Free chapter · Read without an account
TWO DOORS ONE DESTINY
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER-TWENTY TWO:22*
*TWO DOORS, ONE DESTINY*
*JIDDAAH BARKUM*
——————————
A tsakar gida… bayan Baffa Musa ya shiga falon… Mama Sabuwa ta ci gaba da binsa da ido har labulen falon ya rufe.
Sai ta matsa kusa da Mama Indo, ta ɗan sunkuyar da kai, ta sauke murya kamar mai tona wani babban sirri,
“Indo…”
Mama Indo ta ɗago kai,
“Lafiya?”
Mama Sabuwa ta ƙara matsowa,
“Ke me kike tunanin matar nan ta zo yi ne?”
Mama Indo taɓe baki,
“Ni kuma ta yaya zan sani?”
Mama Sabuwa ta ɗan taɓa goshinta,
“Ni dai tunani nake yi...” ta yi shiru kaɗan kafin ta ce,
“Ko dai... ’yan uwansu ne daga Nijar suka gano inda suke?”
Mama Indo ta kalleta da mamaki,
“’Yan uwa daga Nijar?”
“Eh mana!”
Mama Sabuwa ta gyara zamanta,
“Kin manta ne? Hajara ai Buzuwa ce. “ “To?”
Mama indo ta sake tambaya sai mama sabuwa ta matso
“To ai watakila danginsu masu kuɗi ne. Da suka daɗe suna nemansu... yanzu kuma Allah Ya haɗa su.”
Mama Indo ta dafe kai,
“Ke Sabuwa...”
“Uhumm?”
“Duk abin da ya zo ranki sai kin gaskata shi kenan?”
Mama Sabuwa ta yi saurin cewa,
“To ai ni dai abin da nake haɗawa kenan.”
Mama Indo ta girgiza kai,
“Idan ma ’yar uwarta ce... me ya sa za ta ce ‘ina Raihana’ ai sai ta ce ‘ina Hajara’?”
Mama Sabuwa ta tsaya cak,
“Eh fa...” ta ɗan yi shiru, sai kuma ta sake cewa,
“To ko...” ta rage murya sosai,
“…ko dai abinda aka yaɗa a duniya ta gani, ta ga Raihana na kama da Hajara, ta zo?”
Mama Indo ta zaro ido,
“Subhanallah! Ke kin ji abin da kika faɗa kuwa?”
Mama Sabuwa ta ɗan yi dariyar yaqe,
“To ai ina ta tunani ne.”
Mama Indo ta yi murmushi,
“Da alama dai yau ba za ki huta ba sai kin ƙirƙiro labarai goma.”
Mama Sabuwa ta ɗaga gira,
“To ke ba kya son sani ne?”
Mama Indo ta yi dariya,
“Ina so. Amma ba zan ƙirƙiro abin da ban sani ba.”
Mama Sabuwa ta haɗe hannu,
“Wallahi ni dai zuciyata ta kasa nutsuwa. Tun da ta ce ‘ina Raihana’...” ta girgiza kai,
“Lallai akwai wani babban abu da suke ɓoyewa.”
Mama Indo ta yi dariya,
“Ki dai jira. Ba komai ake gano shi da gaggawa ba.”
Mama Sabuwa ta yi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ta ce cikin salon tseguminta,
“Indo...”
“Hmm?”
“Amma ki rubuta wannan maganar...” ta nuna ƙofar falon da yatsa,
“Wannan zuwan... ba haka kawai bane, tabbas ba. ƙaramin abu ya kawo shi ba!”
Mama Indo ta yi murmushi kawai, a zuciyarta kuwa… sai ta ce,
“Allah kaɗai Ya san abin da yake ɓoye a bayan wannan ziyara...”
Bayan sun yi sallama da mutanen gidan… Ummie ta sake rungume Umma cikin mutunci, ta yi wa Baffa Musa godiya, sannan ta yi wa Raihana murmushi mai cike da taushin da ya rage mata a zuciya,
“Allah Ya kiyaye ki, ’yata.”
Raihana ta ɗan sunkuyar da kanta,
“Ameen... nagode.”
Suka fito tsakar gida suka yi wa Mama Indo da Mama Sabuwa sallama, su kuwa suka bisu da ido kawai, bakinsu fal, tambayar da babu mai ba su amsa.
