Free chapter · Read without an account
CAUGHT UNAWARE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER NINETY EIGHT:98*
*CAUGHT UNAWARE*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Seeyama ta ƙara haɗe rai, ta ɗan runtse idanunta tana kallon mahaifiyarta, sannan ta juya kallonta zuwa ga Raihana wacce har yanzu take zaune cikin nutsuwa, ba tare da ta san irin tunanin da ke ratsa zuciyar kishiyarta ba, a hankali ta ciza leɓenta na ƙasa, tana ƙoƙarin danne wani irin haushi da ya fara cinye ta daga cikin zuciyarta, so, this is what Mommy came here for? To help both of us? Ta tambayi kanta cikin takaici, tana jin kamar wani abu ya tsaya mata a maƙogwaro, ta sake kallon Zayd, tana jiran ko zai ce wani abu ko kuma ya nuna wata alama ta rashin gamsuwa da shawarar Hajiya Hauwa, amma abin takaici, Zayd ya kasance kamar wanda ba shi da wata damuwa da lamarin, fuskarsa a sake, kamar yau ya ma fi sakin ranshi, hankalinsa a nutse, kamar komai ya riga ya daidaita a wajensa, wannan ne ya ƙara harzuƙa Seeyama.
Ba tare da ta ce uffan ba, sai ta miƙe tsaye cak! Motsin nata ya sa Suhaila ɗan ɗaga kai ta kalleta, yayin da Hajiya Hauwa ta juyo da idanunta zuwa gare ta, Seeyama kuwa ko kallonsu ba ta yi ba, ta zari wayarta dake gefenta da wani irin sauri mai nuna tsantsar fushi, ta juya ta nufi hanyar fita daga falon da sauri, takunta ya yi sauri, tana tafiya kamar wadda take gudun wani abu, fuskarta a haɗe tamau, hannayenta suna motsi cikin zafin rai, da za ka kalleta, za ka rantse da cewa tana shirin tashi sama ne saboda yadda take ficewa daga falon, “Seeyama?” Hajiya Hauwa ta kira sunanta a hankali, amma ko waiwayowa ba ta yi ba, ta ci gaba da tafiyarta, ta fice daga falon fuuuuuuuu, ta bar ƙofar a buɗe a bayanta.
Na ɗan lokaci, kowa ya yi shiru, Suhaila ta bi ta da kallo, idanunta a buɗe, kafin ta juya ta kalli Mommy, Raihana kuwa ta ɗan ɗago kanta a hankali, idanunta suka bi hanyar da Seeyama ta bi, ta yi shiru, ba tare da ta ce komai ba, amma a zuciyarta ta kasa tantance ko ta kamata ta ji tausayinta ne ko kuma ta bar komai a hannun waɗanda abin ya shafa, Zayd ma ya ɗan ɗaga idanunsa ya bi Seeyama da kallo har zuwa lokacin da ta ɓace daga ganinsa, ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya mayar da idanunsa kan Hajiya Hauwa, fuskarsa har yanzu babu wata alama ta damuwa, babu wanda ya yi magana, babu wanda ya bi ta, kowa ya zauna a inda yake, kamar babu abin da ya faru, Hajiya Hauwa ta sauke ajiyar zuciya a hankali, ta girgiza kai kaɗan, sannan ta mayar da hankalinta kan Zayd, “Ka ga halin nata ko, son?” Ta faɗa cikin wata murya mai ɗauke da gajiyar rashin sanin yadda za ta shawo kan ɗiyarta, Zayd ya ɗan ɗaga gira, ya jingina da kujerar cikin natsuwa, “Let her be, Mummy,” ya faɗa a taƙaice, sannan ya ɗauki wayarsa ya duba, kamar ya riga ya gama magana a kan lamarin, Hajiya Hauwa ta zuba masa ido na wasu daƙiƙu, amma ba ta ce komai ba, a gefe guda kuma, Suhaila ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, tana jin kamar akwai wani sabon rikici da ke jiran ɓarkewa a gidan, domin ta san Seeyama sosai.
