Free chapter · Read without an account
A DREAM DEFERRED
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER-FIFTEEN:15*
*A DREAM DEFERRED*
*JIDDAAH BARKUM*
————-
Da misalin ƙarfe huɗu na yamma… an riga an kammala taron.
Dalibai suna ta ɗaukar hotuna, wasu suna ta taya juna murna.
Sabon Medical Simulation Laboratory kuwa ya cika da baƙi da ke zagayawa suna kallon kayan aikin zamani da aka girka a ciki.
A cikin Faculty Building… Dean tare da HODs da sauran Professors suna tsaye suna tattaunawa.
Raihana na shirin tafiya gida lokacin da Dean ya kira sunanta,
“Miss Raihana.”
Ta waigo cikin ladabi,
“Yes, sir.”
Dean ya yi murmushi,
“Please, come here.”
Ta ƙaraso.
Da ta iso… Professor Ibrahim ya kalleta da murmushi,
“Congratulations once again.”
Ta amsa cikin girmamawa,
“Thank you very much, sir.”
HOD na Surgery ya yi murmushi,
“Your speech was one of the best student presentations we’ve had in recent years.”
Professor Musa ya gyada kai,
“Kuma abin da ya fi burge ni shi ne yadda kika tsaya kan abin da ya shafi ilimi da hidimar al’umma. Ba ki yi ƙoƙarin burge mutane da surutai ba.”
Dean ya yi murmushi,
“Hakika kin wakilci Faculty ɗin nan yadda ya dace. Muna alfahari da ke.”
Raihana ta sauke idanunta cikin kunya,
“Alhamdulillah. Na gode sosai, sirs.”
Dean ya dubi wani envelope dake rike a hannunsa, ya miƙa mata,
“Ga takardunki.”
Ta karɓa a hankali.
Dean ya ci gaba,
“Wannan shi ne official scholarship package ɗinki.”
Professor Ibrahim ya ƙara da cewa,
“Tuition, Accommodation, Living allowance, Research grant,Travel expenses. Everything has been covered.”
Maryam da ke tsaye a gefe ta dafe baki,
“Subhanallah...”
Dean ya yi murmushi,
“Karatun zai fara ne a next academic session. Za ki yi karatu a fannin Clinical Research da Advanced Medical Simulation.”
Na ɗan lokaci… Raihana ta kasa magana, idanunta suka cicciko da ƙwalla, ta haɗiye yawu,
“Na gode sosai. Allah Ya saka muku da alkhairi.”
Dean ya girgiza kai,
“Mu ma muna taya ki murna. Amma ki tuna... wannan dama ta samu ne saboda Armaan Group. Su ne suka ɗauki nauyin wannan scholarship.”
Professor Musa ya gyada kai,
“Allah Ya saka musu da alkhairi. Musamman Mr. Zayd Armaan. Matashi ne da yake ƙoƙarin sauya rayuwar matasa ta hanyar ilimi.”
Raihana ta kalli takardar da ke hannunta, har yanzu kamar mafarki take ji.
Maryam kuwa ta rungume ta,
“Ray... you made it!”
Nan take sauran ɗalibai suka fara zagaye ta,
“Congratulations! We’re proud of you! Kar ki manta da mu idan kin zama babbar likita.”
Dariya ta barke, wasu suna ɗaukar hotuna da ita, wasu suna yi mata addu’a.
Dean ya ɗaga hannu yana murmushi,
“Allah Ya sa wannan ya zama mafarin alkhairi a rayuwarki.”
“Ameen,” kowa ya amsa baki ɗaya.
————————-
*MALALI…*
Lokacin da Raihana da Maryam suka shigo cikin gidan… Baffa Musa na zaune a ƙarƙashin bishiyar mangwaro da ke tsakar gida.
A gabansa kwanukan da ya gama cin abinci ne dan bai dade da shigowa gidan ba shima, ƙamshin Turaren wutan da umma tayi ya mamaye wajen.
Umma kuma na zaune a ɗan tabarmar gefensa tana masa fifita.
Da suka ji motsin ƙofar gate… ta ɗago kai.
Da ta ga Raihana… nan take ta lura da murmushin da ke fuskarta,
“Alhamdulillah...” ta faɗa a ranta.
Maryam ce ta fara magana cikin farin ciki,
“Umma! An yi nasara!”
Raihana ta ƙarasa gaban Baffa, ta durƙusa,
“Ina wuni, Baffa.”
“Lafiya lau,” ya amsa yana shafa gemunsa.
Maryam ta kasa jira,
“Baffa... Ray ta yi speech. Kuma wallahi ta burge kowa. Har Dean da Professors duk suka yaba mata.”
Umma ta yi murmushi,
“Alhamdulillah.”
Baffa ya kalli Raihana,
“Gaskiya ne?”
Raihana ta gyada kai cikin kunya,
“Alhamdulillah. Baffa... sun ba ni Leadership Excellence Award.”
