Free chapter · Read without an account

NEW YORK NEW BEGINNING

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN


*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER-THIRTY SIX:36*

*NEW YORK, NEW BEGINNINGS*

*JIDDAAH BARKUM*

—————

Bintu ta kasa motsi.
Ta tsaya cak kamar an dasa ta a wajen.

Idanunta suna yawo a cikin hall ɗin, amma wannan karon ba don sha’awar kayan ado ko manyan mata ba.
A’a.

Abin da take gani ne ya ɗaure mata zuciya.
Wasu daga cikin matan suna cikin nutsuwa kamar babu wani sabon abu da ke faruwa.
Wasu daga cikin ’yan matan kuwa sun fara nuna tsoro.

Wata ta matse hannayenta biyu a ƙirjinta, tana kallon ƙofar hall ɗin kamar tana neman hanyar tserewa.
Bintu ta kalli su, sai ta sake kallon Hajiya Balaraba,
“Mommy...”
Muryarta ta fito ƙasa-ƙasa.

Hajiya Balaraba ba ta amsa nan take ba, ta ci gaba da kallonta kawai.
“Me ya sa kika kawo ni nan?”
A wannan karon muryar Bintu ta ƙara nuna tsoro.

Hajiya Balaraba ta ɗan matsa kusa da ita,
“Saboda ina sonki.”
Bintu ta daure fuska,
“Kina so na?”
“Fiye da yadda kike tunani.”
Hajiya Balaraba ta kama hannunta,
“Na san abin da kike so.”

Bintu ta ɗan ja hannunta baya,
“Ni ba na son wannan.”
Hajiya Balaraba ta yi shiru, ba ta yi fushi ba, ba ta daga murya ba, kawai ta kalli Bintu da wani irin natsuwa,
“Okay.”

Bintu ta ɗan kalleta.
Hajiya Balaraba ta ɗan gyara zamanta,
“Ba zan tilasta ki ba.”
Bintu ta sauke numfashi, kamar kalaman sun ɗan kwantar mata da hankali,
“Then let’s go.”

Hajiya Balaraba ta yi murmushi kaɗan,
“Za mu iya tafiya.”
Ta ɗan dakata,
“Amma kafin mu tafi...”
Ta kalli hall ɗin,
“Ki duba.”

Bintu ba ta son hakan, amma idanunta suka bi inda Hajiya Balaraba ta nuna.
Bintu ta haɗiye yawu.

“Ki duba yadda suke rayuwa.”
Hajiya Balaraba ta yi magana cikin nutsuwa,
“Ba wai abin da suke yi nake nufi ba.”
Ta juya ta kalli Bintu,
“Duba rayuwar da ke kewaye da su.”

Bintu ta ɗan daure fuska,
“Mommy...”
“Duba kayan.”
Idanun Bintu suka sauka kan wata mace da ke gabansu.
Designer dress, gold jewelry, luxury handbag, ga wata hamshakiyar waya, perfume mai ƙamshi wanda har daga inda take ana jin sa.

Hajiya Balaraba ta ci gaba,
“Duba yadda suke shiga moto.”
“Duba gidajen da suke zama.”
“Duba hotels ɗin da suke sauka, da kasashen da suke zuwa.”
“Duba yadda kowa yake kallonsu.”

Bintu ta yi shiru.
“Wannan shi ne abin da duniya take bayarwa idan kina da connection da money.”
Bintu ta ɗan lumshe idanunta,
“Amma...”
“Amma me?”
“Ba sai na shiga cikin wannan ba.”

Hajiya Balaraba ta yi murmushi,
“Of course.”
Ta ɗan matsa kusa da ita,
“Kin san me ya fi bani mamaki?”
Bintu ta kalleta,
“Me?”
“Tun lokacin da na fara ganin ki...”
Ta ɗan riƙe hannunta,
“Na ga kina son kyau, kina son gayuuuu.”

Bintu ta yi shiru.
“Kin son kaya masu kyau.”
Ta ɗaga gira,
“Kina son a kula da ke.”
Bintu ta sauke idanunta,
“Kina son ki shiga wuri mutane su juya su kalle ki.”
Bintu ta ɗan motsa baki, amma ba ta ce komai ba,
“Kina son rayuwa mai kyau.”

Hajiya Balaraba ta yi murmushi,
“Ba laifi ba ne.”
Bintu ta ɗan kalleta.
“Son luxury ba laifi ba ne.”
Hajiya Balaraba ta jaddada,
“Abin da yake da muhimmanci shi ne... kin san yadda za ki samu.”

