Rayyern yake amfani da ita wajen haɗa wasu bayanai a cikin kansa.... Wani ɗan dukan kansa AJMAAL yayi hadi da ɗan matse takardar tsakanin yatsunsa tare da furta. “Me wannan ke nufi kuma?” Yay maganar da kamar alamar tambaya yana fesar da wata iska mai zafin gaske.

Washe gari da safe tun kafin bakwai din safe kowa ya gama hallara a hedikwatar DSS, wanda kai tsaye yanayin safiyar ranar ya kasance daban da yadda aka saba gani ce. Mutane sai shige da fice kawai suke, yayinda wasu jami'an kuma suke duba bayanai a manyan screens ne, baki daya headquarters din ta dauki wani irin shiru da irin nauyin abin da ke gabansu. Saboda tun bayyanuwar sunan *KIND DADA* case's suka sanja daga yanda suke suna ma zarta tunanin sune. A lokacin da AJMAAL ke shiga cikin ɗakin binciken, ya tarar da Jameel Baita yana tsaye a gaban screen, hannayensa a haɗe a bayansa yana ta aikin safa da marwa. Kai tsaye Ajmaal sara masa yayi wanda shi kuma Jameel Baitan wani numfashi ya fesar kafin ya iya kallon AJMAAL na ƴan daƙiƙu Kafin ya ce, “Ka samu barci kuwa?” AJMAAL ya yi ɗan murmushi mara ƙarfi da furta. “Ba sosai ba.” Wani huci mara zurfi Jameel Baitan ya hurzar da faɗin “Rayyern? Rayyern.” Wani numfashi mara zurfi shima Ajmaal din ya fesar kamar sunan shi kaɗai ya isa ya fahimtar da shi irin abin da ke faruwa, kafin ya miƙa masa file din daya gama shiryawa a daren jiya daya gaza runtsawa tare da furta. “Me ya sa wannan file din yake a boye?”

A natse Jameel Baita amsa file din tare da dan jujjuya shi a hannunsa kafin ya bude, kai tsaye da faɗin “Kabar wannan Ajmaal kayi aikin dake gabanka, don wannan ɗin wani operation ne da aka rufe tun da ba'a son ta do shi.....” a kaikace AJMAAL ya kalle shi sosai kafin ya kaima iska naushi da faɗin yana kuma fitar da numfashin ta baki da faɗin “Operation ɗin Rayyern ne?” Shiru na ɗan lokaci Jameel Baita ya yi kafin ya amsa masa da cewa, “Eh.” wanda ya saka AJMAAL ya ɗan matsa gaba har yana yin kamar zai shi ge cikin jikin J. Baita din da cewa. “Kuma me ya sa ban san shi ba? Bayan duk wani aiki nashi a tare muke gudanar dashi?... " J. Baita ya juya ya kalle shi fuskar nan babu walwalar komai da furta. “Saboda wasu bayanan ba a ɓoye su ne don kada abokan gaba su gani ba, AJMAAL! Wasu lokutan ana ɓoye su ne don kada mutanen cikin gida su tambayi ba'a si ko tambayar da ba a shirya amsawar ta ba irin haka” wani shiru AJMAAL yayi komai bai ce ba sai ma ƙoƙarin son karanta abinda ke ɓoye a bayan idanun J. Baita da yake kokarin yi. “Kuma kana ganin wannan file ɗin shi ne zai bani amsar abin da ya faru da Rayyern?” a wannan karon kam kamar a ɗan zafe J Baita ya juye gare shi da faɗin, “Ban ce haka ba.” Wani kallo Ajmaal din ya masa da faɗin “To me kake nufi kenan?”AJMAAL ya yi tambayar wani ɗan iskan murmushi mai ɗaci na kufce masa, tare da cira file din sama da cewa. “Iyaka wannan kaɗai ya isa ya saka na buɗe wannan file din.....” J. Baita ya ɗan juyo yana kallon sa kafin ya kira sunan. “AJMAAL…” da ɗan karfi, wanda ya saka Ajmaal sara masa da faɗin. “Yes Sir?” Sosai yay ƙoƙarin daidaita nutsuwarsa kafin yace. “Ka tuna cewa Rayyern ya koya maka yadda ake neman gaskiya ne kawai. Amma akwai bambanci tsakanin neman gaskiya da kuma shiga inda gaskiyar ba ta son a shige ta.” AJMAAL ya sauke idanunsa kasa na ɗan lokaci. “Shi ma ya koya min cewa idan gaskiya ta zama mai hatsari, ba yana nufin a daina nemanta ba ne! Yanq nufin a san hanyar da za a taka ne domin nemota .”

