Free chapter · Read without an account
THE PATHS DESTINY CHOSE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER-THIRTEEN:13*
*THE PATHS DESTINY CHOSE*
*JIDDAAH BARKUM*
⸻
Bayan fitar Baffa Musa daga ɗakin…
Umma ta ɗan raka shi da kallo kafin ta maida idanunta kan Raihana, ta yi murmushi a hankali.
A zuciyarta ta san babu wani hukunci da mijinta yake yankewa face bayan ya tabbatar da komai zuciyarshi tayi Naam da abun,
domin Baffa Musa ba mutum ne mai son gaggawa ba, tun yana matashi… haka yake.
⸻——-
*SHIN MA MEYE ASALIN BAFFA MUSA NE??*
*WAIWAYE ADON TAFIYA…*
Baffa Musa ɗan asalin garin Makarfi ne da ke jihar Kaduna, a can aka haife shi, a can ya tashi cikin tarbiyyar addini da sana’a.
Yayi karatun zamani har zuwa matakin degree, saidai baiyi aikin gwamnati ba, ya kama sana’ar gidansu, ita ya sani, ita ya tashi ya gani ana yi, dan haka shima ita yayi.
Marigayi mahaifinsa fitaccen mai haɗa turare ne, sana’ar turare ce ta ɗauki nauyin gidansu tsawon shekaru.
Ba arziki mai yawa ba ne… amma ba su taɓa rasa abin da za su ci ba.
Mahaifiyarsu… Inna Salamatu, mace ce mai tsananin haƙuri da juriya.
Allah Ya azurta ta da ’ya’ya maza biyu kacal.
Na fari… shi ne Baffa Musa, sai ƙaninsa.
Amma shekaru da dama da suka wuce… ƙanin nasa an kai shi jihar Yobe almajiranci, tun daga ranar… bai ƙara dawowa gida ba.
Ba a san inda ya shiga ba, an yi nema, an yi tambaya, har aka kai ga yanke ƙauna.
Batan kaninshi ba dadewa Allah Ya yi wa mahaifinsa rasuwa.
Tun daga wannan lokaci… Baffa Musa ya zama ɗa tilo ga Inna Salamatu, kuma ita ma duk soyayyarta da kulawarta ta koma kansa.
Da ya kai lokacin aure… Inna Salamatu ce ta zaɓo masa mata, Mama Sabuwa.
Ba baƙuwa ba ce a wajenta, ’yar gidan ƙaninta ce, yar ta ce ta jini, saboda haka… tun kafin aure ma tana matukar sonta.
Bayan auren… soyayyar ta ƙara ƙarfi, har ta kai matsayin da duk gidan ya sani.
Baffa Musa ba shi da ikon ɗaga murya a kan Mama Sabuwa idan Inna Salamatu tana nan.
Idan Mama Sabuwa ta kai ƙorafi wajen Inna… to magana ta ƙare, ko Baffa Musa ya na da gaskiya haka zai dauki laifi dan inna bata ganin laifin sabuwa ko kadan, sai ya yi shiru domin girmama mahaifiyarsa.
Abin da Mama Sabuwa ta faɗa… a wurin Inna Salamatu kamar hukunci ne da aka riga aka yanke.
⸻
Auren nasu ya kasance na soyayya da fahimtar juna a farkonsa, Allah Ya albarkace su da ’ya’ya biyar.
Babba ita ce Sadeya, tana aure a jihar Niger.
Sai Maryam, ita kuma tana zaune da mijinta a Katsina.
Sai Shafiu, yana zaune a Legas, an ce kasuwanci yake yi, sai dai… ba kasafai yake dawowa gida ba, wani lokaci har shekara ta zagayo ba tare da an gan shi ba.
Sai Hamza, shi ne ginshiƙin gidan, kuma mafi kusanci da Baffa Musa cikin yaran.
Sai autarsu… Bintu.
A idanun mutane… Mama Sabuwa mace ce mai shige shige.
Ba ta gajiya da zagayawa wajen malamai, duk wanda ya zauna da Mama Sabuwa ya santa da wadannan halayen: hassada, kishi, munafunci, son a ce ita ce ta fi kowa.
