Free chapter · Read without an account

THE PERFECT SCANDAL

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN







*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER-SEVENTEEN:17*

*THE PERFECT SCANDAL*

*JIDDAAH BARKUM*
⸻——————

Washegarin da daddare… ƙaramin fan ɗin ɗakin yana juyawa a hankali.
Ruwan sama da aka yi da yamma ya bar iska mai sanyi tana ratsawa ta window.

Raihana na zaune a bakin katifarta, laptop ɗinta a buɗe gabanta tana gyaran project.
Sai ƙofar ɗakin ta buɗe da ƙarfi, Maryam ta shigo da gudu, wayarta na hannunta, fuskarta cike da farin ciki,
“Rayy!”
Raihana ta ɗaga kai tana murmushi,
“Lafiya?”
Maryam ta ƙaraso ta faɗo kan gadon,
“Wai ke baki shiga social media ba tun jiya?”
Raihana ta girgiza kai,
“A’a. Gyaran project Dina nake son kammalawa.”
Maryam ta dafe kai,
“Ya salam! Ke baki san me kike missing ba.”
Ta kunna Instagram, ta miƙa mata wayar,
“Kalli.”

Raihana ta karɓa, nan take idanunta suka sauka kan official page na jami’ar.
Hotonta da Zayd suna tsaye a stage.
A ƙasa kuwa… an rubuta:
🏆 *Annual Leadership & Innovation Summit 2026*
Meet our Outstanding Student Speaker, Raihana Musa, alongside our Special Guest Speaker, Mr. Zayd Armaan.
❤️ 48.9K Likes
💬 9.3K Comments
↗️ 17K Shares

Raihana ta ɗan buɗe baki,
“Haba...”
Maryam ta yi dariya,
“Wannan ba komai bane. Ki shiga comments.”

Raihana ta latsa, comments suka fara bayyana:
*mariam_01*
She spoke with so much confidence.
❤️ 4.2K Likes

*thearewastudent*
Best female speaker we’ve seen this year.
❤️ 6.1K Likes

*ceo_daily*
She matched Zayd Armaan’s energy effortlessly.
❤️ 8.9K Likes

*lawalmedia*
Beauty, brains and confidence. Rare combination.
❤️ 5.4K Likes

Maryam ta ce cikin murna,
“Ba Instagram kaɗai ba.”
Ta buɗe TikTok, video ɗin speech ɗin Raihana ya fara playing.
A ƙasa…
▶️ 1.8 Million Views
❤️ 412K Likes
💬 27K Comments
↗️ 96K Shares
Caption: “The young lady who left the audience speechless.”

Maryam ta yi dariya,
“Ki ga wannan.”
Ta shiga comments:
*queen_naj*
Who’s this elegant lady?
❤️ 18K
*futuredoctor*
She deserves every applause.
❤️ 9K
*hausa_elite*
Northern girls are making us proud.
❤️ 22K

Raihana ta girgiza kai cikin mamaki,
“Subhanallah...”
Maryam ta ce,
“Har yanzu baki ga komai ba.”
Ta buɗe X (Twitter).
Trending: #LeadershipSummit2026, #ZaydArmaan, #RaihanaMusa, #YoungVoices
Posts suna ta shigowa:
*@NaijaBusiness*
Zayd Armaan wasn’t the only star yesterday, Student speaker Raihana Musa stole hearts too.
❤ 34K
🔁 11K
*@CampusTrend*
The confidence, The diction, The composure.
❤ 21K

Maryam ta sake buɗe Snapchat, story ɗaya bayan ɗaya.
Mutane suna repost, wasu sun ɗauki speech ɗin Raihana, wasu kuma na Zayd, wasu ma sun haɗa su a video guda.
Sai wani edit mai kyau ya bayyana, an haɗa lokacin da Zayd ke jawabi... da lokacin da Raihana ta karɓi certificate, an saka instrumental mai taushi a baya.

