Free chapter · Read without an account
INTO THE CIRCLE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER-THIRTY TWO:32*
*INTO THE CIRCLE*
*JIDDAAH BARKUM*
—————
Bayan Bintu ta shiga motar, ta zauna a kujerar baya tana gyara mayafinta a hankali.
Driver ɗin ya shiga ya kunna motar, amma kafin ya fara tafiya, Bintu ta ɗan ɗago idanunta.
Ta sauke su akan Hajiya Balaraba.
Da idanunta suka sauka kan Bintu… sai ta fara bin ta da kallo, daga sama… har ƙasa.
Ta ɗan kankance idanunta, kamar wacce take nazarin dukkan abin da ke jikinta.
Sai ta matso kusa da ita, ta ɗan sunkuya, sannan hannunta ya kai kan shoulder ɗin Bintu, ta ɗan shafa a hankali.
Murmushi ya bayyana a fuskarta,
“You look yummy, my baby.”
Bintu ta ɗan juya ido, kalaman sun ɗan ba ta kunya, sai ta sauke idanunta tana murmushi kaɗan,
“Thank you, Mummy.”
Hajiya Balaraba ta ƙara murmushi, sai ta kama hannun Bintu, ta riƙe shi cikin nata, ta ɗan matso kusa da ita, sannan cikin wata murya mai ƙasa-ƙasa ta ce,
“Hope kin shirya tafiyar nan?”
Bintu ta jinjina kai,
“Eh, Mommy.”
Hajiya Balaraba ta ɗan matse hannunta,
“Kuma kin ji dukkan abin da na faɗa miki ko?”
Bintu ta ɗan kalli fuskarta,
“Eh, Mommy, na ji.”
Ta ɗan yi shiru,
“Kuma zan yi dukkan abin da kike so.”
Murmushi mai gamsuwa ya bayyana a fuskar Hajiya Balaraba,
“Good.”
Ta saki hannunta a hankali, sai ta gyara mata wani ɗan gefe na mayafinta,
“That’s my girl.”
Driver ɗin ya kalli Hajiya Balaraba ta mirror, sannan ya fara tafiya.
Motar ta bar kofar gidan a hankali.
Bayan ƴan mintuna… ta ɗauki hanyar airport.
Bintu kuwa ta jingina kanta da kujerar, idanunta suna kallon titi ta window.
Bayan wasu awanni na tafiya… daga ƙarshe suka isa Abuja.
Da motar ta shigo cikin birnin, Bintu ta ɗan ɗaga kanta daga jikin kujerar, idanunta suka fara yawo ta window.
Komai ya bambanta, manyan gine-gine… hanyoyi masu kyau… motoci… da kuma irin wannan yanayin da ya sa ta fahimci cewa sun bar duk inda ta saba.
Ba ta daɗe da kallon komai ba sai motar ta juya zuwa wata hanya mai nutsuwa, wacce manyan gidaje suka jere a gefe guda.
Bintu ta ɗan gyara zamanta.
Sai motar ta tsaya a gaban wani uban mansion.
Bintu ta buɗe baki kaɗan.
Gidan kuwa… ba kawai babba bane, wani uban mahaukaci mansion ne.
Babban gate ɗin iron ne mai tsayi, an yi masa elegant design, security cameras suna gefe-gefe, sannan akwai wasu manyan fitilu da suka yi wa entrance ɗin kyau.
Da gate ɗin ya buɗe… motar ta shiga.
Bintu ta kasa boye mamakinta, ta fara kallon dama… sai hagu… sai ta ɗago kanta tana kallon gidan gaba ɗaya.
Fadar gidan ta kasance cike da greenery da aka tsara da kyau, akwai manicured lawn, dogayen bishiyoyi, flower beds masu kyau, da wata ƙaramar fountain a tsakiyar hanyar shiga.
Motar ta tsaya a gaban babban entrance.
Bintu ta sauke numfashi a hankali,
“Subhanallah...”
