Free chapter · Read without an account
WHEN SILENCE SPOKE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER- THIRTY:30*
*WHEN SILENCE SPOKE*
*JIDDAAH BARKUM*
———————-
Zayd ya miƙe a hankali daga durkushen da yayi, babu gaggawa a motsinsa.
Ya ƙarasa gabanta, sannan ya ɗan tsaya na ƴan daƙiƙu yana kallon hannun nata kafin ya rage tsayinsa a hankali, ya durƙusa dai-dai gabanta.
Ba kusa sosai ba, akwai ɗan space tsakaninsu.
Raihana ta ɗan ja jikinta baya saboda kusancinsa, amma da ta lura da idanun Baffa a kanta, sai ta hakura ta zauna yadda take.
Zayd ya ɗaga idanunsa zuwa gare ta na ɗan lokaci,
“Wanne ne?”
Raihana ta ɗan ɗaga hannun da yake ciwo,
“Wannan.”
Muryarta ta fito ƙasa-ƙasa.
Zayd ya kalli hannun sosai, akwai ɗan kumburi a wajen wuyan hannun, kuma yadda take riƙe shi yana nuna cewa duk wani motsi yana mata ciwo,
“Let me see.”
Raihana ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai a hankali ta miƙa masa hannun.
Zayd ya karɓa cikin matuƙar hankali, ya riƙe wuyan hannunta da yatsunsa, ba tare da matsawa ba.
A take… wani irin sensation ya ratsa hannayensu, da sauri ya sake rike hannun na ta dan saura kadan ya kwace daga rikon da yayi masa.
Ta ɗan ja numfashi, shi ma Zayd ya lura, amma bai ce komai ba.
Ya fara examination ɗin cikin nutsuwa, da farko ya duba kumburin, sai ya duba launin yatsunta, ya taɓa gefen wuyan hannun a hankali, yana matsawa wurare daban-daban domin gano inda ciwon ya fi yawa,
“Here?”
Ya taɓa wani wuri.
Raihana ta ɗan runtse ido, sai ta girgiza kai alamun ba nan bane.
Ya matsa ɗan gefe,
“Here?”
Nan take ta ɗan ja numfashi,
“Hmm.”
Zayd ya ɗan kalli fuskarta, sai yayi sauri dauke kai, ya sake duban wajen.
Bai yi gaggawar motsa hannun ba, sai ya riƙe yatsunta a hankali,
“Can you move your fingers?”
Raihana ta motsa yatsunta a hankali, ɗaya bayan ɗaya.
Zayd ya lura da motsin.
Sai ya ɗan taɓa yatsunta,
“Can you feel this?”
Ta jinjina kai,
“Eh.”
Zayd ya kalli tafin hannunta, sannan ya sake duban yatsunta, ya ɗan matsa kusa da wuyan hannun, yana neman ganin ko akwai wani obvious deformity ko kuma ƙashin ya sauya matsayinsa.
A wannan karon ya riƙe hannun nata da kyau,
“Relax your hand.”
Raihana ta ɗan kalleshi,
“I’m trying.”
Zayd ya ɗan ɗaga gira,
“Try harder.”
Imraan dake gefe ya sunkuyar da kansa yana ɓoye dariyarsa.
Raihana ta kalleshi da gefen ido, amma Zayd bai ma lura da Imraan ba, ya ci gaba da aikin nasa.
A hankali ya ɗan gwada ƙaramin movement na wuyan hannun, nan take…
“Aah!”
Raihana ta janye hannunta da sauri, hawaye suka cika idanunta,
“Ya isa...”
Ta yi ƙoƙarin kwace hannun gaba ɗaya daga hannunsa.
Amma kafin ta samu ta janye shi, Baffa ya ɗaga murya daga inda yake tsaye,
“Meye haka?”
Raihana ta kalli Baffa da idanu cike da hawaye,
“Baffaaa...”
Muryarta ta fito cikin wata irin shagwaɓa da ita kanta ba ta san tana yi ba,
“Da zafi faaa...”
Ta ƙara kallon hannunta, hawaye ɗaya ya sulale daga gefen idonta.
Baffa ya ɗan matso da kansa gaba,
“Sannu, toh.”
Muryarsa ta sauka sosai,
“Ai yanzu za a gama.”
Raihana ta haɗiye kukanta, amma hawaye suka ci gaba da zubowa.
Zayd kuwa… ya ɗan tsaya, idanunsa suka sauka kan fuskarta, na ƴan daƙiƙu bai ce komai ba.
