Free chapter · Read without an account

THE FIRST REAL MEETING

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN


*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER - TWENTY NINE:29*

*THE FIRST REAL MEETING*

*JIDDAAH BARKUM*

⸻

A hankali Imraan ya sauke gilashin motar da ke gefensa kaɗan, ya ɗan leƙa wajen da hayaniyar take.
Idanunsa suka bi taron mutanen da suka cika bakin gidan.

Sai ya juyo ya kalli Zayd.
Amma Zayd… kamar wanda bai ma san ana wani abu a wajen ba.
Hannunsa ɗaya yana kan kujerar motar, idanunsa a kan wayarshi yana latsa screen din.

Imraan ya ɗan dafe kansa,
“Wai nan ne unguwar?”
Ba tare da Zayd ya kalleshi ba, sai kawai ya yi ɗan nodding.

Imraan ya buɗe baki yana kallon wajen,
“Taɓ!”
Ya sake leƙawa ta glass ɗin,
“Damn...”
Sai ya juyo wajen Zayd,
“Toh ina ne gidan da muka zo?”

Zayd ya ɗan ɗago kansa, idanunsa suka sauka kan wata ƙofa da ke gabansu, sannan ya kalli window ɗin da ke gefen Imraan, ya sake sauke kansa.
Cikin sanyin muryarsa ya ce,
“Ga gidan nan ai.”

Imraan ya bi inda yake kallo.
Mutane sun cika bakin gidan, wasu a tsaye, wasu sun matsa gefe, wasu kuma suna kallon wani abu da ke faruwa a tsakiyar taron.

Sai Imraan ya zaro ido,
“Don’t tell me...”
Ya sake kallon Zayd,
“Gidan nan ne ake dambe?”
Zayd bai amsa ba, kawai ya yi masa banza.

Imraan ya sake kallon kofar gidan, a hankali idanunsa suka fara bin abin da ke faruwa, sai suka tsaya kan wata yarinya da ke gefe…
Raihana.
Tana riƙe da hannunta ɗaya, fuskarta ɗauke da ɗan hawaye saboda bugun da ta samu.
Yaya Hamza yana tsaye kusa da ita, yana ƙoƙarin taimaka mata ta tashi.

Imraan ya ɗan matsa kusa da glass ɗin,
“Rascal...”
Bai amsa ba, sai ya ce,
“Look at that lady.”

Zayd ya ɗan ɗago idanunsa, kallon da ya yi bai wuce ƴan daƙiƙu ba, amma… ya gane ta.
Ta ɗan sunkuya tana ƙoƙarin gyara hannunta, tana sanye da zanin atamfa kawai, wanda ya yi kama da zanin wanka saboda yadda rikicin ya bar komai ya watse.
A jikinta kuwa akwai wata black T-shirt mai sauƙi.
Wuyan hijab ɗinta ya yage, ya zame daga kafadarta, har gashinta ya fito fili.

Fuskarta ba ta cikin yanayin da ya saba gani a duk sanda ya ganta, ba waccan natsuwar da ya gani a speech ba, ba kuma waccan matar da taɓa tsayar da convoy ɗinsa ba.
A wannan lokacin… tana cikin wani irin yanayi na rikici da rashin shiri.

Zayd ya kalleta na ƴan daƙiƙu, sai ya ɗauke idanunsa, kamar bai gan ta ba, ya mayar kan wayarsa.

Imraan ya kalli Zayd, sai ya sake kallon Raihana, sai ya dawo ya kalli Zayd.
A hankali murmushi ya fara bayyana a fuskarsa,
“Kai...”
Zayd bai kalleshi ba.

Imraan ya ɗan karkatar da kansa,
“Rascal...”
Shiru, sai ya yi wata ƙaramar dariya,
“Wannan ai ita ce yarinyar nan.”
Zayd ya yi shiru.

Imraan ya sake waigo masa, sai ya ƙara da wata irin dariya,
“After they put your picture together with hers...”
Ya ɗan dakata, yana kallon reaction ɗin Zayd,
“…itace muka zo wajenta???”