Hajiya Hauwa ta ɗan kalli ƙofar da Seeyama ta bi, sannan ta girgiza kai a hankali kafin ta mayar da kallonta kan sauran mutanen da ke cikin falon, fuskarta dauke da murmushi tana kallon su ɗaya bayan ɗaya, kamar ba ta son abin da ya faru ya hana ta ci gaba da abin da ta zo yi, “To, bari na je na ganta, daga nan zan wuce,” ta faɗa cikin nutsuwa, tana gyara zamanta kafin ta miƙe tsaye, Zayd ya ɗan ɗago kansa ya kalleta, sannan ya jinjina kai a hankali, ba tare da ya ce komai ba, Hajiya Hauwa ta juya zuwa ga Raihana, wacce har yanzu take zaune cikin ladabi, hannayenta a haɗe a kan cinyarta, ta ƙarasa gare ta, sannan ta ɗan ranƙwafa a gabanta, ta miƙa hannu ta shafa fuskarta a hankali, wani irin murmushi mai cike da kulawa yana bayyana a fuskarta, “Ki kula da kanki, kin ji, my dear?” Ta faɗa cikin taushin murya, “And ki daina zama kina kawowa har waaar haka… kina barin cikinki babu komai haka, ba ki yi breakfast ba! Is not good for your health, kin ji ko?” Raihana ta ɗan buɗe baki, tana kallon Hajiya Hauwa da wani irin kunya, musamman ganin yadda take nuna mata kulawa a gaban Zayd da Suhaila, ta jinjina kai a hankali, “In Shaa Allah, Mommy,” ta amsa cikin sanyin murya, Hajiya Hauwa ta ƙara murmushi, sannan ta shafa kumatunta a hankali, “Good girl,” ta faɗa cikin gamsuwa, kafin ta miƙe tsaye, ta ɗauki jakarta daga kan kujera, ta gyara mayafinta da ya ɗan zame a kafaɗarta, sannan ta juya zuwa ga hanyar fita daga falon, takunta ya kasance cikin nutsuwa kamar yadda ta saba, tana tafiya ba tare da gaggawa ba, har ta isa ƙofar ta fice daga ɗakin.
Suhaila ta bi ta da kallo, idanunta suna bin bayanta har sai da ta ɓace gaba ɗaya daga ganinta, sai ta sauke wata ajiyar zuciya a hankali, tana ɗan gyara zamanta, kafin ta juya da kallonta zuwa ga Zayd, shi kuwa yana zaune cikin nutsuwa, wayarsa a hannunsa, fuskarsa ba ta nuna ko kaɗan abin da ke ratsa zuciyarsa ba, Suhaila ta ɗan karkatar da kanta, tana kallonsa kamar tana son ta fahimci wani abu daga fuskarsa, amma kamar yadda aka saba, Zayd Armaan bai kasance mutum ne mai sauƙin karantawa ba, Suhaila ce ta fara karya shirun da ya mamaye falon, ta juya da kallonta zuwa ga Raihana, “Anty Rayy, ga abincin nan, tashi ki ci mana,” ta faɗa cikin kulawa, Raihana ta ɗan ɗago kanta, ta saci kallon Zayd wanda ke zaune a kujerar da ke fuskantar inda take, amma da ta ga hankalinsa gaba ɗaya yana kan wayarsa, sai ta mayar da idanunta ƙasa da sauri, a hankali ta miƙe tsaye, tana haɗiye yawu, ita kam wallahi, har ta nemi yunwarta ta rasa gaba ɗaya, duk da haka, ba ta da wani zaɓi face ta je ta zauna, ko don kawai kada a ce ta ƙi cin abincin da aka kawo mata, ta ƙarasa dining area ɗin a hankali, ta zauna a kujerar da ke gaban teburin, sannan ta buɗe abincin da Suhaila ta ajiye mata, ta ɗauki spoon ɗin, ta fara jujjuya abincin a hankali, tana kallonsa kamar akwai wani abu a cikinsa da take ƙoƙarin ganowa, amma gaskiyar magana, hankalinta ba ya kan abincin sam.