Sai ya sake kallon hannun, a wannan karon ya rage motsinsa sosai,
“Sorry.”
Kalmar ta fito a hankali.
Raihana ta ɗago idanunta zuwa gare shi, kamar ba ta yi tsammanin zai faɗi ba.
Zayd ya ɗan gyara yadda yake riƙe da hannun nata, ya sake duban wuyan hannun, musamman wajen kumburin, sai ya duba yatsunta, ya sauke hannunta a hankali, ya zauna daidai a kan diddigen ƙafarsa, yana kallon hannun kamar yana haɗa duk abin da ya gani a cikin kansa.
Imraan kuwa haryanzu murmushin fuskarsa bai disashe ba, sai ma ya ciro wayarshi kamar yana wani abu, ya dan dauke su hoto da wani karamin video sanann ya ajiye wayar a gefenshi.
Zayd ya sake kallon hannun Raihana na ƴan daƙiƙu, sannan ya janye kallonsa, ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce,
“Inaga yanzu ya yi daidai.”
Baffa ya kalleshi,
“Buguwa ce kawai?”
Zayd ya jinjina kai,
“Buguwa ne kawai ta fada kan hannun shine ta danyi targade.”
Ya ɗan kalli Raihana,
“Idan ya ƙara kumbura ko ciwon ya tsananta, sai a je a yi X-ray.”
Raihana ta jinjina kai a hankali.
Baffa ya sauke ajiyar zuciya,
“Toh, ba laifi, sannu da ƙoƙari, Zayd.”
Zayd ya ɗan jinjina kai yana dan murmushi, sai ya miƙe a hankali, ya koma inda yake a baya, ya zauna a kan carpet din kamar yadda ya ke dazu.
Baffa ya kalli Raihana,
“Ki kula da hannun.”
“Tohm.”
Baffa ya ɗan kalli Zayd, sannan ya kalli Imraan,
“Toh, ni zan wuce, Allah Ya saka da alkhairi.”
“Amin,” Imraan ya amsa.
Zayd kuwa ya ɗan jinjina kai.
Baffa ya juya ya fita daga falon, da ƙofar ta rufe a bayansa…
Imraan ya juyo a hankali ya kalli Zayd, murmushi ya fara bayyana a fuskarsa, ya ɗan ɗaga gira ɗaya, sai ya yi wa Zayd wink.
Zayd ya kalleshi na ƴan daƙiƙu, fuskarsa babu ko ɗan motsi, sai kawai ya maida idanunsa gefe.
Imraan ya shake dariyarsa,
“Hmm.”
Zayd bai kulashi ba, ya janyo wayarsa daga aljihunsa, ya buɗe screen ɗin ya fara dannawa kamar babu wani abu da ya faru.
Imraan ya girgiza kai a hankali, Mr. Serious.
Ya sake kallon Raihana, fuskarsa ɗauke da murmushi,
“Amarya...”
Raihana ta ɗago kai, kalaman sun ɗan bata kunya, ta kalleshi na ƴan daƙiƙu kafin ta sauke kanta cikin sanyin murya tace,
“Ina yini.”
Imraan ya fashe da wata ƙaramar dariya,
“Lafiya lau.”
Sai ya kalli hannunta,
“Ya hannun?”
Raihana ta ɗan kalli hannun nata,
“Da sauƙi.”
“Sannu toh.”
Ya miƙa hannu ya ɗauki robar ruwan da aka ajiye a kan ƙaramin table ɗin, ya buɗe ta, ya sha ɗan ruwa, sai ya zaro wayarsa, ya kalli screen ɗin,
“Rascal...”
Zayd bai ɗago kai ba.
Imraan ya kalli screen ɗin sannan ya kalli Zayd,
“Let me answer this call outside.”
Bai jira amsar Zayd ba, ya ajiye robar ruwan a hankali, ya ɗaga wayar zuwa kunnensa, sannan ya nufi ƙofar falon.
Yana tafiya kuwa, murmushi bai gushe daga fuskarsa ba, kafin ya fita, ya waiwaya, idanunsa suka fara sauka kan Zayd… sai kan Raihana… sai ya ɗan ɗaga gira.
Zayd ya ɗago kai ya kalleshi, Imraan ya yi murmushi, ya fita.
Sai falon ya yi shiru, shiru na gaske.