Bintu ta yi shiru.
Wannan kalmar ta zauna a zuciyarta.
“Kin san yadda za ki samu.”

Ta sake kallon hall ɗin.
A yanzu idanunta ba sa kallon abin da matan suke yi kawai, suna kallon rayuwar da ke kewaye da su.
Jakar wata mace ta ɗauki hankalinta, ta san wannan brand ɗin, ta taɓa ganin irin wannan bag din a social media.
Farashinsa... ba ƙaramin abu ba ne.

Ta sake kallon agogon da ke hannun wata, sai necklace, sai shoes, sai yadda matan suke magana da confidence, ba tare da sun damu da komai ba.
Bintu ta sauke idanunta.

Wani abu ya fara motsawa a zuciyarta.
Ba amincewa ba.
Amma... sha’awa.

Hajiya Balaraba ta lura, sai ta yi murmushi,
“Kin ga?”
Bintu ta kalleta,
“Me?”
“Kin fara kallon su daban.”
Bintu ta yi saurin girgiza kai,
“No.”
Hajiya Balaraba ta yi ƙaramin dariya,
“Bintu.”
Ta ɗan matsa kusa,
“Ba na cewa ki yarda yanzu.”
Ta riƙe hannunta,
“Just think.”
“Ki tambayi kanki...”
Ta yi shiru na ɗan lokaci,
“Me kike so?”

Bintu ta kasa amsawa.
Hajiya Balaraba ta ci gaba cikin murya mai laushi,
“Kin gaji da rayuwar da kika sani.”
Bintu ta ɗan kalleta,
“Kin gaji da neman abubuwa.”
“Kin gaji da kallon wasu suna rayuwa yadda suke so.”
“Kin gaji da jin cewa dole ki tsaya ki duba farashi abu kafin ki sayi abin da kike so.”

Bintu ta yi shiru, kowane kalma... ta yi mata daidai.
Hajiya Balaraba ta ɗan matsa kusa da kunnenta,
“Ni zan iya canza wannan.”
Bintu ta ɗan lumshe idanunta,
“Ta yaya?”
Hajiya Balaraba ta yi murmushi,
“Ki amince da ni.”
Sai Bintu ta buɗe idanunta,
“That’s all?”
Hajiya Balaraba ta gyada kai,
“That’s all.”

Bintu ta sake kallon hall ɗin.
Wata yarinya ta wuce gabansu, tana sanye da wata shegiyar designer abaya mai tsada, tana ɗauke da handbag mai kafirin kyau.
Bintu ta bi ta da kallo har ta ɓace, sai ta kalli kanta.

Ta tuna da lokacin da Hajiya Balaraba ta kai ta shopping, ta tuna da kayan da aka zaɓa mata, ta tuna da yadda matan suka kalle ta lokacin da Hajiya Balaraba na presenting dinta.
Tabbas zata so a cigaba da kallonta haka.

Ta tuna da kalmar da Hajiya Balaraba ta faɗa mata,
“This is where you belong.”
A hankali ta sauke numfashi,
“Mommy...”
“Hm?”
“Idan...”
Ta yi shiru.

Hajiya Balaraba ta zuba mata ido tana saurarenta,
“Idan na ce ban shirya ba fa?”
Hajiya Balaraba ta yi murmushi,
“Ba matsala.”
“Za mu koma gida.”
Bintu ta kalleta,
“Ba za ki yi fushi ba?”
“Me ya sa zan yi?”
Hajiya Balaraba ta shafa gefen fuskarta,
“Ni ba zan tilasta wa baby ɗina komai ba.”

Bintu ta ɗan saki numfashi.
Sai Hajiya Balaraba ta ƙara da cewa:
“Amma ki tuna...”
Ta ɗan yi murmushi,
“Damar rayuwa ba kullum take zuwa sau biyu ba.”

Bintu ta yi shiru.
Hajiya Balaraba ta miƙe,
“Zo.”
Bintu ta ɗago kai,
“Where?”
“Mu tafi.”
Ta miƙa mata hannu.

Bintu ta kalli hannun.
Na ɗan lokaci… ba ta motsa ba.
Sai idanunta suka sake komawa kan hall ɗin.
Luxury, kudi, attention, rayuwa wacce ta yi kama da wacce ta taɓa mafarkinta.

Ta sake kallon Hajiya Balaraba, sai a hankali… ta miƙa hannunta.
Hajiya Balaraba ta kama ta, wani shegen murmushi ya bayyana a fuskarta.