Ba ta son ganin wani ya samu wata ni’ima sai dai idan za a ce ta hannunta aka samu, ko da mutum ya samu wani alheri da ƙoƙarinsa… zuciyarta ba ta samun natsuwa har sai mutane sun danganta wannan alherin da ita.
Wannan hali nata… ba kowa ne ya fahimce shi ba, sai waɗanda suka daɗe suna rayuwa kusa da ita.
Bayan shekaru kaɗan da aure… sai Baffa Musa ya dan samu aikin gwamnati, amma duk da haka bai bar kasuwancin turare ba, yana yi a ranakun da baya zuwa aiki.
Aikin Baffa Musa ya kawo shi Kaduna, daga nan ne ya tattara iyalinsa, suka bar garinsu na Makarfi, suka fara sabuwar rayuwa a cikin birnin Kaduna… ba tare da sun san cewa wannan hijirar ce za ta buɗe sabon babi na rayuwarsu ba.
Sai dai… ba komai ne ya kasance daidai ba a cikin gidan.
A hankali… wasu halayen Mama Sabuwa suka fara bayyana bayan shekaru da aure, kishi mai tsanani, son a bi nata, rashin haƙuri, da kuma yawan ɗaukar zance zuwa wajen Inna Salamatu.
Saboda tsananin girmamawar da Baffa Musa yake yi wa mahaifiyarsa… ya daɗe yana danne komai a zuciyarsa.
Sau da yawa idan Mama Sabuwa ta kai ƙara… ko da Baffa Musa ne yake kan gaskiya… Inna Salamatu ba ta barin maganar ta tsaya sai ya ba Mama Sabuwa haƙuri.
Shekaru suka ja, har wata rana… Baffa Musa ya kira Inna Salamatu cikin ladabi, ya zauna gabanta, ya ce cikin nutsuwa,
“Inna… na yi haƙuri shekaru da yawa saboda ke. Amma ina jin ba zan iya ci gaba haka ba.”
Inna ta ɗago cikin mamaki,
“Me kake nufi?”
Ya sauke numfashi,
“Ina son ƙara aure.”
Kalmar ta faɗi kamar tsawa.
Mama Sabuwa kuwa… da labari ya kai kunnenta, gidan ya rikice, ta yi kuka, ta dau fushi, ta nemi ta hana shi.
Amma wannan karon… Baffa Musa bai ja da baya ba.
A ƙarshe… ya auri Mama Indo.
Da farko… Mama Indo ta shigo gidan da ƙudirar kare hakkinta, an fara buga kishi, an yi gardama, an yi gwabza ido da ido.
Amma ba daɗewa ba… ta gano cewa Mama Sabuwa tana da babban garkuwa, Inna Salamatu.
Duk wata gardama… Inna tana tsayawa ne a bayan Mama Sabuwa.
Mama Indo ta fahimci cewa faɗa ba zai kai ta ko’ina ba, daga wannan rana… ta sauya salonta, ta fara nuna biyayya ga Mama Sabuwa.
Komai Mama Sabuwa ta faɗa… sai ta ce,
“Haka ne.”
Idan ta ba da shawara… sai Mama Indo ta amince.
A idon mutane… kamar babu kishi tsakaninsu, amma a zahiri… kishin bai mutu ba, sai dai ya koma ƙarƙashin ƙasa, kowa na taka-tsantsan da ɗayan.
Ba a sake samun hayaniya ba… amma zuciya… Allah kaɗai Ya san abin da take ɓoye.
Allah Ya albarkaci Mama Indo da diya mace, Fauziyya.
Bayan haihuwarta ba daɗewa ba… wata tafiya ta sauya rayuwar Baffa Musa gaba ɗaya.
A wancan lokacin… Baffa Musa ya tafi Jamhuriyar Nijar domin kasuwancin turare, ba wannan ne karon farko da ya je ba, domin ana matuƙar son turarensa a can.
Bai je da niyyar neman aure ba, ko kaɗan.
Sai dai… ƙaddara tana da nata shirin.