Daga nan suka fice daga gidan, Sameer ya buɗe musu ƙofar motar cikin ladabi.
Ummie ta shiga ta zauna a bayan mota, Suhaila ta zauna kusa da ita, Sameer kuma ya zagaya ya shiga mazaunin direba.
A hankali motar Mercedes-Maybach ɗin ta fara barin layin unguwar Malali.
Na ɗan lokaci… shiru ne ya mamaye motar, sai sautin karatun Al-Qur’ani mai laushi da ke tashi daga speaker, haɗe da ƙaramar ƙarar AC.
Ummie kuwa… har yanzu idanunta na kallon window, amma ba titin take gani ba, tunanin Raihana ne ya cika zuciyarta, hoton kumburarrun idanunta, muryarta mai rauni, da yadda ta fashe da kuka a jikinta… sai zuciyar Ummie ta sake matsewa.
Ta sauke wani siririn numfashi,
“Allah... Ka sauƙaƙa mata.”
Suhaila kuwa… tun fitowarsu daga gidan take ta kallon Ummie lokaci-lokaci, tambayoyi sun cika mata zuciya.
Ta so ta yi shiru, ta yi ƙoƙarin haƙuri, amma… ta kasa.
A hankali ta matsa kaɗan kusa da Ummie,
“Ummie...”
Ummie ta juyo gare ta,
“Hmmm, sweetheart?”
Suhaila ta ɗan yi murmushi, sai kuma ta girgiza kai,
“Wallahi... tun daga lokacin da muka shiga gidan nan zuciyata take cike da tambayoyi.”
Ummie ta yi murmushi,
“Na sani.”
“Amma kin ƙi gaya min komai.”
Suhaila ta ɗan turo baki kamar ƙaramar yarinya,
“Kinata cewa, ‘za ki gani.’”
Sameer ya ɗan yi murmushi shi kaɗai yana tuki, bai ce komai ba.
Ummie ta kalli Suhaila da idanun da ke cike da wani farinciki wanda ko ita bata san na me ba,
“To... yanzu ki tambaya. Tambayi duk abinda kike son sani.”
Suhaila ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta ce cikin sanyin murya,
“Ummie...”
“Na’am?”
“Da gaske ne... kina son Akhi ya auri Raihana?”
Motar ta yi shiru, ko Sameer da ke tuƙi… sai da ya ɗan rage saurin motar kaɗan, ba don ya ji mamaki ba… sai don yana son jin amsar Ummie.
Ummie ta yi murmushi, murmushin nan nata na manyan mata masu natsuwa, sai ta kalli Suhaila,
“Eh.”
Ta faɗa cikin sauƙi,
“Da gaske nake.”
Suhaila ta zaro ido,
“Amma... Ummie... kin san Akhi da Raihana ba su ma san juna ba. Ba su taɓa wata magana ba. Ba relationship suka yi ba. Incident ne kawai ya haɗa sunayensu.”
Ummie ta gyada kai,
“Na sani. Shi ya sa ma ban taɓa cewa saboda wannan incident ɗin nake son ta ba.”
Ta ɗan yi shiru, sannan ta ɗora cikin nutsuwa,
“Ko da wannan scandal ɗin bai taɓa faruwa ba... da na haɗu da Raihana kamar yadda na haɗu da ita yau...” ta yi murmushi,
“Wallahi da zan yi wannan tunanin.”
Suhaila ta ƙara mamaki,
“Saboda me Ummie?”
Ummie ta ɗan jingina bayanta da kujerar motar, idanunta suka lumshe na ɗan lokaci, sannan ta buɗe su,
“Akwai wasu abubuwa, Suhaila... ba a ganin su a cikin kyau ko a kuɗi. Ba kuma akoya su a makaranta. Allah ne yake dasa su a zuciyar mutum.”
Ta ɗan yi murmushi,
“Na shiga gidan nan... ban ga arziki ba. Amma na ga wadatar zuciya, na ga tarbiyya.”
Ta ci gaba cikin natsuwa,
“Na ga uwa mai haƙuri. Na ga uba mai mutunci. Na ga gida mai tsafta. Na ga nutsuwa. Na ga tsoron Allah.”
Ta ɗan dakata,
“Sannan...” ta sauke numfashi,
“Na ga Raihana.”
Suhaila ta yi shiru tana sauraro.
“Kin lura da yadda take magana?”