Sai suka fara tafiya, Bintu tana biye da ita.
Amma kafin su kai ƙofar hall ɗin… Bintu ta tsaya, ta waigo, ta kalli hall ɗin na ƙarshe.

Wani irin tunani ya ratsa zuciyarta,
“Maybe... maybe zan iya yarda ba tare da kowa ya sani ba. Maybe zan iya shiga cikin wannan duniyar... kuma ma ai duk abinda zaayi ba zanyi ciki ba, no one will notice.”

Ta ɗan haɗiye yawu.
Amma zuciyarta ta yi mata wata tambaya:
“Idan aka ba ki duk abin da kika taɓa mafarki da shi... me za ki iya bayarwa a madadin?”

Bintu ba ta san amsar ba, har yanzu.
Sai ta juya, ta bi Hajiya Balaraba.

—————-

*ARMAAN MANSION*

Zayd yana tsaye a gefen motarsa, hannayensa a cikin aljihun trouser ɗinsa, yayin da motocin convoy ɗinsa suke a jere a bayan shi.
Driver da Sameer sun riga sun shiga cikin motar, suna jiran umarninsa.

Daga Kaduna za su wuce Lagos, daga nan kuma Zayd zai hau jirgin da zai kai shi New York, United States.
Tafiyar ta kasance cikin gaggawa.

Amma kafin ya shiga motar… Ummie ta ƙaraso kusa da shi.
Ta tsaya gabansa na ƴan daƙiƙu tana kallonsa, kallon da mace take yi wa ɗanta wanda zuciyarta ba ta son ya yi nisa da shi.

A hankali ta ɗaga hannu, ta shafa gefen fuskarsa,
“Habibi...”
Zayd ya ɗan kalleta da lumsassun idanunsa,
“Hmm?”

Ummie ta yi shiru na ɗan lokaci, kamar tana ƙoƙarin zaɓar kalmomin da za ta faɗa, sai ta ce cikin murya mai laushi,
“Please... do this for me.”
Zayd ya ɗan buɗe baki,
“Name it Ummie.”

Ummie ta ɗan gyada kai,
“I know you’re already running late to the airport...”
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya,
“But if I ask you to go somewhere before you leave zaka makara...”
Zayd ya kalleta sosai,
“Where?”
Ummie ta rage murya,
“Raihana.”

Zayd ya yi shiru, fuskarsa ta sauya kaɗan.
Ummie ta ci gaba kafin ya samu damar magana,
“Nasan yanzu zaka makara, ba za ka iya zuwa da kanka ba, but at least ka aika Sameer ya nemo number ɗinta.”
Ta ɗan matsa kusa da shi,
“Call her.”

Zayd ya ɗan lumshe idanunsa.
Ummie ta kalle shi da tsananin ƙauna, ta ɗan dakata,
“Tell her you’re leaving.”
Zayd bai ce komai ba.

Sai Ummie ta ɗan sauke murya,
“Ka sani... idan ka tafi yanzu, za ka yi nisa sosai.”
Ta ɗan shafa gefen fuskarsa,
“And I know you.”
Murmushi kaɗan ya bayyana a fuskarta,
“You’ll get busy there... then days will pass... and before you know it, you’ll forget to even check on her.”

Zayd ya buɗe idanunsa sosai, idanunsa suka sauka kan fuskar Ummie.
Akwai wani abu a kallonsa, kamar maganar ta shiga inda ba ya son a taɓa.
Ummie ta yi murmushi,
“Just one call, Habibi.”

Wajen yayi shiru, ƴan daƙiƙu suka wuce.
Daga ƙarshe Zayd ya sauke numfashi a hankali,
“Okay, Ummie.”
Fuskar Ummie ta haskaka,
“Good.”
Ta gyada kai cikin gamsuwa,
“Allah Ya kiyaye hanya.”
Zayd ya yi murmushi kaɗan,
“Amin.”

Ummie ta sake kallonsa,
“I wish you a beautiful and joyful flight to the United States.”
Zayd ya ɗan yi murmushi,
“Thank you, Ummie.”
Sai ya ɗan sunkuya, ya sumbaci goshinta cikin girmamawa.

Ummie ta rufe idanunta na ɗan lokaci, hannunta har yanzu yana kan hannunsa,
“Take care of yourself.”
“I will.”
“Call me when you land.”
“I will.”
“Promise?”
Zayd ya yi ƙaramar dariya,
“Promise.”

