Free chapter · Read without an account

Page 27&28

by Ammey Laylerh · DUHU na DUKAN duhu

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎OCITION.

ꨄ ...Sai dai maganar nata ya makale mata a makoshi ne sakamakon dagowar da tayi da nufin fa ce majina, kai tsaye idonta ya faɗa cikin na Aliyu wanda yake tsaye daga bakin ƙofar shigowar gidan tare da Alhaji Labaran a bayansa, wanda da dukkan alamu shi ne ya masa iso har cikin gidan. Kamar an ɗaure mata numfashi haka Baba Gaje ta yi shiru tana dakatawa cak, domin tun da ta ɗago kanta idanunta suka faɗa cikin na Aliyu, sai kawai ta manta da kalmar da take shirin faɗa, yayin da shi kuma Aliyu tun shigowarsa idonsa ke kafe a kan Nadiya, yana kallon yadda take zaune cikin yanayin da ko da mutum bai san abin da ya faru da ita ba zai gane cewa akwai abinda ke damunta har ya karya mata zuciya irin haka, domin fuskarta ta rame, idanunta sun kumbura saboda yawan kukan da take yi, ga wani irin shirun da ya sake mama ye halayenta wanda ba irin shiru na wanda baya son magana ba ne, a'a, shiru ne na wanda kalmomi suka gagara samun hanyar fita saboda abin da zuciya take ɗauke da shi ya fi ƙarfin baki ya faɗa. Wani irin tausayin Nadiya ne ya kama Aliyu a wannan lokacin, tausayin da shi kansa bai yi tsammanin zai iya ji ba, har ya sa ya ɗan lumshe idanunsa yana sakin wata ajiyar zuciya mai nauyi, domin labarin yadda aka tafi da Baba Auwalu ya riske shi tun farko, kuma duk da cewa bai kasance tare da su a lokacin da aka kama shi ba, shi yasa ma ya dawo saboda ita, kuma da kansa yaje ya amsa Baban ba tare daya kuma dawo musu da Shitun ba. Wani dan sake lumshe idonsa yayi wani abu mai nauyi na kamar tokare zuciyarsa, kafin ya ɗan sunkuyar da kansa kamar mai ƙoƙarin kawar da tunanin dake neman bijiro mada, kai tsaye yana sake buɗe idonsa a kanta yana dawowa daga ɗan duniyar tunanin da ya faɗa, sake kallonta yake irin wannan kallon na wanda yake son faɗin wani abu mai yawa amma bai san ta inda zai fara ba.

“Ki shirya ki fito.”

Shi ne kalmar daya iya furtawa kawai cikin nutsuwa, wanda ya saka Nadiya ɗago da kanta tana kallonsa cikin rashin fahimta. Kafin ta samo karfin halin iya furta.

“Zan... je ina?”

“Gida.” shi ne kawai amsar daya bata a gajarce, wanda ya saka zuciyar Nadiya wani irin bugawa saboda da kalmar gidan daya amabata mata kamar kalma ce data daɗe tana jiran ji daga koma waye, don haka lokaci guda tsoro ya sake mamaye fuskarta saboda tunaninta ya koma kan Baba Auwalu ne. Ta kalli Baba Gaje, ita ma Baba Gajen ta kalleta tana rawar jiki da matse ƙafafu, kafin Aliyu ya sake cewa cikin nutsuwa, “Ki tashi ki shirya. Ba za ki zauna a nan kina ta tunanin abin da ba za ki iya canzawa ba. Abin da ya faru ya riga ya faru, amma yanzu akwai sauran abin da za a iya yi, kuma ba zai yiwu ki yi shi daga nan ba.” Nadiya ta yi shiru tana kallonsa, sannan a hankali ta miƙe, ko da yake jikinta har yanzu yana ɗauke da gajiyar kwanakin da ta shafe cikin tashin hankali. Baba Gaje kuwau ita ma ta tashi da mazarinta tana gyara hijab ɗinta kafin ta bi bayan Nadiya, yayin da Alhaji Labaran ke tsaye daga gefe har lokacin yana jiran su. Aliyu ya juya ya fita daga gidan ba tare da sake cewa komai ba bayan yayi sallama da Alh Labaran din Mijin Baba gaje, sai bayan wasu yan mintuna Nadiya da Baba Gaje suka fito, inda shi kuwa Aliyu har ya riga da ya isa wajen motar. Da kansa ya buɗe mata ƙofar gaba yana tsayawa daga gefe har ta shiga cikin motar, sannan ya rufe mata ƙofar cikin nutsuwa. Baba Gaje ta zo ta buɗe ƙofar baya ta shiga itama, kafin Aliyu ya shiga ya zauna a mazaunin driver, Alhaji Labaran kuma ya tsaya daga waje yana kallonsu kafin ya ɗan sunkuyar da kai ya yi wa Aliyu alamar sai anjima yana daga masa hannu.

