Free chapter · Read without an account
THE UNSEEN LINK
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER EIGHT: 8*
*THE UNSEEN LINK*
*JIDDAAH BARKUM*
————————
Washegari da safe.
Ta kasance Asabar ce, ranar da za a yi yinin bikin Aseeya.
Sai dai, a cikin gidan Baffa babu wanda ya kuskura ya tuna da bikin, ballantana har wani ya ce zai sake zuwa.
Maganar da Baffa ya faɗa a daren jiya ta tsaya wa kowa a rai,
“Daga yau, babu wacce daga cikinku da za ta sake taka ƙafarta wani biki.”
Kalmar kamar an rubuta ta ne a bangon gidan.
Tunda gari ya waye, kowa ya kama aikin gabansa cikin nutsuwa.
Raihana kuwa, bayan ta gama gyara ɗakin da take kwana tare da na Umma, ta ɗauko manyan robobin kayan wanki.
Ta fito da kayan Aminu, ta haɗa da na Yusuf, sai kayan Umma, a ƙarshe kuma ta kawo nata.
Ta jera su tsaf a tsakiyar tsakar gidan, ta kawo bokitin ruwa, sabulai da omo ta ajiye kusa da su.
Sai dai kafin ta fara... ta ɗan tsaya.
Ta ɗaga kai ta kalli ƙofar ɗakin Baffa.
A hankali ta miƙe ta nufi ƙofar, ta tsaya a bakin labulen ɗakin, ta sauke numfashi kafin ta yi sallama.
“Assalamu alaikum, Baffa.”
Daga ciki kuwa, aka amsa cikin muryarsa mai cike da nutsuwa,
“Wa alaikumus salam. Shigo.”
A hankali ta ɗaga labulen ta shiga.
Da shiga, ta durƙusa cikin ladabi.
Ta ga Baffa zaune kan kujerarsa yana duba wasu takardu da suke zube a gabansa.
Ya ɗago kai ya kalleta.
Ta sunkuyar da kanta.
“Baffa... kayi haƙuri da abin da ya faru jiya.”
Ta haɗiye yawu, “In Sha Allah... ba za ka sake jin irin hakan daga gare mu ba.”
Shiru ya biyo baya.
Baffa bai yi magana nan take ba, sai ya ci gaba da kallonta.
Kallonsa ba na fushi ba ne, ba kuma na fara’a ba. Kallon uba ne mai ƙoƙarin fahimtar ɗansa.
Bayan wasu daƙiƙu... ya ce cikin nutsuwa,
“Ba komai. Allah Ya tsare ku. Ya kuma shirya ku.”
“Ameen,” Raihana ta amsa cikin girmamawa.
Sai ta ɗan matsa gaba kaɗan,
“Baffa...”
Ya amsa da, “Naam.”
“Dama... wanki zan yi.”
Ta ɗan yi murmushi, “Na zo na tambaya ko akwai kayan da zan wanke maka.”
Baffa ya sake yin shiru. Ya ɗan jingina bayansa da kujerar, idanunsa suna kanta.
Kafin daga ƙarshe ya ce,
“Babu, duk Hamza yayi min wanki shekaranjiya, sai waɗanda na cire jiya ne kawai.”
Ya nuna wata kujera da ke gefen ɗakin, “Ga su can.”
Raihana ta bi inda ya nuna da kallo.
Farar shaddarsa ce da ya cire daren jiya, sai wata doguwar jallabiya, da kuma hularsa.
Ya ci gaba da cewa, “Na cire su jiya ban kai su wajen Hamza ba.”
Ta yi saurin miƙewa, “Toh Baffa.”
Ta tattara kayan cikin kulawa.
A daidai lokacin ne idanunta suka sauka kan daddumarsa da aka naɗe a gefe.
Ba tare da ta tambaya ba, ta ɗauke ta ita ma.
Ta haɗa da kayan, sannan ta juya ta fita.
Har ta kai bakin ƙofa... Baffa ya ci gaba da binta da kallo.
Sai da ta ɓace daga ɗakin, ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi.
⸻
Raihana ta dawo tsakar gida.
Ta zuba ruwa cikin babban bokiti, ta jiƙa kayan farare daban, masu launi kuma ta ware su.
Ta naɗe mayafinta ta daure shi a kanta sosai, ta ɗaure zaninta da kyau, sannan ta fara wanki cikin nutsuwa.