Ta furta ba tare da ta shirya ba.
Hajiya Balaraba ta kalleta, sai ta kama hannunta,
“Relax.”
Bintu ta kalleta.
Hajiya Balaraba ta ɗan matse hannunta,
“Ki kwantar da hankalinki, kada ki bari komai ya razana ki.”
Bintu ta haɗiye yawu, ta jinjina kai,
“Okay, Mommy.”
Hajiya Balaraba ta yi murmushi,
“Good.”
Driver ya fito ya buɗe musu ƙofa.
Hajiya Balaraba ta fara sauka, Bintu kuma ta bi bayanta.
Da suka shiga babban entrance ɗin… Bintu ta sake tsayawa.
Wannan karon ma… ta kasa magana.
Falon da suka shiga ya yi girma fiye da yadda ta yi zato.
Babban chandelier ne yake rataye a tsakiyar ceiling, haskensa yana sheƙi a ko’ina.
Manyan sofas masu tsada sun cika falon cikin perfect arrangement.
A gefe akwai glass centre table, decorative pieces na musamman, sannan wani babban carpet mai laushi shimfiɗe a tsakiyar falon.
Bango ɗaya kuwa an yi masa marble finish, yayin da manyan curtains suka rufe windows ɗin da suka kai har ceiling.
Bintu ta ɗan kalli ƙasa, sai ta sake ɗaga idanunta, dama… hagu… har ta fara jin kamar idanunta ba za su iya ɗaukar komai ba.
Hajiya Balaraba ta lura da hakan, ta ɗan murmusa,
“Bintu...”
Bintu ta kalleta,
“Hmm?”
“Ki daina kallon komai kamar baki taɓa ganin gida ba.”
Bintu ta ɗan saki murmushi cikin kunya,
“Sorry, Mommy.”
Kafin Hajiya Balaraba ta amsa… sai wata dariya ta tashi daga can gefe,
“Balaraba!”
Hajiya Balaraba ta juya.
Wasu manyan mata ne zaune a cikin falon, kayan jikinsu sun nuna irin matsayinsu—dan ubansun laces masu kyau, jewelry masu sheƙi, ƙamshin turaren yana cika falon kamar nan ne factory din kamshi.
Hajiya Hauwa ta miƙe tana murmushi,
“Finally! Kin iso.”
Hajiya Balaraba ta yi dariya,
“Wallahi Abuja traffic ne ya ɗan tsaida mu.”
Wata ta kalli Bintu, sai ta ɗan yi shiru, kallon da ta yi mata ya fara daga kanta har ƙasa, sai ta juya ta kalli Hajiya Balaraba,
“Balaraba...”
Ta yi murmushi,
“Gaskiya yarinyarki ta haɗu.”
Wata ta yi dariya,
“Haɗuwa fa? Wannan ba haɗuwa kawai ba ce.”
Ta ɗan matsa kusa tana kallon Bintu,
“Kin samu mai jini a jika fa!”
Dariya ta sake tashi a falon.
Bintu kuwa… ta tsaya a gefe, ta kasa cewa komai, ta kalli Hajiya Balaraba, sai ta kalli matan, sannan ta sake sauke kanta ƙasa.
Wata daga cikin matan ta yi murmushi,
“Balaraba, wai ina kika samo wannan yarinyar?”
Hajiya Balaraba ta yi dariya,
“Ku bar min yarinya ta mana.”
Wata ta sake cewa,
“Amma wallahi ta yi kyau.”
Hajiya Balaraba ta kalli Bintu, murmushi ya bayyana a fuskarta,
“Ku bi min ita a hankali, har yanzu tana jin kunya.”
Hajiya Hauwa ta yi dariya,
“Kunyar ma ta yi mata kyau.”
Bintu ta ƙara rakubewa a gefe, hannunta biyu ta haɗa a gabanta, idanunta kuwa… har yanzu suna yawo a cikin falon, kamar wacce har yanzu take ƙoƙarin fahimtar irin duniyar da ta shigo ciki.