A gefe guda kuma, Suhaila ta tashi daga inda take, ta koma kusa da Zayd, ta zauna a kujerar da yake kusa, “Akhie…” “Hmm?” Ya amsa a taƙaice, ba tare da ya ɗago kansa daga wayarsa ba, “Ga breakfast ɗinka nan, kunun gyada ne da kosai, Ummie ce da kanta ta yi maka, na zuba maka?” A hankali Zayd ya ɗago kansa daga wayarsa, ya sauke idanunsa kai tsaye a kan Suhaila, Suhaila kuwa ta buɗe idanunta sosai, tana kallonsa, “What?” Ta tambaya, tana ɗan nuna kanta da yatsa kamar tana son tabbatar da abin da ta gani, Zayd ya lumshe idanunsa a hankali, sannan ya kawar da kallonsa daga kanta, ya sake komawa kan wayarsa kamar ba ya son ɓata lokacinsa da tambayarta, Suhaila ta cigaba da kallonsa, “Na zuba maka?” Ta sake tambaya, wannan karon tana magana a hankali, Zayd ya jinjina kai kawai cikin nutsuwa, “Okay,” Suhaila ta faɗa, tana miƙewa tsaye, ta ɗauki hanyar kitchen ɗin inda ta ajiye basket ɗin da ta kawo, domin ta haɗo masa nasa abincin, da ta ɓace daga falon, Zayd ya sauke idanunsa daga kan wayarsa, kallonsa ya koma kan Raihana, tana zaune tana facing ɗin parlor din, hannunta riƙe da spoon ɗin da har yanzu take ta jujjuya wa a cikin abincin, ya ɗan runtse idanunsa, yana kallon yadda take yi ba tare da ta kai ko da loma ɗaya bakinta ba, for a moment, bai ce komai ba, ya ajiye wayarsa a kan cinyarsa, ya jingina da kujerar, idanunsa har yanzu a kanta, Raihana kuwa ba ta san cewa yana kallonta ba, hankalinta yana wani wuri daban, tana ƙoƙarin shawo kan kanta ta fara cin abincin, amma duk yadda ta yi, sai ta ji kamar yunwar ta ɓace gaba ɗaya, ta ɗauki spoon ɗin, ta ɗan tara abincin a ciki, amma kafin ta kai shi bakinta, sai ta sake tsayawa, a bayanta, Zayd ya ci gaba da kallonta cikin shiru.
Suhaila ta dawo daga kitchen ɗin, ta ɗauko abincin Zayd ta ajiye masa a kan stool ɗin da ke gefensa, a daidai lokacin kuma, wayarta ta fara ringing, ta zaro ta daga cikin jakarta, ta duba screen ɗin na wasu seconds kafin ta ajiye ta a gefenta, ba tare da ta ɗaga kiran ba, sannan ta fara gyara veil ɗinta, tana kallon kanta a fuskar wayarta, “Ni dai tafiya zan yi, yau ina da baƙi,” ta faɗa a hankali, tana kallon yadda ta gyara veil ɗin da kyau, Raihana, wacce ke zaune a dining area, ta ɗan ɗago kanta da jin maganarta, ta juyo tana kallon Suhaila, wacce ta ɗan ɗaga murya ne domin ta ji ta da kyau, Suhaila ta kalli Raihana, ta yi mata murmushi, “Anty Rayy, tafiya fa zan yi, ni ban ma zaci zan daɗe haka ba wallahi,” Raihana ta ɗan langwabe kai, ta ajiye spoon ɗin da ke hannunta, sannan ta kalli Suhaila cikin sanyin murya, “Don Allah, ki bari sai anjima da yamma mana, amma daga zuwanki yanzu sai ki ce tafiya?” Suhaila ta zaro ido, sannan ta fashe da dariya, “Awa na nawa da zuwana? Kina ciki, wallahi na daɗe, kuma bayan zuwan Mommy ma, awa na nawa na a gidan nan? Ni dai tafiya zan yi,” ta ɗan dakata, sannan ta ƙara da cewa, “Banda ma dole Ummie ta sa na kawo miki abinci, ai ba a zuwa gidan amare a irin wannan lokacin, ko kin manta?” Raihana ta ɗan ɓata rai, ta harare ta hararar wasa, tana jin kunya saboda irin maganar da ta yi, Suhaila ta sake fashewa da dariya, tana jin daɗin yadda take sa Raihana kunya, “Toh, sorry mana!” Ta faɗa tana ɗaga hannayenta kaɗan, “Zan dawo idan an kwana biyu, but right