Free chapter · Read without an account

BETWEEN 2 HEARTS

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN




*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER THIRTY EIGHT:38*

*BETWEEN TWO HEARTS*

*JIDDAAH BARKUM*

——————

Felicia ta matso kusa da Zayd.
“Babe, mu je mu kwanta, dare ya yi.”

Zayd ya ɗan buɗe idanunsa ya kalleta, kafin ya amsa cikin ƙasa da murya,
“Zan kwanta a nan, you go inside.”

Felicia ta turo baki kaɗan,
“After all the months we’ve spent apart, yanzu kuma kazo shine zakace zaka kwana a nan?”
Ta ƙara matsowa kusa, sannan ta ɗora kanta a kan cinyarsa,
“I’m sleeping here.”

Zayd ya ɗan lumshe idanunsa,
“Please, go inside.”
Felicia ta ɗago kai ta kalle shi,
“Nima a nan zan kwana.”

Zayd ya dan lumshe idanunsa kafin ya buɗe cikin sanyin murya ya ce,
“A nan zan kwanta, karki sakani ciwon kaiii.”

Felicia ta yi shiru na ƴan daƙiƙu.
Ta san Zayd.
Idan bai shirya yin wani abu ba, ba zai yi ba.

Sai kawai ta miƙe ba tare da ta ƙara magana ba, ta ɗauki hanyar bedroom ɗin.
Zayd ya bi fa da kallo har sai da ta shiga ta rufe ƙofar.
Sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali, ya jingina kansa da kyau a jikin kujerar, sannan ya lumshe idanunsa.

Washegari da suka tashi, Felicia ta dinga share shi sama-sama, ta dinga masa magana, duk lokacin da yayi mata magana sai ya kalleta kawai.

A yanzu tana tsaye a gefen kujerar da yake zaune tana fesa turare a jikin curtains ɗin falon, sai Zayd ya miƙa hannu daga inda yake zaune, ya janyo hannunta.

Nan take ta rasa balance, ta faɗo kan shi.
Zayd ya kafe ta da waɗancan idanunsa nasa masu sa ta manta wacece ita, amma Felicia ta ƙi yarda ta kalle shi, kawai ta kauda kai tana turo baki.

Zayd ya yi ɗan murmushi.
Sai ya matsa kusa, ya hura mata iska a kunne sannan ya ɗan cije gefen kunnenta a hankali.

Felicia ta juyo da sauri, ta kankame shi,
“Babe, stoppp!”
Zayd ya yi ƙaramar dariya,
“Ni kike sharewa, ko?”
Felicia ta turo baki,
“I’m just hurt.”
Zayd ya ɗaga gira,
“Why?”

Ta ɗan kalle shi,
“Because I feel like you’re not happy that I’m here, baka farinciki da ganina a tare da kai bayan tsawon lokacin da muka dauka ba ma tare.”

Zayd ya yi shiru yana kallonta.
Felicia ta ci gaba,
“Jiya ma ka kore ni ka ce na je na kwanta, you didn’t even let us spend the night together.”

Zayd ya ɗan sunkuyo, ya gyara mata zamanta a kan cinyarsa, sannan ya matso da fuskarsa kusa da kunnenta.
Cikin ƙasa da murya ya ce,
“But you know the reason, kin san dalilina na yin haka?”

Felicia ta turo baki,
“Did I ask for intimacy?”
Ta ɗan kalle shi,
“Kawai fa cewa nayi mu kwanta waje daya, that’s all.”

Zayd ya ɗan lumshe idanunsa, sai ya ce cikin sanyin murya,
“I’m sorry.”
Ya ɗan dakata, sannan ya ƙara,
“Okay, get ready, mu je mu ƙarasa siyayyar abubuwan da za ki yi amfani da su gobe.”

Felicia ta sake turo baki,
“I don’t want to.”
Zayd ya yi murmushi, ya ɗan lakace mata hanci,
“Too bad, toh ni ina so.”
ya yi magana yana kwaikwayon muryarta,

Felicia ba ta san lokacin da ta fashe da dariya ba.
Zayd ma ya yi ɗan murmushi yana kallonta.

Felicia ta girgiza kai tana dariya.
Ta dan kamoo hannunshi a hankali taa dora akan kirjinta tana kuma kallon fuskarshi, murmushin fuskarshi ya dan fara sauyawa, ta saki wani nishi tana sake matsa hannunshi da ta dora a kan kirjinta.

Cikin wani seducing voice tace,
“Babe pleaseeeee.”
Ya kalleta, sai kuma yayi saurin janye hannunshi,
“Stop it,” ya faɗa da muryar data fara sauyawa, sannan ta miƙe tana turo baki,
“Fine, bari na shirya.”

Baice komai ba, ta dan sake kamo hannunshi,
“Kayi magana tooohhh.”
Zayd ya dan kalleta sai ya ɗaga gira,
“Okay, beautiful.”
Ya faɗa yana mata murmushi.

Wani uban dadi ya kama ta, jin yace mata beautiful.
Da sauri ta juya tana tsalle ta nufi bedroom din.

————-

*MALALI*

Da safe, Raihana na zaune a kan wata kujera a tsakar gida, idanunta a kan Maryam wadda ke zaune kusa da ita Akan tabarma tana yin assignment ɗinta.

