Free chapter · Read without an account
Wasu mutane suna shigowa rayuwar mu ba tare da mun shirya ba Amma wani lokaci ka
follow me on Arewa pen👇
https://www.arewapen.com/u/fatimayahyaabuba200
Free page 2
Washegari da safe, Haneen ta farka da wani irin yanayi da ba ta iya fassara shi ba.Tun jiya da yamma, tunaninta yana ta komawa kan hirarta da Zayd.
Ba wai tana son shi ba.
A'a.
Ita kanta ba ta san abin da yake faruwa da ita ba.
Ta ɗauki wayarta domin ta duba lokaci.
Sai ta ga wani sabon saƙo.
“Ki kula da kanki.”
Ta tsaya cak.
Ba a rubuta sunan wanda ya turo saƙon ba saboda lambar ba a ajiyeta ba.
Ta sake karantawa.
“Waye wannan?”
Ta danna reply.
“Waye?”
Kafin ta ajiye wayar, amsa ta shigo.
“Mutumin da ya ce ki kula da kanki jiya.”
Haneen ta buɗe ido.
Zayd.
Ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sai murmushi ya bayyana a fuskarta ba tare da ta shirya ba.
Ta share murmushin da sauri.
“Me ya sa yake turo min saƙo?”
Ta rubuta:
“Na gode.”
Amsar ta zo nan take.
“Babu komai.”
Ta ajiye wayar.
Amma bayan minti biyu ta sake ɗauka.
Ta duba saƙon.
Ta sake ajiye ta.
Ta sake ɗauka.
“Allah Ya isa.”
---
A gidan Zayd kuwa, Faris yana zaune a kusa da shi.
Ya lura da yadda Zayd yake kallon wayarsa.
“Me ke faruwa?”
“Babu komai.”
“Ka yi murmushi.”
Zayd ya ɗago kai.
“Ni?”
“Eh, kai.”
“Ba na murmushi.”
Faris ya yi dariya.
“Na san ka fi kowa ɓoye abin da ke zuciyarka.”
Zayd bai amsa ba.
Faris ya matsa kusa.
“Yarinyar jiya ce?”
Zayd ya kalle shi.
“Ka bar maganar.”
“Na gane.”
Faris ya yi murmushi.
“Amma zan faɗa maka abu ɗaya.”
“Me?”
“Ka kula. Wani lokaci mutum yana fara kusantar wani ne ba tare da ya shirya ba.”
Zayd ya yi shiru.
Kalaman abokinsa sun tsaya a ransa.
---
Da rana, Haneen ta je gidan su Maryam.
Maryam tana zaune tana karatun wani littafi.
Da Haneen ta shiga, Maryam ta ɗago kai ta kalle tah
“Ke! Zo nan.”
Haneen ta zauna.
“Me ya faru?”
Maryam ta kalle ta sosai.
“Kin san Zayd yana da wata matsala?”
Haneen ta yi mamaki.
“Matsala?”
“Eh.”
“Wace irin matsala?”
Maryam ta yi shiru na ɗan lokaci.
“Ba zan iya gaya miki komai ba.”
“Maryam!”
“Na ce ba zan iya ba.”
Haneen ta ƙara tambaya.
“Amma me ya sa kika kawo maganarsa?”
Maryam ta yi murmushi.
“Saboda ina ganin kin fara sha'awar saninsa.”
Haneen ta yi saurin amsawa.
“Ni?”
“Eh.”
“Babu.”
“Kin tabbata?”
“Ƙwarai.”
Maryam ta yi dariya.
“To, idan babu, me ya sa kika yi saurin amsawa?”
Haneen ta yi shiru.
Ta kasa samun amsa.
---
Da yamma, Haneen ta fita zuwa ƙaramin lambun gidan.
Ta zauna ita kaɗai.
Ba zato sai ta ji muryar Zayd.
“Kin yi tunani sosai yau.”
Ta juya zayd ne ta gani tsaye yana kallon ta sanye da riga T-shirt fara da baƙin wando se kuma P-cap ɓaka ita ma da talkama me launin Baki da fari yayi masifar yin kyau
“Ka sake tsoratar da ni.”
“Yi haƙuri.”
Zayd ya tsaya nesa da ita.
Haneen ta kalle shi.
“Maryam ta ce kana da matsala.”
Zayd ya yi shiru.
“Me ta gaya miki?”
“Ba ta gaya min ba.”
“Madalla.”
“Amma yanzu zan tambaye ka.”
“Me?”
“Me kake ɓoyewa?”
Zayd ya kalli ƙasa.
A karon farko, fuskarsa ta rasa wancan kuzarin da take gani a kullum.
“Ba komai ba ne da ya shafe ki.”
Haneen ta yi shiru sannan tace“To.”
Ta tashi.
Zayd ya kira ta.
“Haneen.”
Ta tsaya.
“Me?”
“Ki yi haƙuri.”
Dame
Naga kamar kina fushi
Ta kalle shi
“ Ni ba na fushi.”
“Na sani.”
Sai ya ƙara:
“Amma wata rana zan gaya miki.”
“Me?”
“Komai.”
Haneen ta kalle shi na ɗan lokaci.
“Zan jira.”
Ta juya ta tafi.
Zayd ya tsaya yana kallonta.
Bai san cewa kalmar “zan jira” za ta kasance ɗaya daga cikin kalmomin da ba zai taɓa mantawa da su ba.
---
Da dare, Haneen tana kwance a gadonta.Wayarta ta sake yin ƙara.
Saƙo ne.
“Kin isa gida lafiya?”
Zuciyarta ta ɗan buga.
Ta rubuta:
“Eh.”
Sai ya sake turo:
“Madalla. Ki kwanta lafiya.”
