Free chapter · Read without an account
PAGE 5
MEET POV My name is Meet Manbir trijal. I'm studying medicine in university of Munbai vidiyapth, in year three. I'm living with my lovely family in Munbai. Today I met Rumaisa. To be honest I can tell you I adore her because she is so calm. She is not insolent. She talk soft. I want to be one of her friend and I thank God she accepted me as her friend.
RUMAISA POV Haka muka cigaba da zama cikin kawnciyar hankali tare da Pihu da Faazan saboda sune kawaye na Dan ita ma Pihu course mate din mun ce, Ranaku na ta gudu mun gama first semester mun samu holiday din two weeks so na ga yaushe na shirya na koma Nigeria na huta har na dawo. Ko da na fadi wa baba yace shikenan.
A haka tsawon shekara daya Muna kawance da su Meet. Kasance cewa shima medicine ya ke karanta Wani lokacin Yana mana tutorial .
A duk lokacin da muke da free time muna fita. Naga wurare daya wa a garin Munbai. Har ma da gidan su Pihu tare da Faazan.
Ranar Wednesday, Meet ya Kira Pihu ya gayyace mu cin abincin dare wai Kuma a gidan su.
Pihu ta ammince Mai da haka. Ni kuma Banda Wani objections though Ina Jin faduwar gaba. Cin abincin dare a gidan su aboki.
Da maraice muka shirya muka tafi gidan su Meet, daman ya turawa Pihu address din gidan. Muna Isa ta Kira shi a waya ya fito kofar gidan na su ya tarbe mu ya shiga da mu ciki.
Gidan Yana da girma Daman safe contact ne. Ya Kara so damu cikin parlour gidan, parlour Yana da girma dauke da set of furniture guda uku sai dinning daga dayan gefen. Wata yar tsohuwa tafito daga wurin dinning shinfede da fara'a a fuskar ta. Ta karaso kusa damu tare da tanbayar Meet wa inna sune bakin naka? Ta fadi da yaran indiya.
Ya amsa mata da"Eh kaka, wanna ita ce Pihu." Pihu tace ma old woman din "Namaste" tare da hade tafukan hannun ta wuri daya. Sannan yace wanna ita ce Rumaisa. Nima nayi kamar yanda Pihu tayi.
Wata yar matashiya ta fito daga kitchen din. Kaka ta tambaye ta shin komai ya kammalu? Tace mata eh kaka. Kakar tace wa Meet ya karaso damu wurin dinning.
Muka karasa. Kakar tace Mu zauna. Zan zauna wata mata ta dagatar Dani.
Meet yace mama miyasa Zaki dagatar da ita? Sai mamar Meet ta amsa Wani towel daga hannun Mai aikin su ta shinfida akan kujerar da zan zauna. Meet ya Kara tambayar ta mi take Yi haka. Baban Meet shima da ya karaso ya tambaye ta mi take ke yi haka.
Sai mamar tace in zauna bayan tagama shinfida towel din a kujerar da zan zauna. Na tsaya Ina kallon ta Dan da yaran indiya tayi maganar so ban gane ba.
Sai tace:"Oh I forget you're not hind, I mean you can sit now." Nace mata thank you sannan na zauna. Ta Kalli Meet tace mai ita din musulmace toh Dan haka Bai kamata ta zauna ba, Bai ma kamata ta shigo min gida ba.
Meet yace:"Mama wai miyasa ki ke haka ni na gayyace su, Kuma mine aybu Dan ta shigo."
Mamar ta amsa Mai da saboda su din najasa ne. Ta fadi abubuwa marassa dadi akan musulmai. Ganin abin ta yayi yawa mahaifin Meet ya kawbe ta tare da tambayar Meet dafatan bana Jin Hindu.
Meet yace Mai tana ji Amma ba sosai ba. Kakar tace ya Isa haka mu ci abinci. Mai aikin gidan tare da matar yayan MEET suka Yi serving din mu Abinci.
Tunda Dhani (Matar Jeet) ta aje min Abinci a gabana kamshin abincin ya cika min hanci. Ban fara ci ba har sai da Pihu ta min nuni da mu ci sannan na dauki spoon na sa a cikin bowl din da ban San mine ne ba.
Meet yace:"min in Yi testing din Kerala vegetables Stew din, shi ya hada ta da kan shi."
Nayi Bismillah a cikin zuciyata nayi spoon daya, tunanina zai Yi dadi yanda yake kamshi sai na ga akasin haka gishri yayi yawa. Shikuma sai washe Baki yake Yana jiran abin da zan fadi. Da kar na hadeye miyar ganin idon Kowa a Kai na nace Mai "It test nice."
Pihu ma da ta dandana tace Mai tayi dadi. Ta nuna Jin dadin ta. A rai na nace to itama wayance wa tayi ko Kuma haka ake miyar da gishri.
Kakar tace:"Ay jikana ya iya Abinci." Da kar na kara spoon biyu ba Dan naso ba Dan dai kar in bashi kunya gani kowa na santin ta. Na Sha juice tare da Batata vada guda daya shi yayi dadi Amma ban San shi ba na dai ci.
Har muka gama cin abinci Rain mahaifiyar Meet a bace. Sauran su Kuma ana ta raha Dan sun koma yin turanci duk Dan kar in tsargu.
Muka gama cin abincin muka godai wa juna sannan suka rako ni har kofar gidan. Meet ya Kara godai mana da zuwan mu. Mu ka dai Yi sallama muka tafi gani dare ya fara Yi.
RUMAISA MILHAN ✨ MEENAMAJEED03 🥀 VOTE COMMENT AND SHARE 🙏 THANK YOU