Shiru ne ya ratsa tsakanin dakin kafin J. Baita ya yi shiru na ɗan lokaci. A ƙarshe ya ɗaga hannu ya nuna, a natse Ajmaal ya nufi wata tsohon computer da aka keɓe domin tsoffin bayanai. Kai tsaye Ajmaal ya zauna gaban computer din ya shigar da wasu lambobi, sai screen ɗin ya nuna wani tsohon file mai alamar ja. OPERATION + BLACK VEIL AJMAAL ya ɗan tsaya cak, kafin a bayyane ya furta “Black Veil?” tare da juyo da fuskar computer din zuwa ga J. Baita da ya kusan mutuwar tsaye, bai dawo daga cikin wannan mutuwar tsayen da yayi ba Ajmaal ya sake cilla shi a wata sabuwar shork ɗin, ta hanyar cilla masa tambayar “Me ya faru a wannan operation ɗin?” “Ba mu sani ba,” J. Baita ya bashi amsar kai tsaye, “Ba ku sani ba?” kansa J. Baita ya jinjina masa da faɗin. “Abin da file ɗin ya bari kawai muka sani.” J. Baita yayi maganar da buɗe file ɗin. Wasu bayanai suka bayyana a screen din. Sunaye, lambobin wurare, lokuta, wasu kuma ganan bayanan da aka riga da ma aka goge su ne. AJMAAL ya fara karantawa a hankali. Da farko komai ya yi kama da wani tsohon aikin leƙen asiri na yau da kullum da suka saba, kafin idonsa ya tsaya kan wani sashe. *PRIMARY OPERATIVE: RAYYERN KHALID* A ƙasan rubutun kuma akwai wani layin da shima aka rufe gaba ɗaya. *STATUS+ OPERATION TERMINATED* kafin wani layin shima ya sake bayyana dodar dashi *RECOVERY: FAILED*AJMAAL ya ɗan matsa kusa da screen ɗin.“Recovery failed?” J. Baita ya gyada kai “Me aka rasa?” Shi ne bayanin da bai bayyana ba.” AJMAAL ya ci gaba da karantawa. Sai ya ga wata rana. Ranar da aka rufe operation ɗin. Ya ɗan daki kansa tabbas ya san ranar. Ya san ta sosai saboda wannan ita ce ranar da Rayyern ya daina zuwa aiki na wasu kwanaki kafin a sanar da su cewa yana cikin wani aiki na musamman. Amma abin da ya fi ɗaukar hankalinsa fiye da komai shi ne lokacin da aka rubuta.... 02:17 Am.... Tabbas haka ne, a ranar da aka kwana ana sheka wani irin ruwan da ba'a taɓa irinsa ba tun kamawar daminar shekarar, wanda a ranar ma ba zai taba mantawa ba kwanan ukku bai ga Sir Rayyern ɗin saba. Wani zazzafan numfashi ya fesar yana kallar rubutun dake ƙarƙashinsa “One operative missing. No body recovered.” AJMAAL kam kai tsaye a wannan karon sai da ya kusan daina numfashi na ƴan daƙiƙu kafin ya kwato kalmar. “Wannan…” ya furta a hankali muryarnsa na kokarin bayyana rauninsa, amma wannan ɗan banzan taurin kan da kafiya da jarumtaka sak irin ta Rayyern ya saka Ajmaal shanye komai da sake kallon J. Baita yace. “Wannan shi ne ranar da aka ce family na Sir Rayyern....... ?” sai kuma ya kasa karawa ya dafe kansa da furta. “Amma me ya sa aka rubuta one operative missing maimakon dead?” Yay maganar yana sake danna wani sashe wani sabon rubutun na sake fitowa *SECONDARY REPORT SEALED* AJMAAL ya ɗan matse baki da tabewa da furta. “Wannan report ɗin me ya sa aka rufe shi?” Jameel Baita yayi shiru, wanda wannan shirun da yayi yaba AJMAAL amsa fiye da kalmomin da zasu fito daga bakinsa. A hankali AJMAAL ya ɗan turo computer din tare da juyowa ga Jameel Baita yace, “Ka san wani abu?.”