“Come on, my baby.”
Hajiya Balaraba ta janyo ta jikinta.
Sai wata mace kamar maid ta karaso cikin nutsuwa ta kalli Hajiya Balaraba,
“Bari na kai ta ɗakinta.”
Hajiya Balaraba ta jinjina kai,
“Please, make sure she gets everything she needs.”
“Okay, Hajiya.”
Bintu ta bi bayan matar, suna wucewa ta wani corridor mai faɗi, idanunta suka riƙa bin komai da mamaki, kayan ado, manyan paintings, flowers da lights masu kyau duk sun ƙara mata jin kamar ta shigo wani world daban.
Daga ƙarshe matar ta tsaya a gaban wata ƙofa ta buɗe,
“Here you go.”
Bintu ta shiga, matar ta bi bayanta.
Sai ta tsaya cak.
Bedroom ɗin ya fi duk abin da ta taɓa tsammani kyau, babbar king-size bed ce a tsakiyar ɗakin, an shimfiɗa ta da fararen bedsheets masu laushi, a gefe akwai ƙaramar sitting area, vanity mirror mai girma, wardrobe mai cike da haske, sannan manyan curtains suka rufe glass windows ɗin da ke kallon wani kyakkyawan garden.
Bintu ta ɗan buɗe baki,
“Wow...”
Matar ta yi murmushi,
“Ki huta, an riga an shirya miki lunch.”
Kafin Bintu ta amsa, wata ma’aikaciyar gidan ta shigo da tray, a kai akwai abinci iri-iri da aka shirya cikin ƙayatarwa.
Bintu ta kalli tray ɗin,
“Wannan duk nawa ne?”
Matar ta yi dariya kaɗan,
“Eh, Hajiya ta ce a tabbatar kin ci sosai.”
Bintu ta yi murmushi,
“Thank you.”
“Ki ci ki huta, bayan kin gama, ki yi wanka.”
Ta juya zata fita, sai ta tsaya kamar ta tuna wani abu,
“Oh, and one more thing.”
Ta nuna wata babbar box da aka ajiye a gefe,
“An kawo miki outfit ɗin da za ki saka zuwa taron.”
Bintu ta kalli box ɗin,
“Outfit?”
“Eh.”
Matar ta buɗe box ɗin.
Bintu ta zare ido.
A ciki akwai wata luxurious designer abaya, an yi ta da wani kyakkyawan fabric mai sheƙi, an yi mata delicate stones da embroidery masu tsada, a gefenta kuwa akwai matching veil, handbag da shoes da aka tsara su duka su dace, duk designers.
Bintu ta ɗauki gefen kayan da hannunta,
“SubhanAllah...”
Matar ta yi murmushi,
“Hajiya ta zaɓa da kanta.”
Bintu ta sake kallon kayan,
“Ta ce ki saka su bayan kin yi wanka.”
“Toh.”
“Kar ki damu da komai, Hajiya za ta zo ta same ki kafin ku tafi.”
Matar ta fita.
Da ƙofar ta rufe… Bintu ta tsaya ita kaɗai a tsakiyar ɗakin.
Ta sake kallon kayan, sai ta kalli abincin, sai ta kalli ɗakin.
A hankali wani murmushi ya bayyana a fuskarta.
Wannan rayuwar… wannan kulawar… sune irin yadda take nema… ya fara sa ta manta da duk wani shakku da zai iya tasowa a zuciyarta.
Ta sauke ajiyar zuciya,
“Wallahi Hajiya ta na sona...”
Ta faɗa a hankali, sai ta nufi abincin.
Bayan Bintu ta ci abincin da aka shirya mata, sai tayi wanka, bayan ta fito ta tsaya.
Kayan da aka ajiye mata a kan gadon suka sake ɗaukar hankalinta.
A hankali ta ɗauki kayan, ta shiga dressing area, bayan ƴan mintuna kaɗan ta fito.