Raihana ta zauna a gefe, hannunta na ciwo a kan laps dinta, Zayd kuwa yana zaune a kujerarsa, wayarsa a hannunsa.
Amma… a wannan karon, bai sake dannawa ba, kawai yana kallon screen ɗin ne ba tare da yana ganin abin da ke ciki ba.
Raihana ta ɗan ɗago idanunta, ta kalleshi a hankali, sai ta sake sauke su.
Zayd kuma… bai ma san me take ciki ba.
Raihana kam haryanzu kanta a ɗan sunkuye, tana jin wani irin rashin sabo da kasancewar mutumin da ke gabanta.
Ba wai ba ta san Zayd ba, ta san shi, sun taɓa haɗuwa, sun taɓa yin magana, amma wannan… ya bambanta.
A yau ba Zayd ɗin da ta taɓa tsayar da convoy ɗinsa ba ne kawai, ba kuma mutumin da taɓa gani a speech ba, shi ne mutumin da ya zo gidansu da maganar aurenta.
Ta ɗan haɗiye yawu, sai a hankali, cikin sanyin murya ta ce,
“Ina yini.”
Zayd ya ɗago kansa, idanunsa suka sauka kanta, ya kalleta na ƴan daƙiƙu, sai ya ɗauke kansa kamar ba zai amsa ba.
Raihana ta ɗan ɗaga idanunta, tana jiran amsar, bayan ɗan lokaci… sai muryarsa ta fito a sanyaye,
“Ashe kin iya gaisuwa.”
Ya ɗan yi shiru.
Raihana ta ɗan ɗaga gira, Zayd kuwa ya kalli wayarsa na ƴan daƙiƙu, kamar yana tunanin ko ya ƙara wani abu, sai ya ɗago idanunsa kaɗan,
“Na zata sai rashin kunya da dambe a ƙofar gida.”
Ya faɗa a sanyaye, kamar ba shi ne ya faɗi maganar ba, kamar dai magana ce kawai da ta zo masa a baki, sai ya sake mayar da idanunsa kan wayarsa.
Raihana kuwa… ta saki baki, ta kalleshi, na ƴan daƙiƙu ta kasa ko motsi,
“Dambe?”
Ta maimaita a zuciyarta, sai ta ɗan haɗe gira, ta kalli fuskarsa.
Shi kuwa Zayd yana latsa wayarsa cikin natsuwa, kamar bai jefa mata wata magana ba.
Raihana ta ɗan tabe baki, a ranta ta ce,
“Lalle mutumin nan,”
“Wannan ɗan uban masu girman kai...”
Ta ɗan tabe baki,
“Ji yadda yake min magana kamar wani sarki.”
Ta sake kallon inda Zayd yake zaune,
“Lalle ma... baka sanni ba.”
Ta ɗan matsa hannunta a hankali,
“Wallahi ba za ka so gidan ubana kana min wannan sham kamshin naka ba.”
Ta sauke ajiyar zuciya.
Amma shi kuwa Zayd… bai san ma ana yi masa wani zance a zuciya ba.
Ta sake kallonsa sai ta murguda baki, ta ce cikin sanyin murya, amma akwai ɗan ɗacin rai a cikin maganar,
“Ai na zata kai ma ba ka magana kamar wani sarki... sai magana kake da ƙyar.”
Ta faɗa tana juyar da kanta gefe, kamar ba ta damu da abin da ta faɗa ba.
Amma Zayd… ya ɗago daga kallon wayarsa nan take, idanunsa suka sauka kanta cikin wani irin mamaki, ya kalleta na ƴan daƙiƙu, kamar yana ƙoƙarin tabbatar da cewa da gaske ita ce ta faɗi wannan maganar.
Raihana kuwa ta ji kallonsa, amma ba ta juyo ba, ta ci gaba da kallon gefe, tana murɗa gefen hijabinta da yatsunta.
Zayd ya ɗan dage gira, bai saba da irin wannan ba, mutane da yawa idan suna gabansa, sukan zaɓi yin shiru, wasu ma sukan kasa kallonsa kai tsaye, amma ita… ta zauna gabansa tana masa magana kamar ba komai.
Zayd ya ɗan sauke wayarsa a kan cinyarsa, har yanzu idanunsa suna kanta.
Raihana ta ji shiru ya yi yawa, sai ta ɗan motsa kanta kaɗan, amma har yanzu ba ta kalleshi ba.
Zayd ya buɗe baki kamar zai ce wani abu… sai ya dakata, ya sake kallonta.