Sai dai tun kafin yace komai Jameel Baita ya tari numfashinsa da cewa. "Karka ma tsaya kace zaka wahal da kanka Ajmaal, domin kuwa babu abinda zaka iya samu...." Wani irin shegen murmushin gefen baki ne ya subcewa Ajmaal ya koma kan screen da faɗin. “To bari mu gani.” Kai tsaye ya shiga wasu latse latse wani ƙaramin notification ya bayyana a ƙasan screen ɗin sai dai Access Denied kawai ke nuna masa, ya sake gwadawa amma hakan din dai ne, Wani dan lumshe ido Ajmaal yayi yana hurzar da iska. “Wani ya sa lock?” Yay maganar yana sake matsawa kusa da screen ɗin. Ya kalli tsarin lambar, sannan ya kalli Jameel Baita.“Wannan ba na hukumarmu bane.” Jameel Baita ya ɗage gira ɗaya da cewa. “Ta yaya ka sani?” Ajmaal ya yi murmushi kaɗan. “Saboda wanda koma waye wannan wanda ya saka lock ɗin ya yi shi ne da tsarin da Rayyern ne kawai ke amfani da shi.” Tsit haka ɗakin ya dauki shiru kafin Ajmaal ya sake kallon screen ɗin, yayi wani baya da kansa ƙafarsa kuma yana turata karkashin table ɗin dake ɗauke da computer ɗin. A hankali wani abu na fara haɗuwa a cikin kansa. Tabbas idan har Rayyern ne ya bar wannan lock din a cikin tsohon file ɗin kafin ya ɓace… to kuwa yana da tabbacin akwai yiwuwar bai bar shi don ya hana mutane shiga ba. Wataƙila ya bar shi ne domin ya san wata rana wani zai zo gare shi, wani zai yi ƙoƙarin buɗe file ɗin dole, kuma idan har ya kasance mutum ya san tsarin sa… Tabbas zai gane cewa wannan ba ƙofa bace. Alama ceeee.... AJMAAL ya ɗan murmusa 'Ka fara wasan tun kafin mu san cewa wasan ya fara…' yay maganar a cikin ransa yana sake lumshe idanunsa...

*RAYYERN*

Yana zaune shi kaɗai a gaban wani ƙaramin screen. Hannunsa ɗaya yana riƙe da glass cup, ɗayan kuma yana dan jujjuya wata tsohuwar waya a hankali. Yana kallon sakon daya fado masa na ƴan daƙiƙu. Wanda ya saka wani lalataccen murmushi bayyanuwa a saman fuskarsa, ba normal murmushi bane irin na farin ciki, a'ah murmushi ne irin na mutumin da ya daɗe yana jiran wani abu ya faru. A wani irin kasaitance ya ɗaga glass ɗin dake gabansa zuwa bakinsa ya kurɓa red wine nashi kaɗan, “Dole dama nasan zaka fara ne da wannan.” Yay maganar tare da ajiye glass cup ɗin dake rike a hannunsa ya mike tsaye

“AJMAAL…” Ya ɗan dakata idanunsa na komawa kan screen na waya din.

“Ba file ɗin nake son ka gano min ba.. Abin da ya sa aka rubuta file ɗin nake son ka ganema idonka.” daga haka ya kashe screen ɗin daidai da lokacin da wayarsa ta yi ƙara sau ɗaya kawai. Ya bude messeges din sako daya ne kawai....

_THEY ARE OPENING IT_

Rayyern ya karanta shi, sannan ya share saƙon ba tare da ya amsa ba, kamar ba zai ce komai ba kafin ya juya yana nufar wani daki na daban da faɗin. "Zan barka a wannan karon ka gano komai AJ.... Saboda gaskiyar ba ita ce za ta ci gaba da zaman jiran a buɗe mata ƙofa ba.....”

A gefe guda kuwa bangaren Ajmaal har lokacin yana zaune gaban screen ɗin, idanunsa a kan kalmar *BLACK VEIL* tuni zuwa lokacin K Mashi ya jima da fita. Wayarsa ya dauka ya kira wata number cikin wani yaren dayafi kama Dana sirri Yay maganar tare da ajje wayar ya ce a zuciyarsa.