Abayar ta zauna a jikinta da kyau sosai, luxury fabric ɗin yana haskawa a ƙarƙashin hasken ɗakin, stones ɗin da aka yi mata ado suna catching light duk lokacin da ta motsa.
Bintu ta ƙarasa gaban babban mirror ɗin da ke jikin bango, ta tsaya, ta kalli kanta daga sama… sai ta sauke idanunta har ƙasa, ta sake juyawa kaɗan,
“Wow...”
Ta furta a hankali,
“Gaskiya na haɗu.”
Ta yi murmushi tana kallon kanta.
Ta ɗaga hannunta ta shafi sleeve ɗin abayar a hankali,
“Oh my God...”
Ta sake kallon reflection ɗinta,
“See how I’m screaming luxury.”
Ta yi wata ƙaramar dariya,
“Dama ni ban dace da gidan talakawa ba.”
Ta sake kallon kanta a mirror, wannan karon murmushinta ya ƙara faɗaɗa,
“Hmm...”
Ta ɗan gyara veil ɗinta,
“Bintu... yanzu kin fara gane inda kika fi dacewa.”
Kafin ta ƙara wani abu… aka yi knocking, ta waigo.
Ƙofar ta buɗe.
Hajiya Balaraba ta shigo.
Ita ma ta yi kyau sosai, ta saka wani uban arnen lace mai ɗaukar ido, an yi masa ƙyalli da stones masu tsada, sannan ta yi ado mai kyau da accessories na gold.
Gold bracelets sun cika hannayenta, necklace ɗin da ke wuyanta kuwa ya zauna mata sosai, sai wani mahaukacin kamshi take zubawa.
Da ta ga Bintu… sai ta tsaya, idanunta suka sauka kanta daga sama har ƙasa, ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, sai murmushi ya bayyana a fuskarta,
“Ahhh...”
Ta ƙarasa wajenta,
“My baby...”
Ta riƙe hannun Bintu, ta sake kallonta sosai,
“Look at you.”
Bintu ta ɗan sunkuyar da kanta cikin jin kunya.
Hajiya Balaraba ta girgiza kai tana murmushi,
“Wallahi wannan kayan sun dace da ke.”
Ta ɗaga hannun Bintu kaɗan tana kallon stones ɗin,
“Kin yi kyau sosai.”
Bintu ta yi murmushi,
“Thank you, Mommy.”
Hajiya Balaraba ta ɗan matse hannunta,
“Na gaya miki ai, you deserve this kind of life.”
Bintu ta ɗan kalli kanta a mirror, a yanzu kuwa… kalaman Hajiya Balaraba sun ƙara mata confidence.
Hajiya Balaraba ta sake kallonta,
“Ready?”
Bintu ta jinjina kai,
“Yes, Mommy.”
“Good.”
Ta kama hannunta sosai,
“Come on, kada su fara taron ba tare da mu ba.”
Suka fara tafiya.
Bintu tana bin bayanta a hankali, idanunta suna yawo cikin hallway ɗin mansion ɗin, kowane abu yana da wani irin tsari, lights masu kyau, large paintings, luxury furniture, fresh flowers a gefe, komai yana ihu da kuɗi.
Bintu ta ɗan yi murmushi ita kaɗai, so this is the kind of life…
Hajiya Balaraba ta ɗan waigo ta kalleta,
“Relax, baby.”
Bintu ta ɗan gyada kai,
“I’m fine, Mommy.”
Hajiya Balaraba ta yi murmushi,
“Good girl.”
Suka ci gaba da tafiya har suka isa babban hall ɗin.
Da suka shiga… Bintu ta tsaya na ƴan daƙiƙu.
Hall ɗin ya kasance cike da manyan mata cikin kaya masu tsada, jewelry masu sheƙi da turaren da ya cika wajen, wasu suna zaune suna hira, wasu kuma suna dariya.
Da suka ga Hajiya Balaraba ta shigo… sai wasu suka fara kallonsu.