A cikin ɗaya daga cikin manyan gidajen sarauta da yake kai wa turare… ya haɗu da wata budurwa, mai kamala, mai nutsuwa, mai cike da kunya da tarbiyya.
’Yar asalin gidan sarauta ce, sunanta… Hajara.
Tun farkon haɗuwarsu… ba ta ce masa komai ba, sai dai halayensa, gaskiyarsa, da mutuncinsa… suka mamaye zuciyarta.
Kwana suka zama makonni, a duk lokacin da Baffa Musa zai kai kaya… sai ta nemi wata hanya ta gaida shi cikin mutunci.
Har wata rana… ta bayyana wa iyayenta abin da ke cikin zuciyarta,
“Shi nake so.”
Fadar ta kaɗu.
Ta yaya ’yar gidan sarauta… za ta auri ɗan kasuwa daga wata ƙasa?
An yi ta lallashi, an yi kokarin hanata, amma ta nace.
Daga ƙarshe… mahaifinta ya kira ta, ya ce cikin murya mai cike da iko,
“Idan wannan shi ne zaɓinki… ba za mu hana ki ba.”
Ya ɗan dakata,
“Amma ki sani… da zarar kin bi mijinki ki bar wannan ƙasa… kada ki sake dawowa da sunan zama. Ko bakin border ɗin Nijar… ba za ki ƙara takawa ba.”
Ɗakin ya yi tsit.
Hajara ta runtse idanunta, ta san girman abin da ake nufi, za ta bar iyayenta, za ta bar sarauta, za ta bar ƙasar da aka haife ta, har abada…
Amma duk da haka… ta ɗago kanta cikin natsuwa, ta ce,
“Na amince.”
A wannan rana… ba Hajara kaɗai ta yanke shawara ba… ƙaddara ma ta fara rubuta sabon babin rayuwar Baffa Musa… da kuma zuwan wadda daga baya za ta zama Umman Raihana.
Auren ya gudana cikin sauƙi, ba a yi wata hayaniya ba, ba a yi wani bikin da ya ɗauki hankali ba.
Baffa Musa ya ɗauko amaryarsa… ya nufi Kaduna, bai sanar da kowa ba.
Sai dai… ranar da ya taka ƙofar gidansa tare da sabuwar matarsa… kamar ya jefa garwashi cikin busasshiyar ciyawa.
Gidan ya rikice.
Mama Sabuwa ta rasa abin yi.
Tun daga nesa… da idanunta suka sauka kan Hajara… zuciyarta ta karye.
Ba wai don Baffa ya ƙara aure kaɗai ba… sai don kyawun Hajara.
Doguwa ce, farar fata mai ɗaukar ido, siffarta irin ta ’yan gidan sarauta, akwai nutsuwa da annuri a tare da ita.
Ko ba ta yi kwalliya ba… mutum zai tsaya yana kallonta.
Mama Sabuwa ta ji kamar an zo da wadda za ta kwace mata komai.
Da gudu ta nufi wajen Inna Salamatu, ta fara da kukan rashin hankali da ƙorafi, da zuga mai mugun zafi, sai ta cika kunnen tsohuwar da maganganu iri-iri.
Har abin ya kai… Inna Salamatu ta kusa yi wa Baffa Musa baki saboda wannan auren.
Tun daga wannan rana… rayuwar Hajara ta sauya.
Ba a yi mata maraba irin ta sabuwar amarya ba, maimakon haka… an tarbe ta da ƙyara, da tsangwama, da maganganu masu zafi, da nuna mata cewa ba a son zamanta a gidan.
Ko ta yi shiru… laifi ne, ko ta yi magana… laifi ne, idan ta yi girki… a ce ba ta iya, idan kuma ta ƙi shiga harkar wani… a ce girman kai take yi.
A hankali… ta fara shiga matsin lamba.
Sau da yawa idan dare ya yi… sai ta zauna ita kaɗai tana kuka, har ta kai ga tunanin… ko ta gudu ta koma ƙasarta? Ko da kuwa hakan yana nufin ta rasa komai?
