Free chapter · Read without an account

PRETENDING

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN




*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER FORTY:40*

*PRENTENDING*

*JIDDAAH BARKUM*

⸻

Seeyama ta ƙara matsa ƙafarta a kan accelerator ɗin motar, tana kallon babban gate ɗin mansion ɗin Armaan da ke gabanta.
Tun daga nesa ma gate ɗin ya isa ya nuna irin gidan da yake bayan sa.

Babban ƙarfe ne mai tsayi, an yi masa finishing mai kyau, akwai security post a gefensa, sannan wani security guard yana tsaye kusa da ƙofar yana kallon motar da ta ƙaraso.
Da motar ta ƙara matsowa kusa, Seeyama ta ɗan rage gudu.
Ta sauke gilashin motar kaɗan.

Sai ta danna horn.
Piiiiiip!
Sautin horn ɗin ya cika wajen.

Guard ɗin ya ɗago kai, ya kalli motar, sai ya ɗan matso gaba, kamar yana son tabbatar da wanda ke ciki.
Seeyama ta ɗaga glasses ɗinta kaɗan, ta kalle shi ta cikin gilashin ta buga wani uban tsaki kafin ta daga murya,
“Open the gate joor!”

Guard ɗin ya juya da sauri, ya san halin ta, bata da kirki duk sanda tazo gidan nan sai ta yi wani abu na rashin albarka.
Nan take ya matsa gefe, ya yiwa ɗayan security ɗin da ke kusa alama.

Ƙofar gate ɗin ta fara buɗewa a hankali.
Seeyama ta jingina bayanta da kujerar motar, tana kallon gate ɗin har ya buɗe gaba ɗaya.
Ta danna motar ciki da uban gudu ta shiga.

Da ta isa cikin compound ɗin, sai ta rage gudun motar.
Idanunta suka fara yawo a hankali.
Babban compound ɗin ya shimfiɗe a gabanta.

Garden ɗin ya yi kyau, ciyawa ta yi lami-lami, furanni sun jere a gefe, manyan bishiyoyi suna tsaye cikin tsari, motocin gidan kuma suna ajiye a wani gefe.
Seeyama ta ɗan ɗaga gira.
Ta duba hagu.
Ta duba dama.
Sai ta sauke glasses ɗin da ke kan idanunta kaɗan, kamar tana son ta kalli komai da kyau.

A ƙarshe ta samu parking area kusa da entrance ɗin mansion.
Ta juya steering ɗin a hankali, ta shiga parking ɗin.
Ta gyara motar sau biyu kafin ta tsaya daidai.
Sai ta kashe engine.
Click.
Shiru ya ratsa cikin motar.

Seeyama ta zauna na ƴan seconds ba tare da ta fito ba.
Ta kalli kanta a cikin mirror, ta gyara veil ɗinta, ta ɗan gyara lip ɗinta da yatsanta.
Sai ta ɗauki handbag ɗinta.

Ta buɗe ƙofar motar, ta fito a hankali.
Takalmanta suka taɓa ƙasan compound ɗin.
Ta tsaya kusa da motar, sannan ta ɗaga idanunta zuwa mansion ɗin.
Ta ɗan yi murmushi.

Wannan shi ne gidan da ta daɗe tana son ta samu kanta a ciki ba a matsayin gidan yayan mahaifiyarta ba, sai dai a matsayin matar gidan.

Ta kalli suitcase ɗin da ke kujerar bayan motar, sannan ta ɗan gyara hannun bag dinta dake kafadarta,
“Finally...”
Ta furta a hankali.

Sai ta buɗe bayan motar ta ciro suitcase ɗinta, ta ja shi a hankali.
Amma kafin ta kai ga entrance ɗin, sai idanunta suka tsaya kan wani ma’aikacin gidan da ke gefe.

Mutumin yana tsaye a cikin garden yana shayar da furanni, ruwan yana fitowa daga hose ɗin da ke hannunsa, hankalinsa gaba ɗaya yana kan aikin da yake yi.
Bai ma lura da cewa Seeyama ta shigo ba.