Maryam ta yi murmushi,
“Wannan edit ɗin ya fi burgeni.”
Raihana ta ɗan yi dariya,
“Mutane dai akwai batawa kai lokaci.”
“Ba bata lokaci bane,” Maryam ta ce tana ƙwace wayar,
“Kin zama celebrity na kwana ɗaya.”
Raihana ta girgiza kai tana murmushi, ta mayar da hankalinta kan laptop ɗinta.

⸻

*ARMAAN MANSION*

Ummie na zaune kan sofa tana Jan chasbaha cikin nutsuwa, a gabanta akwai wasu takardu a ajiye da ta gama dubawa.
Sai ta ji saurin takun Suhaila daga saman stairs, wayarta na hannunta, tun kafin ta iso… ta fara magana,
“Ummieee! Wallahi abin ya wuce tunanina.”
Ummie ta ɗago tana murmushi,
“Lafiya kuma?”
Suhaila ta zauna kusa da ita, ta buɗe Instagram,
“Ki duba wannan.”
Ta miƙa mata wayar.

Ummie ta karɓa, idonta ya sauka kan official page na university, thousands of likes, thousands of comments, thousands of shares.
Ta ɗan yi murmushi,
“Maa Sha Allah.”
Suhaila ta ce cikin farin ciki,
“Ba Instagram kaɗai ba fa. Har TikTok. Har X. Har Snapchat. Speech ɗin Raihana ya shiga ko’ina. Mutane suna ta repost. Har yanzu videos suna ta hawa.”
Ummie ta mayar mata da wayar,
“Allah Ya ƙara albarka.”
“Amin,” Suhaila ta ce,
“Wallahi yarinyar nan ta yi abin a zo a gani. Duk inda ka shiga... ko dai ana maganar speech ɗinta... ko kuma ana maganar Akhi. Wasu ma sun haɗa su a edit guda.”
Ummie ta ɗan ɗaga gira,
“Edit?”
Suhaila ta yi dariya,
“Eh mana. Social media fa. Duk abin da ya burge su... sai sun yi editing.”
Ummie ta girgiza kai kawai.

A dai-dai lokacin…. Zayd ya sauko daga stairs, sanye yake cikin ash-coloured kaftan mai sauƙin kyau, Apple Watch ɗinsa a hannunsa, wayarsa kuma na ɗaya hannun, kafarshi sanye da slippers mai laushi na gida.

Yana saukowa… Suhaila ta yi murmushi,
“Akhiii...”
Ya waigo,
“Hm?”
Ta ɗaga wayarta,
“Congratulations.”
Ya ɗan ɗaga gira,
“For what?”
“Speech ɗinku fa. Ya tafi viral.”
Zayd ya tsaya na ɗan daƙiƙa,
“Really?”
“Really mana,” ta buɗe TikTok ta nuna masa,
“Million views. Instagram ma kusan mutane dubu hamsin sun yi likes. X ma trending. Mutane suna ta magana.”

Zayd ya kalli screen ɗin na daƙiƙa biyu kacal, sai ya mayar mata da wayar,
“Good.”
Suhaila ta yi dariya,
“Good? Shi kenan? Baka ma yi mamaki ba.”
Zayd ya nufi dining area, yana tafiya cikin natsuwa, ya ce,
“It’s normal. Every successful event gets attention.”
Suhaila ta bi bayansa,
“Amma wannan ya fi na baya. Remember the Kano conference? Wannan ya zarce shi.”

Zayd ya tsaya ya juyo, ya kalli wayar da ke hannunta, sannan ya ce cikin sanyin murya,
“The attention isn’t on me. It’s on the event. And that’s how it should be.”
Ya juya zai ci gaba da tafiya, sai Suhaila ta yi saurin cewa,
“Ba event kaɗai ba fa. Raihana ma tana trending.”
Zayd bai tsaya ba, sai dai ya amsa cikin natsuwa,
“She delivered a good speech. People appreciate competence. Nothing unusual.”
Ya ci gaba da tafiya, kamar batun ya ƙare a gare shi.