Sai ya sake gyada mata kai, daga nan ya juya a hankali.
Ya buɗe ƙofar back seat ɗin motar, Sameer yana zaune a gaba tuni, yayin da driver yake jiran umarnin tashi.
Zayd ya shiga ya zauna, ya janyo ƙofar ya rufe.

Motar ta fara motsawa a hankali.
Ummie ta tsaya a inda take, hannunta ya ɗago sama, tana masa sallama.
Zayd ya kalleta ta cikin glass ɗin motar, sai ya ɗaga hannu ya amsa mata.

Har motar ta fara yin nisa… Ummie ba ta sauke hannunta ba, ta ci gaba da kallonsa har sai da motocin convoy ɗin suka ɓace daga ganinta.
Sai ta sauke hannunta a hankali, ta yi murmushi,
“Allah Ya tsare min kai, Habibi.”

⸻

Motar ta fara ɗaukar saiti a titin Kaduna, tana nufar hanyar airport.
Zayd yana zaune a back seat, bayansa a jingine da kujerar, idanunsa a lumshe.

A fuskarshi akwai nutsuwa, amma duk wanda ya san shi zai iya gane cewa hankalinsa yana wani wuri.
Bayan ƴan mintuna, sai ya ɗan buɗe idanunsa, ya ɗaga kansa a hankali, ya kalli gaba inda Sameer yake zaune.

Sai ya buɗe baki,
“Sameer.”
Sameer ya ɗan juya kai cikin girmamawa,
“Yes, Boss?”

Zayd bai amsa nan take ba, ya sake yin shiru, kamar yana tunanin yadda zai faɗi abin da yake son faɗa.
Daga ƙarshe sai ya ce cikin sanyin murya,
“Get her number for me and send it to me.”

Sameer ya ɗan juya fuska kamar bai fahimta ba, saura kaɗan ya tambaya “who?”
Amma kafin kalmar ta fita gaba ɗaya, sai wani abu ya haskaka a brain ɗinsa.
Raihana.

Ya gyada kai nan take,
“Yes, Boss.”
Zayd bai ƙara cewa komai ba, ya sake jingina kansa da kujerar, ya lumshe idanunsa.

Sameer ya kalli screen ɗin wayarsa na ƴan daƙiƙu, sannan ya koma kan wasu files da ke gabansa.
Shiru ya sake mamaye motar.

Amma ba daɗewa ba Sameer ya karya shirun,
“Boss...”
Zayd bai buɗe idanunsa ba,
“Hmm?”
“There are a few things waiting for you at the office.”
Zayd ya ɗan buɗe ido ɗaya,
“Like?”

Sameer ya buɗe tablet ɗin da ke gabansa,
“First, the final report for the Lagos project is ready, the board wants your approval before it’s submitted.”
Zayd ya gyada kai a hankali,
“Send it to me.”
“Yes, Boss.”

Sameer ya sauke idanunsa kan tablet ɗin,
“Then there’s the meeting with the investors, they moved it to Monday morning.”
Zayd ya ɗan kalli agogon hannunsa,
“Monday?”
“Yes.”
“Who’s handling it while I’m away?”
Sameer ya yi shiru na ɗan lokaci,
“That’s actually one of the things I wanted to discuss with you.”

Zayd ya kalle shi.
Sameer ya ci gaba,
“There are also two contracts that need to be reviewed before the end of the week, and the Abuja branch sent another request concerning the new project.”
Zayd ya ɗan sauke numfashi,
“Anything else?”
“Your meeting with the legal team is also scheduled for next week.”

Zayd ya yi shiru, ya sake kallon window, kamar yana lissafa duk abubuwan da zai bar a baya.
Daga ƙarshe ya kalli Sameer,
“You can put someone in charge while I’m away.”
Sameer ya ɗan ɗaga gira,
“Who, Boss?”
Zayd bai yi tunani mai tsawo ba,
“Fahad.”
Sameer ya gyada kai,
“Fahad?”
“Yes.”
Ya ɗan gyara zamansa,
“Make him act on my behalf.”

Sameer ya ɗan rubuta wani abu a tablet,
“Should he handle the day-to-day operations only, or—”
“Everything that doesn’t require my direct approval.”
Sameer ya ɗago kai,
“Understood.”

Zayd ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙara,
“Let him oversee the office, the Lagos project and the Abuja branch.”
“Yes, Boss.”
“Any major decision should still come through me.”
Sameer ya gyada kai,
“Of course.”