Zayd bai amsa ba, kawai ya ɗan lumshe idanunsa.
Imraan ya ƙara kallon Raihana, sai ya dawo da kallonsa kan Zayd,
“Gaskia Zayd kai munafuki ne kutttt!.”
Ya faɗa da mugun mamaki a fuskarshi.

Zayd ya ɗan juya masa kai, ya dago kaɗan ya kalli Imraan sai ya sake hade fuska.
Imraan ya fashe da dariya,
“Dama wajenta zamu zo asheee??”

Zayd ya kalleshi kafin yace,
“Imraan stop it!”
“Okay, okay...”
Ya ɗaga hannunsa,
“I’m quiet.”

Amma bayan seconds biyu… sai ya sake leƙawa wajen,
“Amma Rascal...”
Zayd ya ɗan kalleshi.
Imraan ya yi murmushi,
“Your future wife is currently fighting for her life outside.” 

Zayd ya sake ɗauke kansa gefe,
“Imraan.”
“Okay! Okay!”
Imraan ya rufe bakinsa yana dariya, amma idanunsa… har yanzu suna kan Raihana.

A daidai lokacin da hayaniyar ke fara raguwa, ƙarar kiran sallar Magariba ta fara tashi daga masallacin da ke kan layin,
“Allahu Akbar... Allahu Akbar...”

Nan take yanayin wajen ya sauya, mutanen da suka tsaya suna kallon rikicin suka fara watsewa ɗaya bayan ɗaya, kowa ya kama gabansa.
Wasu suka shiga gidajensu, wasu suka wuce zuwa masallaci, yayin da sauran suka tsaya kaɗan suna jiran a gama watsewar gabaɗaya.

A ƙofar gidan Baffa Musa kuwa… Bintu, Maryam, Raihana da Mama Sabuwa sun riga sun shiga ciki, kayan da suka watse a ƙasa ma an kwashe su gaba ɗaya.
Babu sauran taron mutane, babu hayaniyar da ta cika layin mintuna kaɗan da suka wuce, kowa ya kama gabansa.

A cikin motar kuwa, Imraan ya ɗan kalli wajen ta glass ɗin motar, sai ya sauke ajiyar zuciya,
“Finally...”
Zayd ya ɗan kalli agogon motarsa, sai ya juya ya kalli Imraan,
“Mu je mu yi sallah.”
Imraan ya ɗan jinjina kai,
“Okay.”
Ya kashe motar.

Suka buɗe ƙofofin motar a hankali suka fito.
Zayd ya gyara gefen shaddarsa, ya ɗan daidaita hularsa, sannan ya kalli hanyar masallacin da ke ɗan gaba a layin.
Imraan ya rufe motar ya kulle ta, suka fara tafiya tare, a hankali, ba tare da wata magana ba.
Zayd yana gaba kaɗan, Imraan yana gefensa, har suka shiga cikin layin da ke kaiwa zuwa masallacin.

————

Mama Sabuwa ta shigo da Bintu tana riƙe da hannunta gam, kamar ba za ta sake ta ba, fuskarta cike take da fushi, tana jan ta zuwa cikin gidan yayin da take sababi ba tare da ta damu da wanda yake sauraron ta ba,
“Wallahi duk wani shege da zai sake ɗaga hannu ya daki min yarinya, na rantse da girman Allah sai mun je gaban ’yan sanda! Saboda rashin kunya da rashin mutunci, a bakin ƙofar gida zaku tarar mata kuna duka wai saboda me? Saboda ta ari kaya?”

Bintu ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta.
Mama Sabuwa ta ci gaba,
“Sabida uban baqin hali da rashin albarka! Wannan yarinyar da kuke gani ai ’yar uwarku ce, amma kuna ɗaukar ta kamar ba ta da daraja. Kayan da take sawa kuna gani ai kunsan kalar suturunta bana banza a ciki, kafin ta jira ubanta ya siya mata kaya, da kudinta ma tana siya! Nima ita ce take siyo min kaya wani lokaci!”