Suhaila ta gyada kai,
“Eh.”
“Kin lura da yadda take girmama iyayenta?”
“Eh.”
“Kin lura cewa duk da abin da zata yi sai ta kalli mahaifiyarta tana jiran ta ga ko zata ce aa ko eh?”
Suhaila ta sake gyada kai,
“Na lura.”
Ummie ta yi murmushi,
“Yarinya irin wannan... ba kasafai ake samunta ba.”
Ta ɗora hannunta kan na Suhaila,
“Ke ma mace ce. Idan Allah Ya ba ki ɗa namiji nan gaba... ba irin wannan yarinya za ki so ta zama matar ɗanki ba?”
Suhaila ta yi shiru, a hankali… sai murmushi ya bayyana a fuskarta, ta gyada kai,
“Zan so.”
Ummie ta shafa hannunta cikin ƙauna,
“Shi ya sa na ce... na je ne da zuciyar uwa. Ba zuciyar mai ba da haƙuri ba. Ba kuma zuciyar mai tausayi kawai ba. Na je ne saboda na ga ƙimar yarinyar.”
Sameer da ke gaba ya yi murmushi a hankali, a ransa ya ce,
“Yanzu na fahimci dalilin da ya sa Ummie ta nace sai ta zo da kanta...”
Sai ya ci gaba da tuƙi cikin nutsuwa, yayin da motar ke ci gaba da tafiya zuwa Armaan Mansion, zuciyar kowane ɗayansu cike da tunanin abin da ke gaba.
⸻
*ARMAAN MANSION*
Yamma ta yi… hasken ranar yamma mai launin gold yana ratsawa ta manyan glass windows na mansion ɗin, yana sauka a kan farin marble floor yana ba falon wani irin annuri.
A falon… dariya ce ta mamaye wajen.
Suhaila na zaune a kan babban L-shaped sofa, ta cire veil ɗinta ta ajiye a gefe, gashinta a ɗaure cikin neat low bun.
A gefenta kuma… Ikraam ce, ɗiyar yayar Ummie, budurwa mai shekaru kusan ashirin da ɗaya, fara ce mai kyakkyawar fuska da fara’a. Sanye take cikin wata sky-blue casual kaftan mai sauƙin kyau.
Wayar Ikraam ce a hannunta, ta kunna wani short video da aka turo musu a family group.
Da mutumin cikin bidiyon ya yi wata irin faɗuwa mai ban dariya…
“Pfffft!”
Ikraam ta fara dariya,
“Wallahi wannan mutumin ba zai taɓa hankali ba!”
Suhaila ma ta kwanta jikin cushion tana dariya,
“Ki mayar baya! Ki mayar baya!”
Ikraam ta sake kunna shi, da mutumin ya sake faɗuwa… su biyun suka fashe da dariya gaba ɗaya.
Har Kubura da ke fitowa daga dining area da tray a hannu ta tsaya tana kallonsu, ta girgiza kai tana murmushi.
Ikraam ta ɗaga kai,
“Kubura zo ki gani mana!”
Kubura ta yi saurin girgiza kai,
“Anty Ikraam aiki nake yi,” ta faɗa tana murmushi.
“Kin yi missing,” Suhaila ta faɗa tana sake fashewa da dariya, sai Kubura ta ci gaba da tafiyarta tana murmushi.
A dai-dai wannan lokacin… takun Ummie ya bayyana yayinda take saukowa daga upstairs, sanye take cikin wani elegant silk house boubou mai launin ivory, ta ɗora mayafinta cikin tsari, ƙamshin turarenta ya fara cika falon tun kafin ta iso.
Da ta ga yadda Suhaila da Ikraam suke ta dariya… sai murmushi ya bayyana a fuskarta,
“Lallai... yau kam ai kun hadu ba zan ji kunne ba a gidan nan.”
Su biyun suka ɗago kai,
“Ummie!”
Suhaila ta yi dariya,
“Dan Allah kalli video nan.”
Ummie ta girgiza kai tana murmushi,
“A’a wallahi, ban da lokacin kallon TikTok ɗinku.”
Ta ƙaraso ta tsaya gabansu,
“Suhaila.”
“Na’am Ummie.”
“Ku shirya.”
Suhaila ta ɗan daidaita zamanta,
“Ina zamu je Ummie?”
“Eh.”
“Akwai wani saƙo da nake so ku kai yanzu.”