Ta miƙa masa envelope ɗin da Dean ya ba ta,
“Kuma... suka ba ni international scholarship.”
Baffa ya karɓa, ya saka gilashinsa dake gefensa.
Tsakar gidan ya yi shiru, har Mama Indo da ke wanke kayan miya a gefe ta ɗaga kai, Mama Sabuwa ma ta dakata daga abin da take yi.
Baffa ya ci gaba da dan dubawa, can… sai ya ga tambarin ARMAAN GROUP a saman takardar.
Baffa Musa ya sake kallon takardun da ke hannunsa, ya gyara gilashinsa, ya sake karanta sunan kamfanin, _ARMAAN GROUP._
Ya ɗaga kai ya kalli Raihana,
“’Raihaaanatu... wannan kamfanin da kika ce shugaban nasu ya zo makaranta yau kenan?”
“Eh, Baffa.”
“Shi ne ya ba ku wannan scholarship ɗin?”
“Eh.”
Baffa ya ɗan yi shiru, sai ya ce,
“Subhanallah... ai shine wanda nake aiki a kamfaninshi. Ni dai duk da ban taba haduwa dashi fuska da fuska ba amma... mutane da yawa suna cewa suna taimakon marasa ƙarfi. Suna gina makarantu. Suna tallafa wa marasa lafiya. Suna ba matasa damar yin karatu.”
Ya gyada kai cikin gamsuwa,
“Allah Ya saka musu da alkhairi. Musamman wannan Zayd Armaan. Allah Ya ƙara masa arziki da lafiya.”
Umma ta amsa da,
“Ameen Ya Rabb.”
Maryam ta kasa ɓoye farin cikinta, ta matso kusa da Baffa,
“Baffa... wallahi da ka ga yadda suka yaba wa Ray. Dean da Professors duk suna ta cewa ta sa su alfahari. Har CEO ɗin kamfanin ya ce speech ɗinta ta burge shi.”
Baffa ya yi murmushi,
“Alhamdulillah.”
Ya kalli Raihana,
“Na san kina da ƙoƙari tun kina ƙarama. Allah bai taɓa tozarta ƙoƙarin mutum ba.”
Idanun Raihana suka cika da ƙwalla,
“Baffa... na gode.”
Ya ɗauki takardar scholarship ɗin, ya ci gaba da karantawa, can… sai ya tsaya, ya gyara zamansa, murmushin da ke fuskarsa ya ɗan ragu,
“Na yi farin ciki da wannan nasara. Wallahi kin matukar sakani alfahari. Kuma na san wannan ba ƙaramin abu ba ne.”
Maryam ta yi saurin cewa,
“Shi ya sa nake cewa Baffa, ai yanzu Ray za ta je ƙasar waje ta yi karatu.”
Baffa ya girgiza kai a hankali,
“Maryam... ba komai ake dubawa da ido ɗaya ba.”
Tsakar gidan ya yi shiru.
Ya ci gaba cikin nutsuwa,
“Mu Hausawa ne, kuma muna da al’adunmu. Ke kuma Raihana... ’ya mace ce. Ba zan ji daɗin ki tattara kayanki ki tafi wata ƙasa ke kaɗai ba.”
Maryam ta ce da sauri,
“Amma Baffa ai makaranta ce...”
Ya ɗaga hannu a hankali, ta yi shiru,
“Na sani. Na san makaranta ce. Na san ba yawon buɗe ido za ta je ba. Sai dai... zuciyar uba daban take. Mutum ba ya tsoron ’yarsa. Yana tsoron duniya ne.”
Ya juya ya kalli Raihana,
“Na yarda da tarbiyyarki. Na yarda da addininki. Na kuma san ba za ki aikata abin da bai dace ba. Amma hakan ba yana nufin zan saki ki tafi ke kaɗai ba, hankalina ba zai kwanta ba.”
Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce,
“Idan wannan scholarship ɗin tana da muhimmanci kamar yadda kuka ce... ina ganin su jira. Ki yi aure. Idan Allah Ya ba ki miji nagari, kuma ya amince... sai ku tafi tare. Hakan ne zai fi kwantar min da hankali.”
Raihana ta sunkuyar da kanta, zuciyarta ta cika da abubuwa iri-iri.
Wannan dama ce da ta daɗe tana mafarkinta, amma kuma… ba taɓa tunanin ta saɓawa Baffa ba.
Cikin girmamawa ta ce,
“In Sha Allah, Baffa. Duk abin da ka ga ya fi alkhairi a gare ni... Allah Ya sa shi ne alkhairin.”
Baffa ya yi murmushi,
“Allah Ya miki albarka.”
“Ameen.”
Umma ta kalli mijinta, ta ce cikin hikima,
“Allah ne Mai tsara rayuwa. Wataƙila ma ba wannan lokacin Allah Ya rubuta mata tafiyar ba. Idan lokacin ya yi... Shi da kansa zai buɗe mata ƙofa.”
Baffa ya gyada kai,
“Haka nake.”