Amma duk lokacin da ta kalli Baffa Musa… sai zuciyarta ta sake ƙarfafa, ta san yana ƙaunarta, kuma ita ma tana sonsa, saboda haka… ta zaɓi haƙuri, ta zaɓi juriya.
Ba da daɗewa ba… Allah Ya azurta ta da juna biyu.
Sai dai… saboda tsoron abin da zai biyo baya… ta ɓoye cikin nata.
Ko da Baffa Musa ya fahimta… bai bari labarin ya fita ba, haka suka ci gaba da ɓoyewa, har cikin ya kai wata shida.
Amma daga ƙarshe… asiri ya tonu.
Nan ma… an sake tada ƙura, an yi maganganu, an yi gulma, an yi zargin cewa ta ɓoye cikin ne da wata manufa.
Hajara kuwa… ta yi shiru, domin ta san ba kowace magana ce ake amsawa ba.
Bayan watanni… Allah Ya sauke ta lafiya, ta haifi kyakkyawar diya, Raihana.
Kamar yadda ƙaddara ta tsara… watanni biyar kacal bayan haihuwar Raihana… Mama Indo ma ta haifi Maryam.
Rayuwa ta ci gaba.
Daga baya… Allah Ya sake azurta Hajara da yara biyu maza, Yusuf, sai Aminu.
Duk da ƙarin ’ya’yan… gidan bai taɓa rasa ɗanɗanon rikici ba.
Wata rana… a zauna lafiya, kowa na dariya, kowa na cin abinci tare, washegari kuma… sai wata ƙaramar magana ta rikide ta zama babbar matsala.
Haka rayuwa ta kasance a gidan Baffa Musa.
Gidan da suke zaune kuwa… ba wani katafaren gida ba ne, gida ne irin na tsohuwar unguwar Malali, mai sauƙi… yana dan kamar bangare ne dai guda uku amma duk tsakar gida daya ne, kowacce kafarta ta daki a tsakar gidan take, dan haka kowa na ganin kowa.
Kowane sashe na ɗauke da ƙaramin falo da dakunan kwana biyu, ɗaya daga cikin dakunan yana da bandaki a ciki, kowane sashe na da kitchen ɗinsa, a tsakar gida kuma akwai babban bandaki da ake amfani da shi tare.
A gefe guda… akwai ɗakin Baffa Musa, sai kuma wani ɗaki kusa da gate wanda samarin gidan ke amfani da shi, har ila yau… akwai wani ƙarin ɗaki da ake ajiye shirgin gidan.
Ba gidan masu kuɗi ba ne… amma ba gidan talauci ba ne.
Baffa Musa mutum ne mai ƙoƙarin ciyar da iyalinsa, bai taɓa wasa da ilimin ’ya’yansa ba, abinci, makaranta, sutura, magani… duk gwargwadon ƙarfinsa yana cikawa.
Sai dai… akwai abu guda da yake raunana gidan.
Ko da yake Baffa Musa ba mutum ba ne mai saurin yarda da jita-jita, idan aka ci gaba da cika masa kunne a kan Hajara, wani lokaci fushinsa kan rinjayi natsuwarsa, ya kan yanke hukunci cikin fushi, daga baya kuma… ya yi nadama, ko kuma wani lokacin si banko masa asirin da zai kasa controlling kanshi sai ya ci mata mutunci.
Mama Indo kuwa… ita ce wadda ba kowa ya iya karantar zuciyarta ba.
Wata rana… za ka rantse ita ce mafi son Hajara a gidan, washegari kuma… za ka ji tana goyon bayan Mama Sabuwa, ba ka taɓa sanin inda ta dosa ba.
Ba ta da yawan faɗa, ba ta da hayaniya, amma zuciyarta… sirri ce.
Shi ya sa… a gidan Baffa Musa… kowa yana rayuwa ne da taka-tsantsan, domin babu wanda ya san abin da gobe za ta haifa.
*CIGABAN LABARI*
Safiyar Asabar… ranar da Raihana ta daɗe tana jira.
Tun kafin fitowar rana dadewa ta idar da sallarta, ta daɗe tana zaune kan sallaya tana maimaita speech ɗinta a hankali.