A natse yake driving na motar wanda dan danan suka iso gidan, duk inda kuma motar ta gilma sai kaga idanun jama'a caaa a kansu, don duk kusan dama zaman gulma suke tu farkon da aka fara rade radin wani Soja ya dawo da Baba Auwalu gida, don haka kuma ganin Nadiya a cikin motar tare da Aliyun ne ya sake saka idanun yin ca a kansu, ita kuwa Nadiya duk wannan uban ababuwan da ake yi bata damu kota kula da kowa bama, domin duk wani tunaninta yana kan gidan da za su je ne, zuciyarta tana ta bugawa da tambayar da ta kasa samu amsar ta kai tsaye, Shin me zan tarar a gidan? Ire iren wannan tunanin shi ne fal cikin kanta, Shin za ta sake jin muryan Mahaifinta ne ko kuwa a'a?. Ko da motar ta faka a bakin ƙofar gidansu, Nadiya kam kasa ko wanne kalan motsi tayi, sai dai dago kanta da ta yi ne taka mutanen da suka zo kamar wani jaje ko ta'aziyya ne ya saka ta saurin buɗe ƙofar motar tun kafin Aliyu ya samu damar saukowa ya bude mata, kai tsaye kuwa idanunta suka kafe ƙofar gidansu kamar irin wacce din ta shekara bata gansaba, yadda take kallonsa kuwa like shi kaɗai ne abinda ta fi so a duniya, Baba Gaje ma ta fito daga baya tana gyara hijab ɗinta, yayin da Aliyu ya rufe ƙofar motar ya bi su da kallo. A hanzar ce Nadiya ta nufi ƙofar zauren gidan nasu, kai tsaye tana kutsa kanta cikin harabar gidan nasu, sai dai abin da idonta ya fara gani shi ne bishiyar mangwaro da take can gefe guda, bishiyar da a lokuta da dama take zama wurin ita da Mahaifinta a karkashin inuwar mango ɗin suna irin wannan firar nasu cikin natsuwa, sai ga shi a wannan karon tana kallon mutum ɗin da ta yi ta addu'ar farabganin fuskarsa cikin waɗannan kwanaki. Tabbas ba gizo ko cutar gane gane ce ta soma taɓa taba Baba Auwalu ne zaune a gindin bishiyar mangwaron, yana dan jingine da bishiyar kamar wanda gajiyar duniya ta sauka masa gaba ɗaya, hannayensa a kan cinyarsa idanunta masu cike da tawakkali a buɗe kamar ba makaho ba, kansa a ɗan karkace, wanda kallo ɗaya zaka masa yasa kaji kamar ya karya zuciyarka, ita kuwa Nadiya ji tayi duk wani shingen da ta kafa a zuciyarta kamar ana yaye mata koma miye “Baba...” Ta furta kalmar data fito da wani irin amo mara sauti mai tafe da alamar ganɗoki da zakuwa amma kuma muryan babu karsashi a cikinta. Sai ma da wani irin wani ɗaci da raɗaɗin data fito, kafin ƙafafunta su daina sauraron umarnin jikinta, ta ruga da gudu zuwa gare shi.

“Baba!”

Ta sake furta sunan kamar me tsoron wani ya kwace mata shi, hawaye kwance cikin idanunta suna fitowa su tarwatse mata a fuska, Baba Auwalu ya ɗago kansa cikin sauri yana neman gane inda muryar ke fitowa, kafin ya ji ta faɗa jikinsa tana rungumarsa da dukkan ƙarfin da ya rage mata. Shi ma ya miƙa hannuwansa yana neman inda kanta yake, yana kankameta a cikin jikinsa ya matse ta a kirjinsa, zuciyarsa na cika da wani irin yanayin da shi kansa bai san yadda zai iya bayyana shi ko misalta shi ba. “Nadiya...” Haka ya kira sunanta cikin murya mai ɗauke da gajiyar kwanakin daya kwashe ba tare daji daga gare taba, ƙara ƙanƙame shi sosai tayi tana tsananta kukanta, domin a wannan lokacin babu wata kalmar da za ta iya maye gurbin abin da rungumar uba da ɗiya suka kasance. Baba Gaje kuwa dake tsaye daga gefe hawaye kawai take sharcewa da suka cika idanunta, yayin da Aliyu kuwa ya tsaya nesa kaɗan yana kallon su, ba tare da ya katse wannan irin tsadadden lokacin nasu ba, domin akwai wasu ababuwan da baya kamata mutum ya katse su da kalmomi, ya kamata a bar zuciya ta faɗi abin da baki ba zai iya faɗar su ba.

A wannan rana Nadiya ta fahimci cewa wani lokacin mutum kan yi tunanin an ƙwace masa komai ne, alhali ALLAH yana barin masa abin da ya fi duk abin da yake tsoron rasawa, domin ita da a nata tunanin tayi tunanin kwanakin sun zo mata ne da nufin su karya ta baki daya, amma da ta ga mahaifinta a ƙarƙashin bishiyar mangwaron da suka saba zama, sai ta fahimci cewa har yanzu akwai abin da za a iya karewa, akwai abin da za a iya gyarawa, kuma akwai dalilin da ya sa zuciyarta ta ƙi mutuwa duk da irin abinda aka mata ta ƙarfin tsiya.