Wata daga cikinsu ta yi murmushi,
“Balaraba!”
Hajiya Balaraba ta amsa da fara’a,
“Ahh, sisters!”
Sai idanunta suka sauka kan Bintu.
Hajiya Balaraba ta ɗan ja ta kusa da ita,
“Come and see who I brought.”
Matan suka fara kallon Bintu.
Wata ta yi murmushi,
“Ahhh, so this is the girl?”
Hajiya Balaraba ta yi dariya,
“Yes, this is my baby.”
Bintu kuwa… ta tsaya kusa da ita cikin nutsuwa, amma idanunta… har yanzu suna yawo cikin hall ɗin, tana ƙoƙarin fahimtar irin duniyar da ta tsinci kanta a cikinta.
Hall ɗin ya yi shiru na ƴan daƙiƙu bayan Hajiya Balaraba ta shigo da Bintu.
Wasu daga cikin matan suka fara kallon juna suna murmushi.
Wata daga cikinsu ta ɗaga glass ɗin da ke hannunta,
“Finally, Balaraba has arrived.”
Hajiya Balaraba ta yi dariya,
“Sorry, sorry, mun ɗan makara ne.”
“Makara?”
Hajiya Hauwa ta yi dariya,
“Da ace kin san abin da kika rasa kafin ki zo.”
Hajiya Balaraba ta ɗan ɗaga gira,
“Really?”
“Hmm.”
Ta kalli Bintu,
“Especially this one.”
Dariya ta sake tashi a hall ɗin.
Bintu ta ɗan sunkuyar da kanta cikin kunya.
Hajiya Balaraba kuwa ta riƙe hannunta sosai,
“Come, baby.”
Ta ja ta zuwa inda sauran matan suke.
A tsakiyar hall ɗin akwai wasu manyan kujeru da aka shirya kamar yadda ake gudanar da formal gathering.
Wasu daga cikin matan suna zaune tare da ’yan matan da suka zo da su.
Bintu ta ɗan kalli su, sai ta lura da wani abu, kusan kowacce daga cikin matan tana tare da wata yarinya.
Wata yarinyar tana zaune kusa da wata mace tana dariya, wata kuma tana magana da wadda ta kawo ta cikin wani irin confidence.
Bintu ta ɗan kalli Hajiya Balaraba,
“Mommy...”
“Hm?”
“Wannan taron na me ne?”
Hajiya Balaraba ta yi mata murmushi,
“Just relax.”
Ta ɗan matse hannunta,
“Za ki gane komai.”
Bintu ta jinjina kai, ba ta sake tambaya ba.
Wata mace da ke zaune a gaba ta tashi, ta gyara veil ɗinta, sannan ta kalli sauran matan,
“Okay ladies...”
Dariya ta fara raguwa,
“Since everybody is finally here, let’s start.”
Ta kalli wata yarinya da ke gefenta,
“Come, darling.”
Yarinyar ta miƙe.
Matar ta kama hannunta ta kai ta gaba,
“This is my girl.”
Wasu suka fara tafa hannu,
“Beautiful!”
“Wow!”
“She’s gorgeous!”
Yarinyar ta yi murmushi cikin kunya.
Matar ta ci gaba da magana tana yabon ta, tana bayyana yadda suka haɗu da kuma yadda ta yi farin ciki da ta kawo ta cikin circle ɗin.
Bintu ta tsaya tana kallonsu.
A farkon ta ɗauka kawai wata irin social gathering ce, ta yi murmushi,
“Manyan mata ne kawai suke da irin nasu circle din.”
Presentation ɗin farko ya ƙare.
Sai wata ta miƙe,
“Mine is next.”
Dariya ta sake tashi, ta zo da yarinyar da ke gefenta, ta riƙe hannunta tana gabatar da ita, sauran matan suka yi ta compliment,
“She’s so pretty!”
“Look at her skin!”
“Balaraba, kin ga wannan?” Cewar Hajiya Hauwa.