Ta ɗan ja numfashi, sannan ta ƙara da zafi,
“Shine kawai saboda ta ɗauki wasu ’yan tsumman kaya sai ku haɗu a bakin gida ku mata tijara?”

Mama Indo wadda take tsaye a gefe tun shigowarsu, ta yi huci mai ƙarfi, sai ta tako kai tsaye zuwa gaban Mama Sabuwa,
“Wallahi Sabuwa, kin ji kunya kuwa?”
Mama Sabuwa ta tsaya.

Mama Indo ta ci gaba cikin fushi,
“Ke fa katuwar balagaggiya ce! Da kika kama yarinyar nan kika buge ta, idan kin daki Maryam, uwar me za ki ji?”
Mama Sabuwa ta ɗan ɗaga gira,
“Saboda na kare yarinyata, bazan zauna ina kallo su kashe mun ita ba, sun taru a kanta kamar sun samu jaka.”

“Yarinyarki?”
Mama Indo ta yi dariyar takaici,
“Wannan shi ne abin da nake magana a kai! Girman banza kawai, dama ke ba ki da aikin komai sai ki shigar wa Bintu fada ta fita ta yi wa mutane hayaniya a gaban jama’a.”
Ta nuna ƙofar gidan da hannu,
“Ba kunya, ba tsoron Allah.”

Mama Sabuwa ta matse hannun Bintu sosai,
“Amma uban mesa Maryam ta mare ta!”
“Ta mare ta ne bayan Bintu ta zage ta!”
Mama Indo ta katse ta,
“Ko kin manta abin da ya faru?”

Bintu ta ɗago kai,
“Wallahi ni dai kar wacce ta sake kiran sunana, idan ba haka ba sai na zagi mata—”
“Ke dallah rufewa mutane baki!”
Mama Indo ta dakatar da ita,
“Uwarkice sa’ar yi na bake ba mara kunya.”

Sai ta sake kallon Mama Sabuwa,
“Wannan maganar kayan ma, bari mu faɗi gaskiya, idan Bintu ba ta da wani abu a ranta, me ya sa za ta shiga ɗakin Hajara ta ɗauko kayan Raihana ba tare da izini ba?”
Bintu ta zubawa Mama indo harara.

Mama Sabuwa ta kalleta.
Mama Indo ta ci gaba,
“Ta ce za ta ara?”
Ta yi ɗan dariya,
“Me ya sa ba ta jira Raihana ta dawo ta tambaye ta da kanta ba?”
“Tun da dai duk inda ta je, za ta dawo gidan nan, me ya sa ba ta jira ba?”

Mama Sabuwa ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, amma Mama Indo ba ta tsaya ba,
“Saboda akwai wata tsiyar da kuke kullawa ke da ita.”
Ta kalli Bintu,
“Ke kuma, makirci ya kai ki har ɗakin Raihana.”
Bintu ta sake zuba mata harara, kafin cikin gunguni tace,
“Wlh ni ba makira bace, tunda baa tsaya anji me zance ba—”
“Uban me zakice toh?”
Mama Indo ta katse ta,
“To me ya kai ki wardrobe ɗinta?”
Shiru.
Bintu ta kasa amsawa.

Mama Sabuwa ta ɗan kalleta, wannan karon fushin da ke fuskarta ya ɗan ragu.
Sai Mama Indo ta sauke murya,
“Allah dai Ya sa iya kayan da kika ɗauka kenan...”
Ta ƙarasa tana kallon Mama Sabuwa kai tsaye.

Tsakar gidan ya yi shiru.
Bintu ta tsaya tana kallon ƙasa.
Mama Sabuwa ta ƙara matse hannun Bintu, ta janyo ta kusa da ita,
“Dalla mu tafi! Ki kyale wannan tsohuwar munafukar nan, dama daga ita har ’yarta, ba abinda suka iya sai shishigi da neman suna!”
Ta juya ta kalli Mama Indo da wani irin kallo,
“Idan ba haka ba, me ya sa ita Raihana da Hajara, uwar Raihana, ba su ce komai ba? Sai ku iyayen bani na iya?”