*RAYYERN*

A ta bangaren Rayyern kuwa ya sake tashi ne a cikin wani irin yanayi da ya fi na farko fin birkita kai amma kuma yana jurema hakan. Yana zauna daga gefen gadonsa daga shi sai farin dogon wando a jikinsa na barci, cike da wani irin yanayi yake kallon hannunsa, kafin ya ɗaga kansa ya kalli table din da ke gabansa wanda sune makare da kayan maye. Kafin a natse ya kai hannunsa ya ɗauki cigarettes din da ke gefen Red wine nashi, ya kunna ta a hankali, yana jan hayaƙin farko cikin zurfin kirjinsa kafin ya fitar da shi yana kallon yadda hayaƙin yake watsewa a gaban fuskarsa. "Shiru na ba yana nufin sunci bagas bane!..." Tsam daga haka ya miƙe a hankali, ya ɗauki wayarsa, yana fara tafiya yana duba wani saƙon da aka aiko masa, wanda kai tsaye idanunsa suka tsaya cak a kan sunan da ya bayyana a saman screen din. AJMAAL. Ya ɗan kalli sunan na wasu daƙiƙu yana ci gaba da tafiya....

Ajmaal kuwa a wannan lokacin yana can a cikin ɗakinsa, file ɗin da ya samo har yanzu a gabansa, amma abin da ya fi ɗaukar hankalinsa yanzu ba takardun da ke cikinsa ba ne, sai wata ƙaramar alamar da ta bayyana a ƙarshen wani tsohon shafi. Yana ci gaba da kallar file ɗin da aka rufe yana ɗauke da wata alama da aka yi amfani da ita bayan an bayyana Operation Black Veil a matsayin gazawa, kuma wanda ya sanya wannan alamar ba wani ba ne face wanda yake da cikakken damar shiga bayanan da suka fi zurfi fiye da nasa. Ya ɗan ɗaga kai yana kallon bango, kafin hoton Rayyern ya dawo masa a zuciya, yadda ya koya masa dabarun da ya sani, yadda ya ceci rayuwarsa sau babu adadi, yadda yake kiran sa da Ajmaal a lokacin da kowa yake kiransa da sunan aiki, da kuma yadda yanzu yake shirin farautar mutumin da ya taɓa ɗauka a matsayin abin koyinsa. “Idan kai ne ka ɓoye min gaskiyar wannan lamari dole ne in gano dalilin da ya sa ka ɓoye min, ko da kuwa ƙarshen wannan binciken zai kai ni ga rasa raina.” Ya rufe file ɗin, ya ɗauki wayarsa, amma kafin ya kira kowa sai wani sabon tunani ya faɗo masa. Ya kamata ya fara daga inda aka fara karya Operation Black Veil, domin wani abu ya faru a can, kuma idan ya samu asalin abin da ya faru, watakila zai samu amsar dalilin da ya sa Rayyern ya zama mutumin da yake yanzu wato uban daba.

Babyboo kuwa ita kanta ta san cewa tayi busy ba kaɗan ba tabbas, duk yadda taso ɓatar da tunanin wannan mai laifin amma hankalinta ya ƙi samun nutsuwar hakan. Ko a yanzun ma zaune take wasu files shimfiɗa a gabanta, tsadaddar wayarta na gefe kusa da kwamfutan dake gabanta tana nuna wani bayanin da ta kwashe lokaci tana ƙoƙarin warwarewa. Tun lokacin da ta fara binciken Rayyern, akwai wani abu da yake ta damunta, duk inda ta yi ƙoƙarin bin sawunsa, sai ta ga kamar an riga an share sawun kafin ta isa, kuma duk inda ta yi ƙoƙarin gano inda aka fara, sai ta samu wata sabuwar ƙofa da ke buƙatar wani matakin izini. Ta ɗan jingina da kujerar da tane kai, tare da wani kalan lumshe idanunta tana tunanin duk abin da ya faru tun bayan sace Sameer, sai sunan Rayyern Khalid ya sake bayyana a cikin tunaninta kamar wata inuwa da ba ta son barin ta. “Me ya sa duk abin yake komawa gareka?” ta tambaya a hankali, kafin ta buɗe idanunta ta kalli allon kwamfutar. A daidai wannan lokacin wata sabuwar sanarwa ta bayyana, ba daga tsarin da take amfani da shi ba, sai daga wata tsohuwar hanya da ba ta kamata ta sake aiki ba. Babyboo ta zauna da kyau, idanunta suka tsananta kan allon, kafin ta fara duba bayanin. Abin da ta gani ya sa ta kasa motsi na wasu daƙiƙu, domin tsarin ya nuna cewa wani mutum ne ya yi ƙoƙarin shiga wani ɓangare na bayanan da suka shafi Sameer, amma abin da ya fi ɗaukar hankalinta shi ne wurin da aka yi ƙoƙarin shiga daga gare shi, wanda ya sakata sake dubawa da kyau sannan ta tuna da abin da ta riga ta gano, da kuma yadda Rayyern ya kasance yana aika mutane su bi sawu na ƙarya. Ta ɗan yi shiru, kafin ta sauke wayar a hankali, tana fara tambayar kanta ko ita ce take bin sirrin Rayyern, ko kuwa tun farkon lokacin da ta fara bincikensa, wani ne ya riga ya shirya mata hanyar da za ta bi don isa gare shi?...