A ƙarshe, cikin sanyin muryarsa ya ce,
“Da gaske?”
Raihana ta ɗan tabe baki,
“Hmm.”
Ta amsa ba tare da ta kalleshi ba.
Zayd ya yi shiru, sai wani ɗan murmushi kaɗan ya bayyana a gefen bakinsa, ba ta gani ba.
Ya sake ɗaukar wayarsa, amma wannan karon… bai koma dannawa ba, kawai ya riƙe ta a hannunsa yana kallon screen ɗin, yayin da a zuciyarsa yake mamakin yadda yarinyar da kowa yake kallonta cikin natsuwa… ashe tanada baki haka...
Sai kawai ya saka wayarshi a aljihuu, ya ɗan kalli agogon hannunsa, sai ya ɗago kansa, babu wata magana.
A hankali ya miƙe.
Raihana ta ɗan ɗago idanunta ta kalleshi.
Zayd ya zira hannu cikin aljihunsa, ya ciro wasu ɗaruruwan daloli, ko ƙirga su baiyi ba ya ajiye su a gabanta.
Raihana ta kalli kuɗin, sai ta kalli Zayd.
Zayd kuwa kamar bai lura da yanayin fuskarta ba, cikin sanyin murya ya ce,
“Gobe ma kiyi dambe a kofar gida, tunda har tare motar mutane kin iya a hanya.”
Sannan ya juya, ya nufi hanyar fita cikin nutsuwa.
Raihana ta tsaya cak, idanunta suka bi shi, ta kalli kuɗin da ke gabanta, sai ta sake kallon bayansa, ta ɗan buɗe baki tana kallon bayansa da mugun mamaki, ta kasa cewa komai.
Har ya kai bakin ƙofar falon, har ya ɗaga labulen, har ya fita.
Raihana har yanzu tana zaune tana kallonsa da baki a buɗe.
A zuciyarta kuwa…
“Wannan kuma me yake nufi?”
Ta sake kallon kuɗin,
“Yanzu me ya kawo wannan?”
Ta ɗan girgiza kai,
“Girman kai dai ya haɗu da rashin magana, idan ma zaiyi maganar a wani gadarance...”
Ta sauke ajiyar zuciya.
——————
Zayd na fita daga falon ya samu Imraan yana jingine a jikin motar, hannayensa haɗe a ƙirjinsa, kamar wanda ya daɗe yana jiran fitowarsa.
Da ya hango Zayd, sai murmushi ya bayyana a fuskarsa, ya gyara tsayuwarsa, ya ƙaraso kusa da shi,
“Wai... har kun gama hirar?”
Zayd bai ko kalleshi ba, ya wuce kai tsaye zuwa motar, ya buɗe passenger side, ya shiga ya zauna.
Imraan ya tsaya yana kallonsa na ƴan daƙiƙu, sai ya girgiza kai yana murmushi,
“Hmm...”
Ya zagaya zuwa driver’s side, ya shiga, ya kunna motar, sannan suka fara barin layin a hankali.
Ba wanda ya yi magana, sai da suka hau kwalta… Imraan ya ɗan kalli Zayd.
Zayd ya lumshe idanunsa, kansa a jingine da kujerar, kamar wanda ya gaji da duniya gaba ɗaya.
Imraan ya kasa riƙewa, sai ya fashe da dariya.
Zayd ya buɗe idanunsa a hankali, ya juyo ya kalleshi.
Imraan ya yi kamar bai ga kallon ba sai kuma ya ce,
“Whattt??”
Zayd ya masa banza, ya sake lumshe idanunsa.
Imraan ya girgiza kai, yana mai da hankali kan tukinsa, amma bayan ɗan lokaci…
“Rascal...”
Babu amsa.
Imraan ya yi murmushi,
“Wallahi sai ka yi wankan tsarki.”
Zayd ya buɗe idanunsa nan take, ya sauke su tsaf a kan Imraan, fuskarsa a dinke, kamar mutum wanda yake jiran explanation.
Imraan ya kalleshi da gefen ido, sai ya fashe da dariya.
Zayd ya ɗan daure fuska,
“What did you mean?”
Imraan ya ƙara dariya,
“Kai dai da na sani... inde kai ne Zayduu ɗin nan!”
Zayd bai ce komai ba.
Imraan ya ci gaba da tukinsa yana dariya,
“Toh wallahi, yadda na gan ka riƙe hannun yar mutane...”