“Wooooohooooo!”
Mama Indo ta ɗaga murya da ƙarfi,
“Babbar banza! Katuwar banza!”
Ta tako gaba,
“Ke da kika yi dambe da yar cikinki a gaban mutane, har yanzu kina da bakin magana?”
Mama Sabuwa ta tsaya cak,
“Kin ji kunya kuwa, Sabuwa.”
“Ke—”

Amma kafin ta ƙarasa, Mama Indo ta sake ɗaga murya,
“Ke dai girman kai ne ya cika ki! Kullum sai ki ga laifin kowa, amma naki ba ki taɓa gani!”
Mama Sabuwa ta yi mata kallon banza, sai ta ja Bintu,
“Mu tafi!”
Ta juya da sauri, ta nufi ɗakinta, Bintu ta bi bayanta ba tare da ta ƙara cewa komai ba.

Da suka shiga, Mama Sabuwa ta banka ƙofar ɗakin da ƙarfi,
Tak!
Ta turo ƙofar.
Falon ya sake yin shiru.

Mama Indo ta tsaya tana kallon ƙofar da Mama Sabuwa ta rufe.

*Dakin Umma…*
A cikin ɗakin Umma kuwa, Raihana tana zaune a gefen kujera, hawaye suna gangarowa a fuskarta ba tare da ta damu da share su ba.
Hannun da ta fadi da shi yana mata zafi sosai.

Yaya Hamza yana zaune kusa da ita, yana kallon yadda take kuka cikin damuwa.
Umma kuwa tana zaune a gefe, shiru kawai ta yi, idanunta a kan Raihana.

Yaya Hamza ya ɗan kalli hannun Raihana, sannan ya ɗago idanunsa zuwa Umma,
“Ina ganin ya kamata mu kai ta wajen mai duba karaya.”
Umma ta kalle shi,
“Kana ganin kamar ta karye ne?”
Yaya Hamza ya girgiza kai,
“A’a, gara mu je a duba a tabbatar.”
Ya sake kallon Raihana,
“Kalli yadda take kuka, kar mu yi sakaci, Umma, ko hannun ya samu karaya ne, ko kuma akwai gocewar ƙashi... sai an duba.”

Umma ta ɗan yi shiru, sai ta jinjina kai,
“Toh, sai ku je.”
Ta kalli Raihana,
“Allah Ya sa ba karaya ba ce.”
Raihana ta share hawayenta da ɗayan hannunta.

Umma ta ci gaba,
“Tashi ki saka hijabinki, ku je a duba.”
Raihana ta jinjina kai, a hankali ta miƙe, ta nufi ɗakinta tana riƙe da hannun da ke ciwo.

Bayan ƴan mintuna ta dawo sanye da hijabinta, ta gyara shi a kanta… sai suka ji muryar Baffa daga tsakar gida,
“Assalamu alaikum.”
Yaya Hamza ya ɗago kai.
Umma ta kalli ƙofar ɗakin.

Baffa ya shiga tsakar gidan, sannan kai tsaye ya nufi ɗakin Umma.
Da ya kai bakin ƙofar, ya ɗan daga labulen, sai ya yi ɗan turuus.
Idanunsa suka sauka kan Yaya Hamza da ke zaune kusa da Raihana, amma bai ce komai ba, kawai ya kalli Umma,
“Hajara...”
Umma ta ɗago kai,
“Naam?”
Baffa ya ɗan kalli Raihana, sannan ya maida idanunsa kan Yaya Hamza,
“Kinada baƙi a waje.”

Bai jira Raihana ta amsa ba, sai ya ce,
“Hamza, ka je ka yi musu iso zuwa falona.”
Ya ɗan kalli tsakar gidan,
“Tunda babu NEPA, kar su zauna a tsakar gida, akwai sauro.”
Yaya Hamza ya jinjina kai nan take,
“Toh, Baffa.”
Ya miƙe.