Bayan kusan mintuna goma... Maryam ta fito daga ɗaki tana hamma.
Dogon hijabi ne a jikinta.
Ta zauna bakin dakali, ta buɗe ƙaramin mirror, ta fara tsifar dogon gashinta cikin natsuwa.
Lokaci zuwa lokaci tana kallon Raihana.
“Ray.”
“Na’am.”
“Da wuri kika fara.”
Raihana ta yi murmushi, “Yau kayan sun yi yawa.”
Maryam ta girgiza kai, “Gaskiya.”
Ba su ƙara wata magana ba.
Can ɗan lokaci kaɗan... labulen ɗakin Baffa ya motsa.
Ya fito cikin farar shadda mai kyau, hula fara ƙal, turare mai ƙamshi na tashi daga jikinsa.
Ya tsaya tsakiyar gidan.
Umma da ke kitchen ta leko ta gaishe shi, ya amsa.
Sannan ya ce, “Zan tafi ɗaurin aure.”
Umma ta amsa, “Allah Ya kai lafiya.”
“Ameen.”
Ya juya ya fita.
Bayan fitarsa... sai labulen ɗakin Mama Sabuwa ya buɗe.
Ta fito cikin wata atamfa mai launin ruwan hoda, fuskarta cike da annuri.
Kai tsaye ta shimfiɗa tabarma a tsakiyar tsakar gidan.
Ta shige ɗaki ta fito da manyan ledojin da Bintu ta dawo da su daren jiya.
Ta zauna tana buɗe su ɗaya bayan ɗaya.
Abu na farko da ta fito da shi... wasu manyan skincare products ne masu tsada:
La Mer Moisturizing Cream, Estée Lauder Advanced Night Repair Serum, Lancôme Génifique Serum, Dior Prestige Micro-Huile de Rose, har da cikakken Fenty Skin gift set.
Sai ta fito da wasu kayan kwalliya: Charlotte Tilbury Airbrush Flawless Foundation, Dior Backstage Palette, MAC Lipsticks, Huda Beauty Eyeshadow Palette, YSL Libre Eau de Parfum, Chanel Coco Mademoiselle.
Ta ɗauko su tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, idonta na ƙara cika da annuri.
Leda ta biyu... gashasshiyar kaza ce da aka shirya cikin foil pack, ragowar da suka ci jiya aka rage dan a nunawa jama’ar gidan.
Har yanzu ƙamshin kayan ƙamshi na cikinta yana tashi.
Sai wasu bottled juices masu tsada: Berri, Chivita 100%.
Sai manyan cups na yoghurt: Hollandia Greek Yoghurt, da wasu imported chocolates.
Mama Sabuwa ta kasa ɓoye farin cikinta, “Subhanallah...”
Ta faɗa tana shafa kwalbar turare.
A daidai lokacin... Mama Indo ta fito daga ɗakinta saboda surutun da ake yi.
Da ta hango kayan... sai ta tsaya cak,
“Lallai Sabuwa... duniya ta samu.”
Mama Sabuwa ta yi wata shewa,
“Haihuwa ce mai rana.”
Ta ƙara gyara zamanta, “Bintu jiya daga zuwa dinner kawai... Allah Ya haɗa ta da ɗan babban gida.”
Ta nuna skincare ɗin, “Ki duba mana. Daga haɗuwar farko... ya kashe mata wannan uban kuɗi.”
Ta ɗan rage murya tana murmushi, “Ina ga an kwana biyu.”
Mama Indo ta matso kusa, ta ɗauki kwalbar YSL Libre tana jujjuya ta a hannunta,
“Ahh... lallai. Ba shakka.”
Mama Sabuwa ta ɗaga haɓa,
“Kin san ni. ‘Ya’yana akwai farin jini.”
Ta yi murmushi mai cike da alfahari, “Allah dai Ya albarkace su.”
A gefe guda kuwa... Raihana tana ci gaba da wankinta, kamar ba ta ji ko kalma ɗaya daga cikin hirarsu ba.
Amma Maryam... ta ɗan ɗaga kai ta kalli kayan, sannan ta kalli Raihana.
Ta lura ko da sau ɗaya Raihana ba ta waiwayo ba.
Kawai ta ci gaba da wanke kayan Baffa cikin nutsuwa, ranta na neman yardar Allah da ta iyayenta fiye da duk wata kyauta da duniya za ta iya kawowa.