Suhaila ta tsaya tana kallonsa, sai ta kalli Ummie, ta yi murmushi,
“Kin ga Akhi? Ko duniya ta tsaya... attitude ɗinsa ɗaya.”
Ummie ta yi murmushi mai cike da natsuwa,
“Ba kowa ne yake iya ɗaukar yabo ba tare da ya canza ba.”
Suhaila ta sauke numfashi,
“Amma wallahi... da ni ce... da tuni na tsaya ina karanta comments.”
Ummie ta yi dariya,
“Shi ba irin ku ba ne. A gare shi... an yi aiki. An gama. Shi ke nan.”

A can kuwa… Zayd ya shiga study ɗinsa, ya ajiye wayarsa a kan desk, bai buɗe Instagram ba, bai shiga TikTok ba, bai kuma nemi ganin comments ba.
A gare shi… trending ba shi ne abin da yake nema ba, abin da yake nema… shi ne a cimma manufar aikin da aka yi.
Shi ya sa, yayin da duniya ke ci gaba da yabawa speech ɗin da ya yi tare da na Raihana… shi kuwa… ya riga ya koma kan takardun meeting ɗin washegari, kamar babu wani abu na musamman da ya faru.

Ɗakin ya yi tsit kamar kullum, manyan bookshelf ne suka kewaye bangon, a tsakiyar ɗakin akwai babban mahogany desk, laptop ɗinsa a buɗe, wasu files kuma a jere cikin tsari.
Ya zauna a kujerarsa, ya buɗe wani confidential document yana dubawa.

Bai wuce minti biyu ba… sai aka yi knocking a ƙofar,
“Come in.”
Ƙofar ta buɗe a hankali, Sameer ne ya shigo, hannunsa riƙe da tablet da wasu files,
“Good evening, Boss.”
Zayd bai ɗaga kai ba nan take,
“Good evening, Sameer.”

Sameer ya ƙaraso ya ajiye file a kan desk,
“These are the documents for tomorrow’s investors’ meeting.”
Zayd ya ɗauki file ɗin, ya buɗe shafuka biyu yana dubawa,
“Have they all confirmed?”
“Yes, Boss. All six investors have confirmed. They’ll be here by ten o’clock sharp.”
Zayd ya gyada kai,
“Good.”

Sameer ya ci gaba,
“And the presentation has been updated based on your corrections. I’ve also informed the legal team. They’ll be present.”
“Excellent.”
Zayd ya rufe file ɗin, ya ɗaga kansa ya kalli Sameer,
“What about the China project?”
Sameer ya buɗe tablet ɗinsa,
“The Shanghai partners have finalized everything. They’re expecting you next week. The private jet clearance has already been approved. The schedule is ready.”

Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci yana nazarin kalandar da ke gaban sa,
“How many days?”
“Five days in China. Then one day in Singapore before returning.”
Zayd ya gyada kai cikin gamsuwa,
“Okay.”

Sameer ya yi murmushi,
“Gaskiya Boss... wannan project ɗin idan ya kammala... Armaan Group zai sake ɗaukar wani sabon matsayi.”
Zayd ya rufe file ɗin da ke gabansa,
“Ba girma nake nema ba. Ina neman ci gaba. Kasuwa tana canzawa kullum. Idan ba ka ci gaba ba... za a bar ka a baya.”
Sameer ya gyada kai,
“Hakane. Shi ya sa nake ganin duk inda na je ana magana a kanka. Mutane suna yabon yadda kake tafiyar da kamfani.”
Zayd ya ɗan yi murmushi kaɗan,
“Yabo ba ya biyan bills, Sameer. Dole aiki ya yi magana.”
Sameer ya yi dariya,
“Wallahi Boss... wannan maganar taka ba ta canzawa.”

Zayd ya miƙa masa wani file,
“Ka sake duba figures ɗin nan. Ina son komai ya kasance daidai kafin gobe.”
Sameer ya karɓa,
“In Sha Allah.”