now, I’m leaving,” Zayd, wanda ke zaune a kujerarsa, ya kasance yana jin duk hirar tasu, amma kamar yadda ya saba, bai ko juya kansa ya kalli ɗayarsu ba, hankalinsa ya koma kan wayarsa, sai dai babu wanda ya san ko yana karanta wani abu ne ko kuma yana jin abin da suke faɗa ne kawai, Suhaila ta ɗauki handbag ɗinta, ta rataya a kafaɗarta, sannan ta miƙe tsaye, “Akhi, na tafi,” sai a wannan karon Zayd ya ɗago kansa daga wayarsa, “Sameer ya tafi, wa zai kai ki?” Suhaila ta ɗan sosa kanta, tana murmushi kamar wadda ta riga ta shirya amsar tun kafin ya tambaye ta, “Uhm… Farouq is at the gate,” Zayd ya zuba mata ido na wasu seconds, fuskarsa babu alamar abin da yake tunani, bai ce komai ba, kawai ya ci gaba da kallonta, Suhaila ta yi wata ‘yar dariya, tana bin fuskarsa da ido, sai kuma ta fara murmushi, sannan ta juya ta nufi inda Raihana take, da ta ƙarasa wajenta, sai ta sunkuya kaɗan ta ba ta side hug, “Bye, Anty Rayy, sai na sake dawowa,” Raihana ta yi saurin ajiye spoon ɗin da ke hannunta, ta fara ƙoƙarin miƙewa domin ta raka ta, amma Suhaila ta ɗora hannu a kafaɗarta ta mayar da ita zaune, “A’a, ke dai ki yi zamanki ki ci abincinki, ba sai kin raka ni ba, na yafe miki,” ta faɗa cikin wasa, tana ɗan matsa kafaɗarta a hankali, Raihana ta ɗan yi murmushi, sannan ta koma ta zauna yadda take, tana kallon Suhaila da wani irin yanayi na rashin son tafiyarta, “Toh, ki gaishe da Ummie da Inno, don Allah,” “Zasu ji, in Shaa Allah,” Suhaila ta amsa, sannan ta gyara handbag ɗinta a kafaɗarta ta juya zuwa ƙofar fita, Raihana ta bi ta da kallo, tana jin kamar ta yi sauri sosai wajen tafiya, tun lokacin da ta shigo gidan, Suhaila ta kasance tana sa ta ɗan saki jiki, kuma kasancewarta a kusa da ita ya rage mata jin cewa baƙuwa ce a gidan, ta sauke ajiyar zuciya a hankali, idanunta har yanzu suna kan hanyar da Suhaila ta bi, a gefe guda kuma, Zayd ya ɗan ɗago kansa daga wayarsa, idanunsa suka sauka a kan Raihana na ɗan lokaci, ya lura da yadda ta bi Suhaila da kallo har ta ɓace daga ganinta, amma bai ce komai ba, kawai ya ɗauki kofin kunun gyadarsa, ya kai bakinsa a hankali.
Seeyama ta shigo part ɗinta da wani irin fushi, ta banko ƙofar da ƙarfi har ta yi wani sautin da ya cika falon, ta tsaya cak na ɗan lokaci, tana huci kamar wadda ta yi doguwar gudu, kafin ta juya ta kalli inda Hajiya Hauwa ta shigo bayanta, “Mommy!” Ta kira cikin tsawa, tana zare dankwalinta daga kanta ta jefa shi a kan sofa, Hajiya Hauwa ta kalleta a hankali, sannan ta rufe ƙofar da ta shigo ta ƙaraso cikin falon ba tare da ta nuna wata damuwa ba, “Me ya faru kuma, Seeyama?” “Me ya faru?” Seeyama ta maimaita, tana buɗe hannayenta cikin mamaki, “Mommy, you embarrassed me! Kin wulaƙanta ni a gaban waccan yar iskar yarinyar! Kina zaune kina gaya wa mijina cewa ban iya komai ba, kina bayyana duk gazawata kamar wata ƙaramar yarinya da ba ta san komai a rayuwa ba!” Ta ɗan tsaya, tana ƙoƙarin haɗiye haushin da ya tokare mata maƙogwaro, amma hakan bai taimaka mata ba ko kaɗan, “Kin gama ba ni kunya a wajensa, sannan kuma sai kika juya kika ce ita ma za ki samo mata mai aiki? Like, how does that even concern you? In ruwanki da yar aikinta?” Ta ɗaga hannu tana nuna hanyar da ta fito daga can, “Waccan yarinyar da ta taso