Mama Sabuwa ta sake ɗaga murya da gangan, tana tabbatar da duk wanda ke cikin gidan zai ji,
“Mu da ake ganin ‘ya’yanmu ba farare ba ne, ba kyawawa ba ne... gashi nan ai suna ta tashi ɗaya bayan ɗaya. Allah dai Mai iko ne. Ba wai sai farar mace ba ce take samun rabo.”
Ta sake gyara zamanta a kan tabarmar,
“Mutane dai suna raina abin da Allah Ya ba wani. Ashe ba su san Allah na raba arziki yadda Ya ga dama ba.”
Sai ta sake sakin wata shewa,
“Ni ai tun daɗewa na san Bintu ta daban ce. Allah Ya zuba mata karɓuwa. Kallo ɗaya mutum zai yi mata ya rasa kansa.”
Ta buɗe murya sosai, da gangan,
“Ai duk wanda ya ce ruwan wani ba zai tafasa ba... to nasa ko ɗumi ba zai ba.”
Kalaman nata suka ratsa cikin gidan gaba ɗaya.
A cikin kitchen kuwa, Umma na tsaye tana juyawa abincin da take dafawa.
Ta ji komai, sai dai ko kallon inda muryar take fitowa ba ta yi ba.
Ta sauke numfashi kawai a hankali, ta ci gaba da abin da ke gabanta.
Mama Indo kuwa ta saki dariya,
“Kaii Sabuwa... kina da son ƙananan magana wallahi.”
Mama Sabuwa ta juya ta kalleta da gefen ido,
“Ke ni barni kawai. Kin san ni ban iya munafurci ba. Ban iya fuska biyu ba. Abin da yake zuciyata shi nake faɗa. Ba na tsoron uban kowa.”
Mama Indo ta ɗan gimtse fuska,
“Kar dai ki zageni ni fa. Wallahi ni ba ruwana.”
“Mts*** Mama Sabuwa ta buga tsaki,
“Ke ma kin san gaskiya. Amma dai mutane ba sa son a faɗa musu.”
Ta sake sunkuyawa kan kayan.
Ta ɗauki wani kwalin skincare ta juya shi gefe da gefe,
“Ki duba wannan mana. Wannan kaɗai ma kuɗinsa ba ƙarami ba ne. Ga turare, ga kayan makeup, ga body lotion... duk original.”
Ta ɗauki wani perfume ta buɗe.
Da ta fesa kaɗan a iska, ƙamshi ya gauraye ko’ina cikin tsakar gidan.
“Hmmm...” ta lumshe ido tana shaƙar ƙamshin,
“Wallahi kuɗi suna magana a nan.”
Ta ajiye shi, sannan ta janyo ledar abinci.
Da ta buɗe, gasasshiyar kazar da sauran nama, tare da ledojin yogurt da juice masu tsada.
“Lallai wannan yaron ya san yadda ake kula da mace.”
Ta ɗauki cinyar kazar ta cire ɗan nama da haƙora,
“Tunda safe ban karya ba ma.”
Ta sake cizon wani yanki tana tauna shi cikin jin daɗi.
“Bintu!” ta kira da ƙarfi.
Bintu ta fito daga ɗaki tana mika alamar kasala,
“Na’am Mama.”
Mama Sabuwa ta miƙa mata kwalin juice,
“Zo ki zauna mu karya tare. Ai irin waɗannan abubuwan ba a ɓoyewa. Allah idan Ya yi maka baiwa, sai ka gode masa.”
Bintu ta zauna tana murmushi.
Idanunta cike suke da alfahari yayin da take kallon kayan da aka kawo mata.
A gefe guda kuma, Raihana da Maryam suna ci gaba da abin da suke cikin nutsuwa.
Sun ji duk abin da ake faɗa.
Maryam ta ɗan ɗago kai, idanunta suka sauka kan Mama Sabuwa, sannan ta sake maida hankalinta kan tsifarta ba tare da ta ce komai ba.
Raihana kuwa, ko daƙiƙa ɗaya ba ta ɗaga kanta ba.
Ta ci gaba da murza kayan Baffa cikin natsuwa, kamar ba ta ji komai ba.
Sai dai a zuciyar Umma... kalaman Mama Sabuwa sun sauka da wani irin nauyi.