Seeyama ta tsaya, ta kalle shi.
Mutumin bai juyo ba.
Ta kalli suitcase ɗin da ke hannunta, sai ta sake kallonsa, har yanzu bai kula ta ba.

Seeyama ta ɗan dafe gefen handbag ɗinta, fuskarta ta fara canjawa.
Ta ɗaga murya,
“Hey!”
Mutumin bai ji ba.

Seeyama ta ƙara tsawa,
“You there!”
A wannan karon mutumin ya firgita, ya juyo da sauri.
Da ganinta tsaye, sai ya kashe ruwan,
“Madam...”

Seeyama ta nuna suitcase ɗin da ke hannunta,
“Can’t you see this?”
Mutumin ya kalli suitcase ɗin, sai ya kalli Seeyama,
“Sorry, madam...”

Seeyama ta katse shi,
“Kana tsaye kana jirana na dauka da kaina kenan?”
“Sorry, madam, I didn’t know you had arrived.”
Seeyama ta yi wani ɗan murmushin rashin mutunci,
“Obviously you didn’t.”
Ta ɗan matsa kusa,
“What are you people here for? Decoration?”

Mutumin ya sunkuyar da kai,
“No, madam, I’m sorry.”
Seeyama ta nuna suitcase ɗin,
“Come and take it.”
“Sorry, madam.”
Da sauri ya ƙaraso, ya karɓi suitcase ɗin daga hannunta.

Seeyama ta saki hannunta daga handle ɗin, sai ta kalle shi na ƴan seconds,
“Next time, learn to look around you.”
“Yes, madam.”

Ta juya, ta fara tafiya zuwa cikin mansion ɗin, mutumin ya bi bayanta yana jan suitcase ɗin.
Seeyama kuwa ko waiwayawa ba ta yi ba, ta ɗaga kai kaɗan, tana kallon babban entrance ɗin da ke gabanta.

Kai tsaye ta shiga lounge ɗin.
Babu kowa a wajen... sai Suhaila kaɗai da ke zaune a dining area, tana ɗan cin abinci yayin da take dan danna wayarta.

Da ta ji karar buɗe ƙofa, sai ta ɗan juyo.
Nan take idanunta suka sauka kan Seeyama, ta ɗan buɗe ido, kamar ba ta yarda ita take gani ba, sai kuma wani murmushi ya suɓuce mata,
“Heyyy!”
Ta faɗa da ɗan ƙaramar murya.

Seeyama ta waigo, da ta hango Suhaila a dining area, sai ta nufi wajenta kai tsaye.
Amma kafin ta ƙarasa… sai ta tsaya.
Ta juya ta kalli mutumin da ya shigo mata da suitcase ɗin.

Har yanzu yana tsaye a wajen, suitcase ɗin na hannunsa, bai kuskuren ajiyewa ya tafi ba, saboda tsoron kada a ci masa mutunci.
Seeyama ta ɗaga murya cikin tsawa,
“Toh, what exactly are you still doing here?”

Mutumin ya firgita,
“Ba dai ka shigo cikin gidan ne saboda za ka tsaya kana kallona ba?”
Ta ɗan matsa gaba,
“Or are you planning to follow me everywhere I go?”

Da sauri mutumin ya ajiye suitcase ɗin a ƙasa, ya ɗan sunkuyar da kansa,
“I’m sorry, ma’am.”
Seeyama taɓe baki,
“Dismissed.”
Ta ɗan girgiza kai cikin raini,
“Useless people.”

Mutumin bai ƙara cewa komai ba, da sauri ya juya ya fice daga lounge ɗin.
Suhaila ta bi shi da ido har ya fita, daga nan ta maido kallonta kan Seeyama.
Ta girgiza kai kaɗan kafin ta ce,
“Kin zo kuma za ki fara bala’i kenan?”
Ta ɗan yi murmushi,
“Gaskiya Seeyama, sai kin rage wannan halin naki, yanzu ne fa mutumin ya shigo miki da kayanki, amma kika hau masa da faɗa.”