A hankali kwanaki biyar suka shuɗe tun daga ranar da komai ya sake ɗaukar wani sabon salo a tsakanin mutanen da labarin ya riga ya raba su zuwa wani ɓangarori daban-daban, kwanaki biyar din da suka isa su sa abubuwa su yi kamar sun lafa, amma ba su isa su goge abin da ya riga ya zauna a cikin zuciyar mutum ba sakamakon ababuwan da suka faru. Kamar yadda a cikin jerin waɗannan kwanaki biyar din kuwa, Rayyern Khalid ya koma yaci gaba gudanar da rayuwarsa kamar yadda ya saba, kamar dai babu wani dare da jikinsa ya taɓa ƙin ɗaukar umarninsa, kamar dai babu wata magana da ta taɓa tsaga zuciyarsa har ta kai shi ga rasa iko da kansa, kamar dai sunan da ya taɓa jefa shi cikin wani irin yanayin da ba kowa ne ya taɓa gani ba bai taɓa wanzuwa a bakinsa ba. Ya koma hasalin irin Rayyern ɗin da duniya ta saba gani, wanda idan akwai wanda bai san abin da ya faru da shi kwanakin nan ba, da ba zai taɓa zaton cewa wannan mutumin ne wanda ya kwana yana yaƙar kansa da abubuwan da babu wanda ya san ya kalan zurfinsu yake ba. Sai dai abinda mutane ba su sani ba shi ne, wasu lokutan mutum ba ya warkewa daga ciwo gaba ɗaya, kawai dai yana iyaka bakin ƙoƙarin sane wajen koyon yadda zai sa ciwon ya zauna a inda babu wanda zai iya sake ganinsa. Don haka kai tsaye ya koma bakin aikinsa yana ci gaba da gudanar da harkokinsa kamar yadda yake so, ba tare daya bari kowa ya karanta abin da yake cikin idanunsa ba bare kuma zuciyarsa. Har Tiger da Mark da suka san shi fiye da sauran mutanen da ke kusa da shi, ba su sami damar gano abin da yake cikin ran saba. Don tun daga ranar da aka kwantar da shi bayan halin da allurar nan ta jefa shi ciki, bai sake bari wani daga cikin mutanen da ke kewaye da shi ya ga wani irin rauni a tattare dashi ba, ya binne komai a inda ba za su iya taɓa gani ba.