'Rayyern, idan ka bar min hanya ne domin in same ka… to kuwa tabbas zan bi ta har ta kawoni gareka...' daga nan shima ya fita saboda kowa daya gama hallara a wurin meeting din. Gaba ɗaya tun ma daga farkon shigowarka headquarters din zaka gane cewar ehhh lallai tabbas ba ƙalau ba, don manyan jami'an majiya karfi sai famar kaiwa da komowa suke hankalin kowa ba'a kwance ba, musamman ma waɗanda suka san ko waye ainihin Rayyern khalid, daga can cikin ainihin babban dakin taron nasu kuwa tsaitsaye kowa yake yana fuskantar Director-General na Department of State Services (DSS) ɗin wato KHABEER K. MASHI.... Wanda gaba ɗaya kusan duka manyan jami'an su na tsaye a wurin, Ajmaal ne kawai tsaye daga dab da tabla din yana fuskantar KHABEEER K MASHI hannun za daya kafe a goshinsa. Hakan ya sanya babu abinda zaka iya kalla a jikin sa inba lallausan gashin kansa da yake kwance ba, yana sanye cikin cikakkiyar shigar uniform na kayan aikinsu. Ɗan table ɗin dake gabansu masu ɗauke da tarin files KHABEEER K MASHI ya ɗan daka, tare da Furta. "Dole na tabbata akwai wata alaka bayan ɓoyayyan al'amarin dake gabanmu, domin kuwa RAYYERN KHALID ya sake kwamushe ɗan mataimakin gwamnan Kaduna. Waye na gaba? Nine!? Kune? Ko kuma dai Mr. President?....." Yay Maganar a zafe da kallon Ajmaal da tun da taron ya gama hallara komai K Mashin yaki cewa sai ya yanzun." Nasan tabbas zuwa wannan lokacin babu wanda bai san abinda ya faru ba... Abin haushi sai dai mun gaza tabuka uban komai tun da ga can Sameer tsare a hannunsa mun gaza kwatoshi daga hannunsa gashi yau an sake wayar gari ya sake kwamushen ɗan mataimakin gwamna...."

Sara masa Ajmaal yayi tare da furta "Yallabai ina mai tabbatar maka da cewar idan har da akwai mutumin da zai gano iya gano Rayyern khalid cikin sauƙi to ni ne...." Yay maganar yana fesar da wata numfashi mai zafi, sai dai tun kafin yaci gaba da cewa komai K Mashi ya katse shi a zafe da faɗin. "To uban me yasa ka baka gano shin ba har yau tsayin kwanaki tara da baka aikin? Ko rainin hankalin daka saba mana cikin aiki yau din ma zaka taɓa ma irin na wancan banzan ɗan ta'addar ?" Yay maganar a kufule a kuma mugun zafafe da ci gaba da faɗin "Mai yasa har yanzu Don't it Ajmaal duk kayan aikin da muke dasu camares da wasu nau'o'in na'urorin amma kun kasa gano inda yake, miye dalilin da yasa? Hakan na nufin dukka basu da amfani kenan a wurinmu? Ko kuwa so kuke sai ya gama karar damu kokuwa mai kuke nufi?..... " Ya sake faɗa a fusace da kallon Ajmaal din dake kame yaci gaba da cewa. "Idan har Ƴan ta'adda suna jin cewar zasu iya shigowa cikin ƙasar mu kuma su kawo mana hari irin haka, To ina son su sani cewar mu ba gajiyayyu bane, kana kuma bamuyi lalacewar da ƴan ta'adda zasu yi nasara akan muba. Dole Rayyern khalid yasan cewar muba sa'anninsa bane" Wani kalan runtse idonsa Ajmaal yayi, kafin ya bude idonsa kamar wani zakin daya fito farauta ya daki table ɗin dake gaban K Mashin yace. "Mainene asalin dalilinsa na yin hakan? Shi ne hasalin abinda kawai nake son fara sani kafin gano inda yake...." Ya faɗa a mugun fusace yana manta gaban wa ye yake, yana manta cewa tsaye yake gaban shugabansu kaf na Nigeria din ma bama