Seeyama ta wani harare ta,
“An masa masifar.”
Ta ɗaga gira,
“Meye aikin maids da servants ɗinmu idan ba su yi mana hidima ba?”
Ta ɗan ɗaga kafaɗarta,
“We pay them.”
Ta nuna ƙofar da mutumin ya bi,
“They are here to work, not to stand around staring at people.”
Sai ta kauda kai,
“Karki fara ɓata min rai tun yanzu, na gaji.”

Daga haka kawai ta juya, ta nufi hanyar stairs ba tare da ta jira amsar Suhaila ba.
Suhaila kuwa ta tsaya tana kallonta, bakinta a ɗan buɗe, ta bi bayanta da ido har sai da Seeyama ta ɓace daga ganinta.
Sai kawai ta girgiza kai a hankali,
“Allah ya kawo mu kuma aii...”
Ta furta a ƙasa-ƙasa, kafin ta maida hankalinta kan abincinta da wayarta.

⸻

*NEW YORK*

Motar Zayd ta tsaya a gaban wani katafaren luxury boutique da ke ɗaya daga cikin manyan titunan New York.
Zayd ya kashe engine ɗin.

Felicia ta kalli wajen ta ɗan buɗe baki,
“Babe...”
Zayd bai kalleta ba,
“Hmm?”
“Are we shopping here?”
Sai ya ɗan kalleta,
“Yes.”
Kawai.
Ya buɗe ƙofar motar ya fito.

Felicia ma ta sauka da sauri ta bi bayansa.
Da suka shiga cikin boutique ɗin, ma’aikatan wajen suka tarbe su cikin girmamawa,
“Good afternoon, sir.”
Zayd ya ɗan jinjina kai,
“Good afternoon.”

Felicia kuwa idanunta suka fara yawo.
Kayan da ke wajen sun yi kyau sosai, daga handbags zuwa shoes, perfumes, dresses da sauran kayan da za ta buƙata.
Zayd ya kalli ɗaya daga cikin ma’aikatan,
“Get everything she needs please.”
“Yes, sir.”

Felicia ta kalle shi,
“Everything?”
Zayd ya ɗan kalleta,
“Yes.”
“Babe, ba fa wash abubuwa da yawa nake so ba.”
Zayd ya ɗaga gira,
“Ban tambayi abinda kike so ba.”

Felicia ta yi shiru, sai kawai ta yi murmushi.
Ma’aikatan suka fara kawo mata kayan ɗaya bayan ɗaya.
Zayd kuwa yana tsaye gefe, hannunsa ɗaya a aljihunsa, yana kallonta cikin nutsuwa,
“Take this one.”

Felicia ta ɗaga dress ɗin tana kallonsa,
“Shi kake so na saka?”
Ya dan daga gira yana kallonta amma baiyi magana ba, sai ya cigaba,
“Babe, this one is expensive.”
Zayd ya kalleta,
“So?”
Felicia ta yi shiru,
“Okay...”
Ta ci gaba da zaɓe.

Bayan kusan awa ɗaya, kayan da aka tara mata sun cika manyan bags da dama.
Felicia ta kalli bags ɗin,
“Babe...”
“Hmm?”
“I think that’s enough.”
Zayd ya kalli ma’aikacin,
“Anything else you think she would like?”
“Yes, sir.”
“Add it.”

Felicia ta zaro ido,
“Babe!”
Zayd ya kalleta,
“What?”
“You’re spending too much.”
Ya ɗan kalli kayan,
“Don’t you worry about it.”
Sai ya koma kallon wayarsa kamar babu wani abu da ya faru.

A ƙarshe aka kawo invoice ɗin, Zayd ya karɓa, ya kalli adadin na ƴan seconds, babu wani expression a fuskarsa.
Ya miƙa card ɗinsa,
“Pay.”
“Yes, sir.”

Felicia ta tsaya tana kallonsa, sai ta ɗan girgiza kai.
Wannan mutumin kamar ba shi ne yake wahalar neman kuɗin ba.