Zayd ya sake jingina kansa da kujerar,
“And Sameer...”
“Yes, Boss?”
“Make sure the investors don’t feel my absence.”
Sameer ya yi ƙaramin murmushi,
“I’ll handle it.”
Zayd ya lumshe idanunsa,
“I know.”

Motar ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa.
Sameer ya koma kan tablet ɗinsa yana tsara duk abin da Zayd ya umurce shi.
Amma a cikin zuciyarsa… wata tambaya ce kawai take yawo,
“Me ya sa Boss ya damu da samun number ɗin Raihana kafin ya tafi?”

Ya kalli Zayd a cikin rear-view mirror.
Zayd kuwa… idanunsa a lumshe suke, fuskarsa babu wani abu da zai iya bayyana abin da yake tunani.
Kawai sai yayi murmushi ya maida hankalinsa kan abinda ke gabansa.

—————-

Bayan doguwar tafiya… jirgin ya sauka lafiya a filin jirgin saman John F. Kennedy International Airport (JFK) — Queens, New York.

Da aka gama duk wani abu na airport, Zayd ya fito daga cikin aircraft ɗin cikin nutsuwarsa.
Tafiyar ta gajiyar da shi sosai, amma duk da haka, babu wani abu a fuskarsa da zai nuna hakan.

Ya fito cikin wani simple but classy travel outfit—dark trousers, white shirt da aka buɗe maɓalli ɗaya a sama, sai dark jacket da ya ɗora a kafaɗarsa.
Wayarsa tana hannunsa.

Da ya kunna screen ɗin… sai ya ga notifications da yawa.
Felicia.
Missed calls, messages, calls, more messages.

Ya ɗan rufe idanunsa,
“Seriously?”
Tun daga Lagos take ta fara zuba masa kira, ya ƙi ɗauka.
Da farko ya ce ba zai sanar mata yana zuwa ba har ya isa, amma Felicia… ba irin mutanen da suke iya ɗaukar shiru bane.

Har saukar jirgin ma ta ci gaba.
Daga ƙarshe, saboda yawan kiran da wayarsa ta dinga yi masa, sai ya buɗe message dinta ɗaya,
“I know you’re coming to New York, don’t even try to disappear on me.”

Zayd ya ɗan girgiza kai, sai ya rubuta mata kawai:
“I’m here.”
Bai ƙara wani bayani ba.

A wajen Arrivals kuwa… wata matashiyar mace ce tsaye kusa da entrance.
Felicia.

Tana sanye da wani simple but expensive-looking outfit—cream fitted top da wide-leg black trousers, ƙaramin handbag a kafaɗarta, da white sneakers masu tsabta.
Dogon gashinta mai laushi ta gyara shi cikin sleek ponytail, wasu ƙananan strands suka zubo gefen fuskarta.

Fuskarta kyakkyawa ce sosai.
Large brown eyes, well-shaped brows, soft full lips, small straight nose, da kuma wani irin murmushi da yake sa mutum ya san cewa wannan mace tana da confidence fiye da kima.

Ta yi kyau, very beautiful.
Amma abin da ya fi komai jan hankali a jikinta shi ne yadda take ɗaukar kanta—confident, playful, kuma kamar ba ta damu da wanda yake kallonta ba.

Da ta ga wasu mutane suna fitowa daga arrivals, sai ta fara kallon kowanne mutum,
“Where is this man?”
Ta ɗan duba wayarta, sai ta sake ɗaga kai,
“Zayd...”
Ta faɗa cikin shagwaba,
“Babe, where are you?”

Sai can… idanunta suka sauka kan wani mutum da yake fitowa daga cikin corridor.
Ta tsaya, sai murmushinta ya faɗaɗa,
“Finally!”
Zayd ne.

Ya fito yana jan ƙaramin suitcase ɗinsa, bai ma lura da ita ba.
Har sai… da yaji kawai an rungume shi.

Zayd ya tsaya cak.
Felicia ta rungume shi sosai,
“BABEEE!”
Zayd ya sauke idanunsa zuwa gare ta, ya yi shiru na ƴan daƙiƙu yana kallonta from head to toes, sai ya girgiza kai,
“Felicia...”

Ta ƙara matse shi,
“My man!”
Zayd ya ɗan ja numfashi,
“Can you breathe?”
Felicia ta fashe da dariya, amma ba ta sake shi nan take ba,
“I missed you!”
Ta ɗago kai tana kallonsa, murmushi cike da fuskarta,
“Look at you!”
Ta sake kallonsa daga sama har ƙasa,
“Still looking this good after that long flight? Honestly, it’s unfair.”