iyaka Abuja ba. Saboda abinda kawai idonsa ke hasko shi ne wannan tsayayye jajirtaccen bazara ten matashin Jami'in nasu wato Sir Rayyern din sa. Wannan Jami'in da yake bada rayuwarsa akan ƙasar sa, wanda yake tinkarar mutuwa a yayin da kowa ke gudun ta, wannan dai mutumin da ita kanta mutuwar ke tsoronsa, shi kuma a kullum kwanan duniya yake sake kusanta kansa gareta yana tunkararta amma kuma tana sake ja baya da shi. Idanunsa da har suka fara sirka tsantsanar ɓacin ransa ya ɗago yana kallar sir ɗin, tare da wani kalan juyi yana ɗaukar ƙafarsa ɗaya ya ɗora saman teburin dake manyan nasa, yana binsu da wani kalan kallo wanda yafi kama dana tuhumar nan, tare da furta. "Ka da fa ku manta shi fa Sir Rayyern ne fa?!, wanda ya taso cike da kishin ƙasar sa. Ina son ku dukanku ku ku tuna cewar koda da daƙiƙa ɗaya na cikin rayuwarsa bai taɓa jinkirin baima ƙasar sa rayuwarsa ba, Ita kuma wannan zafin kan kuke maganar su a kai na ku sani da cewar dasu ne aka haife shi shi kuma ya koya min, don haka a koda yaushe su ne ɗabi'una..... Ina son sanin mai ya faru da sir Rayyern???... Tabbas idan har nasan hasalin abinda ya faru dashi har ya saka shi rikidewa zuwa dan ta'addar da duniya ke nema ruwa a jallo nai alkawarin cewa duk inda yake a cikin wannan duniyar sai na nemo shi, na gurfanar dashi bayan na gama tabbatar da cewa bashi da laifin komai, domin kuwa rantsuwa nayi da rai da rayuwata zan kare al'umma ta, na zama jam'i ne domin kare waɗan da basu da ƙarfi, kana a shirye nake da duk wani ƙalubalen da zan fuskanta..." Chief security Intalligence office (CSIO) wato Abba Aminu, shi ne ya mike da faɗin." A koda yaushe cikin tsarin ayyukan mu kai da Rayyern khalid kun fi kowa bamu matsala, saboda a cikin ranku kuna jin cewa kunfi kowa kune kuma mafiya kwazo da wannan kuke jahiltar kan ku...." Tukur Baba ne ya Mike shi ma da ɗorawa da faɗin. "And shi yasa suka fi kowa daukar suspension ba, saboda jiji da kan da kan da suke da, da kuma ganin kamar su kaɗai ne masu kwakwalwa bayan kuma muna da irin su ninkin ba ninkin kawai suna iya sarrafa kan sune ba kamar su ba..." Yay maganar yana nuna Tukur Baba da faɗin cewa. " Sanin kan ku ne cewar ko Assistant director I (ADII) Jameel Baita yana daya daga cikin wadanda ma suka zarce su, sai dai azarɓaɓin da suka fisu ne ke naku sar da karsashin kowa... " Chief security Intalligence office (CSIO) Abba Aminu ne ya ɗan dafe kansa da jujjuyawa kafin ya mike da ɗagawa Tukur Baban hannu yace. "Duka fa ba wannan bane ya taramu anan ba! KIND DADA shi ne mutumin daya taramu a nan ba wai wani Rayyern khalid ba, domin mu a wannan hukumar tamu bamu ma taɓa sanin wani mai irin wannan sunan ba, KIND DADA shi ne mutumin da muka saka farautarsa kota halin Yayaneeee..." Yay maganar tare da juyawa ya kalli Mai girma DG K Mashi. Wanda tun da Abba Aminu din ya soma magana yaji wani kwanciyar hankali na kama shi, sai a lokacin ya sauke wata ɓoyayyar ajiyan zuciya da miƙewa tsaye. "Kuma kai tsaye alhakin wannan aikin har kwanan gobe yana nan a wuyan AJMAAL SUHAAL...." Daga haka zaman tattaunawar nasu ya tashi duk da cewar Ajmaal din yaso cewa wani amma basu bashi kowacce iriyar damar ba.....