Hajiya Balaraba ta yi dariya,
“Wallahi you people...”
Bintu ta yi murmushi kaɗan, amma a hankali… wani abu ya fara ɗaukar hankalinta.
Ba presentation ɗin kawai ba, yadda matan suke kallon waɗannan ’yan matan, yadda suke musu compliments, yadda suke riƙe hannayensu, yadda suke nuna musu kulawa.
Ta ɗan kaɗa kai, maybe wannan kawai irin friendship ɗinsu ne, ta ƙoƙarta ta kawar da tunanin.
Sai wata ta sake tashi, presentation na uku, na huɗu, na biyar, duk lokacin da aka gabatar da wata sabuwar yarinya, hall ɗin sai ya cika da tafi da dariya.
Bintu ta fara jin wani irin yanayi, sai ta matsa kusa da Hajiya Balaraba,
“Mommy...”
Hajiya Balaraba ta waigo,
“Hmm?”
“Ni ma za a gabatar da ni?”
Murmushi ya bayyana a fuskar Hajiya Balaraba,
“Of course.”
Bintu ta ɗan zaro ido,
“Me zan ce?”
Hajiya Balaraba ta yi dariya,
“Ba ke za ki yi magana ba.”
Ta ɗan matse hannunta,
“Ni zan yi.”
Bintu ta yi shiru.
Hajiya Balaraba ta ɗan gyara mata veil ɗinta,
“Just relax.”
Ta sake kallonta,
“Ki tuna abin da na gaya miki.”
Bintu ta jinjina kai,
“Okay, Mommy.”
A wannan lokacin… wata mace ta kalli Hajiya Balaraba,
“Balaraba...”
“Hm?”
“It’s your turn.”
Dariya ta tashi.
Hajiya Balaraba ta yi murmushi, ta tashi a hankali, sannan ta kama hannun Bintu,
“Come with me, my baby.”
Bintu ta ɗan ja da baya saboda kunya,
“Mommy...”
“Come.”
Hajiya Balaraba ta ja ta zuwa tsakiyar hall ɗin.
Nan take idanun kowa suka koma kansu.
Bintu ta ji zuciyarta ta fara bugawa, ta kalli matan, sai ta sauke idanunta.
Hajiya Balaraba kuwa ta tsaya kusa da ita cikin confidence, ta riƙe hannunta, ta kalli sauran matan,
“Ladies...”
Hall ɗin ya yi shiru.
Hajiya Balaraba ta ɗan kalli Bintu daga gefe, murmushi ya bayyana a fuskarta,
“Meet my baby...”
Ta ɗan ja Bintu kusa da ita ta dan rungume ta, tana shafa fuskarta ta na mata wani shegen kallo,
“Bintu.”
Tafi ya cika hall ɗin.
Bintu ta ɗan zaro ido.
Wata mace ta ɗaga murya,
“Balaraba!”
Hajiya Balaraba ta kalleta,
“Where did you find this beauty?”
Dariya ta tashi.
Hajiya Balaraba ta yi murmushi,
“Let’s just say...”
Ta ɗan kalli Bintu,
“I saw something special in her.”
Wata ta ce,
“Gaskiya kin gani.”
“Wallahi!”
“She’s gorgeous!”
Bintu ta ƙara sunkuyar da kanta.
Hajiya Balaraba ta ɗan matse hannunta,
“She’s very sweet, very respectful...”
Ta ɗan yi murmushi,
“And she deserves the best.”
Sauran matan suka tafa hannu.
Bintu kuwa… ta ji wani irin daɗi a zuciyarta, a karo na farko a rayuwarta… ta ji kamar ana kallonta da wani sabon ido.
Ba kamar yarinyar gidan da take zaune ba, ba kamar wacce take bukatar ta nemi komai ba, a yanzu… tana tsakiyar manyan mata, tana sanye da kaya masu tsada, kuma mace mai iko tana riƙe da hannunta tana kiran ta my baby.