Baffa ya ɗan matsa gefe ya ba shi hanya, Yaya Hamza ya fita daga ɗakin.
Baffa kuma ya ɗan tsaya yana kallon Umma na ƴan daƙiƙu, kamar akwai wani abu da yake son tambaya… amma sai kawai ya karaso ciki.

Umma ta kalli Raihana, sannan ta yi mata magana cikin sanyin murya,
“Ki je ɗaki ki ɗan kintsa kafin su shigo, idan kin dawo sai ku je a duba hannun.”
Raihana ta jinjina kai,
“Toh, Umma.”
Ta juya ta shiga ɗakinta.

Baffa ya bi ta da kallo na ƴan daƙiƙu, sannan ya juya ya kalli Umma,
“Meye ya faru da hannunta?”
Umma ta ɗan sauke ajiyar zuciya, ta san sosai cewa idan ta faɗa masa abin da ya faru a yau a ƙofar gidan, sabon rikici zai balle a cikin gidan nan, saboda haka ta zaɓi kalma mafi sauƙi,
“Fāɗuwa tayi ne... ta bugu da hannun.”

Baffa ya yi shiru, bai tambayi komai ba, kawai ya kalli Umma na ƴan daƙiƙu, sannan ya ɗauke idanunsa.
Shiru ya sake ratsa ɗakin.

Bayan ɗan lokaci, Baffa ya ɗago kai,
“Raihana.”
Daga cikin ɗakin ta amsa,
“Naam, Baffa?”
“Kinata zaune kin bar mutane suna jira, meye kike yi ne?”
Muryarsa ba ta da ƙarfi, amma akwai irin wannan nutsuwar da ke sa mutum ya san cewa ba a son a ɓata lokaci.

A cikin ɗakin kuwa, Raihana ta tsaya cak, ta ɗan daure fuska.
Waɗanne mutane? Waye zai zo wajenta yanzu?
Ta san dai ba Haris ba ne, idan Haris ne, da farko zai nemi izini kafin ya zo.
Amma Baffa ya ce mutane suna jira.

Ta ɗan tsaya tana tunani, sai ta tuna da halin Baffa, idan ta tsaya dogon tunani, zai iya faɗa,
“Gani nan, Baffa.”
Ta gyara hijabinta da sauri, sannan ta fito daga ɗakin.

Da ta bayyana a bakin ƙofar, Baffa da Umma suka ɗan kalleta.
Baffa bai ce komai ba, kawai ya juya ya nufi hanyar fita, sai ya ce cikin nutsuwa,
“Wuce.”
Raihana ta sunkuyar da kanta,
“Toh.”
Ta fara tafiya a gaba, Baffa yana biye da ita a baya.

Umma kuwa ta tsaya a ɗakin tana kallonsu.
Raihana ta yi ƴan matakai kaɗan, har suka isa bakin falon Baffa.
Kafin ta shiga… ta ɗan sauke ajiyar zuciya, har yanzu ba ta san wanda yake jiran ta a ciki ba.

Sai ta taka ƙafar ta cikin falon, Baffa ya shigo bayanta.
Tun kafin Raihana ta ga waye a cikin falon… sai wani irin kamshin turare ya fara risƙar hancinta, ta ɗan tsaya a bakin ƙofar.

Kamshin… ta san shi, tabbas ta taɓa jin wannan kamshin a wani wuri, amma ina? Kuma daga wajen wa?
Ta kasa tuna wa.
Ta ɗan ja numfashi a hankali, sannan ta shiga,
“Assalamu alaikum.”

Imraan ne ya amsa,
“Wa alaikumussalam.”
Ya ɗago kansa daga wayarsa, idanunsa suka sauka kanta, sai ya yi shiru na ɗan daƙiƙu.

A wannan lokacin ne Baffa ya shigo falon.
Zayd kuwa… da ya ji sallamar, ya ɗan ɗago kansa, nan take idanunsa suka sauka kanta.
Raihana.
Ya gane ta.
Kamar yadda ita ma, a wannan lokacin, idanunta suka fara ɗaga wa… sai suka sauka kansa.
Zayd.