Yana yin magana da Mark idan akwai abin da ya kamata su tattauna, yana ba Tiger umarni cikin murya ɗaya tak wadda ba ta ɗauke da wata alamar abin da ya faru a baya cikinta, har ma da waɗanda suke kusa da shi sun fara yarda cewa abin da ya faru a kwanakin baya ya wuce, domin Rayyern bai sake basu damar ganin ko da ƙaramin gibi bane a cikin abinda ya faru. Amma abin da babu wanda ya sani shi ne, Rayyern bai manta ba komai, kawai ya koyi yadda zai binne abin da bai shirya bari kowa ya gani ba ne. Cikin yammacin ranar Lahadi ya shirya fita kamar yadda ya saba, duk ranar Lahadin duniya outing yake fita yayi ta zaga wurare. A natse ya fito cikin shiga ta alfarma zuwa compound na gidan, inda kai tsaye samudawansa har sun riga da sun shirya motocin da zai fita dasu, kai tsaye yana shiga cikin motar suka yi reverse suna cilla kawunansu zuwa saman titi domin fita zaga garin daya saba. Wani babban wurin da ya saba zuwa lokaci zuwa lokaci suka nufa kai tsaye, wani katafaren Mall din irin hasalin luxury din nan na alfarma, wanda mutane ke cike da wurin tun daga wajen shiga har zuwa cikin manyan shagunan da ke ciki. Ba don yana buƙatar wani abu na musamman ba ya zo ba, domin Rayyern ba mutum ne da zai fito saboda kawai yana son ya kashe lokaci ba, hakan ya zama kamar dole ne don fitar nashi da abubuwan da yake zuwa ya duba da kansa, wasu wuraren da ya saba ziyarta, wasu mutane da ya saba gani, kuma wannan ya sa Ajmaal, wanda ya kwashe kwanaki yana bin sawunsa daga nesa ba tare da ya bari ya fahimci cewa yana binsa ba, ya samu abin da yake nema. Ajmaal ya fahimci cewa Rayyern yana da wasu abubuwan da bai taɓa canzawa ba, kamar yadda yake da wasu abubuwan da ya daina yi tun bayan da duniya ta ɗauka ya mutu. Ya lura da lokacin da yake fita, wuraren da yake fin zuwa, da irin yadda yake ɗaukar lokaci kafin ya bar wani wurin, har a ƙarshe ya gane cewa wannan mall ɗin shi ne inda Rayyern yafi zuwa akai akai kamar yadda yau ma ya zo Mall ɗin. Tun da Manyan motocin Rayyern suka faka idanuwan Ajmaal suke a kansu yana tsaye daga ɗan nesa yana kallon su, har zuwa lokacin da Boss din ya fito cikin wannan ɗan banzar izza da tafiyar nashi. Yayin da Rayyern ke tafiya cikin mutane ba tare da wani gaggawa ba, hannunsa ɗaya cikin aljihun wandon jikinsa fuskar nan babu wata alama ta tsoro ko fargaba tattare da ita, yayinda idon nasa ke rufe cikin baƙin shade yana ci gaba da tafiyarsa a natse. Ajmaal tun farkon sauƙe idonsa akan Uban gidan nasa kuwa ya ji zuciyarsa ta motsa da wani abu, kafin ya fara jin bugawar zuciya da wani irin ƙarfi, ba wai don saboda ya tsorata da ganin Rayyern din ba ne, a'a saboda shi ne mutumin da ya taɓa koyar da shi yadda ake fuskantar abin da ke tayar da hankali ba tare da mutum ya bari abin ya gagareshi ba, amma saboda duk lokacin da yake kallon wannan mutumin, wani ɓangare na zuciyarsa kan motsa masa da kuma tunasar da shi cewa wanda yake shirin fuskanta ba wani ba kowa bane illa malaminsa, mutumin da ya taɓa ɗauka a matsayin wanda ba zai taɓa zama abokin gabar sa ba. Tun yana kan wasu yan ƙananun matakai a hankali, har zuwa lokacin da ya soma kusantar Rayyern acan baya. Shi kuwa Rayyern a cikin jikinsa yake jin yadda aka kafe shi da kallo, kallon da yake jinsa a jikinsa don kallo ne irin wanda yayi kewa sosai, yadda idanunsa suka kafe a kansa da kuma irin wannan shirun da ka iya kassara rayuwar mutum. Shi kuwa Ajmaal jin kallon yake kamar yana wanke masa zuciya ne na kallon malamin nasa bayan shekaru kusan huɗu, a wata irin natse Rayyern ya ci gaba da tafiya har sai da ya isa kusa da wata ƙofar gilashin da ke shiga wani ɓangare na mall ɗin, sannan ya tsaya ya juya yana kallon Ajmaal wanda shi ma ya tsaya ɗan nesa dashi kaɗan daga ta bayansa, duk da cewar yanda jikin Rayyern ke son fin karfinsa na son tilas tama kansa kallon Ajmaal amma sai da ya shanye hakan, yaki tsayawa sai ma takun da yaci gaba dayi, shan gabansa Ajmaal din yayi tare wanda ya saka Rayyern dakatawa cak dole, samudawansa suka yi yunkurin far masa yana dakatar dasu ta hanyar daga musu hannu alamar su bar shi... Ya juya a hankali kai tsaye idonsa na sauka kan Ajmaal,wani irin shiru na ratsa tsakanin su, irin shirun nan mai ɗauke da tarin abubuwa da yawa fiye da abin da baki ba zai iya faɗa ba. A kaikace Rayyern ya masa wani kallo ta cikin black shade din daya toshe fuskarsa dashi.. Ajmaal ya ɗan matso kusa, yana kallon fuskarsa kamar yana neman wata alama ta tsohon Rayyern din sa da ya sani a baya, amma abin da ya gani shi ne wannan dai rasa gane inda ya dosa ne, rasa gane gaba bare bayansa wanda ya saba gani a lokacin da yake koyar da shi, wannan rashin bama kowacce iriyar kofa damar gane inda ya saka gabansa bare mutum ya gane abin da ke gudana a cikin zuciyarsa. wanda a wannan karon ya riga ya fara jin wani irin motsin da bai saba ji ba a jikinsa, domin duk da cewa Ajmaal bai faɗi komai ba, amma yanayin yadda idanunsa suke kafe a kansa da kuma irin wannan kallon ya isa ya sanar da Rayyern cewa wannan ba gaisuwar tsohon ɗalibi ba ce da ya zo domin yi wa malaminsa bayan shekaru kusan huɗu, a'a, wannan zuwan yana ɗauke da wani abu ne mai nauyi a bayan hakan....

"Why!? Who? Me yasa? Mai yasa zaka yi haka Sir an.... " Wani daga masa hannu Rayyern yayi da masa alamar zipping bakinsa, yana soma wata irin tafiya a gabansa kafin ya fesar da wata zazzafar numfashi. “Akwai wasu abubuwan da dolen dole mutum yake koyar yadda ake iya sarrafasu bata cikin fushi irin haka ba right and understand?... " Wani irin abu ne ya sauya a cikin fuskar Ajmaal, Hannunsa ya motsa cikin gaggawa da nufin daukar bindigar dake jikinsa ganin Rayyern har ya soma yunkurin ci gaba da tafiyarsa, aikuwa tun kafin Rayyern ya samu damar karantar abin da yake shirin yi, Ajmaal ya yi yunƙurin fitar da makamin da yake ɗauke da shi. Yayinda da Ajmaal da Rayyern suka tsaya suna kallon juna cikin wani irin yayi. Kafin cikin wani irin ɗan iskan taku Rayyern ya isa ga Ajmaal yana kama hannunsa ya sauke shi kasa mai bindigar, ba tare da shi yayi yunkurin masa wani abun da zai cutar da shi ba. Sai dai ya matse shi ne sosai ta yadda har sai da Ajmaal ya kasa sake yin yunƙurin komai, sai ma sunkuyar da kansa kawai dadi. A wata irin natse da kamewa mai tafe da class Rayyern ya ɗan rankwafo kansa zuwa ga Ajmaal don ya fishi tsayi da cikar zati nesa ba kusa ba, cikin wannan bugaggen sautin mai tafe da kamar bada umarni wacce Ajmaal yayi missing ji Rayyern ya furta.