A gefe kuwa… Mama Sabuwa tana zaune tana sauraron su, tun farkon maganar… ba ta ce komai ba, sai dai fuskarta ta nuna ba ta ji daɗi ba.
Ta taɓe baki, ta kalli Mama Indo, cikin kasa kasa da murya ta ce,
“Hmm... ni dai ban san wane irin scholarship ne za a ba wa ɗiya mace... har ace sai an tura ta Turai.”
Ta yi dariyar rainin wayo,
“Kamar dai wacce za a tura bariki.”
Mama Indo ta ɗan yi murmushi irin nata, ba ta goyi bayanta kai tsaye ba, ba kuma ta hana ta ba, sai ta ce a hankali,
“Duniya ai ta canza.”
Mama Sabuwa ta girgiza kai,
“Ko ta canza... ni kam ban ga amfanin mace ta riƙa yawo ƙasashen waje ita kaɗai ba.”
Ta ɗan kalli Raihana daga nesa,
“Allah dai Ya kyauta.”
Umma ta ji kalamanta, sai dai ba ta bi ta kanta ba, ta kalli Raihana kawai, ta yi mata murmushi mai cike da kwantar da hankali, kamar tana gaya mata cewa…
“Ki yi haƙuri. Ba kowace magana ce ake mayarwa ba.”
*ARMAAN RESIDENCE*
Bayan an kammala taron… convoy ɗin Armaan Group ya fice daga harabar jami’ar cikin tsari.
Rolls-Royce Phantom na gaba, security vehicles suna biye da ita.
A cikin motar… shiru ne ya mamaye wajen.
Zayd na zaune a kujerar baya, iPad ɗinsa yana buɗe a gabansa, yana duba wasu reports na kamfani.
Imraan daya zo daga baya yana kujerar gaba, Suhaila kuwa… tun da suka bar makarantar… ta kasa yin shiru.
Ta juya ta kalli ɗan’uwanta,
“Akhii...”
Zayd bai ɗaga kai ba,
“Hmm?”
“Yau ka ga student representative ɗin nan kuwa?”
Zayd ya ci gaba da kallon screen,
“Wace?”
Suhaila ta yi dariya,
“Please mana. Miss Raihana. Wadda ta yi speech.”
“Oh...” ya amsa a taƙaice,
“I saw her.”
Suhaila ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta sake cewa,
“Wallahi yarinyar ta bani mamaki.”
Zayd bai ce komai ba.
Ta ci gaba,
“Da farko ma... na yi tsammanin ba ’yar Najeriya ba ce.”
Zayd ya ɗan ɗaga gira,
“Why?”
“Kalli kamanninta mana. Very unique. Sai idanuwanta. Sai yadda take tafiya cikin nutsuwa. Kuma Turancinta...” ta girgiza kai,
“Honestly... it was almost flawless.”
Imraan da ke zaune a gaba ya yi dariya,
“Suhaila... kin fara analysis kenan?”
Ta harare shi,
“I am very serious Yaa Imraan.”
Ta sake kallon Zayd,
“Akhii... ba ka ga yadda kowa yake kallonta ba? Even the professors looked proud of her. Speech ɗinta ma... wallahi ta yi min sosai.”
Zayd ya rufe iPad ɗin a hankali, ya jingina bayansa da kujera, cikin nutsuwa ya ce,
“She prepared well.”
Suhaila ta ɗaga gira,
“Abinda zaka fada kenan? Prepared well? Ai ka ji yadda hall ya yi tsit. Kowa ya maida hankali kanta. Ba kowa ne yake iya tsayawa a gaban irin wannan taro ya yi magana ba.”
Zayd ya gyara agogon hannunsa,
“Confidence comes from preparation. She earned it.”
Suhaila ta yi murmushi,
“Toh ai shi kenan. Ka yarda ta yi ƙoƙari.”
“I do,” ya amsa ba tare da wani ƙarin bayani ba, sai ya sake buɗe iPad ɗinsa, alamar tattaunawar ta ƙare kenan.
Suhaila taɓe baki,
“Wai kai... wani lokacin sai ka ba mutum haushi.”
Imraan ya yi dariya,
“Kin san halinsa. Ba zai taɓa zama yana yabon mutane ba.”
Suhaila ta haɗe hannayenta,
“Ni dai... ina son irin mutanen nan masu hankali. Kuma Raihana...” ta ɗan yi murmushi,
“I think she’s going to become a very big doctor one day.”
A wannan karon… Zayd bai amsa ba.
Sai dai… kafin ya maida hankalinsa kan iPad dinsa… wata ɗan gajeriyar ƙwaƙwalwa ta sake dawo masa.
Yarinyar da ke tsaye a kan podium… cikin emerald green abaya… tana cewa,
“Knowledge remains the greatest wealth... and integrity remains the greatest legacy.”
Ba tare da ya sani ba… sai ya lumshe idanunsa na daƙiƙa guda, sannan ya ci gaba da aikinsa.
Not edited