A hankali Zayd ya sauko daga kan kujerar da yake zaune, bai yi sauri ba, bai yi magana ba, kawai ya durkusa cikin nutsuwa.
Sky-blue shaddar da ke jikinsa ta zauna masa da kyau, hular da ke kansa kuma ya ƙara masa wani irin tsari na musamman.

Raihana kuwa… ta tsaya a gefe, hannunta ɗaya ya kama bakin hijabinta gam, zuciyarta ta fara bugawa da wani irin sauri.
Ba don ba ta san Zayd ba, ta san shi, sun riga sun taɓa haɗuwa, sun riga sun yi magana, har ma suna da wani irin history da ba zai taɓa sa ta manta shi da sauƙi ba.

Amma… wannan haɗuwar ta yau ta bambanta, domin yanzu ta san dalilin zuwansa, shi ne mutumin da ya zo neman aurenta.

Baffa ya ƙaraso cikin falon, bai ma zauna ba, sai ya kalli Raihana,
“Zauna mana.”
Raihana ta ɗan kalli kujerun, sai ta zaɓi wani waje a can gefe, nesa kaɗan da su, ta zauna a kan carpet a hankali, hannunta har yanzu rike gamm da bakin hijabinta, kanta kuma ta sunkuyar.

Baffa ya kalli Zayd,
“Ka koma kujerarka mana, ka zauna.”
Zayd bai yi magana ba, sai ya dan girgiza kai kafin a hankali yace,
“Baba nan ma ya isa.”
Imraan kam murmushi kawai yake yana, kallon Zayd a ranshi kuwa cewa yake, kai rascal a gaban sirukaii.

Baffa ya ɗan gyara tsaiwarsa, sannan ya kalli Raihana,
“Dama na biyota ne.”
Ya ɗan dakata,
“Ina so in gaya muku cewa ashe ciwo ma ta ji.”
Raihana ta ɗan ɗago kai.

Baffa ya ci gaba,
“Ummanta ta ce hannunta yana mata ciwo, yayanta zai kaita a duba.”
Ya ɗan kalli Zayd,
“Shine nace bari dai na sanar da ku, idan kun gama za su je can a duba.”

Zayd yana zaune shiru, kansa ɗan sunkuye, bai ce komai ba.
Imraan kuwa ya ɗan karkatar da kansa yana kallon Zayd, murmushin nan nasa har yanzu yana kwance a gefen bakinsa,
“Baffa, ai shi ma likitan ƙashi ne,” ya faɗa cikin natsuwa, “ina ganin ba sai an je asibiti ba, zai iya duba hannun nata.”

Baffa ya ɗan ɗaga gira,
“Zayd?”
A hankali Zayd ya ɗago kansa, idanunsa suka fara sauka kan Baffa, sannan suka ɗan wuce kan Raihana, sai suka tsaya a kan hannun nata da take riƙe da ɗayan hannunta.

Raihana kuwa… da ta ji maganar Imraan, zuciyarta ta yi wani irin tsalle, ta ɗan ɗago idanunta.
A wannan karon, idanunta suka haɗu da na Zayd.
Na ƴan daƙiƙu… dukansu suka tsaya, kamar babu wani abu a wajen, kamar hayaniyar da ta faru a waje ba taɓa faruwa ba, kamar kuma wannan shi ne karo na farko da suka haɗu ido da ido.

Zayd ya kalli hannunta na ɗan lokaci, sannan ya ɗauke idanunsa.
Baffa ya kalli Zayd,
“Za ka iya dubawa?”
Zayd ya yi ɗan nodding,
“Ehh.”
Muryarsa ta fito a hankali, ba tare da wani ƙarin bayani ba.

Imraan kuwa ya kasa riƙe murmushinsa, ya ɗan kalli Raihana, sannan ya kalli Zayd,
“Shi kenan Baffa, problem solved.”
Baffa ya yi ɗan murmushi,
“Toh.”
Sai ya kalli Raihana,
“Ki nuna masa hannun.”

Raihana ta ɗan haɗiye yawu, ta kalli hannunta, sai ta kalli Zayd.





Not edited

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.