cikin wahala! Idan ba ta iya yi wa kanta komai ba, uban waye zai yi mata? Ai ba yau ta fara rayuwa ba! Tun kafin ta zo gidan nan, ba ita take kula da kanta ba? To, me ya canza yanzu?” Hajiya Hauwa ta tsaya tana kallonta, fuskarta babu wata alamar mamaki, ta san halin ɗiyarta, amma wannan karon, Seeyama ta wuce inda take tunani, Seeyama kuwa ba ta gama ba, “Amma abin da na kasa ganewa, Mommy, shi ne yadda kika saki jiki da wannan matsiyaciyar har haka!” Ta faɗa, tana matsowa kusa da mahaifiyarta, “Kin zauna da ita, kina shafa mata fuska, kina yi mata murmushi, kina tambayarta ko ta ci abinci, har kina cewa ba ta karya ba! What is all this?” Ta buɗe idanunta sosai, kamar har yanzu tana ganin abin da ya faru a falon Raihana, “Sannan abin da ya fi ba ni mamaki, kina zaune a kujerarki, ita kuma kika zaunar da ita a gefenki kamar wata ’yar cikinki! Mommy, ke ce kika haife ni fa! Ni ce ɗiyarki! Your own daughter!” Muryarta ta fara rawa, amma ba ta san ko saboda fushi ne ko kuma saboda yadda abin ya taɓa zuciyarta ba, “Me ya sa kika yi haka? Me ya sa kika nuna mata irin wannan kulawar a gabana? Kin san yadda nake ji kuwa?” Ta yi shiru na ɗan lokaci, tana kallon mahaifiyarta da wani irin kallo mai ɗauke da zargi da rashin yarda, “Kar ki sa kwakwalwata ta buga, Mommy! Please!” Ta faɗa, tana ɗaga hannayenta sama, “What exactly is going on? Me wannan yake nufi ne wai?” Ta ja dogon numfashi, sannan ta ƙara da cewa cikin zafin rai, “Don Allah ki gaya min gaskiya, tun yaushe kika fara son wannan yarinyar haka? Ko kuwa akwai wani abu da ban sani ba?”
Hajiya Hauwa ta ɗan karkatar da kanta, tana kallon ɗiyarta a hankali, “Kin gama?” Seeyama ta buɗe baki da sauri, “Mommy—” “Na ce kin gama, Seeyama?” Wannan karon muryar Hajiya Hauwa ta fito da ɗan kaifi, wanda ya sa Seeyama ta dakata na ɗan lokaci, amma fuskarta ta nuna a fili cewa ba ta ji daɗin yadda mahaifiyarta ta katse ta ba, “Fine,” ta faɗa cikin fushi, tana ɗaga hannunta, “Talk, I’m listening,” ta faɗi haka ne kawai, amma daga yadda take kallon mahaifiyarta, ya bayyana cewa har yanzu ba ta samu amsar tambayar da ta fi damunta ba.
Hajiya Hauwa ta zuba wa Seeyama ido na wasu daƙiƙu, tana nazarin fuskarta mai cike da rashin yarda da kuma zafin rai, ta girgiza kai a hankali, ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ƙaraso ta zauna a kan sofa, tana nuna wa Seeyama kujerar da ke fuskantarta, “Zauna,” ta faɗa cikin nutsuwa, amma muryarta na ɗauke da wani irin iko da ba ya barin mai sauraro ya yi wasa da maganarta, Seeyama ta ɗan tabe baki, ta zauna a ɗayan ƙarshen sofa, tana hararar gefe, Hajiya Hauwa ta kalleta, ta ɗan gyara zamanta, sannan ta fara magana cikin sanyin murya, “Seeyama, ke ba ki da hankali ne, ko kuwa da gangan kike ƙin fahimtar abin da nake gaya miki?” Seeyama ta ɗago kai da sauri, “Mommy!” “Shiru ki saurare ni tukuna!” Hajiya Hauwa ta katse ta, tana ɗaga yatsa kaɗan, “Na sha gaya miki, ba haka ake yaƙar kishiya ba, ba da hauka ba, ba da shashanci ba, ba kuma da wannan halin naki na yin fushi a kan duk abin da bai yi miki daɗi ba,” ta ɗan dakata, tana kallon ɗiyarta da idanunta masu zurfin basira, “Ke yarinya ce a wannan harkar, Seeyama, kina tunanin duk abin da zuciyarki ta raya miki shi ne gaskiya, sannan