Ya girgiza kai,
“Zaman lafiyar ka kawai kana zuwa gıda alhaji ka wuce bathroom.”
Zayd ya lumshe idanunsa,
“I don’t know what exactly you are talking about.”
Imraan ya kalle shi,
“Ka sani mana.”
Zayd bai amsa ba.
Imraan ya sake dariya,
“Rascal, billahillazi sai kayi wanka sabida ina kallon yanda ka kusa cika hannun yarinyar nan, kai kadai kasan wani electric ne ya gifta maka.”
Zayd ya ɗan buɗe ido,
“Imraan.”
“Hmm?”
“Drive.”
Imraan ya yi dariya,
“I’m driving.”
Zayd ya sake rufe idanunsa.
Imraan ya girgiza kai yana murmushi,
“Mr. Serious...”
Sai ya maida hankalinsa kan hanya amma haryanzu bai daina dariya ba.
Zayd bai sake cewa komai ba, amma a cikin shiru… fuskarsa ta ɗan sauya, kamar kalmar Imraan ta tunasar da shi wani abu da shi kansa bai shirya tunawa da shi ba.
Ya buɗe idanunsa a hankali, ya kalli hanyar da ke gabansu, sai ya sake jingina kansa da kujerar ya lumshe idanunsa.
Har suka isa gida…
Zayd bai sake kula da surutun Imraan ba, tun daga lokacin da suka bar Malali, Imraan yake ta magana yana tsokanar sa, amma Zayd ya yi kamar bai ma ji shi ba.
Kawai ya jingina kansa da kujerar motar, idanunsa a kan hanya, fuskarshi cike da wannan irin nutsuwar da babu wanda zai iya gane abin da ke yawo a zuciyarsa.
Har suka shiga cikin Armaan Mansion.
Imraan ya shigar da motar cikin compound a hankali, ya nufi inda aka saba parking.
Da ya yi parking ya kashe engine, sai ya kalli Zayd.
Zayd kuwa ya buɗe seatbelt ɗinsa a hankali.
Imraan ya ɗan jingina bayansa da kujerar, ya kalli Zayd daga gefe,
“I’m going.”
Zayd ya ɗan kalleshi,
“Ba zan shiga ba, ina da party anjima.”
Ya ɗan daga gira, sannan ya ƙara da wani irin murmushi,
“Amma idan kai ma za ka je...”
Ya ɗan tsaya, idanunsa suka bi Zayd daga sama har ƙasa,
“Toh dai.”
Sai ya ɗan gyada kai,
“Don naga kamar yarinyar can ta kunna ka.”
Zayd ya tsaya cak, Imraan ya kasa riƙe murmushinsa,
“Sai mu je ka ɗan rage zafi.”
Ya ƙare maganar yana kashe wa Zayd ido ɗaya.
Zayd ya ɗan kalleshi, kallon da ya yi masa ya isa ya sa mutum ya fahimci cewa ya gaji da shi, amma bai ce komai ba, kawai ya buɗe ƙofar motar, ya fito, ya rufe ƙofar a hankali, sannan ya nufi entrance ɗin lounge ɗin gidan ba tare da ya waiwaya ba.
Imraan ya bi shi da ido, sai ya girgiza kai yana dariya,
“Don’t forget...”
Zayd bai tsaya ba.
Imraan ya ɗaga murya,
“Ka yi wankan faaa!”
Ya ƙare maganar yana fashewa da wata shegiyar dariya.
Zayd ya ɗan tsaya na ɗan daƙiƙu a bakin ƙofar, ya lumshe idanunsa, ya sauke ajiyar zuciya a hankali, sai ya girgiza kai kawai,
“Imraan...”
Ya faɗa a hankali,
“Rascal!”
Ya ƙara faɗa daga cikin motar.
Zayd bai waiwayo ba, ya shiga lounge ɗin, ƙofar ta rufe a bayansa.
Imraan kuwa… ya girgiza kai yana dariya,
“Wallahi yau na ga al’amari mr serious a gidan su budurwa.”
Ya yi reverse da motarshi ya fice daga mansion din.
—————-
Zayd ya shiga cikin gidan.
Da ya taka ƙafarsa cikin lounge ɗin, sai idanunsa suka fara bin falon a hankali.
Ummie ce zaune a kan sofa, yayin da Suhaila take a gefe.
Da Ummie ta ɗago kai… idanunta suka sauka kansa, nan take murmushi ya bayyana a fuskarta.
