Free chapter · Read without an account

PAGE 10

by Aminatu nazeer · Rumaisa milhan

RUMAISA PROVERBS

Washegari da rana wayata na hannun su zara pihu ta kira ni muka gaisa. Bayan na gama waya da ita ina kunna waya naga suna kallon picture din birthday di na. Gabana ya matukar faduwa gani next picture din, wato picture din da Meet yake bani cake a baki. Da ace sun ganshi da kashi na ya bushe karatun ma da shikenan, gashi kuma ban so in goge su sai na dora su a kan gmail dina na goge su daga Cikin waya.

Sati uku da nayi a gida ina tayin baki yan`uwa da abokan arziki suna zuwa duk wanda ya zo sai yace in bashi labarin Munbai.

Haka dai har na gama hutu na koma .

Ina komawa ba dadaiwa aka yi bikin Holi ba Muslmi ba Hinduism kowa nayin su.

Bayan an gama holi da sati biyu a ka fara azumi, na ji takaicin yin azumi a makaranta, ga lokacin lokacin zafi ney.

Banda zabi dolle sai na fita na siyo abincin da zan ci da iftar da kuma safur.

Wani lokacin pihu ta siyo min ko kuma Meet, Mohit ko Fazan su kawo min. Haka har nayi azumi 27 a makaranta, sai ana sauran kawna biyu sallah a ka bada hutu. Toh Fazan ta roke ni da in zo gidan su nayi sallah hakan ya sa na bita gidan su.

Azumi biyu da nayi a gidan su Faazan naji dadi sosai saboda duk in da 3pm tayi an fara aikin abincin buda baki kala kala. Bayan anyi buda baki dukka yan gidan za a tafi masallaci a yi sallah isha`i tare da tarawee. Bayan an dawo daga tarawee a ka kara cin abinci sai ayi fira, ba a bacci.

Wurin 12:30am sai kowa yayi alwalla a shirya a tafi tahajjud, bumu dawo ba sai 3:35am nan a ka fara aikin safur shima abinci kala-kala, nan muka gama safur mukayi sallah, bayan rana ta fito kowa ya koma bacci.

Shiyasa duk lokacin da muke da morning lecture Faazan in ta zo ba ta komi sai bacci saboda gidan su goman karshe till down a ke yi sai bayan sallah asuba ake komawa in ka koma sai azzahar.

Ranar edi muna tashi kowa yayi wanka ya shirya muka sha madara sanna a ka tafi masallaci domin yin sallah edi. Muna dawo wa abinci akaci sanna a kayi wishing juna edi mubarak tare da gift hakan ya birge ni. Na kira gida na musu baraka da sallah.

Aroun two muka fita picnic a one day water picnic in Panvel Maharastra Munbai. Kannan Faazan su biyu da yayan kannan baban suka yi wasa ba mu dawo ba sai dare haka ma washegari muka je amite animal ark da AMUSEMENT PARK nan ma sai dare muka dawo.

Saida muka jera kawna biyar muna zuwa wurare. Pihu, Meet, & Mohit sun kawo min sallah gift.

A gaskiya naji dadin yin sallah ta a gidan su Faazan.

Bayan holiday ya kare muka koma makaranta a ka cigaba da inda a ka tsaya. Muna ta struglling na makaranta yanzu bumu fiye samun free time ko da mun samu ranar a gajiye muke.

Da yarda Allah muka gama second semister level two. Mun samu holiday din 3 week na koma gida dan wannan karan ba zan tsaya ba musanmman ma da mun koma ba dade wa ba za ayi sallah layya.

RUMAISA MILHAN ✨ MEENAMAJEED03 🥀 VOTE COMMENT AND SHARE 🙏 THANK YOU

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.