Bayan komai ya kammala, suka fito daga boutique ɗin.
Felicia ta riƙe hannunsa,
“Babe...”
Zayd ya kalleta,
“Hmm?”
Ta ɗan turo baki,
“Ba ka siya min flowers ba.”
Zayd ya ɗan ɗaga gira,
“Flowers?”
Ta gyada kai,
“Yes.”
Ta ƙara matsowa kusa da shi,
“And a card.”

Zayd ya kalleta kamar yana son fahimtar abin da take nufi,
“Why?”
Felicia ta sake turo baki,
“Because you’re supposed to give me flowers and a card a gaban kawayena gobe.”
Zayd ya yi shiru, fuskarsa ta dawo cikin wannan CEO expression ɗinsa.

Felicia ta kama hannunsa da hannaye biyu,
“Please, babe...”
Zayd ya sauke idanunsa kan hannunta, sai ya ɗaga su ya kalleta.
Felicia ta ƙara shagwaɓa,
“Babe, pleaseee...”
Zayd ya ɗan lumshe idanunsa,
“Felicia...”
“Yes?”
Ya ɗan girgiza kai,
“You’re unbelievable.”

Felicia ta yi murmushi,
“Is that a yes?”
Zayd ya kalleta na ƴan seconds, sai ya ɗauki wayarsa,
“Get the flowers and the card.”
Felicia ta yi wani irin farin ciki,
“Really?”
Zayd ya ɗan kalleta,
“Yes.”
Ta rungume hannunsa,
“Thank you, babe!”
Zayd ya yi ɗan murmushi kaɗan,
“Sai kuma me?”

Felicia ta ɗan yi tunani,
“Hmm...”
Zayd ya ɗaga gira,
“Don’t push your luck.”
Felicia ta fashe da dariya.

⸻

Washegari…
Tun da safe gidansu Felicia ya cika da hayaniya, yayin da ita kuma uwar gayyar tana Tribeca tare da masoyinta.

Graduation party ɗin da aka shirya mata ya kasance a wani katafaren venue da ke cikin ɗaya daga cikin wuraren da ake yin manyan events a New York.
A wajen an kawata komai da kyau.

Furanni masu kyau sun cika entrance ɗin, manyan balloons masu launukan graduation ɗin sun jere a bango, sannan a tsakiyar wajen an rubuta sunan Felicia da shekarar graduation ɗinta da manyan haruffa.
A gefe guda kuwa akwai babban photo booth da aka shirya domin pictures.

Wurin ya cika da mutane.
’Yan uwa, abokai, classmates, wasu daga cikin iyayen abokanta.
Kowa yana sanye da kaya masu kyau, wasu cikin suits da elegant dresses.

Felicia ta shigo cikin venue ɗin tare da iyayenta. Ba haka taso ba, ta so ne ta shigo ita da Zayd amma ya dage ya ce ta shiga da yan gidansu, ba yanda ta iya haka ta kyale shi dan ta ga yana mata kirki a zuwan nan fiye da yanda ta zata, bata son ta kure shi su rabu tsiya tsiya.

Fuskarta cike take da farin ciki.
Mahaifiyarta ta riƙe hannunta tana ta gaya mata yadda take alfahari da ita, yayin da mahaifinta yake tsaye kusa da su yana kallonta da murmushi,
“Look at my baby...”
Mahaifiyarta ta ce cikin farin ciki.
Felicia ta rungumeta,
“Mom...”
“I’m so proud of you.”
Ta sumbaci goshinta.

A gefe guda kuma… Zayd ya shigo.
Cikin bakar suit ɗinsa mai tsari, farin shirt a ciki, babu wata hayaniya a jikinsa.
Kawai sai wannan natsuwar tasa, sai wannan irin kallon da yake yi kamar komai yana ƙarƙashin control ɗinsa.

Wasu daga cikin abokansa suka hango shi,
“Zayd!”
Ya ɗago kai, sai suka ƙaraso wajensa,
“Bro!”
Zayd ya yi murmushi kaɗan ya gaisa da su,
“Congratulations, man.”
“Thanks.”