Ba don sun ɓata mata rai saboda magana ba, sai don tana jin tsoron irin hanyar da ake fara jan Bintu a hankali, ba tare da ita kanta ta lura ba.
⸻
Wajen ƙarfe goma sha biyu na rana... Baffa ne ya shigo gidan.
Da sallama ya ƙaraso cikin tsakar gidan, hannunsa riƙe da wata brown envelope, yayin da wani irin annuri ya bayyana a fuskarsa.
Tun daga nesa, za ka fahimci cewa akwai wani abu mai daɗi da ya faru.
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.”
Kowa ya amsa masa.
A lokacin, kusan duk mutanen gidan suna tsakar gida.
Mama Indo da Mama Sabuwa suna zaune kan tabarma suna hira.
Umma kuma ta fito daga kitchen tana goge hannuwanta da ƙaramin tawul.
Raihana ta riga ta gama wankin tun da safe. Har ta yi wanka, ta canza kaya cikin doguwar riga mai sauƙi. A lokacin tana zaune a kan kujera tana gyara farcen hannunta.
Maryam kuma tana gefe tana taya Yusuf da Aminu gyaran littattafansu.
Baffa ya cire hularsa ya ajiye a gefe.
Sannan ya zauna kan tsohuwar kujerarsa da ke ƙarƙashin bishiyar mangwaro.
Har yanzu murmushi bai bar fuskarsa ba.
Ya kalli iyalansa ɗaya bayan ɗaya, sai ya ce cikin annashuwa,
“Albishirinku.”
Nan take kowa ya ɗago.
“Mun amsa da goro,” Mama Indo ta fara faɗa tana murmushi.
“Meye albishir ɗin Malam?”
Baffa ya ɗan gyara zamansa.
Ya sauke numfashi cikin godiya,
“Alhamdulillah... Allah Ya amsa addu’armu.”
Duk suka zuba masa ido.
“Na samu wani aiki.”
Nan take tsakar gidan ya kaure da,
“Alhamdulillah! Masha Allah! Allah Ya ƙara buɗi.”
Baffa ya yi murmushi,
“Wannan aikin da na samu... ina saka ran zai fi wanda nake yi yanzu sauƙi, kuma albashinsa ma ya fi.”
Sai ya ɗaga brown envelope ɗin da ke hannunsa.
“Kun san kwanakin baya da na ce na kai takarduna neman aiki?”
Duk suka gyada kai.
“An ce za a kira ni interview.”
Ya ɗan yi shiru, “Sai yau ina wajen daurin aure aka kirani na je... aka ce ma ba sai na yi interview ba.”
Kowa ya ƙara zuba masa ido.
“An riga an amince da ni.”
Mama Indo ta dafe ƙirji, “Subhanallah!”
Mama Sabuwa ta yi saurin cewa,
“Allah Sarki! Allah da girma yake.”
Baffa ya buɗe envelope ɗin.
Ya ciro takardar appointment letter,
“An ɗauke ni a matsayin Administrative Store Officer. Zan riƙa kula da kayan da ke shiga da fita daga babban store na kamfanin, tare da rubuta bayanansu.”
Ya yi murmushi, “Ba wani aiki ne mai wahala ba. Kuma albashin ma ya fi wanda nake samu yanzu.”
Umma ta ɗaga hannayenta sama,
“Alhamdulillahi Rabbil Aalameen. Allah Ya sanya alkhairi. Allah Ya sa ya zama buɗin alheri.”
“Ameen.”
Kowa ya amsa.
Aminu ya yi tsalle yana murna,
“Baffa ya samu sabon aiki!”
Yusuf ma ya fara dariya yana tafa hannu.
Maryam ta yi murmushi, “Congratulations, Baffa.”
Raihana kuwa... tun da ta ji labarin, murmushi ya bayyana a fuskarta.
Ta miƙa hannu ta karɓi takardar daga hannun Baffa domin ta gani.
Idanunta suka sauka kan saman letterhead ɗin:
*ARMAAN GROUP OF COMPANIES*
Ta tsaya cak.
Murmushinta ya ɗan lafa.
Ta sake karanta sunan, “A ina na taɓa jin wannan sunan?”
Ta tambayi kanta a zuciya.
Ta yi ƙoƙarin tuna wani abu, sai dai... komai ya ƙi dawowa mata.
Kawai ta ji kamar sunan ya saba da kunnenta, amma ta kasa tuna daga ina.