Duk da ta haddace shi tsaf… har yanzu zuciyarta na bugawa, ba ƙaramin nauyi ba ne, yau ba kanta kaɗai za ta wakilta ba, za ta wakilci College of Medicine gaba ɗaya.
A cikin ɗakin Umma… akan gadonta, an shimfiɗa wata kyakkyawar abaya mai launin deep emerald green, wadda aka yi da lafiyayyen Dubai silk.
Abayar ba ta da yawan ado, sai ɗan aikin stones masu matuƙar ƙanƙanta da aka jera daga kafadu zuwa hannuwa, suna walƙiya a hankali duk lokacin da haske ya sauka a kansu.
Wide sleeves ɗinta sun sauko cikin tsari, ƙasan abayar kuma ya yi flowing sosai, yana ƙara mata armashi idan mutum ya kalle ta.
A gefenta kuwa… veil ne mai tsayi, mai launin iri ɗaya, an yi masa siririn embroidery na azurfa a gefuna, simple… amma yana kururuwa da elegance.
Raihana ta saka abayar cikin nutsuwa, ta ɗora veil ɗinta yadda ya rufe jikinta gaba ɗaya.
Ba ta yi makeup mai yawa ba, sai powder kaɗan, lip balm mara launi, da siririn kajal da ya fito da kyawawan idanunta.
Da ta tsaya gaban mirror… Umma ta ɗan tsaya tana kallonta, wani irin murmushi ya bayyana a fuskarta,
“Masha Allah... kin yi kyau.”
Raihana ta yi murmushi tana sauke idanunta,
“Nagode Umma.”
Umma ta ƙaraso gabanta, ta gyara mata veil ɗin da kanta, ta dafa mata kafaɗa,
“Ki tuna... confidence ba yana nufin rashin tsoro ba ne. Confidence yana nufin ki yi abin da ya dace duk da kina jin tsoro.”
Raihana ta gyada kai,
“In sha Allah.”
A dai-dai lokacin… Maryam ta shigo ɗakin da sauri, da idonta ya sauka kan Raihana… sai ta tsaya cak,
“Subhanallah...” ta ƙaraso kusa da ita tana zagayawa tana kallonta,
“Wallahi Rayy... yau kin yi wani irin kyau. Abayar nan ta yi miki wani irin kyau kamar an ƙera ta ne saboda ke.”
Raihana ta yi dariya tana girgiza kai,
“Ki daina fa.”
Maryam ta riƙe hannunta,
“A’a. Wlh da gaske.”
Sannan ta waigo ta kalli Umma,
“Umma... ni ma ina son zuwa. In ga speech ɗinta.”
Umma ta yi murmushi,
“Ni ba ni da matsala. Amma ki je ki nemi izinin Mama Indo.”
Maryam ta yi saurin gyada kai,
“To.”
Ta fito zuwa tsakiyar gidan.
A can ƙarƙashin inuwar mangwaro… Mama Indo da Mama Sabuwa ne zaune, kowacce a gabanta da aikinta.
Mama Indo na tsince zogale a wani babban kwando, Mama Sabuwa kuwa na ware kayan miya cikin nutsuwa.
Maryam ta ƙarasa cikin ladabi, ta durƙusa, ta kalli Mama Indo,
“Mama... ina so in raka Raihana makaranta. Yau za ta yi speech.”
Mama Indo ta ɗago ta kalle ta, ta yi murmushi mai laushi,
“Shi kenan. Ki je mana. Allah Ya ba ta sa’a.”
Fuskar Maryam ta washe,
“Nagode Mama.”
Mama Sabuwa kuwa… tun farkon maganar bata ce komai ba, sai kawai ta ɗaga idanunta ta kalli Maryam da Raihana da ke tsaye daga nesa cikin abayar kore mai matuƙar kyau, taɓe baki kaɗan, ta sake maida hankalinta kan aikin gabanta, kamar dai babu abin da ya faru.
Maryam kuwa… ba ta ko kula da yanayin da Mama Sabuwa ta nuna ba, ta juya da sauri tana murmushi, ta koma ɗakinta dan tayi maza ta shirya.