kina son kowa ya yi yadda kike so, idan wani abu bai yi miki daɗi ba, sai ki yi masifa, idan aka yi wa wata magana mai daɗi, sai ki ji kamar an ƙwace miki wani abu, to, har yaushe za ki ci gaba da rayuwa haka?” Seeyama ta juya fuskarta gefe, tana jin haushin yadda mahaifiyarta ke yi mata magana kamar ƙaramar yarinya, Hajiya Hauwa kuwa ta ci gaba, ba tare da ta bari ta katse ta ba, “Kina zaton saboda tana kishiyarki ne, ni ma uwarki zan zama maƙiyiyarta a zahiri, duniya ta shaida? Ko saboda kina son Zayd, dole ne duk wanda yake kusa da shi ya zama maƙiyinki? Seeyama, idan har wannan shi ne tunaninki, to wallahi kina buƙatar ki sake duba kanki,” ta ɗan jingina da kujerar, ta haɗa hannayenta a kan cinyarta, “Ki saurare ni da kyau, ni uwarki ce, kuma ina son abin da zai amfane ki, amma ba zan zauna ina kallonki kina lalata rayuwarki da hannunki ba saboda kawai kin kasa sarrafa zuciyarki,” Seeyama ta juya gare ta, tana son yin magana, amma Hajiya Hauwa ta ɗaga mata hannu, “Ki bari na gama!” Ta faɗa da ɗan kaifi, sannan ta ci gaba, “Kin ga yadda kika shigo wancan falon ɗazu? Kin ga yadda kika yi magana a gabansu? Kina tsammanin kin nuna ƙarfi ne? A’a, Seeyama, abin da kika nuna shi ne rashin iya sarrafa kanki, kuma mace mai hankali ba ta bari kishiya ta san duk abin da ke damunta, ba ta buɗe zuciyarta ta zubar da komai a fili, har kowa ya fahimci inda za a taɓa ta ta fusata,” ta ɗan yi murmushi, amma murmushin bai kai idanunta ba, “Wata rana za ki fahimci cewa shiru a wasu lokuta ya fi magana amfani, ba don kin rasa abin faɗa ba, sai don kin san lokacin da ya dace ki yi magana da lokacin da ya dace ki yi shiru,” Seeyama ta cije leɓenta, tana kallon mahaifiyarta cike da takaici, “To, yanzu kina so in zauna ina kallonta tana karɓe min komai ne, Mommy?” Hajiya Hauwa ta yi mata wani kallo mai zurfi, “Karɓe miki me, Seeyama? Me ta karɓa miki a yanzu? Zayd mijinki ne, kuma har yanzu kina cikin gidansa, shin kin taɓa ganin ya ce ki bar gidan? Ko kin taɓa jin ya ce ki daina zama matarsa?” Ta ɗan karkatar da kanta, “Amma idan kina tunanin za ki yi rayuwar aure ta hanyar tsana, masifa, da ƙoƙarin ganin ba a kula da wata ba sai ke, to wallahi ba za ki yi dogon zango a wannan gidan ba,” ta faɗi maganar cikin nutsuwa, amma nauyinta ya isa ya sa Seeyama ta yi shiru, Hajiya Hauwa ta ci gaba da magana, wannan karon cikin wata murya mai taushi amma mai ɗauke da gargaɗi, “Ki koyi yadda za ki zauna da mijinki, ki koyi yadda za ki kula da gidanki, ki koyi yadda za ki yi magana a lokacin da ya dace, da yadda za ki riƙe mutuncinki ko da kina cikin fushi, ba wai ina ce miki ki zama kamar Raihana ba ne, a’a, ina gaya miki ne ki zama mace mai hankali, wacce ta san darajarta kuma ta san yadda za ta tafiyar da rayuwarta,” ta ɗan matsa gaba, tana kallon ɗiyarta ido-da-ido, “Domin idan har kina tunanin Zayd zai zauna yana kallon duk wannan halin naki har abada, kina yi wa kanki ƙarya, shi ba irin mutanen da za ki yi wa ihu su zauna suna lallashinki ba ne, kina ganin yadda yake? Ko kin yi fushi, ko kin yi magana, ba lallai ya ba ki reaction ɗin da kike so ba, kuma idan kika ci gaba da ƙoƙarin tilasta masa abubuwa, kina iya tura shi nesa da ke ba tare da kin sani ba,” Seeyama ta sauke idanunta, amma