Kafin ya juya ya fita… sai ya tuna wani abu,
“Af Boss... na ga speech ɗin jiya har yanzu yana yawo a social media. Wasu daga cikin investors ɗin ma sun ambace shi. Sun ce sun ji daɗin yadda aka shirya taron.”
Zayd ya gyada kai kawai,
“Alhamdulillah. Abin da ya fi muhimmanci shi ne sakon ya isa ga mutanen da aka yi taron domin su.”
Sameer ya yi murmushi,
“Allah ya ƙara ɗaukaka.”
“Ameen.”
“Good night, Boss.”
“Good night, Sameer.”

Sameer ya fita ya rufe ƙofar a hankali.
Study ɗin ya sake yin shiru.
Zayd ya jingina da kujerarsa na ɗan lokaci, sai ya ɗauki wani file mai rubutun China Expansion Project, ya buɗe shafi na farko.
Hankalinsa ya riga ya koma kan babbar yarjejeniyar da ke gabansa.

A gefe guda kuwa… wani account mai suna *@InsiderReveal* ya riga ya sauke duk hotunan event ɗin, yana kallon su ɗaya bayan ɗaya.
Yatsansa ya tsaya kan wani hoto, hoton da Raihana ke karɓar certificate daga hannun Zayd.
Ya yi zoom, sai ya yi murmushi a hankali,
“…Interesting.”
Ya latsa Save Image, sannan ya rufe wayar.

⸻

A wani ɓangaren birnin Kaduna… a cikin ɗakinta, Seeyama na kwance a kan gadonta, wayarta a hannunta.
Tun kusan rabin awa kenan tana scrolling a Instagram, sai wani post ya sake bayyana, hoton Zayd da Raihana.
Ta tsaya, ta sake kallon hoton, sannan ta shiga comments.

Comment ɗaya... biyu... uku... sai idanunta suka fara canzawa:
“They’re such a perfect duo.” ❤️
“Chemistry between them is effortless.”
“Who else thinks they look good together?”
“Future power couple?”

Ta ɗan cije leɓenta, ta ci gaba da scrolling.
Sai wani edit ya bayyana a TikTok, an haɗa lokacin da Zayd yake magana... da lokacin da Raihana ta karɓi certificate, an saka waƙar piano mai taushi a baya.
Comments kuwa… sun fi na farko yawa:
“They’re giving CEO and First Lady vibes.”
“Please tell me they’re together.”
“I ship them already.”

Numfashinta ya ɗan yi nauyi, ta kashe wayar na daƙiƙa guda, sai kuma ta sake buɗewa, ta sake duba comments.
Kamar tana fatan za ta ga wani abu dabam, amma abin da take gani ɗaya ne… mutane suna yabon Raihana, wasu kuma suna haɗa sunanta da Zayd.

Ta miƙe daga kan gado cikin damuwa, kai tsaye ta nufi ɗakin Mommy Hauwa.
Mommy Hauwa na zaune tana shan shayi cikin nutsuwa, da ta ga Seeyama ta shigo da wannan fuskar… sai ta ɗan ɗaga gira,
“Lafiya?”
Seeyama ta zauna kusa da ita, ba tare da magana ba… ta miƙa mata wayar,
“Mommy... kalli wannan.”

Mommy Hauwa ta karɓi wayar, ta fara duba comments ɗin, ta gama, sai ta mayar mata da wayar, ta yi murmushi a hankali,
“Shi kenan?”
Seeyama ta yi saurin cewa,
“Mommy... ba ki ga yadda mutane suke magana ba? Wasu ma suna cewa sun dace. Wasu suna cewa... wai kamar ma’aurata.”
Ta sauke ajiyar zuciya,
“Ban ji daɗin hakan ba.”