————————-
*ARMAAN MANSION*
Safiyar Asabar… tun kafin ƙarfe tara na safe… Armaan Mansion ya riga ya shiga yanayin motsi.
Ma’aikata na kai da kawo cikin tsari, motoci an goge su suna jere suna walƙiya, security guards na tsaye cikin cikakken shiri.
Yau ba ranar meeting ba ce, ba kuma ranar signing contract ba ce, ranar da Armaan Group zai ƙaddamar da sabon Medical Simulation Laboratory tare da gudanar da babban Medical Outreach a College of Medicine.
A saman bene… Zayd ya fito daga dakin Ummie ya yi mata sallama.
Sanye yake cikin perfectly tailored charcoal grey three-piece suit, farar shirt mai tsananin tsafta, dark burgundy tie, black Italian leather shoes masu walƙiya, agogon da ke hannunsa kaɗai ya isa ya nuna matsayin mutumin da yake.
Duk da haka… fuskarsa ba ta da wata alamar farin ciki, yana nan dai kamar ko yaushe, ba yabo ba fallasa.
Ya sauko matakalar mansion cikin nutsuwa, kamar kullum… duk ma’aikacin da ya haɗu da shi sai ya gaishe shi cikin girmamawa,
“Good morning, sir.”
“Morning,” ya amsa cikin taƙaitacciyar murya.
Da ya isa falo… ya ɗauki key ɗin motarsa daga kan console table.
A dai-dai lokacin… wata murya ta fito daga bayansa,
“Akhii...”
Zayd bai ma waigo ba, ya riga ya san mai muryar,
“Suhaila.”
Ta ƙaraso gabansa tana murmushi, ita ma cikin shiri take, sanye take da wata elegant sky-blue abaya mai sauƙin ado, veil ɗinta ya yi mata matuƙar kyau, a hannunta kuma akwai ƙaramin designer handbag.
Ta haɗe hannayenta tana kallonsa,
“Ni ma zan raka ka.”
Zayd ya ɗaga gira,
“Raka ni?”
Ta gyada kai da sauri,
“Eh. Please. Na daɗe ban fita tare da kai ba.”
Ya girgiza kai cikin natsuwa,
“Suhaila... business event ne. Ba picnic ba ne.”
Ta turo baki,
“Na sani. Shi ya sa ma nake son zuwa. Medical students ne ko? Ina son ganin programme ɗin.”
Ta ƙara matsowa kusa da shi,
“Please Akhii... wallahi ba zan dame ka ba. Zan zauna daidai inda za a nuna min.”
Zayd ya sauke ajiyar zuciya, ya san halin ƙanwarsa, idan ta dage akan abu…
Ya ɗan lumshe idanunsa,
“Kin gaya wa Ummie?”
Ta yi saurin gyada kai,
“Eh. Ta ce idan kai ka amince babu matsala.”
Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ya ce,
“Fine. Five minutes. Ki tabbata kin gama komai.”
Fuskar Suhaila ta haskaka,
“Really?”
Zayd ya kalle ta,
“Don’t make me change my mind.”
Ta yi saurin dariya,
“No! Two minutes ma sun isa.”
Ta juya da gudu zuwa sama.
Zayd ya girgiza kai yana murmushi kaɗan.
A cikin mintuna kaɗan… Suhaila ta dawo ƙasa, ta riga ta shirya tsaf, ta tsaya gabansa tana juyawa,
“How do I look?”
Zayd ya ɗan kalle ta daga sama har ƙasa, sannan ya gyada kai,
“You look good.”
Ta yi murmushi,
“I know.”
Ya girgiza kai,
“Let’s go.”
Nan take wani daga cikin security ya buɗe musu ƙofar mansion.
Baƙar Rolls-Royce Phantom ta riga ta tsaya a ƙofar, driver ya yi saurin buɗe ƙofar baya.
Zayd ya shiga, Suhaila ta shiga bayansa cikin farin ciki.
Motar ta bar Armaan Mansion a hankali…
Not edited