“Wannan shi ne abin da ka koya daga gare ni?”

Cikin wani irin deep sound ɗin daya saka Ajmaal kallonsa da idanun da suka cika da wani irin zafi a zafe ya bashi amsa da...

“Kai ne ka koya min kada in bari tsoro ya hana ni yin abin da ya dace.”

“Ban koya maka ka kashe wanda ka taɓa kira malaminka ba.”

“Ni ma ban zo nan domin in kashe ka ba.”

Rayyern ya ɗan sake shi kaɗan, amma idonsa bai bar kan fuskarsa ba, kamar yadda wani kalan lalataccen murmushin daya saki bai bar kan fuskar sa ba. "Really?" Ya fadi yana wani ɗan jujjuya idanunsa kafin ya sake tsinkayar muryan Ajmaal cikin kaushi yana mai sake furta... "Me yasa ka tashi daga hasalin suna RAYYERN KHALID ka koma a matsayin *KIND DADA?*..." Wani ja da baya Rayyern yayi da ɗan karkada masa yatsun hannunsa biyu da faɗin. "DUNIYA!...." Rayyern din yay maganan yana cilla hannayensa cike da wani kalan kill smile a face nashi. "Na rantse saina kamaka! Na kuma yima maka alkawarin saina gurfanar da kai akan gwiwwowinka". Yay maganar a zafen daya saka shi sakin wani shegen murmushi Rayyern ya sake saki irin na shegun nan tare da tafa hannuwansa da sake kallon Ajmaal... "Ka sani ba wai nazo kamaka bane a matsayin RAYYERN KHALID, nazo ne domin kama KIND DADA"... Ajmaal ya fadi muryarsa ba ta ɗauke da kowacce irin girmamawar da ta kasance a garesu a baya, sai dai ma wani irin nauyin da ya nuna cewa ya riga ya yanke shawarar abin da ya zo yi ne kai tsaye wato kama KIND DADA.

Wani ɗan dage girarsa ɗaya Rayyern yayi yana kallon Ajmaal cikin natsuwar da ta fi komai tayar da hankalin magautansa ko a da can baya

"Ka ce?....."

RAYYERN ya furta alamar yana son Ajmaal ya sake maimaita masa abinda yace din. Cike da jin kwarin gwiwwar nan nashi da itama ya koya ne kai tsaye daga Rayyern din Ajmaal ya yi taku ɗaya zuwa gare shi. "Na zo ne domin in kama KIND DADA" Wani dan karkatar da kansa gefe Rayyern yayi cikin nuna ko in kular nan nasa dake kashe mutan da takaicin hakan yace.

"Kama KIND DADA really? Kuma zaka iya? Akan me bisa wane dalili?"

Ajmaal ya matse haƙoransa idanunsa na ɗan cika da wani irin zafi.

“Saboda mutanen da suke mutuwa ata sanadiyyarka!.” Ya furta kalaman da suka saka zuciyar Rayyern wani kalan dakatawa cak da aiki yana gaza ko wanne kalan motsi sai ma kafe Ajmaal din da yayi da ido, bai kuma daga dawo daga cikin mutuwar tsayen da yayi ba ya sake tsinkayar muryan Ajmaal din a zafe naci gaba da faɗin.

“Saboda waɗanda aka kashe! saboda waɗanda aka sace, saboda duk wani abu da yake faruwa a cikin wannan ƙasa wanda yake komawa ga sunanka ko kuma hannunka yana ciki.”

A hankali Rayyern ya zare baƙin shade ɗin daya toshe idanunsa dashi, ya na riƙe shi a hannunsa yana kallon Ajmaal kai tsaye. “Really?”

“Na tabbata da abin da na sani.”

“Abin da ka sani ba koyaushe yake iya zama gaskiyar abin da ya faru ba.”

“Shi ya sa na zo da niyyar tabbatarwar.”