Ɗaya daga cikinsu ya ɗan taɓa kafadarsa,
“Man, you actually came.”
Zayd ya ɗan ɗaga gira,
“Why wouldn’t I?”
Suka yi dariya,
“Because you’re always busy.”
Zayd ya girgiza kai,
“Not today.”
Sai ya kalli inda Felicia take.

Nan take murmushinsa ya ɗan canja.
Abokinsa ya bi kallonsa,
“Ohhh...”
Zayd ya kalle shi,
“Don’t.”
Ya faɗa cikin nutsuwa.
Abokin nasa ya fashe da dariya,
“Okay, okay.”

A lokacin ne Felicia ta hango shi, fuskarta ta sake washewa kamar dai ba yanzu suka rabu an entrance din ba,
“Babe!”
Ta nufi wajensa da sauri, da ta ƙarasa, ta rungume shi sosai.

Ta yi murmushi, sannan ta ɗan tsaya a gabansa,
“Do I look beautiful?”
Zayd ya kalleta daga sama har ƙasa,
“Very.”
Felicia ta yi murmushi mai cike da jin daɗi, sai ta ɗan miƙe ta sumbaci kumatunsa.

Wasu daga cikin abokansa suka fara ihu,
“Woooo!”
Felicia ta fara dariya, Zayd kuwa ya girgiza kai yana kallonsu,
“Grow up.”
Suka sake dariya.

Daga baya aka fara ɗaukar pictures.
Felicia ta fara da iyayenta, ta rungume mahaifiyarta, mahaifinta kuma yana tsaye kusa da ita.
Sannan da ’yan uwanta.

Daga nan classmates ɗinta suka kewaye ta, Felicia ta shiga tsakiyarsu tana dariya sosai,
“Three, two, one!”
Click!

Sai ta nufi wajen Zayd,
“Babe, come.”
Zayd ya ɗan kalleta,
“Me?”
“Picture.”
“Felicia...”
“Come on.”
Ta kama hannunsa ta ja shi.

Abokansa suka fara dariya,
“Boss, you have no choice!”
Zayd ya ɗan girgiza kai, ya tsaya kusa da Felicia.
Ta matso sosai, ta ɗora hannunta a gefen kugunsa, sai ta ɗan jingina kanta a kafaɗarsa.

Zayd ya kalli camera,
“Smile!”
Ta faɗa tana kallon yanda yayi da fuskar shi, fuskarta dauke da murmushi sosai.
Zayd kuwa ɗan ƙaramin murmushi ne kawai ya bayyana a fuskarsa.
Click!

“Another one!”
Felicia ta juya ta rungume shi, Zayd ya kama ta.
Ta ɗan ɗago kanta ta yi masa peck a kumatu.

Kowa ya fara ihu,
“Again!”
“Felicia ya isa haka!”
Felicia ta fashe da dariya, ta ɓoye fuskarta a kirjinsa.
Zayd ya yi murmushi yana girgiza kai,
“Are you guys done?”
“Never!”

Ɗaya daga cikin friends ɗinsa ya ɗaga waya,
“Boss, look here!”
Zayd ya kalli camera, Felicia ta tsaya kusa da shi tana murmushi.
Click.
Wani a cikin su ya ɗauka.

Sai aka sake ɗaukar na Zayd da friends ɗinsa, su na ɗaga glasses ɗinsu, suna dariya, suna yi masa teasing.
Zayd ya tsaya a tsakiyarsu, hannunsa cikin aljihunsa, yana ɗan murmushi.

Daga baya aka koma wajen abinci.
Manyan tables sun cika da abinci iri-iri, drinks, cakes da desserts.
Music yana tashi a hankali, wasu suna rawa, wasu suna hira, wasu kuma suna ɗaukar pictures.

Felicia ta kasance kamar ba ta san gajiya ba, ta dinga zagayawa daga wajen iyayenta zuwa friends ɗinta, tana karɓar congratulations, tana dariya, tana ɗaukar pictures.
A ƙarshe ta dawo wajen Zayd.

Ta tsaya gabansa,
“Babe...”
“Hmm?”
Ta ɗan kama hannunsa,
“Thank you for coming.”
Zayd ya kalleta na ƴan seconds,
“It’s your day.”
Ta yi murmushi, sai ta sake rungume shi.

