Free chapter · Read without an account
BOOK ONE CHAPTER NINE
*ZAINAB*
Washe gari haka ta tashi suku-ku jikinta duk babu ƙwari. Ga idanuwanta da suka kumbura saboda kuka.
Aikam yaran na ganin ta suka dinga tambayan ta mai yasameta tace dasu babu komai kawai wani abune yafaɗa mata a'ido.
Ramlat da Anis da basu da wayau sun yarda. Amma Khalid da Khadija jinta kawai sukeyi zuciyoyinsu na raya musu wani abu dai Abbansu yai mata.
Tana sallaman yaran suka tafi makaranta itama ta ƙara shirya wa.
Ta fito tanufi bakin titi don hawa adai-dai ta zuwa gidan Yaya Yusha'u.
Tun jiya data dirji kukanta ta more ta yanke hukuncin kaisa ƙara wurin magabatan sa duk da iyayen sa sun rasu amma yanada ƴan uwa maza manya da suke gaba dashi.
Sedai zuciyar ta dokawa take yi. Tana jin kamar ta koma ta haɗiye damuwar gidanta. Ta rufa ma kanta asiri.
Tun fari Ahmed ba mutum bane mai son ana jelangiyar kaisa ƙara.
Ya kan ce"Ni fa natsani naga mutum da girmansa an tutsiye shi ana mai magan ganu akan iyalinsa. Wasu lokutan harda zagi da cin mutunci.
Ni dai Baby duk abinda zan miki. Ki hakuri, kizama *ƘYAURE KARIYAR GIDANA* musulhunta komai a tsakanin mu"
Ƙwalla ne suka ciko idanunta. Da zata iya data biyema wani tsagin dake ceda ita ta koma ta rufe asirin gidan ta amma abinda Ahmed ya ɗauko wannan karon mai girma ne da batada wuyar dauka ita kaɗai.
Ta lumshe idanunta wasu lafiyayyun hawaye masu zafi da ciwo suka zubo mata.
Ta daure ta riƙe kukan dake taso mata. Suna isowa gidan ta sauko ta bama mai adai daita kuɗinsa ta shiga gidan da sallaman ta.
Gidan shiru yake yara duk sun tafi makaranta. Ɗakin kishiyar ta ma arufe yake ta tafi wurin aiki. Malama ce a makarantar primary dama can Yaya Yusha'u da aikinta ya aurota, ita dai Aunty Saude ce cima zaune babu sana'a babu aiki.
Seda tazo ƙofar kicin na tsakar gida ta kuma sallama aka amsa.
Aunty Saude ta leƙo da fara'ar ta dake kwance a fuskar ta kodayaushe.
"Maraba da uwar gidan Ahmadu...yau kece a gidan. Sannu da zuwa."
"Yawwa Aunty. Ya gida. Ya yayara."
"Lafiya ƙalau. Yaran ma duk suna makaranta."
Tai maganar tana mata jagora zuwa cikin dakin ta dayake ashare fess dashi sai ƙamshi yake yi.
Zainab ta zauna. Yayin da Aunty Saude ta nufi fridge tana cewa:
"Yasu Ahmadun suka koma gida? Shekaran jiya suka zo shida amaryar tasa na mayi zaton ganinku atare sena tina shuwagabannin namu idan suka ƙara aure rawan kaine dasu. Uwar gida tazama tsohon yayi."
Ta dasa aya tana ajiye ma Zainab ruwa a plate da zoɓo.
Godiya kawai tai mata batareda tayi tinanin kai wani abu cikin ta dake cunkushe da damuwa ba.
Zuciyarta nata kai komo akan ta inda zata fara taji muryan Aunty Saude tana cewa:
"Zainab lafiya kuwa? Na ganki sukuku dake kodai Ahmadun ne yai miki wani abu?!"
Wani kakkaurar yawu ta haɗiye. Murya a dakushe ta furta"Eh Aunty"
"Inna lillahi wainna ilaihirra jiun! Wai meyasa maza basu da adalcine arayuwa? Yaransu da manyansu babu gwamma? Mutum yana zaune da matarsa sai kawai yaƙara aure babu gaira babu dalili.