Ta kalli saƙon.
Ta yi murmushi.
“Kai ma.”
Ta kashe wayar.
Amma kafin ta yi barci, ta tuna kalaman Zayd “Wata rana zan gaya miki komai.”
Ta fara tunanin me zai iya kasancewa wannan sirrin me ya sa Zayd yake ɓoye shi?Me ya sa yake kula da ita?
Kuma me ya sa duk lokacin da suka yi magana, zuciyarta take samun wani irin yanayi da ba ta saba da shi ba?
Ba ta san amsar ba.Amma wata rana za ta gano
Washegari da safe, Haneen ta isa gidan Maryam tun da wuri amma tun kafin ta shiga gidan, ta ga wata mota da ta saba ganibMotar Zayd.
Ta tsaya na ɗan lokaci me ya kawo shi nan kuma?”Ta shiga gidan Maryam tana cikin ɗakin girki tana shirya breakfast.
“Haneen! Zo ki taimaka min.”
Haneen ta ajiye jakarta ta shiga kitchen ɗinSai ta ji ƙarar dariyar maza daga falonTa gane muryar ɗaya daga cikinsu
Zayd.
Ta yi kamar ba ta ji komai ba Maryam ta kalle ta ta yi murmushi.
“Kin san wa ke falo?”
“Na sani.”
“Ba za ki je ki gaida shi ba?”
“Me zan je yi?”
“Gaisuwa kawai.”
Haneen ta girgiza kai.
“Ki je ke.”
Maryam ta yi dariya.
“Kin fara jin kunya ne?”
“Ba kunya ba ce.”
“To mece ce?”
“Babu komai.”
---
Bayan ɗan lokaci, Haneen ta fito daga ɗakin girki.
A daidai lokacin Zayd ya fito daga falo Suka haɗu a ƙofar Haneen ta yi saurin matsawa gefe Zayd ya tsaya “Good morning.”
“Morning.”
“Kin yi bacci lafiya?”
“Eh.”
“Madalla.”
Ta yi niyyar wucewa.
Zayd ya ce:
“Haneen.”
Ta tsaya.
“Me?”
“Har yanzu kina tunanin abin da na gaya miki?”
“Wanne?”
“Cewa wata rana zan gaya miki komai.”
Ta kalle shi.
“Eh.”
“Me kika gano?”
“Babu komai.”
Zayd ya yi murmushi.
“Da gaske?”
“Eh.”
“Ki yi haƙuri.”
“Me ya sa?”
“Saboda har yanzu lokaci bai yi ba.”
Haneen ta ɗan yi shiru.
“Na fahimta.”
Zayd ya kalle ta.
“Kin yi fushi?”
“A'a.”
“Kin tabbata?”
“Na tabbata.”
Sai ya ce a hankali:
“Madalla.”
Ya wuce.
Haneen ta tsaya tana kallonsa Ta kasa gane dalilin da ya sa kalmomin mutumin suke shiga zuciyarta haka.
---
Da yamma, Haneen tana zaune a waje ita kaɗaibWayarta ta yi ƙara Saƙo ne daga Zayd.
“Ki duba taga.”
Ta ɗago kai.
Ta kalli taga.
Zayd yana tsaye a can gefe.Ta buɗe baki cikin mamaki.
Ya daga mata hannu.
Ta yi murmushi ba tare da ta shirya ba Sai ya ɗaga ƙaramin takarda “Ki zo.”
Haneen ta fito.
“Me ya faru?”
Zayd ya miƙa mata takardar.
“Wannan taki ce.”
Ta buɗe.
Sai ta ga wani ƙaramin rubutu:
“Wasu mutane suna shigowa rayuwarmu ba tare da mun shirya ba.”
Ta ɗago kai.
“Me wannan yake nufi?”
Zayd ya yi murmushi.
“Ba komai.”
Haneen ta kalle shi.
“Ka daina cewa ba komai.”
“Me zan ce?”
“Gaskiya.”
Zayd ya yi shiru.
Ya kalle ta cikin nutsuwa.
“Gaskiyar ita ce…”
Ya dakata.
Haneen ta jira.
Sai ya ce:
“Har yanzu ni kaina ban fahimci abin da ke faruwa ba.”
Haneen ta kasa magana.
Zayd ya yi murmushi kaɗan.
“Amma zan gano.”
Ya juya ya tafi.
Haneen ta tsaya tana riƙe da takardar a hannunta Zuciyarta tana bugawa Ba ta san me ke faruwa tsakanin su ba.
Amma abu ɗaya ta fara gane wa Zayd ya fara zama wani ɓangare na tunaninta Kuma ita ma a hankali tana fara zama wani ɓangare na nasa.
---
Da dare, Haneen ta kwanta.Ta sake karanta takardar.
Sau ɗaya,Sau biyu,Sau uku Sai ta yi murmushi.
“Zayd…”
Ta faɗi sunan a hankali Amma kafin ta rufe idanunta, wayarta ta sake yin ƙara. Wani sabon saƙo.“Haneen, akwai abin da nake son gaya miki gobe. Amma ki yi alkawari ba za ki tsorata ba.”
Haneen ta zauna a gadon Zuciyarta ta fara bugawa da sauri Ta rubuta “Me ya faru?”Saƙon ya tafi.
Amma Zayd bai amsa ba Mintuna biyar Goma Ashirin Babu amsa Haneen ta fara damuwa.Ba ta san cewa a can gidan Zayd…
wani abu mai girma ya faru Kuma abin da Zayd yake shirin gaya mata gobe…
*BY TEEMARH'S WRITES
SOYAYYAR DA ƘADDARA TA RUBUTA NA KUDI NE AKAN 500 KACAL
***