A wannan karon Zayd ya rungumeta sosai.
Felicia ta ɗan lumshe idanunta,
“I’m happy.”
Zayd ya ɗan sauke kansa kusa da nata,
“Good.”
Sai ta ɗan ɗago kai ta sake masa peck a kumatu,
“Very happy.”
Zayd ya yi murmushi,
“Na gani.”

Daga nesa kuwa wasu daga cikin friends ɗinta suka fara kiran ta,
“Felicia! Cake time!”
Ta juya,
“Coming!”
Sai ta kalli Zayd,
“Let’s go.”
Zayd ya girgiza kai yana murmushi,
“Go.”
Ta kama hannunsa,
“A’ah ni dai kazo muje tare, zamu yanka, ka tuna naka ma lokacin graduation dinka tafe muka yanka.”

Ya dan kalleta amma baice komai ba, daga karshe suka nufi wajen cake ɗin tare, yayin da flash ɗin cameras ke ci gaba da haskawa a ko’ina.

Felicia ta tsaya a gefen cake ɗin tana murmushi, yayin da friends ɗinta suka kewaye su suna ta ɗaukar hotuna,
“Okay, cake time!”
Wata daga cikin friends ɗinta ta yi ihu.

Felicia ta fara dariya, sai ta kalli Zayd,
“Babe, come.”
Zayd ya matso kusa da ita, Felicia ta miƙa masa knife ɗin,
“You cut it.”
Zayd ya ɗan kalleta, sannan ya karɓa ba tare da musu ba.

Kowa ya fara ƙirga,
“Three...”
“Two...”
“One!”
Zayd da Felicia suka riƙe knife ɗin tare.
A hankali suka yanka cake ɗin.

Nan take aka fara tafa musu,
“Congratulations, Felicia!”
“Wooo!”
Felicia ta yi dariya tana kallon cake ɗin.

Zayd ya ɗauki ɗa cake a hannunsa, ya kai mata baki,
“Here.”
Felicia ta yi murmushi, ta dan buɗe baki ya saka mata.

Wasu suka fara ɗaukar hotuna,
“Look at them!”
“Cute!”
Felicia ta kalli Zayd,
“Your turn.”
Ta ɗauki ɗan cake a cokali ta miƙa masa.

Zayd ya girgiza kai a hankali,
“No.”
Felicia ta ɗan daure fuska,
“Why?”
“Bana ci kin sani.”
Ta sake miƙa masa,
“Just one bite.”
Zayd ya sake girgiza kai,
“No, Felicia.”

Ta ɗan kalle shi na ƴan seconds, sai wani murmushi ya bayyana a fuskarta,
“Okay...”
Zayd ya ɗan kankance idanunsa, kamar ya san akwai wata dabara data shirya,
“Don’t.”

Felicia ta yi kamar ba ta ji ba, ta ɗaga cokalin kusa da bakinsa.
Zayd ya juya kai gefe, nan take Felicia ta yi amfani da damar.
Ta matso da sauri ta danna masa ɗan cake a baki.

Zayd ya tsaya cak.
Kowa ya fashe da dariya,
“WOOOOOO!”
“Felicia!”
“Got you!”

Felicia ta fara dariya tana gudu kaɗan daga gabansa.
Zayd ya share bakin nasa da tissue, ya kalleta da wannan kallon nasa.
Felicia kuwa ta ɗora hannunta a bakinta tana dariya,
“Babe, just one bite!”

Zayd ya girgiza kai yana kallonta.
Wata daga cikin friends ɗinsu ta ɗaga camera,
“Wait! I got that!”
Nan take aka sake ɗaukar wani hoton.

Zayd yana kallon Felicia da fuskar ‘I can’t believe you just did that’, ita kuma tana dariya tana kallonsa.
Mutanen da ke wajen suka ci gaba da dariya da tafi.