Ji dai figaggiyar matar daya ɗauko kamar an ɗaura ma muciya zani. ƙirji aƙeƙashe babu komai tsakani da Allah, shiyasa idan za'a ƙara miki abokiyar zama sai kin ƙara da addu'a da shiyasa da muka zo yinin bikin naso nai miki magana akan addu'ar amma sanin halinku na yaran yanzu senai shiru da bakina."
"A'a Aunty da kin gayamin dan ayanzu ina cikin matsananciyar buƙatar ta"
Aunty Saude tagyara zamanta ta fuskance ta da kyau.
"Ai kinyi kyan kai. kuwwa ya iya allonsa ya wanke. In baki zama ta ɗaya awurin mijiba tom karki zama ta biyu. akwai wani malami da zan kaiki zai miki duk abinda yadace, ga ladan addu'oinsa babu tsada."
Jikin Zainab ya ɗan saki jin kalaman Aunty Saude na ƙarshe. Ita ta ɗauka addu'oine na Allah da Manzonsa zata bata ta runguma taje tai tayi duk da ba gwana bace ita ta wannan fannin to amma zuwa wurin wani malami abune da take tsoro harga Allah kada aje arabata da imaninta.
"Uhm-Uhm Aunty indai akwai addu'oin da zaki taimakeni dasu na dingiyi aɗakina Ki bani a...."
"Kinga ya isaka haka basai kinyi alaye ba Ni banida wata addu'a in kin shirya bismillah. In kuma zaki tsaya kallon ruwa kwaɗo yai miki ƙafa shikenan. Yayan naku yaje shago sai nanda ɗan anjima zai dawo"
Sororo tabi bayan Aunty Saude da kallo. Can ƙasan zuciyar ta tana mamakin abinda ya hassalata haka! Ita dai aganinta bata faɗi wani magana da ze sanyata kumfan bak.....
"Kinga idan zaki fita ki kakkaɓemin maganar da mukayi anan kibar min atsakar ɗakina kada aje asakani abakin duniya inzama topic abakin dangin miji."
"Insha Allah "
Tafaɗi. Jikinta duk yayi evening. Aunty Saude ta sauke labulen ta juya dama har ta fita tsakar waje abin yaciwota ta dawo.
Tagumi tayi harda tallafe haɓa zuciyar ta duk adagule.
Jiran kusan awannin biyu tayi kafin Yaya Yusha'u yadawo dan alokacin har tayi sallahn azuhur, yara duk sun dawo makaranta, Aunty Saude ta kawo mata jellof ɗin talliya sai ƙamshi take amma bata ciba.
Aunty Saude daketa cika tana batsewa tace mata ta tashi taje seat room din Yaya Yusha'u.
A nutse tamiƙe tanufi ɗakin nasa. Da sallamar ta ta shiga. Ya amsa. Yana kora ruwan da yake sha bayan yagama cin abinci.
A mutunce suka gaisa. Ya tambaye ta "yara" tace "suna nan lafiya ƙalau" suka ɗanyi shiru suduka.
Zainab tai ƙundun bala ta gayama Yaya Yusha'u abinda yake faruwa.
Nan take ran Yaya Yusha'u yaɓaci. Dama shi fusatacce ne. Yaɗaga waya yakirashi yace mai duk inda yake yazo gidansa yana nimansa.
Ko mintuna talatin ba ayiba sai gashi yazo.
Ƴan hanjin Zainab sukai wani irin yamutsawa suna curewa wuri guda. Wani gumi da bayada alaƙa da zafi yakaryo mata. Da ƙyar ta iya ɗaga harshenta daye mata nauyi ta amsa sallamar sa daya shigo ɗakin. Ko ido kasa ɗagawa tai ta kallesa asanda Yaya Yusha'u ke zayyano mai abinda tafaɗi cikin matsanancin ɓacin rai.
"Yaya kayi haƙuri insha Allah baza'a ƙaraba"
Yafaɗi cikin sanyinsa inda zuciyar sa ke tafasa da ɓacin rai mai tsanani.
"Gaskiya Ahmadu ka ɓata wayanka, yanzu gayamin mai yarinyar nan tai maka da kai mata wannan cin mutuncin harda cewa tariƙe yara kabar mata kuma wai ta manta kataɓa zama mijinta to sakinta kai ko me?"