Ata bangaren RAYYERN kuwa tun da ya riga da yabar baya da ƙurar nan bai sake bi ta kan kowa ba, duk kuwa irin media da jama'a harma da jami'an tsaron suke famar yin magana kansa, amma haka yayi shiru yayi biris komai bai ce ba, yaƙi magantuwa akan komi din kuwa dake ci gana da yawo. Badan baya da yacce zai yi ba a'a sai don kawai yana son ganin iyaka gudun ruwansu ne, ya dai manna musu bajon haukane kawai ya fisge abin sa, burin sa dama saƙon nashi ya Isa duk wuraren da yake son isar kuma Alhamdulillah duk sun gama isa da dukkan alamu, don haka yaci gaba da shimfiɗa life nasa yadda yake so. Yana zaune a washegarin ranar data kasance kwanaki biyu cif kenan da kwamushe Zayed da yayi, Zaune yake akan ƴar ƙaramar couch ɗin dake dining room din, cikin hadaddiyar shigarsa da mafi yawanci yafi amfani dasu a lokuta irin haka da suke kasance na hutu a garesa, guntun fararen Dior sweet shirt ne sanye a jikinsa, da kuma dan guntun wandon da kunyar zama dashi baya yi na trouser. Kansa sanye cikin luxury fcap ɗin da a koda yaushe baka rana kansa da ita, Cokies ne a gabansa kala da kala babu kalan da babu cikin natsuwa yake breakfast nashi da ƙayatattun dinner ɗin da Mark ya musu odar daga wani tsadadde kuma hadadden eatary luxury Chips pepper soup, sai kuma ketchup. Hankali kwance yaci gaba da yin ɗinner gefe guda kuma yana sarrafa laptop ɗin dake gabansa. Kamar koda yaushe yauma zagaye samudawamsa suke dashi tamkar wasu masu gadin gidan wuta, a kasaitance yaci gaba da dakilar laptop ɗin bayan ya kammala breakfast in da kamar 20 minute ya kunna cigarettes yana busa hayaƙin. Almost 30 minutes ya ɗauka kafin ya miƙe cikin takun nan nasa yana nufar upstairs.... Babu wani jimawa kuma zai gashi ya dawo a cikin shirin fita, yana tunkaro parlourn sanye da straight leg trim trouser, sai black Versace greco hoodie din dake kansa, ƙafafunsa sanye cikin wasu haɗaɗɗaun black hermes cover shoe, sai hannunsa dake sanye cikin wasu haɗaɗɗun safan hannu, ga kuma facemask ɗin dake saman fuskarsa dake saye cikin sun glasses ɓaki wuliƙ dashi. Kai tsaye yaransa suka mike suna fita zuwa coumpaund ɗin, wanda tuni har wannan samudawan yaran nasa sun gama masa shirin fitan dama, sun gama shirya rantsatstun baƙaƙen motocin su. Suna ganinsa suka hau fito da shewa suna faɗin "BOSS! BOSS!! BOSS!!!" Mark ne ya bude masa wata rantsatstsiyar black car, a natse ya sanya kansa cikin motar yana shige wa, Mark ya koma bangaren driving yana tashin motar sauran ukun dake bayansa na rufa masa baya. Tun da motocin nasu suka hau saman titin babu abinda kakeji sai suuuuuu suuuuuu suuuuuu shi ne kaɗai sautin dake tashi, kai tsaye suka nufi wani katafaren dakakken royal gate. Wanda ke dauke da wani shifiɗaɗɗen gini na musamman din da kai a iyaka kallonka baka isa ka ce ga yadda asalin tsarin ginin yake ba. Katafaren palace mai hawa da dama da rikitarwa kirar ginin architecture na zamani very luxurious kuma. Gaba ɗaya kusan ginin gidan na wasu manyan glass walls ne tun daga ƙasa har sama, tare da premium dark-framed glass. Ga wasu porcelain tiles a entrance da courtyard masu masifar ɗaukar hankalin da aka tsara. Daga ta babban entrance na shiga gidan kuwa ai ba'a magana, ga wani irin babban royal emblem a saman entrance din da aka masa ado dashi. Exterior lighting mai kyau da ɗaukar hankali, kai ta ko ta ina tsarin wannan ginin ya hadu very powerful an elegant and intimidating. Daga parking space na gidan kuwa wasu shegun tsadaddun motoci ne maƙare a parking space ɗin, tamkar companyn kera motocin kaco kam haka yake, kowani mota ka ɗaga idanu ka kallah sai ka sake kallah saboda tsabar tsananin kyau da tsadar motar, kallo ɗaya zaka ma dogon ginin da yafi kama da masarrafin kera motoci ƙasan cewa yes wannan wuri na musamman ne, daban a cikin daban kuma babu karya. A jere waje guda motocin nasu suka yi parking, ɗaya daga cikin manyan samudawan sane ya fito tare da buɗe masa ƙofar motar, cikin zallar izzar nan ya fito yana ƙara gyara zaman p-carp ɗin dake saman kansa, wanda lallausar sumar kansa ta fito ta ƙasar ƙeyarsa. A natse suka tunkararma shiga gidan inda nace ya Ilahi wannan gida kacokam ɗinsa saidai mu ƙirashi da aljannar duniya, ga wasu haɗaɗɗun beneye wajen hawa ashirin da wani abu. Su dukka daga nan suka dakata shi kuma ya soma tafiya cikin tsananin izzar nan zuwa ainihin cikin gidan. A lokacin da yake tsintar kansa a Floor ɗin daya kasance wani irin kayatacce, wanda ke kukan irin wata uwar dukiyar da aka narka masa, luxury polished marble tiles, huge staircase, modern curved design, glass balustrades, large artistic chandelier sophisticated design, manyan sofas da royal chairs very luxury upholstery, large indoor plants da elegant decorations kawai ne ke kuka da magana a wurin malam.