Zayd bai ce komai ba, kawai ya ɗan kalleta.
Felicia ta yi dariya,
“I missed you, you know?”
Ya dan lumshe idanunshi Akan fuskarta amma baice komai ba, fuskarshi babu wani expression.

“Don’t give me that face, I called you so many times!”
Ta ɗaga wayarta tana nuna masa screen ɗin,
“Look! I almost thought you were ignoring me on purpose.”
Zayd ya kalli wayar, sai ya ɗaga gira kaɗan.

Felicia ta fashe da dariya,
“Okay, maybe you were.”
Ta sake kama hannunsa,
“Come on, babe, I’ve been waiting for you.”

Zayd ya ɗauki suitcase ɗinsa.
Felicia ta kama dayan hannunsa kamar ance zai gudu ne,
“Do you know how excited I am?”
Bai amsa ba,
“My graduation is literally around the corner!”
Ta ɗan tsaya gabansa,
“And you actually came.”

Zayd ya kalleta.
Felicia ta yi murmushi mai cike da farin ciki,
“I knew you wouldn’t disappoint me.”
Zayd ya ɗan juya idanunsa gefe.

Felicia ta ci gaba da magana,
“Actually, I already told everyone you were coming.”
Ya kalleta,
“Everyone?”
“Of course!”
Ta yi dariya,
“My friends, my cousins... everyone.”
Zayd ya sauke numfashi.

Felicia ta ɗan matso kusa,
“And since you came all the way here because of my graduation...”
Ta yi murmushi,
“Zaka sauka a gidanmu, sabida kazo ne sabida ni.”
Zayd ya girgiza kai a hankali,
“No.”
Felicia ta tsaya,
“No?”
Zayd ya kalleta,
“I’ll stay at my place.”

Felicia ta buɗe baki,
“Your place?”
Ya gyada kai.
Ta ɗan yi shiru na ƴan daƙiƙu, sannan ta ɗaga gira,
“But babe...”
Zayd ya kalleta kawai,
“I thought you were coming to stay with us.”
Yayi shiru kawai yana kallonta.

Felicia ta sake kama hannunsa da kyau,
“My mom is already expecting you.”
Zayd ya ɗan kalleta.

Felicia ta ci gaba cikin shagwaɓa,
“And you know how happy she’ll be if you stay.”
Zayd ya girgiza kai,
“Felicia.”
“Hmm?”
“I’ll stay at my house.”
Ta yi wani irin ajiyar zuciya,
“Fine.”
Ta saki hannunsa, amma murmushin da ke fuskarta bai ɓace ba.

Sai ta ɗan yi tunani,
“Okay...”
Ta ɗaga kai,
“If you’re staying at your place...”
Zayd ya kalleta,
“Nima zan zauna tare da kai a can.”
Zayd ya tsaya, ya kalle ta.

Felicia ta yi murmushi kamar wacce ta riga ta yanke hukunci,
“Yes, that’s it.”
“I’m coming with you.”
Zayd ya ɗan lumshe idanunsa.

Felicia ta yi saurin ƙara bayani,
“Don’t even argue, you came here for my graduation, remember?”
Zayd bai ce komai ba.
Ta yi murmushi,
“So I’ll keep you company until the graduation.”

Zayd ya ɗauki suitcase ɗinsa ya nufi motar, ta da riga yayi booking.
Felicia ta bi bayansa cikin farin ciki,
“See? You didn’t even say no.”
Zayd ya buɗe ƙofar motar ya ja baya, ta fara shiga.

Ta ɗago kai ta kalle shi,
“Babe?”
Ya kalleta,
“Thank you for coming.”
Wannan karon Zayd ya tsaya na ɗan lokaci, ya kalleta kawai, sai ya ɗan gyada kai, yana murmushi.

Felicia ta yi murmushi,
“That’s all I needed.”
Zayd ya shiga gefenta ya rufe.

Motar ta fara tafiya.
Felicia ta jingina da kafadarshi, tana murmushi ita kaɗai,
“New York just got better.”
Zayd ya kalleta na ɗan lokaci, sai ya maida idanunsa gaba.

Bai ce komai ba.
Amma Felicia… ta riga ta fara jin kamar wannan tafiyar ta kawo mata fiye farinciki fiye da graduation kawai.




Not edited

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.