Mommy Hauwa ta ɗan shafa hannunta,
“Seeyama... social media ba wurin ɗaukar komai da muhimmanci ba ne. Mutane suna rubuta duk abin da ya zo musu a rai. Yau wannan. Gobe kuma wani daban.”
Ta yi ɗan murmushi,
“Kin san Zayd. Irin wannan abubuwan basu dame shi ba. Kada ki bari comments na mutane su tayar miki da hankali. Za su gaji. Su kuma manta. Rayuwa za ta ci gaba.”
Seeyama ta sauke numfashi,
“Okay, Mommy.”
Ta yi ƙoƙarin yin murmushi, sai ta miƙe, ta yi mata sallama, ta fita daga ɗakin.

Mommy Hauwa ta bi bayanta da kallo… har sai da ƙofar ta rufe, murmushin da ke fuskarta ya ɓace sannu a hankali.
Ta ɗauki wayarta daga gefen tebur, ta shiga contacts, ta danna wani number da ba a bayyana sunansa ba.
Bai daɗe ba… aka ɗaga.

Mommy Hauwa ta ɗan yi shiru na daƙiƙa biyu, sannan cikin sanyin murya ta ce,
“I think it’s time to begin.”
Ta ɗan saurara, sai ta ƙara da cewa,
“Everything is falling into place.”
Ba tare da ta ƙara wata magana ba… ta kashe wayar, ta jingina da kujerarta, idanunta suka tsaya kan window ɗin ɗakin.
A hankali wani siririn murmushi ya bayyana a gefen bakinta… murmushin da ya nuna cewa… wani shiri da aka daɗe ana ɓoye wa… ya kusa fara aiki.

——————————

Washegarin Litinin da safe… safiyar Litinin ce, hasken rana ya fara ratsawa ta tagogin gidan.

A falo… Bintu na kwance a kan doguwar kujera, wayarta na hannunta, ta gama chatting da Hashim, sai murmushi take yi ita kaɗai.
Can… ping!
Notification ya shigo, *Khadija* 💬
Ta taɓe baki,
“Da sassafen nan kuma? Ko uwar me zanyi mata sarkin aron kayan mutane,” tayi tsaki.

Da farko ta yi niyyar wucewa, sai kuma ta buɗe message ɗin.
Nan take… ta tashi zaune, idanunta suka zaro, numfashinta ya tsaya.
A saman message ɗin an rubuta—
“Bintu... wannan ba Raihanar gidanku ba ce??”
A ƙasa… pictures.
Ba guda ba, ba goma ba, sama da hamsin.

Bintu ta fara scrolling:
Hoton farko... Raihana da Zayd suna zaune a cikin motarshi, ta dora kanta a shoulder dinshi.
Na biyu... kamar suna tafiya tare a wani shopping mall.
Na uku... kamar suna cin abinci a wani restaurant mai tsada.
Na huɗu... kamar suna fitowa daga wani hotel.
Na biyar... kamar Zayd ya rungume ta a cikin wani haddadden bathroom, ba komai a jikinta shima hakaaa.
Na shida... suna bakin wani swimming pool, ita sanye da bikini, shi kuma da short kadai, ya rungumeta suna dariya.

A ƙasa kuma… an rubuta da manyan haruffa:
*“THE REAL REASON BEHIND RAIHANA’S SUCCESS?”*
*“CEO ZAYD ARMAAN’S SECRET LOVER EXPOSED!”*

Bintu ta dafe ƙirji,
“Ya Allah...”
Ta miƙe da gudu,
“Mamaaa!! Mamaaa!!”
Ta kutsa cikin ɗakin Mama Sabuwa.

Mama Sabuwa ta taso a firgice,
“Ke! Lafiya?”
Bintu ba ta iya magana, sai ta miƙa mata wayar,
“Mama... kalli...”

Mama Sabuwa ta karɓa, ta fara scrolling, idonta ya fara faɗaɗa, ta sake scrolling.
Sai wani fake article ya bayyana, “University Girl Secret Relationship With Billionaire CEO.”
Ta ci gaba, wani kuma, kamar suna cikin private jet.

Mama Sabuwa ta ɗago, idanunta sun cika da wani irin walƙiya,
“Subhanallah...”
Ba ta ƙara cewa komai ba, ta juya da sauri, kai tsaye ta fito tsakar gida.