Raihana ta ɗan sauke idanunta ƙasa.
Zuciyarta ta yi mata wani irin nauyi.
Ba wai komai bane... amma ganin yanzu kowa yana zuwa makaranta, ita kuwa tun bayan abin da ya faru bata koma ba, yana damunta fiye da yadda take son nunawa.

Maryam ta ɗan ɗago kai daga kan littafinta, ta kalleta,
“Ray?”
Raihana ta ɗago idanunta,
“Hmm?”
Maryam ta ɗan ɗaga takardar da ke gabanta,
“Don Allah, mene ne reaction ɗin?”
Raihana ta ɗan kalli littafin,
“Chemical reaction.”
Maryam ta karasa tana kallon ta.

Raihana ta amsa kai tsaye,
“Chemical reaction is a process in which one or more substances change to form new substances with different properties.”
Maryam ta ɗan buɗe baki,
“Ohh...”
Sai ta maida hankalinta kan rubutunta, ta fara rubuta amsar da sauri.

Raihana kuwa ta sake sauke idanunta, kawai ta yi shiru.
Amma a zuciyarta, tambayar da take ta maimaitawa ita ce—
“Yaushe ni ma zan koma makaranta?”

Baffa kuwa yana tsaye a bakin ƙofar ɗakinsa, idanunsa a kanta.
Ko da yake bai san ainihin abin da ke yawo a cikin zuciyarta ba, amma “labarin zuciya a tambayi fuska”—tun kafin yau ya riga ya fahimci cewa rashin komawarta makaranta yana damunta.
Shi kansa ba ya jin daɗin ganin hakan.

Ya ɗan girgiza kai, sannan cikin sanyin murya ya ce,
“Raihana.”
Raihana ta ɗago kai,
“Na’am, Baffa?”
Ya yi mata alama da hannu,
“Zo nan.”

A hankali Raihana ta miƙe, ta nufi ɗakinsa.
Da ta isa, sai ta durƙusa a gabansa.
Baffa ya kalleta,
“Shigo ciki.”
Ta gyada kai, ta bi shi.

Bayan sun zauna na ƴan daƙiƙu cikin shiru, Baffa ya kalleta sosai,
“Nasan rashin makaranta yana damunki.”
Raihana ta sauke idanunta ƙasa.

Baffa ya ci gaba,
“Ki yi haƙuri, za ki koma, In Shaa Allah.”
Ta ɗago idanunta kaɗan,
“Na san yadda kike matuƙar son karatunki.”
Ya ɗan yi shiru,
“Abin da ya faru bai kamata ya sa ki ji kamar komai ya tsaya ba, in Shaa Allah shekarun da kika bata ba za su tashi a banza ba.”

Raihana ta ɗan jinjina kai,
“Na gode, Baffa.”
Baffa ya ɗan kalleta na ƴan daƙiƙu, sai ya sauke numfashi a hankali,
“Amma akwai wani abu da nake son tambayarki.”
Raihana ta ɗago kai.

Baffa ya ɗan matsa zamansa,
“Tsakanin Haris da Zayd... wanne ne ya fi kwanciya a zuciyarki?”

Raihana ta kafe shi da ido, zuciyarta ta buga.
Kwata-kwata bata kawo Baffa zai yi mata wannan tambayar ba.
Ta matse yatsun hannunta waje ɗaya.

Sai brain ɗinta ya dawo mata da muryar matar da ta ji a wayar Zayd jiya,
“Babeeeeee...”
Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci,
“Maybe ma yana da mata...”

Sai kuma fuskar Haris ta yi mata popping a tunaninta, yadda yake kallonta, yadda yake nuna mata kulawa, yadda muryarsa ke sauyawa idan yana magana da ita.

Baffa ya katse tunaninta,
“Ke nake sauraro.”
Raihana ta ɗago idanunta a hankali, ta haɗiye yawu, bakinta ya yi mata nauyi.

Ta kalli Baffa, sannan ta sake sauke idanunta.
Baffa bai matsa mata ba, kawai ya jira,
“Ki faɗa min gaskiya, Raihana.”
Ya ɗan dakata,
“A matsayina na mahaifinki, bana son ki yi min ƙarya, kuma bana son ki ɓoye min abin da yake cikin zuciyarki.”

Raihana ta matse hannunta, ta ɗan rufe idanunta, sai ta ja numfashi a hankali.
Daga ƙarshe… ta daure,
“Haris...”
Muryarta ta fito ƙasa-ƙasa.

Baffa ya ɗan kalleta, yana nazarin fuskarta na ƴan daƙiƙu, kamar yana son gano abinda ta boye a cikin zuciyarta.

Daga ƙarshe ya jinjina kai, ya na jingina bayansa da jikin kujerar da yake kai, cikin nutsuwa ya ce,
“Ki sanar da Haris ya turo min da magabatansa.”

Raihana ta ɗan tsaya, zuciyarta ta sake bugawa, sai ta jinjina kai a hankali, tana haɗiye yawu,
“Toh, Baffa.”

Baffa ya nuna mata ƙofa da hannunsa,
“Za ki iya tafiya.”
A hankali Raihana ta miƙe, ta nufi ƙofar ba tare da ta ƙara cewa komai ba.
Baffa ya bita da kallo har sai da ta kai bakin ƙofa.
Da ta fita, sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali.





Not edited

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.