Ikraam ta ɗaga gira,
“Mu biyu?”
Ummie ta gyada kai,
“Eh. Ke ma ki shirya.”
Ikraam ta yi murmushi,
“To Ummie.”
Daidai lokacin kuma… suka ji sautin buɗewar babban gate, bayan wasu daƙiƙu… wata baƙar Range Rover Autobiography ta shigo cikin compound a hankali, aka kashe headlights, engine ya mutu, driver ya fito ya buɗe ƙofar baya.
Sai wani dogon mutum ya fito cikin natsuwa, Zayd Armaan.
Sanye yake cikin fitted black polo shirt mai ɗan matse jikinsa, ash-grey chinos trousers da fararen sneakers masu tsabta, a hannunsa smartwatch ɗin luxury na walkiya a hankali.
Gashin kansa ya ɗan jiƙe da zufa kaɗan, alamar daga horse riding club ya dawo, ya gyara agogon hannunsa kafin ya nufi cikin gidan.
Da ya shiga falon… idanunsa suka sauka kan Ummie, nan take murmushi ya bayyana a fuskarsa,
“Assalamu Alaikum, Ummie.”
“Wa Alaikumus Salam, habibi.”
Ya ƙaraso cikin ladabi, ya ɗan rungume Ummie ta baya kaɗan sannan ya zuro kanshi, ya ɗan sunkuya ya sumbaci goshinta kamar yadda ya saba,
“Welcome back.”
Ummie ta shafa kafaɗarsa cikin ƙauna,
“Allah Ya dawo da kai lafiya.”
“Na dawo Ummie na.”
Sannan ya juya ya kalli Suhaila da Ikraam, kafin ma ya yi magana Ikraam ta yi dariya,
“Yayaaa welcome.”
Suhaila kuwa… tun shigowarsa take ta faman murmushi, ta kasa riƙe abin da ke zuciyarta, ta miƙe tsaye da sauri,
“Akhiii... guess what?”
Zayd ya ɗaga gira,
“What?”
Suhaila ta buɗe baki za ta yi magana... sai muryar Ummie ta katse ta cikin natsuwa,
“Suhaila.”
Suhaila ta yi shiru nan take, ta juya ta kalli Ummie, Ummie ta kalleta da seriousness amma bata sake cewa komai ba.
Suhaila ta fahimci abinda Ummie take nufi, sai ta cije leɓenta tana murmushi,
“Sorry Ummie...”
Ikraam ta riƙe hannunta tana dariya,
“Zo mu tafi muyi abinda aka ce mana.”
Zayd ya haɗe gira kaɗan yana kallonsu, ya kalli Ummie, ya sake kallon Suhaila, sai ya yi murmushi,
“Hmmm... na ga akwai wani secret da ake ɓoye mini.”
Ummie ta gyara mayafinta cikin natsuwa,
“Ba wani secret ba ne.”
Ta juya ta kalli Suhaila da Ikraam,
“Ku tafi kar lokaci ya ƙure muku.”
“To Ummie.”
Su biyun suka nufi stairs dan su shirya, suna hawa sama amma… Suhaila ta juyo ta sake wa Zayd kallon da ya sa ya ƙara rikicewa.
Har ta kai ƙarshen staircase din… sai ta juya tana murmushi,
“Akhi...”
Ikraam ta ja hannunta,
“Zo mana!”
Ta yi dariya,
“Okay, okay... I’m going.”
Suka shige.
Zayd ya ci gaba da binsu da ido har suka bace, sai ya waigo ya kalli Ummie,
“Ummie... what is going on?”
Ummie ta yi murmushi kawai,
“Ka fara zuwa ka ci abinci. Na sa an haɗa maka abinci.”
Zayd ya yi dariya a hankali,
“Ummie... kin canja topic kenan?”
Ta ɗan ɗaga gira,
“Ka yi abin da na ce.”
Ya ɗaga hannayensa cikin surrender,
“As you wish...”
Ya nufi dining area yana girgiza kai cikin murmushi… amma a zuciyarsa… tambaya ɗaya ce kawai ke yawo,
“Me suke son ɓoye mini?”
Bayan da Ikraam da Suhaila suka fice daga gidan gaba ɗaya… Ummie ta juya ta kalli Zayd tana gyara masa kujerar da zai zauna, ta ɗan yi murmushi kafin ta ce cikin murya mai cike da kulawa,
“Zo.”