Ta ɗan girgiza kanta a hankali,
“Na manta.”
Ta maida takardar hannun Baffa tana murmushi,
“Masha Allah, Baffa. Allah Ya sanya alkhairi.”
Baffa ya karɓi takardar yana murmushi,
“Ameen, ’Raihanatu.”
Tsakar gidan ya sake cika da farin ciki.
Kowa na taya Baffa murna, ana ta addu’o’i, ana ta godiya ga Allah.
—————————
Da yamma wajen ƙarfe uku...
Raihana na zaune a kan laushin carpet ɗin falon Umma.
A gabanta kuwa... Umma ce ta kwanta tana jingina da cinyarta.
Raihana na tsife mata kai a hankali.
Kowane sashe na gashin sai ta raba shi da nutsuwa kafin ta taje mata.
Falon ya yi shiru, sai ƙamshin man kitson da Raihana ta shafa wa hannunta da ƙaramar hirar da suke yi lokaci zuwa lokaci.
Can... Raihana ta ɗan yi shiru.
Sai ta ce, “Hmmm... Umma.”
Umma ta ɗan ɗago kai kaɗan,
“Lafiya? Mene?”
Raihana ta ci gaba da tsifar gashin kafin ta ce,
“Umma... tunda da muka je wajen bikin nan... Bintu ba ta sake ko kallonmu ba. Kamar ba tare muke ba. Ta makale wa wasu ’yan mata, sai binsu take yi.”
Ta ɗan yi shiru, sannan ta ci gaba,
“Har a ƙarshe ma da muka ce ta zo mu tafi... ta ce mu yi tafiyarmu. Ita za ta taho.”
Ta sauke numfashi,
“Kin ji... ashe har saurayi ta yi. Shi ne ya kawo ta gida. Shi kuma ya siya mata waɗancan kayan.”
Umma ba ta ce komai ba, sai ta yi shiru tana sauraron ’yarta.
Bayan wasu daƙiƙu... sai murmushi ya suɓuce mata.
Ta ce a hankali,
“Tunda dai ta dawo lafiya... itama ai shi kenan.”
Kafin wani daga cikinsu ya sake magana... sai suka ji sallama daga ƙofar falon,
“Assalamu Alaikum.”
“Wa Alaikumus Salam.”
Maryam ce ta shigo.
Sanye take da uniform ɗin Islamiyya.
Sky blue riga ce da wando, rigar ta zo har kusa da gwiwa.
Hijab ɗinta kuwa ya sha guga.
Ta ƙaraso cikin falon, ta durƙusa ta gaida Umma.
Daga nan ta juya ta kalli Raihana.
“Ray... wai baki shirya ba? Ba za ki Islamiyya ba ne?”
Raihana ta ɗago tana kallonta.
Maryam ta ci gaba,
“Malam Habu fa yau zai karɓi hadda. Kin ji dai abin da ya faɗa mana ranar Laraba. Dama mun ba shi uzuri cewa za mu je biki. Tunda kuma ba mu je ba... ai gwara mu je ko?”
Raihana ta zuba mata ido, sai ta ce,
“Ke ni fa kina kallo. Yanzu na yi wanki. Saboda ban san za mu je ba. Kayan uniform ɗin ma babu guga. Duk sun yi squeezing. Ni wallahi ba zan iya fita da su a haka ba.”
Kafin Maryam ta yi magana... Umma ta katse su cikin sanyin murya,
“Haba... ko da kayan gida ne... ki daure ku je. Sai ki faɗa wa Malam uzurinki. Ai ba dukan uniform yake ba.”
Maryam ta ce,
“Karaf! Ina da babban hijab ma, wanda har ƙasa yake. A goge yake. Bari na kawo miki.”
Ba ta jira amsa ba.
Da gudu ta juya... ta fice daga falon.
————————
Bayan Raihana da Maryam sun tafi Islamiyya...
Umma ta idar da sallar La’asar.
Har yanzu tana zaune a kan sallayarta. Ba ta tashi daga inda take ba.
Ta ɗaga hannayenta sama, ta yi doguwar addu’a cikin nutsuwa.
Da ta shafa addu’ar a fuskarta... sai aka yi sallama a ƙofar ɗakinta.
“Assalamu Alaikum.”
“Wa Alaikumus Salam.”
Mama Indo ce ta shigo.
Ta ƙarasa cikin ɗakin, ta ja wata kujera ta zauna a gefe.