Zayd bai tsaya nesa ba, kai tsaye ya ƙarasa gabanta, sannan a hankali ya durƙusa a gabanta, ya kama hannunta cikin ladabi, suka yi musabaha.
Daga nan ya ɗaga hannunta zuwa bakinsa ya sumbace ta cikin girmamawa,
“Barka da dare, Ummie naa.”
Muryarsa ta fito cikin sanyin murya.
Ummie ta shafi gefen fuskarsa a hankali, murmushi har yanzu yana kan fuskarta,
“Barka da zuwa, habibi, ka dawo lafiya?”
“Alhamdulillah.”
Ya amsa a takaice.
Sai Ummie ta janyo shi kusa da ita,
“Zo nan.”
Ta nuna masa gefenta.
Zayd ya ɗan kalli wajen, sannan ya zauna kusa da ita.
Suhaila kuwa… tun lokacin da ya shigo take binsa da kallo, murmushi ne kawai yake kwance a fuskarta, sai ta kasa riƙe bakinta,
“Akhiii...”
Zayd ya ɗan juyo ya kalleta,
“Ina Raihana?”
Ya ɗan kalleta na ƴan daƙiƙu, sai ya amsa cikin nutsuwa,
“I don’t know.”
Suhaila ta zaro ido,
“Daga gidansu fa kake!”
Ta ɗan matso gaba,
“Shine zaka ce ba ka sani ba?”
Zayd bai amsa ba, kawai ya mata banza, ya jingina bayansa da kujerar, sannan ya lumshe idanunsa.
Ummie ta kalle shi, murmushi kaɗan ya bayyana a fuskarta,
“Habibi...”
“Hmm, Ummie.”
Ya amsa ba tare da ya buɗe idanunsa ba,
“Ya ka barota?”
Zayd ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai ya buɗe idanunsa a hankali,
“Lafiya lau.”
Ummie ta ɗan kalleshi,
“Hope ba ka je ka yi shirun nan naka ba ko?”
Zayd ya ɗan yi murmushi,
“A’a.”
Ya ɗan dakata,
“Ba ta ma da lafiya.”
Nan take… Ummie da Suhaila suka kalli juna.
Suhaila kuwa ta matsa kusa da shi da sauri,
“Ba ta da lafiya kuma?”
Muryarta cike take da mamaki,
“Me ya same ta?”
Zayd ya sake jingina kansa da kujerar, idanunsa suka lumshe na ɗan lokaci.
A zuciyarsa kuma… hoton abin da ya faru a bakin gidan ya sake dawowa masa, Raihana tana ƙoƙarin raba Maryam da Bintu, yadda aka ture ta, yadda ta faɗi, da yadda daga baya ya ga tana riƙe da hannunta cikin ciwo, yanda ya karasa gabanta zai duba yanda ta ce “baffa da zafi faaaa”, yanda ya ga kumburin hannun nata.
Sai ya buɗe idanunsa a hankali, muryarsa ta fito cikin sanyi,
“Hannunta ne ya gurde... ta ji ciwo.”
Suhaila ta ƙara matsowa,
“Gurɗewaa?”
Zayd ya ɗan jinjina kai,
“Hmm.”
Ya faɗa a takaice,
“Subhanallah.”
Suhaila ta faɗa cikin tausayawa halin da Raihana ke ciki.
Ummie kuwa ta yi shiru tana kallonsa, ta lura da yadda Zayd yake magana, bai yi wani dogon bayani ba… amma yadda ya ambaci ciwon hannun Raihana, da yadda idanunsa suka sauya na ƴan daƙiƙu, ya isa ya nuna mata cewa abin ya tsaya masa a rai.
Suhaila ta ɗan kalli Ummie, sannan ta dawo da kallonta kan Zayd,
“Ka duba hannun nata?”
Zayd ya yi shiru, sai ya ɗan ɗaga gira,
“Hmm.”
Suhaila ta yi murmushi a hankali,
“Akhii...”
Zayd ya kalleta,
“Me?”
“Nothing.”
Ta ce tana murmushi.
Amma Zayd ya riga ya san wannan murmushin nata.
Ya ɗauki wayarsa daga aljihunsa, ya fara kallon screen ɗin.
Ummie kuwa ta kalleshi a hankali, a zuciyarta kawai ta yi murmushi, domin a karo na farko… ta fara ganin wani abu a fuskar ɗanta da shi kansa bai san yana nunawa ba.
Not edited