Zayd ya ƙaraso yana murmushi,
“Zo ka ci wani abu.”
Ba tare da ya ƙara gardama ba, ya zauna cikin nutsuwa.
Dining ɗin ya haskaka da manyan crystal chandeliers masu walƙiya, yayin da doguwar dining table ta marble ke ɗauke da kyawawan flower arrangements da aka sauya da fresh white lilies.
Dama already Kubura ta shirya komai.
A tsakiyar table ɗin… an jera nau’o’in abinci iri-iri cikin tsari mai kayatarwa.
Akwai farfesun kaza mai ƙamshi, da aka yi da kayan yaji masu ƙanshi, a gefe kuma akwai jollof rice mai launin gold, tare da grilled chicken da aka kawata da lemon slices.
An kawo white rice mai laushi tare da miyan vegetable sauce, akwai mashed potatoes da buttered vegetables, sai fresh garden salad mai cike da lettuce, cucumber, cherry tomatoes da olives.
A wani gefen kuma akwai warm butter bread rolls, croissants da cheese platter, sai fresh fruit platter mai ɗauke da strawberries, grapes, watermelon, pineapple da kiwi.
Abin sha kuwa… fresh orange juice, fresh watermelon juice, mint lemonade, da kuma chilled water.
Komai cikin tsari irin na gidan da aka saba da alfarma, amma babu hayaniya ko nuna isa.
Ummie da kanta ta ɗauki plate, ta zuba masa ɗan jollof rice, ta ɗora masa grilled chicken, ta ƙara salad kaɗan a gefe, ta ajiye masa,
“Ka ci.”
Zayd ya ɗan yi murmushi,
“Ummie...”
Ta ɗaga gira,
“Hm?”
Sai ya ɗan langwabe kai cikin shagwaba,
“Yayi yawa faa.”
Ta ɗan taɓe baki cikin wasa,
“Ni dai na ce ka cinye komai a nan, idan ba haka ba zamu kwana a nan ne.”
Ya yi dariya a hankali,
“Now eat.”
“Shi kenan.”
Ta matsa kujerarta kusa da shi kaɗan, ta zauna tana kallonsa.
Zayd ya fara cin abincin cikin nutsuwa, lokaci zuwa lokaci… Ummie tana ƙara ɗora masa wani abu,
“Ɗan ƙara salad.”
“Ga juice.”
“Ka ɗan ci wannan chicken ɗin ma.”
Zayd ya yi murmushi yana girgiza kai,
“Ummie... kina kula da ni kamar har yanzu ina ɗan shekara goma ne.”
Ta yi murmushi mai taushi,
“A wurina...” ta ɗaga hannu ta shafa gefen goshinsa,
“Ko shekara hamsin ka kai... za ka ci gaba da zama ƙaramin ɗana.”
Zayd ya ɗan yi dariya, ya ci gaba da cin abincinsa cikin natsuwa.
Amma duk da murmushin da ke kan fuskarsa… Ummie ta lura da wani abu, tun lokacin da ya shigo gidan… ya yi ƙoƙarin ɓoye gajiyarsa, amma idanunsa sun nuna gajiya, fuskarsa kuma ta nuna cewa kwanakin nan bai samu cikakken hutu ba.
Ta zuba masa ido cikin tausayi,
“Zayd...”
Ya ɗago yana tauna abincin,
“Na’am Ummie.”
“Ka gaji.”
Ba tambaya ba ce, tabbatarwa ce.
Zayd ya yi murmushi kaɗan,
“A little.”
“‘A little’ ɗin nan da kake faɗa...” ta girgiza kai,
“…ni na san ya fi haka.”
Ya sauke cokalin hannunsa na ɗan lokaci,
“Everything is under control now.”
Ummie ta yi shiru, ta san ɗanta, duk lokacin da yake cikin damuwa… kalma ɗaya yake amfani da ita, “everything is under control,” alhali ita ce kalmar da ke nuna cewa akwai abubuwa da yawa da yake ɗauke da su shi kaɗai.
Ta ɗan shafa hannunsa,
“Bayan ka gama... ka haura sama. Ka huta. Kada ka sake buɗe laptop yau. Kada ka sake duba wani report. Kada ka sake shiga meeting. Weekend ne.”
Zayd ya yi murmushi,
“Yes, ma’am.”