Ta kalli Umma,
“Sallah ake kenan?”
Umma ta ɗan jinjina kai,
“Na idar ma.”
Mama Indo ta yi murmushi,
“To Madallah. Allah Ya amsa.”
“Ameen.”
Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu.
Sai Mama Indo ta ɗan matsa kusa, ta rage murya,
“Hajara... shawarace da ni.”
Umma ta ɗaga kanta tana kallonta,
“To... ina jinki.”
Mama Indo ta sake rage murya kamar mai tsoron kada wani ya ji,
“Kin ga dai ni... yara biyu kaɗai Allah Ya ba ni. Daga Fauziyya sai Maryam. Na samu Fauziyya ta yi aure da ƙyar. Duk da uban asirin da Sabuwa ta dinga banka mata kar ta auru. Yanzu saura Maryam.”
Ta ɗan yi shiru, sannan ta ci gaba,
“Ke ma kuma kina da macen nan... Raihana. Kin ga su kaɗai ne suka rage mana. Tunda ita fa ta aurar da ‘ya’yanta. Sai Bintu kaɗai. Ga dukkan alamu ma... Bintu ba za ta wani daɗe ba. Itama za ta tashi.”
Ta ɗan matso gaba,
“Shi ne nace... ko za mu nema wa Raihana da Maryam taimako ne? Mu samu duk su tashi tare da Bintu.”
Ta ƙanƙance idanunta,
“Kin san wallahi... idan Bintu ta riga namu ya’yan aure... kashinmu ya bushe a wajen Sabuwa.”
Ta yi ƙaramar dariya,
“Ko akwai masu taimako da kika sani a yankinku can Nijar? Ni ko nawa ne... sai mu haɗa. Mu samu a taimaka mana.”
Ta ƙarasa cikin murya can ƙasa.
Umma kuwa... tun daga farkon maganar Mama Indo sai kawai take kallonta.
A ranta kuwa,
“Subhanallah... lallai Indo inde kissaa ce, ta zarce tunanin mutane.”
Amma duk da haka... fuskarta ba ta nuna komai ba.
Sai murmushi kaɗai ta yi, ta ce cikin nutsuwa,
“A’a Indo. Wallahi babu wani taimako. Aure lokaci ne da shi. Idan lokacin Raihana da Maryam ya yi... za su yi. Kuma idan bai yi ba... ko an tara duk duniya, ba za a iya ɗaura musu aure ba.”
Mama Indo ta yi shiru tana sauraronta.
Umma ta ci gaba da magana cikin hikima,
“Kin san abin da mutane da yawa ba sa fahimta?”
Mama Indo ta girgiza kai.
Umma ta yi murmushi,
“Kamar yadda Allah Ya rubuta ranar haihuwar mutum... haka Ya rubuta ranar aurensa. Ba wanda zai iya gaggauta abin da Allah Ya jinkirta. Ba wanda kuma zai iya jinkirta abin da Allah Ya ƙaddara.”
Ta ɗan yi shiru, sannan ta sake cewa,
“Mu aikinmu shi ne mu tarbiyantar da ‘ya’yanmu. Mu koya musu addini. Mu yi musu addu’a. Mu kuma zaɓa musu abin da ya dace idan lokacin ya yi. Amma ba mu ne za mu tilasta musu ƙaddararsu ba.”
Mama Indo ta lumshe ido tana jin maganar.
Umma ta ƙara da cewa,
“Kuma ki tuna... ba kowanne wuri da ake gaggawar shiga ne alkhairi yake ciki ba. Wani lokacin jinkiri shi ne rahamar Allah. Wani lokacin kuma abin da muke ganin ya makara... ashe Allah yana kare mutum ne daga abin da bai sani ba.”
Ta yi murmushi,
“Saboda haka... ki bar komai a hannun Allah. Lokacin Maryam idan ya yi... ko ba tare da kin nema mata taimako ba, mijin da Allah Ya rubuta mata... shi zai zo ya neme ta.”
Mama Indo ta sauke numfashi.
Ta girgiza kai a hankali,
“Wallahi Hajara... duk lokacin da na zo wajanki... sai na koma da wani sabon darasi.”
Umma ta yi murmushi,
“Mu dai ci gaba da addu’a. Allah Ya zaɓa musu mafi alkhairi.”
“Ameen.”
Mama Indo ta amsa da zuciya daya…
***