Felicia ta sake matsowa kusa da shi,
“Smile, babe.”
Zayd ya ɗan ɗaga gira,
“After what you just did?”
Ta yi dariya, sai kawai ta kama hannunsa,
“Come on.”
Zayd ya girgiza kai, amma ya bi ta.
Camera flash ɗin ya sake haskawa.

—————

*MALALI*

Raihana tana kwance a kan gadon dakinta da misalin ƙarfe tara na dare.
Ta juya gefe guda, tana kallon rufin ɗakin ba tare da wani takamaiman abu da ke gabanta ba. Tunani ne kawai ya mamaye kanta.

Ta ɗaga hannu a hankali, ta gyara hular kanta wadda ta zame kaɗan daga kan gashinta, sai ta sauke numfashi.
Ta kwana biyu rabonta da shiga wani platform na social media.

Tun bayan yadda hotunansu suka bazu, ta ɗauki ɗan break, ba don ba ta son social media ba, sai don kawai tana son ta ba kanta lokaci.
Ta so wannan yanayin ya huce, ta so zuciyarta ta daina jin kamar duk inda ta juya, mutane suna kallonta.

Amma yau... sai ta ji kamar tana son ta duba.
Ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta daga gefen pillow, ta buɗe screen ɗin.
Finger ɗinta ya yi yawo a kai na ƴan daƙiƙu, kamar tana tunanin ko ya dace ta shiga.

Daga ƙarshe… ta shiga Instagram.
Kai tsaye ta fara scrolling.
Video ɗaya, ta wuce.
Wani, ta tsaya ta kalla na ƴan seconds, sai ta ɗan yi murmushi.
Finger ɗinta ya danna like.

Ta sake scrolling, ta dan kalli wanda ya burgeta sai ta danna like.
Sai kwatsam… wani post ya bayyana.

Raihana ta tsaya, idanunta suka tsaya cak a kan screen ɗin.
A cikin hoton, Felicia ta rungume shi tana dariya, shi kuma yana kallonta da ɗan murmushi a fuskarsa.

Raihana ba ta motsa ba, ta sake kallon hoton.
Sai ta dan hi sliding zuwa next.
Wannan karon Felicia ce ta kamo kugunsa, jikinta a manne da shi yayin da Zayd yake kallonta.

Ba ta san dalilin da ya sa hannunta ya ɗaga wayar kusa da fuskarta ba, finger ɗinta ya taɓa screen ɗin, ta yi zooming a hankali.
Sai ta tsaya,
“Hmm...”
Ta furta a ƙasa-ƙasa.

A hoton, Zayd yana dauke da wannan irin murmushin da ba kasafai yake yi ba, kuma a gefensa... akwai wata kyakkyawar mace.
Raihana ta ɗan taɓe baki.

Ta ja screen ɗin zuwa hoton gaba, sai wani short video ya bayyana.
Lokacin da suke yanka cake, Felicia tana kusa da shi, Zayd yana riƙe da knife ɗin.
Daga baya aka ga Felicia tana ba shi cake, shi yana girgiza kai, sai ta shammace shi ta saka masa cake a baki.
Mutanen da ke wajen suka fashe da dariya.

Raihana ta kalli video ɗin har ya ƙare.
A ƙarƙashin post ɗin kuma akwai captions masu daɗin karantawa,
“Graduation looks better with your favorite person.”
“Some moments are simply unforgettable.”

Ta sake kallon hoton, ta yi shiru, sai kuma a hankali ta kashe data, ta kashe screen din ta ajiye wayar a gefe.
Ta juya ta rungume pillow ɗinta, ta rufe idanunta.

Amma bayan ƴan seconds… kamar wadda aka mintsina.
Sai ta sake buɗe idanunta, ta miƙa hannu, ta janyo wayar.
Kai tsaye ta shiga Contacts.

Finger ɗinta ya gangara ƙasa, har sai da ta ga sunan—
Haris.

Ta tsaya, ta kalli sunan na ƴan seconds, zuciyarta ta buga da sauri.
Sai ta ɗan ja numfashi, kafin ta danna Call.
Wayar ta fara ringing.

Raihana ta matse pillow ɗin da ke kusa da ita, kiran ya ci gaba da ringing…





Not edited

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.