fuskarta har yanzu a haɗe take, maganar mahaifiyarta ta fara taɓa wani ɓangare na zuciyarta, duk da cewa girman kai bai bar ta nuna hakan ba, Hajiya Hauwa ta lura, sai ta ɗan sassauta muryarta, “Seeyama, ba kowace faɗa ce ake cin nasara a cikinta da hayaniya ba, wani lokaci, abin da kika ɗauka a matsayin rashin adalci yana iya zama dama ce gare ki, idan kin san yadda za ki yi amfani da ita, amma idan kika bari fushi ya rufe miki ido, za ki iya lalata damar da kanki,” ta ɗan yi shiru, sannan ta ƙara da cewa, “Saboda haka, daga yau, ina so ki daina wannan haukan, ki daina ɗaukar duk abin da ya shafi Raihana a matsayin hari a kanki, ki fara tunanin yadda za ki inganta matsayinki a gidan nan ta hanyar halayenki, ba ta hanyar ƙoƙarin rage darajar wata ba,” ta miƙe tsaye a hankali, ta ɗauki jakarta daga kan sofa, sannan ta sake kallon Seeyama, “Ni na faɗa miki abin da ya kamata ki sani, sauran kuma ya rage naki, amma ki tuna da maganata, Seeyama: idan ba ki iya sarrafa zuciyarki ba, wata rana ita ce za ta sarrafa rayuwarki, ita kuma Rabi, anjima da yamma driver zai kawo ta,” bayan ta gama, Hajiya Hauwa ta juya ta nufi hanyar fita, ta bar Seeyama a zaune, tana kallon ƙofar da mahaifiyarta ta bi, Seeyama ta haɗe hannayenta a kirjinta, ta na cizon leɓenta da ƙarfi, a zuciyarta, har yanzu ba ta gamsu da komai ba, amma a karon farko tun lokacin da suka bar falon Raihana, ta fara tunanin ko da gaske halinta ne yake ƙara dagula mata al’amuranta, sai dai girman kanta bai bari ta amince da hakan da sauƙi ba.
Zayd yana zaune a kujerarsa, yana sipping kunun gyadarsa a hankali, amma idanunsa suna kan Raihana, da za ka kalle shi, za ka rantse cewa hankalinsa gaba ɗaya yana kan kunun da yake sha ne, amma a zahiri, idanunsa na satar kallonta a hankali, suna bin duk motsin da take yi, ya lura da yadda take ta jujjuya abincin da spoon ɗinta, tana haɗawa tana warewa, amma ba ta kai ko da loma ɗaya bakinta ba, tun ɗazu yake kallonta haka, yana ƙoƙarin fahimtar abin da ke damunta, amma ita kamar ba ta ma san akwai wanda yake kula da ita ba, a hankali ya sauke mug ɗin kunun daga bakinsa, ya ajiye shi a kan stool ɗin gefensa, sannan ya ɗan gyara zamansa, “Hey,” muryarsa ce ta katse mata tunanin da ta yi nisa a ciki, Raihana ta juyo da sauri, kamar wadda aka taso daga barci, gabanta ya faɗi, ta zuba masa idanunta cike da ruɗani, tayi nisa a tunani, ba ta tsammanin zai kira ta a wannan lokacin ba, “Uhmm?” Ta amsa a hankali, muryarta ƙasa-ƙasa, Zayd ya ɗan karkatar da kansa, yana kallonta da lumsassun idanunsa, “Bring your plate and come here,” ya faɗa cikin nutsuwa, Raihana ta haɗiye yawu, a take, ta ji kamar wani abu ya tsaya mata a maƙogwaro, ta kasa motsi na ƴan daƙiƙu, tana kallonsa, zuciyarta kuwa tana bugawa da wani irin sauri da ita kanta ta kasa fahimta, Zayd bai sake cewa komai ba, kawai ya ci gaba da kallonta, yana jiran ta yi abin da ya ce, Raihana ta sauke idanunta a hankali, ta miƙe tsaye, sannan ta ɗauki plate ɗin da ke gabanta, tana ƙoƙarin riƙe shi da kyau duk da yadda hannayenta suka fara yin sanyi, ta juya ta nufi inda yake, takunta a hankali, kamar tana tafiya ne a kan ƙwai, a zuciyarta kuwa, tana ta addu’ar kada ya sake faɗin wani abu da zai ƙara rikita mata tunani, da ta isa