Ta ɗan kalli Hajiya Balaraba, murmushi ya bayyana a fuskarta.
Hajiya Balaraba ta mayar mata da murmushin, sai ta ɗan karkata kanta kusa da kunnenta, cikin murya mai ƙasa-ƙasa ta ce,
“See?”
Bintu ta kalleta,
“This is where you belong.”
Bintu ta ɗan haɗiye yawu, sai ta jinjina kai a hankali,
“Thank you, Mommy.”
Hajiya Balaraba ta ƙara murmushi, sai suka koma wurin zama.
Amma Bintu… ba ta san cewa kalmar da Hajiya Balaraba ta faɗa mata ba ta kasance kawai compliment ba ce,
“This is where you belong.”
A hankali… ta fara zama gaskiya a cikin tunanin Bintu.
Bayan an gama presentations ɗin… sai wata daga cikin matan ta miƙe a hankali,
“Okay ladies...”
Ta kalli sauran matan,
“Let’s continue.”
Wasu daga cikin matan suka fara miƙewa, waɗanda aka kawo a matsayin guests kuwa suka fara kallon juna cikin rashin fahimta.
Bintu ma… ta tsaya a gefe tana kallonsu.
Da farko ba ta fahimci abin da ke faruwa ba, sai ta ga wasu daga cikin matan suna matsawa kusa da waɗanda suka zo da su, cikin wani irin yanayi da ya wuce yadda Bintu ta ɗauka da farko, aka fara rungume rungume, wasu na kissing, wasu na shafa juna, abubuwan dai kala, kowa da abinda yakeyi.
Wata daga cikin sabbin ’yan matan ta zaro ido, ta kalli wadda ta kawo ta, kamar wacce take son tambaya,
“Me ake yi?”
Wata kuma ta ɗan ja baya.
Bintu ta lura da hakan, sai ta sake kallon hall ɗin, a hankali… fuskarta ta canza, abin da take gani ya fara zama clear.
Ta sake kallon wata daga cikin matan, sai ta kalli yarinyar da ke kusa da ita, nan take zuciyarta ta buga,
“Wait...”
Ta ɗan ja numfashi, wani irin shock ya bayyana a fuskarta.
Ta juya da sauri ta kalli Hajiya Balaraba,
“Mommy...”
Hajiya Balaraba ta kalleta cikin nutsuwa,
“Hm?”
Bintu ta matsa kusa da ita, ta rage murya sosai,
“Me... me haka?”
Hajiya Balaraba ba ta amsa nan take ba, ta kalli Bintu na ƴan daƙiƙu, sai ta kama hannunta,
“Relax, baby.”
Bintu ta sake kallon hall ɗin, idanunta har yanzu a zare,
“Amma Mommy...”
Ta kasa ƙarasa maganar.
Hajiya Balaraba ta katse ta cikin sanyin murya,
“Ki yi shiru.”
Ta ɗan kalli sauran matan,
“Just watch.”
Bintu ta sauke idanunta, amma zuciyarta ta ƙara bugawa.
A kusa da ita, wasu daga cikin sauran girls ɗin ma sun fara fahimtar abin da taron yake nufi.
Wata ta kalli ƙofar hall ɗin, kamar tana tunanin fita, wata kuma ta zauna cak, jikinta ya yi sanyi.
Bintu ta kalli su, sai ta gane… ba ita kaɗai ba ce wadda ba ta san komai ba.
Hajiya Balaraba kuwa… har yanzu tana zaune kusa da ita cikin cikakkiyar nutsuwa, ta ɗan sunkuya kusa da kunnenta,
“Baby...”
Bintu ta kalleta,
“Ki kwantar da hankalinki.”
Bintu ta haɗiye yawu,
“Amma Mommy... me ya sa kika kawo ni nan?”
Hajiya Balaraba ta yi ɗan murmushi, sai ta ce a hankali,
“Because I love youuuuuuuuuu.”
Not edited