Dasauri yagirgiza kansa dake duƙe"A'a Yaya ban saketa ba. Laifi tai min raina yaɓaci harna faɗi waɗannan maganganun amma bawai ina nufin haka bane. Dan Allah kaya haƙuri!"
Jikin Yaya Yusha'u yaɗanyi sanyi jin yanda yaketa bada haƙuri sai yace
"Ai bani zaka bama haƙuri ba. Zainab kaima laifi. Ita zaka nimi afuwanta bani ba."
"Dan Allah Ki ya hakuri."
Ahmed yafadi dasauri tun kafin Yaya Yusha'u yasauke numfashi.
Zainab ta lumshe idanunta wasu hawaye data rasa kona menene suka sauko mata. Ga wani irin abu dake yawo aduk jikinta bayan kalaman Ahmed datake sauraro yana fadin wai laifi tai masa yayanke wannan hukuncin da zata iya da ba abinda zai hanata bude baki tace ƙarya yake to amma ba doguwar jayayya take nimaba. Ita fatanta ya janye kalaman sa hakan ma ya wadatar.
Muryan Yaya Yusha'u taji a tsakiyar kanta.
"Zainab kiya hakuri dan Allah. Insha Allahu rabbi hakan bazai ƙara faruwa ba. Kin san mu maza in ranmu yaɓaci komaima faɗi mukeyi."
"Ba komai Yaya insha Allah ya wuce."
"Nagode. Amma dai shikenan matsalar ko akwai wani?"
Ta sunkuyar da kanta tana amsa shi cikin ladabi.
"Shikenan Yaya. Nagode."
"Tom Allah yaki yaye."
Da haka sukai sallama suka fito tare dashi. Bece mata komai ba har suka iso inda yai packing ɗin motarsa ananne yakasa haƙuri ya kalleta da kyau.
"Yanzu Zainab akan wannan maganar kika kaini ƙara?!"
Yafaɗi murya acun kushe da ɓacin ran daya gama cika mai zuciya.
Duk da zuciyar ta na rawa haka ta daure tai magana.
"Ahmed! mai yasa...."
"Kinga Ni ba dogon magana zanyi dake ba dan jin zuciyata na keyi kamar zata tarwatse. Wani abu nakeji atsaye a ƙahon zuciya ta idan ina haɗa numfashi dake. So bazan matsa miki ba idan bazaki iya tsayawa a matsayar dana ajiye Ki jiyaba to zaki iya kama gabanki Ki koma inda kika fito but kada Ki ƙara kaini ƙara."
Kalaman Ahmed sun sauka a zuciyar Zainab kamar wani abu mai nauyi da aka ɗora mata ba tare da an tambaye ta ko za ta iya ɗaukarsa ba.
Ta tsaya cak.
Idanunta suka sauka kan fuskar mijin nata, tana kallonsa kamar ba ta fahimci abin da ya faɗa ba. A hankali ta buɗe bakinta, amma babu wata kalma da ta iya fita.
Ko kafin ta sami zarafin magana har ya zagaya ya haye motarsa yai mata key ya buɗeta da ƙura.
Ba tare da sanin ko ƙafafuwanta zasu iya cigaba da ɗaukan taba taci gaba da tsayuwa har tasami napep ta hau.
A cikin napep ɗin ta jingina da ƙarfe tana kallon titi zuciyar ta cike phall da saƙe saƙe marasa limit balle iyaka.
Da suka isa. Ta biya kuɗin napep. Ta sauko.
Sai da ta shiga gidan ta hangi wasu matan unguwar su zaune a veranda.
Kawayen Zalika ne. Duk suka juya suka kalle ta.
Kallon da suka yi mata bai kasance na tausayi ba. Kallo ne na wulaƙanci.
Na wanda ya riga ya san labarinta, kuma ya zo ya ga yadda karyewar zuciyarta take.
Zainab ta rage saurin tafiyarta. Ta sunkuyar da kanta.
Amma kalmar da wata daga cikinsu ta furta ta sa ƙafafuwanta suka tsaya cak.