A wannan karon kam wata murmushi mara daɗi Rayyern ya saki, tare da crossing hannunsa a saman shoulder nashi. “To ka tabbatar din na gani” Wani numfashi mai zafe Ajmaal ya fesar tare da furta. "Don me ya saka zaka koma Mutumin da mutane suke ambatar sunansa cike da tsoro? Don me ya saka zaka zama mutumin da duk inda aka ambaci wasu manyan laifukan daya danganci kashe-kashe ko ɓacewar mutane sai sunanka ya fito a gefe? Don me ya sa zaka kasance Mutumin da duniya ke tsoro fiye da komai?... " Bai bama Rayyern damar furta ko wacce kalma ba a karo na biyu yana sake zaro bindigar dake ɓoye a jikinsa yana arresting na Rayyern kai tsaye ba tare da wani jinkiri ba. Nan take hayaniyar da ke wajen ta rikice, wasu daga cikin mutanen da suke kusa suka ja da baya cikin firgici, wasu suka fara gudu, wasu kuma daga cikinsu masu dakakkiyar zuciya suka tsaya cak suna kallon abin da ke shirin faruwa, kamar kiftawar ido haka Rayyern ya komar da bindigar saman goshin Ajmaal tare da ɗan matsa kusa dashi sosai ya na kallon shi da wani irin kallo mai ɗauke da tsananin rashin yarda.

“Ka duba ka gani.”

Ajmaal ya kalle shi cikin fushi wanda ya saka Rayyern ya ɗan dage kafadarsa ɗaya cikin wannan irin salon nasa na raini mai kumar da kutane, kamar yana gaya masa cewa right ɗinka ne kayi harbin cikin dandazon taron mutanen nan ruwanka ne, kafin kamar wanda ke amfani da wani magic Ajmaal ya sake jin furucin uban gidan nasa, don bai ga sanda ya bude bakin saba kawai sai saukar kalaman sa yayi “Idan kana ganin kai ne mai gaskiyar, yi abin da zaka iya yi” Kafe shi da ido kawai Ajmaal yayi yana kallar ashe dai komai ma uban gidan nasa na nan sai ma wasu ci gaban da aka sake samu cikin sabbin halayensa, tare da kallon gefe da gefensa, sai ya ga jama'a sun sake cika wurin fiye da farko. Saukar gun din Rayyern yayi yana jefama Ajmaal din da furta.

“Me kake jira? Bayan kuma ka ce ka zo ne domin kama Kind Dada.”

Ajmaal ya matse bindigar dake hannunsa wacce ya amsa wanda shirun da Ajmaal din yayi ne ya saka Rayyern ɗan murmusa dole. “Ka ga kenan har yanzun akwai bambanci tsakanin abin da ka zo yi da abin da kuma zuciyarka ke umartaka da aikatawa ba?.... Cike da wani kalan zafi Ajmaal ya kalle shi da tare da furta . “Kada ka yi tunanin na ji tsoronka.” Wani kalan jan idonsa baya luuuu Rayyern yayi kamar zai lumshe amma kuma bai lumshe ɗin ba.

“Ban ce ka ji tsoron ba dama” Juyawa Ajmaal yayi yana kallar jama'ar da ke kewaye da su, sannan ya sake kallon Rayyern, kafin daga ƙarshe ya sauke hannunsa gaba ɗaya. Ba don ya daina zargin sa ba, ba don ya yafe masa ba, amma saboda ya fahimci cewa wannan ba wurin da zai iya yin abin da ya zo yi ba tare da ya jefa rayukan mutanen da ba su san komai ba ne cikin haɗari duba da yadda yaran Rayyern din ke kewaye da wurin. Wani dan kallonsa Rayyern yayi tare da gyara gefen rigarsa cikin natsuwa kamar babu abin da ke faruwa. Yana mayar da shade ɗin sa saman idonsa, ya juya zuwa ga ƙofar wata glass ɗin da ke gabansa tun kan ya isa yaransa suka buɗe masa yana wucewa suna mara masa baya. Kafin Rayyern ya tsaya a cikin ƙofar, ya ɗan juya kansa ya kalli Ajmaal sau ɗaya kawai, wannan kallon na mutumin da yake da abubuwa da yawa da zai iya faɗa amma ya zaɓi ya bar su a cikin zuciyarsa. Shi ma har zuwa lokacin Ajmaal bai ce komai ba haka har ya juya yaci gaba da nufar ƙofar daya nufa. Ajmaal ya tsaya yana ci gaba da bin Rayyern da idonsa yana kallon yadda yake tafiya zuwa cikin elevator ɗin da ke can gaba, har zuwa lokacin da ƙofar elevator ɗin ta buɗe, Rayyern ya shiga, ya juya ya tsaya yana fuskantar waje. A wannan karon idanuwansu suka sake haɗuwa ta cikin gilashin, kuma babu wanda ya kawar da nasa. Ajmaal ya tsaya cak, yayin da Rayyern ya ɗan ɗaga kansa kaɗan, kamar gaisuwar ƙarshe tsakanin mutane biyu da suka taɓa zama abu ɗaya kafin rayuwa ta raba su. Daga karshe ƙofar elevator ɗin ta fara rufewa a hankali kuma har zuwa lokacin suna kallon juna, har sai da gilashin ya rufe fuskar Rayyern gaba ɗaya, daga nan sai elevator ɗin ya tashi ya ɓace daga idanun Ajmaal. Wani kalan dukan kansa Ajmaal yayi tare da sauke numfashi mai nauyi ya rufe idanunsa na ɗan lokaci. Ya zo nan da niyyar kama KIND DADA, amma ya tafi da wani irin nauyi da ya fi abin da ya zo da shi. Domin a cikin waɗannan ƴan mintuna kaɗan, ya sake ganin wani ɓangare na tsohon malaminsa da ya daɗe yana ƙoƙarin kashewa a cikin zuciyarsa, kuma abin da ya fi tayar masa da hankali shi ne, har yanzu wani ɓangare na zuciyarsa yana ƙin yarda cewa Rayyern ɗin da ya sani ya zama Kind Dada ɗin da ake tsoro a yau.