Lokacin… Baffa Musa na zaune a ƙofar ɗakinsa yana karatun Al-Qur’ani, Mama Indo na kitchen, Maryam na wanke-wanke, Umma da Raihana na cikin ɗaki.

Mama Sabuwa ta ɗaga murya da ƙarfi,
“Tooo!! Alhamdulillah! Yau dai asiri ya tonu!”
Maryam ta tsaya cak, Mama Indo ta fito daga kitchen da sauri, Baffa Musa ya ɗago kai.

Mama Sabuwa ta ci gaba da shewa,
“Mu ake cewa yaranmu ne lalatattu! Mu ake yi wa’azi kullum! Ashe... ga abin da ake ɓoyewa a cikin gidan nan!”
Umma ta fito daga ɗaki,
“Lafiya dai?”
Mama Sabuwa ta juya gare ta,
“Lafiya? Kina tambayar lafiya? Ki fara tambayar ’yarki!”
Raihana ta fito a bayanta, fuskarta cike da mamaki,
“Me ya faru?”
Mama Sabuwa ta yi wata irin dariya,
“Ke ce har yanzu kike tambaya? Wallahi yau... sai an san wacece mai tarbiyya!”

Baffa Musa ya miƙe tsaye,
“Sabuwa. Ki daina ihu. Faɗi abin da yake faruwa.”
Mama Sabuwa ta ƙarasa gabansa, ta miƙa masa wayar,
“Ga shi. Ka gani da idonka. Ni ba zan ƙara magana ba.”

Baffa Musa ya karɓi wayar, sai ya gungura ƙasa, ya tsaya, ya sake kallon hoton.
Fuskarsa ta sauya, ya ƙanƙance idanunsa, ya sake gungurawa.
Caption ɗin ya fito:
“Behind every successful speech... there’s a billionaire sponsor.”
Sai wani, “Love in disguise?”
Sai wani, “Exclusive photos of the hidden relationship.”

Baffa Musa ya tsaya cak, hannun da yake riƙe da wayar ya ɗan yi rawa.
Tsakar gidan ya yi tsit.
Maryam ta zuba wa Baffa ido, Umma ta fara kallon Raihana… Raihana kuma ta na tsaye kamar statue, ba ma ta fahimci me ke faruwa ba.

Da sauri Umma ta karaso, ta karɓi wayar daga hannun Baffa, idanunta na sauka akan screen din, gabanta ya faɗi, ta ci gaba da kalla, tana zuwa kan wanda suke toilet sai tayi maza ta kauda kanta gefe, zuciyarta ta sake bugawa.

Umma ta dafe ƙirjinta da hannu biyu,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un...” shi kaɗai ne kalmar da ta iya furtawa.
Sai jikinta ya fara rawa, numfashinta ya koma sama-sama, idanuwanta suka cika da hawaye.
Ta sake kallon screen ɗin na daƙiƙa guda… sai ta yi saurin kau da kanta kamar abin da take gani zai ƙone mata ido.
Wayar ta zame daga hannunta… ta faɗi ƙasa da ƙarfi,
“Ya Allah...” ta furta cikin murya mai rauni.

Sai jikinta ya yi laushi.
Da sauri Maryam ta yi ihu,
“Ummaa!”
Ta ruga ta tare ta kafin ta faɗi ƙasa gaba ɗaya.
Mama Indo ma ta fito da gudu daga kitchen,
“Subhanallah! Me ya faru?”
Ta kama Umma daga ɗaya gefen.

Raihana haryanzu tana tsaye tana kallon kowa kamar an daureta, ta kasa ko motsawa.

Baffa Musa kuwa…… ya ɗaga kai da sauri, da ya ga yadda Umma ke neman sumewa… sai ya karaso da sauri,
“Maryam! Riƙe ta da kyau.”

Mama Sabuwa kuwa… ta na tsaye gefe, ta haɗe hannaye, a fuskarta akwai wani irin murmushin da take ƙoƙarin ɓoyewa.





*** ✍️ 




Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.