Ta ɗan yi dariya,
“Haka nake so.”
Ya ƙarasa cin abincinsa cikin nutsuwa, bayan ya gama… ya ɗauki tissue ya goge hannunsa, sannan ya miƙe tsaye,
“Thank you, Ummie.”
Ta gyada kai cikin murmushi, ya ɗan sunkuya ya sumbaci goshinta cikin girmamawa,
“I’ll go upstairs and rest.”
“Good.”
Ta bi shi da ido har ya juya ya nufi babban staircase, da ya ɓace daga ganinta murmushin da ke fuskar Ummie ya ragu a hankali, ta sauke wani dogon numfashi, ta san… lokaci ya yi, lokacin da za ta yi magana da ɗanta game da abin da ke zuciyarta.
————————
*MALALI …*
Bayan tafiyar Ummie… falon gidan Umma ya sake komawa cikin nutsuwa.
Baffa Musa ya zauna shiru na wasu daƙiƙu, kamar yana tattara kalmomin da zai faɗa, daga ƙarshe… ya ɗaga kai ya kalli Raihana,
“Raihanatu...”
“Na’am, Baffa.”
Ya yi mata alamar ta ƙara matsowa kusa, ta matsa cikin ladabi, ta zauna a kan daddumar kusa da shi, Umma ma tana zaune gefe, idanunta na kan mijinta.
Baffa ya yi murmushi a hankali,
“Kin ji duk abin da Hajiya ta faɗa ko?”
Raihana ta gyada kai,
“Na ji.”
Ya ɗan yi shiru, sannan ya ce cikin natsuwa,
“Na san wannan maganar ta zo miki ba zato. Saboda haka... ba na son ki firgita.”
Raihana ta yi shiru tana sauraro.
Baffa ya ci gaba,
“Da farko dai... ina so ki sani... ba zan taɓa tilasta miki aure da kowa ba. Ko da wa ne. Saboda aure ibada ne. Kuma zaman lafiya ba ya samuwa sai da yardar zuciya.”
Raihana ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta.
Baffa ya ci gaba,
“Kin san akwai Haris. Tun kafin wannan abin ya faru... ya zo ta ƙofar da ta dace. Ya nemi izini. Amma na ba shi dama ya nemi yardarku.”
Ya ɗan yi murmushi,
“Yanzu kuma... ga wata ƙofa Allah Ya buɗe mana. Wata uwa ta zo da kanta. Ta nuna abin da ke zuciyarta.”
Ya sauke numfashi,
“Saboda haka... ba zan fifita kowa ba. Ba zan hana kowa ba. Ba kuma zan matsa miki ba.”
Ya kalli Raihana cikin ƙauna irin ta uba,
“Abin da kawai nake so... shi ne... ki ba wa kowannensu dama. Ba wai damar soyayya ba. A’a. Damar a san su yadda ya kamata. Ki yi addu’a. Ki yi istikhara. Ki kuma yi tunani cikin natsuwa. Wanda Allah Ya ga alkhairi yana tare da shi... shi ne Allah zai daidaita al’amari da shi.”
Shiru ya mamaye falon, Raihana ta sunkuyar da kanta, maganar Baffa ta yi mata nauyi, amma ta ji daɗin yadda bai matsa mata ba.
Daga ƙarshe ta ɗaga kai,
“Baffa...”
“Na’am.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci,
“Duk abinda kuka zaɓa min zan karba, na san ba zaku taɓa zabamin abinda zai cutar da ni ba.”
Baffa ya yi wani murmushi mai cike da jin daɗin kalamanta, amma duk da haka sai ya ce,
“Raihana, ina so ki nemi zabin Allah da kanki, wanda duk ya fi kwanciya a ranki shi ne zabina nima.”
Sai ta jinjina kai kafin ta ce,
“…zan bar abin a hannun Allah.”
Baffa ya yi murmushi mai cike da gamsuwa,
“Haka nake so. Domin... abin da Allah Ya rubuta... shi ne mafi alkhairi.”
Umma ta yi murmushi tana kallon ’yarta,
“Allah Ya zaɓa miki abin da zai zama alkhairi a duniya da lahira.”
“Ameen.”
Falon ya sake yin shiru… amma wannan karon… ba shiru ne na damuwa ba, shiru ne na mutane da suka miƙa al’amuransu ga Allah.
Not edited