Few minutes

Tun da Rayyern ya komo gida yake zube a tsararren parlournsa, ya cire agogon hannunsa ya ajiye shi a kan teburin parlour, baka jin motsin komai a parlourn sai na hayaƙin da yake busawa ya karama sama hazo. Wanda tuni hayakin har ya fara cika sararin da ke gabansa a hankali yayin da yake kallon wani wuri daban ba tare da bari abinda ya faru sun sake dawo masa ba, sai dai duk a banza don maganganun Ajmaal ne kawai ke dawoma Rayyern cikin kansa, kalmomin na wani kalan yankar zuciyarsa, amma bai bari fuskarsa ta nuna komai ba. Sai ma hayaƙin daya sake shaƙa na cigarettes ɗin sosai sannan ya fitar da shi a hankali, yana ƙoƙarin kwantar da zuciyarsa amma hakan na neman gagaransa. Tsam haka ya mike a wurin yana soma tafiya zuwa ga bedroom nashi, kai tsaye yana ya fara zame rigar dake jikinsa ba tare daya zame dogon wandon dake jikinsa ba ya nufa ƙofar bathroom yana wuce, kai tsaye shower ya sakarma kansa yana tsayawa ƙarƙashin ruwan dake dukan jiki da kuma kansa. 'Saboda mutanen da suke mutuwa ata sanadiyyarka' haka yaji kalaman Ajmaal sun dawo masa kamar tsawa. Wani dafe hannunsa yayi a jikin glas din dake gabansa yana bama ruwan damar dakar tsakiyar bayansa da kuma kuma kansa da kyau.

'Saboda waɗanda aka kashe! saboda waɗanda aka sace, saboda duk wani abu da yake faruwa a cikin wannan ƙasa wanda yake komawa ga sunanka ko kuma hannunk.... Wani irin saurin buɗe idonsa Rayyern wanda kai tsaye ruwan dake dukan jikinsa suka cika idonsa ɗaya bude a hagunce. Sosai yayi ƙoƙarin kawar da maganar, amma sai sake dawowa cikin kansa yake. Wani kalan buɗe baki yayi da nufin kwala ihu yana wata kalan bankarewa da toshe kunnuwansa duka biyun da hannayensa, amma wannan muryan mai sanyi, mai cike da nutsuwa ta musamman yaji kamar ta gitta ta cikin tsakiyar kansa. "Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir³ Rabbi inni magalubun fantasir³! Wa la haula wala quwwati illa billahil aliyal azeem³, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³....." haka yaji muryan ta wani kalan daki zuciyarsa, muryan nan da ita kaɗai ce ke sanin yadda za ta rage masa zafin fushi kafin ya zama bala'i a gare shi. 'MAIRAH' zuciyarsa ta ambaci sunan da bai taɓa iya binne shi gaba ɗaya daga cikin kansa ba yana tasowa daga cikin duhun tunaninsa... “Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir... Ita kawai ya furtawa yana matse hannunsa da ƙarfi. Yanayin bugun numfashinsa na sauyawa, wani sake shigewa karkashin shower din yayi da nufin dukan ruwan zai saka ya gigice har ya manta komai amma maimakon ya samu nutsuwa sai wani irin zafin da yake jin yana dada mamaye gangar jikinsa. Da kyar ya iya buɗe idonsa dake cike da ruwa ya kalli madubin da ke gabansa, sai ya ga kansa a ciki, fuskar da ta saba zama kamar dutse, amma a wannan karon akwai wani abu a idanunsa da shi kansa bai so gani. A cikin wani irin yanayi na zafin ran da ya kasa iya sarrafawa, ya saka hannunsa yana fasa mirrorn da ke gabansa da ƙarfi, kai tsaye mirrorn na watsewa a ƙasa hannunsa na soma fitar da jini. Tsai kawai yay a wurin har zuwa lokacin shower din na dukan jikinsa yana kallon hannunsa dake digar da jini, kafin ya ɗaga idonsa zuwa ga ragowar madubin daya rage. A cikin ɗaya daga cikin gutsattsarin da bai faɗi ba, ya sake ganin fuskarsa. Amma wannan karon bai ga Rayyern Khalid ɗin da duniya ta sani ba, ya ga mutumin da ya daɗe yana gudu daga abin da yake cikin kansa ne kawai...

Ya wani lumshe idanunsa yana juyawa yana juyawa daga madubin ya bar wurin....

BY AMMEY LAYLERH ✍🏻

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.