gabansa, sai Zayd ya ɗan matsa gefe, ya nuna mata gefen shi, “Sit here,” Raihana ta ɗago idanunta ta kalle shi, “Ina?” Ta tambaya a hankali, kamar tana son tabbatar da cewa ba ta yi kuskuren fahimtar abin da ya faɗa ba, Zayd ya ɗan ɗaga gira, “Yes, sit,” ya maimaita, wannan karon muryarsa ta ɗan yi ƙasa, amma har yanzu babu wata alamar wasa a fuskarsa, Raihana ta haɗiye yawu, ta ji kamar zuciyarta za ta fashe saboda yadda take bugawa, ta sauke kanta, sannan ta zauna a hankali a inda ya nuna mata, tana riƙe da plate ɗin da hannayenta biyu kamar wani abu mai daraja da ba ta son ya zube, amma ta bar ɗan tazara a tsakaninsu, ta takure kanta a gefe, tana ƙoƙarin saita numfashinta, Zayd ya juya kansa ya kalleta, “Eat,” Raihana ta ɗan buɗe baki, amma ba ta ce komai ba, “Eat your food, all of it,” ya ƙara faɗa, idanunsa a kanta, Raihana ta kalli abincin, sannan ta ɗan ɗago idanunta zuwa gare shi, ta so ta ce ba ta jin yunwa, amma da ta ga yanayin fuskarsa, sai ta sake haɗiye maganar da ta taso a bakinta, a hankali ta ɗauki spoon ɗin, ta debi abincin kaɗan, sannan ta kai bakinta, loma ta farko ta shiga bakinta, amma da ƙyar ta iya haɗiyewa, ta ji kamar dukkan hankalinta ya bar abincin ya koma ga mutumin da ke zaune a gefenta, Zayd kuwa ya ɗauki mug ɗinsa ya sake sipping kunun gyadarsa, yana kallonta daga gefen ido, bai ce komai ba, amma tunda taci na farko ta cigaba da juya abinci, idanunsa suna sauka a kan plate ɗinta, “Finish it,” ta ɗaga idanunta ta kalle shi, sannan ta sake kallon plate ɗin gabanta, a hankali Zayd ya ajiye cup ɗin hannunsa, sannan ya karkata kansa ya kalle ta, “Are you planning to eat that food or just stare at it?” Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, kafin ta sake kallon plate ɗin, “Ina ci fa kuma ni wallahi, wnn yayi min yawa,” ta amsa cikin ɗan shagwaɓa, tana sake ɗaukar cokalin, ya dan lumshe idanunshi, sai ya kuma ya bude, yana kallonta ƙasa ƙasa, idanunsa suka tsaya a kan fuskarta, musamman bakin nata da har yanzu take ɗan turo wa, Raihana kuwa tana kallon plate ɗin ne, ba ta ma san irin maganar da ta yi ta fito da ita a zahiri ba, Zayd bai yi saurin magana ba, ya ci gaba da zuba mata idanu, fuskarsa a sanyaye, sai dai wannan irin kallon nasa ya sa yanayin ya ɗan canza, a hankali ya ɗan karkatar da kansa, “Yayi miki yawa?” Ya maimaita kalaman nata cikin nutsuwa, sai a lokacin Raihana ta ɗago ta kalle shi, idanunsu suka haɗu, wani abu ya faɗo mata a zuciya, wayyyo Allah na! Nan take ta gane yadda ta yi maganar, ba kawai amsar da ta ba shi ba ce—irin shagwaɓar da ta yi, yadda ta turo baki, har da jan kalmar a ƙarshe! Ta buɗe idanunta kaɗan, sannan ta sauke su da sauri, zan faɗa a zuciyata ne fa! Wayyo Allah na?? Idanunshi still na kanta, yana kallonta cikin nutsuwa, a hankali ya ɗan yi murmushin gefen baki kafin ya jingina da bayansa, sannan cikin calm voice ɗinsa ya ce, “Hmm… ki gama gulmarki, idan na fice, ki lallaba ki cinye rabin abincin warmer ɗin ki cika cikinki,” ya ɗan dakata, yana kallon yadda ta sunkuyar da kanta, kamar tana son ɓoye fuskarta daga gare shi, sai ya ɗan karkatar da kansa, murmushin gefen bakinsa bai gushe ba, “Sai na dawo kuma ki dinga noke-noke ke, wai, amarya, ba kya cin abinci… ba haka aka ce ku ke yi ba?”