Banda wasu uwayen malls ɗin da aka musu combination na marble panels and glass, a gefe ga wani private royal floor wing nan. Wani nabban private corridor ya tunkara mai dauke da wani irin shimfiɗar lallasan royal Gras Carpet mai wani irin kyau, glass walls da panoramic view din dake jere a corridor ɗin kawai abin a tsaya a kalla ne, an tsara wajen view ɗin yana fuskantar wani tabkeken beach mai kyau da daukar hankali. Kai tsaye Mark ne yayi saurin nufar wata private elevator mai shiga kai tsaye cikin royal Deep prisoner nashi, wato inda yake killace wanda ya kwamuso. Shi kansa elevator din na musamman ne, ga wasu manyan smart doors, security system, Cctv Footage, security control hidden. Kai tsaye suna shiga cikin elevator din yai sama da su, a cikin wani babban royal parlo suka sauka, wata rantsatstsiyar ƙofa ya dosa tare da seta ƙofar da ƙwayar tsaƙiyar idanunsa a take kofar na buɗewa, sai gashi cikin wani irin azababben parlour. Baki ɗaya parlourn ɗauke yake da wasu uban lumtsuma lumtsuman kujeru wajen set huɗu, ga ta ko ina na parlourn kewaye da na'u'rorin sarrafa abubuwa, gaban wata kerarriyar ƙofar glass ya sake nufa, bayan ya shiga cikin lifter ɗin ya danna Block E Ploor 9 zuuu haka lifter ɗin tayi ƙasa dashi idanunsa Lumshe a haka har ta kawo shi parlourn, still wasu kofofin ne dai gasu nan barkatai, inda kai tsaye gaban wani ɗaki da yafi kama dana masu bada horo ya tsaya. Nan da duka tafin hannunsa yayi amfani kafin kofar ta buɗe ya sanya ƙansa cikin ɗakin, tare da ɗan yin baya da p-cap ɗin dake saman kansa yayi yana kuma hurzar da wata zazzafar iska daga cikin bakinsa. Zaune yake gabansu ƙafar nan harde ɗaya kan ɗaya. Tun da ya iso Jikin Sameer ke wata kalan rawa banda Zayed da bai san dawar garin ba, don tun da aka wullo shi ba'a kara ko bi ta kansa ba sai a yau din. Wasu madannai Mark ya danna take wata yar loka ta fito, wani abu a gongoni ya ciro tare da bude gongonin wata farar leda na bayyanuwa, wacce take ɗauke da wani farin abu liɓis yawa fulawa. Kai tsaye ya bude ledar yana isa gaban Rayyern, a kasaitance ya mike tsaye tare da amsan leda din yana nufar mutane biyun dake daddaure. Inda Sameer yake ya fara isa wanda idonsa tsabagen ja har wani haurewa sukayi, kai tsaye ya dago fuskan Sameer din, tare da kifa ledar a fuskarsa yana kama baki da hancinsa ya matse. Wani kalan zabura Sameer yayi ya fara shure shure da doka kafafu. Sai da ya masa hakan wajen zubi uku kafin ya kyale shi yana ja da baya, shi kansa zuciyarsa wata irin ƴar banzar tafasa take masa fat fat kamar ta faso cikin kirjinsa ta fito. Zayed ya nufa wanda tuni ya gane abinda ke faruwa, shima shaka masa din yayi sau biyu, kafin ya juya bayan sa wanda take Mark ya riga da yasan ko mai zai faru gaba. Wata bugaggiyar kofa ya bude wasu kattin samudawa suka bayyane, jikinsu duk zagaye da zanen tattoo na marasa hankali. Kunnuwansu tun daga farkon zagaye har zuwa karshensa a huje yake zagaye da ƙawanyu silver color. Kai tsaye wannan jiga jigan samudawan sukayi kan su, wanda idon Sameee yake cak a kansu, shi kuma Zayed da karfin ko miye ma abinda aka shaka masa ya masa ya yawa ya fara ganinsu bibbiyu. A cikin bibbiyun ya hangi kamar wannan kattin samudawan sun farma Sameer din ne. Duk yadda yaso daya bude idonsa sa kyau ya kuma dawo cikin hayyacinsa sai da ya kasa hakan.

A dai cikin wannan halin da yake ciki yake kallon yadda suke da Sameer din sai dai ko yatsar hannunsa ya gaza dagawa, kafin kamar gittawar abu yaga shima sun fado kansa. Bai san ko ainihin mai nene suke shirin masa ba, sai dai tsananin zafin azaba da masifar daya ratsa ko ina na cikin jikinsa ne ya saka shi fasa wani uban ihun da babu mai jinsa ko iya saurarensa bare a kawo masa ɗauki, yadda sukayi da Sameer din haka shima sukayi dashi wanda tashin farko sai da suka masa fata fata ganan jini sai gudu yake daga cikin jikinsa....

Babyboo....

Tana zaune gaban system nata wanda kusan kullum take zaune gabanta, sai dai yau din saɓanin abinda ta saba yi take, kallon labaran da ke yawo take kalla din, musamman wuraren da aka kafe sunan. *SAMEER KIDNAPPING CASE* da emog na abin tausayi, ɗayan kuma *WHO IS KIND DADA?* da alamar dangerous... Gefe guda kuma a gidan wata jarida sun kafe sunan..*RAYYERN KHALID- DEAD OR ALIVE?* Wani numfashi Babyboo ta sauƙe a hankali, tana ta son tuna lallai kamar ta taɓa sanin mutumin nan sai kwakwalwarta taki hasko mata da hakan, tasan bata taɓa aiki a karkashin kulawar kowacce ma'aikata ba bare tace aiki ne ya taɓa haɗa su. Kawai dai kamar a wasu lokutan ne takan ji kamar ana yawan ambatar sunan Rayyern Khalid cikin wani yanayin da ba ta manta ba. Ba ta san cikakken labarin sa ba, haka bata san ko minene ainihinsa na komawa Kind Dada ba, amma ta san cewa duk lokacin da sunan ya fito, manyan mutane kan yi shiru ne kawai. Sake kallon screen ɗin tayi tana maimaita sunan a bayyane.

"Rayyern Khalid..."

Ta furta sunan a hankali wanda taji kamar ya bugar mata da zuciya ne, kamar dai sunan na son tuna mata da wani abu ne da ta daɗe tana ƙoƙarin mantawa. Inda a kuma daidai wannan lokacin ne wayarta ta haska. Kai tsaye sabon labari ne daga media suka mata notifications, na sabon labarin daya fito. "MASU BINCIKE SUN CE BAYYANAR KIND DADA BA TA KAMATA TA ZAMA ABIN MAMAKI BA. WASU MA'ABOTA RA'AYI SUN CE TSOHON JAMI'IN DSS DIN NA IYA SAMUN DALILIN DA YA SA YA ZABI WANNAN HANYAR."

Haka Babyboo ta karanta sakon wanda ta wani jishi kamar a juye, kamar kuma ana son wasa da hankali da kwakwalwa tane. A natse ta mike tsaye tana fara zagaye babban parlorn gidan da ambatar... "Dalili..." Ta furta a bayyane saboda tuno da abinda ya faru duk da bata a wajen amma tana da ido, komai daya faru haka ta ganshi tamkar a zahiri. Wani luuu tayi da idonta kamar zata rufe ne sai kuma ta fasa da fesar da wani abu mai dumi da faɗin. "Me ya sa kowa yake tambayar dalilin da yasa ya zama haka, amma babu wanda yake tambayar me aka yi masa in banda Ajmaal?" haka kalaman suka fito daga cikin zuciyarta kai tsaye...

A gefe guda kuma tuni kafafen yaɗa labarai da social media sun ci gaba da ɗaukar zafi game da lamarin. Wasu suna kiran Rayyern Khalid babban mai laifi ne, yayinda wasu ke cewa tsohon jarumin DSS ne da aka zalumta, wasu kuma suna cewa babu wanda zai iya tabbatar da abin da ya faru da shi tun bayan bacewarsa. Inda wani gidan jarida mai suna IDON MIKIYA suka fitar da labarin cewa. _Idan Rayyern Khalid ne Kind Dada, tambaya ba wai me ya sa ya zama criminal bane... tambayar a nan ita ce me aka yi wa Rayyern Khalid? Ya koma babban criminal irin haka? And mai ya sa baya dauke kowa sai Yayan shugabanni?...._

Wannan rubutun shi ya fi komai fara yaduwa, inda wasu suka fara daukar dumi dangane da lamarin har da masu mayar da martanin cewa. _DSS ba za ta taɓa barin irin wannan mutum ya yi magana ba. Idan kuma har da gaske ne ya taɓa yi wa ƙasa aiki, bai kamata a manta da abin da ya yi mata ba..._

Gaba daya wannan abu shi ya sake rikita Abuja dama duniyar baki daya........

BY AMMEY LAYLERH ✍🏻

***

༺𝙂𝙐𝘿𝙐𝙉 𝘿𝘼 𝘽𝘼𝘽𝙐 𝙏𝙎𝙄𝙍𝘼༺

Kᴡᴀɴᴄɪʏᴀ ᴛᴀ ғɪsʜɪ

𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.