Free chapter · Read without an account
WHEN PRIDE SPOKE
ZAYD ARMAAN
CHAPTER FORTY EIGHT : 48
WHEN PRIDE SPOKE
JIDDAAH BARKUM
⸻
Wayar Zayd ta fara ringing, Sameer ya yi shiru na ƴan seconds yana fatan Allah Ya sa ya ɗauka, domin ya san idan dare ya yi haka Zayd ba kasafai yake ɗaukar waya ba. Musamman ma da wayar tasa ba ringing take yi ba, sai dai vibration.
Yana cikin wannan tunanin ne sai muryar Zayd ta sauka a kunnensa cikin wannan husky tone ɗinsa da ke nuna alamun bacci ya fara ɗaukar shi, ya ce, “Hello?”
Sameer ya gyara zamansa da sauri, “Sorry, Boss… nasan ka fara bacci.” Ya ɗan yi shiru kamar yana tunanin ta inda zai fara maganar, Zayd kuwa daga can ya yi shiru yana sauraron Sameer. Sameer ya ɗan sauke numfashi, “Ahh… Boss…” Ya ɗan dakata, “Ta kira ne.”
Zayd bai ce komai ba. Sameer ya ci gaba, “Tana son magana da kai.” A ɗayan ɓangaren Zayd ya ɗan buɗe idanunsa, “Who?” Muryarsa ta fito ƙasa-ƙasa cike da kasala.
Sameer ya yi shiru kamar ya rasa yadda zai faɗa, daga ƙarshe ya ce, “Boss… from Malali ne.”
Shiru ya ratsa tsakaninsu, sai wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskar Zayd. Ƙarami, amma a bayyane yake. “Okay.” Kawai ya ce, sai ya cire wayar daga kunnensa.
Kiran ya katse. Sameer ya kalli screen ɗin na ƴan seconds ya yi jimm, “What should I do?…” Ya furta ƙasa-ƙasa bai sake cewa komai ba, sai kawai ya shiga messages ya buɗe sabuwar number ɗin da ta kira. Ya kwafa number ɗin Zayd ya tura mata, sai ya ajiye wayar.
⸻
Raihana kuwa… Ta kasa tsayawa, ta kasa zama, ta kai mari, ta kai gauro. Haka ta dinga kai-kawo a cikin ɗakinta, idanunta gaba ɗaya a kan screen ɗin wayarta. Ba ta kai mintuna biyu ba, sai wani notification ya yi popping a kan screen ɗin. Da sauri ta buɗe, SMS ne daga Sameer da wasu digits. Ta tsaya cak, idanunta suka sauka kan number ɗin, ta sake kallonsa na wasu seconds. Sai kuma without second thought ta danna copy, ta koma keyboard ɗinta ta yi pasting, ta danna Call.
Wayar na ringing, haka zuciyarta ke bugawa da mugun ƙarfi kamar za ta fito daga ƙirjinta. Kiran ya kusa yankewa, babu amsa, sai kiran ya katse. Raihana ta ja wani irin dogon tsaki, “Wallahi ko ka ɗauka, ko mu kwana a haka…” Ta sake dialing, a wannan karon ma zuciyarta ta sake tsalle. Kiran ya kusa yankewa sai aka ɗaga, amma babu wanda ya ce komai.
Raihana ta sauke ajiyar zuciya, wani irin sauƙi ya ratsa ta. Wannan shirun da aka mata ya isa ya tabbatar mata wanda take nema ne, da sauri ta fara magana kamar tana tsoron za’a kashe idan ta tsaya wani jinkiri, “Bawan Allah, yaushe na ce maka na amince da wani aure?” Ta ɗan tsaya numfashinta yana fita da sauri, “Da za ka je ka yi min sharri a wajen babana, ka ce wai ni na ce na amince?”
Zayd ya yi shiru kamar ba ya jin abin da take faɗa. Raihana ta ɗan jira, amma shiru kawai ya ci gaba da ratsa tsakaninsu. Ta ƙara ɗaure fuska, da ta fahimci ba shi da niyyar magana sai kawai ta ɗora zancenta, “Toh wallahi ba na sonka.” Ta haɗiye yawu, “Ban taɓa sonka ba.” Muryarta ta ƙara ƙarfi, “Kuma ba yadda za a yi na auri wanda ban so.” Ta ɗan ja numfashi, “Ka san duk yadda za ka yi kar ka soma sanar da wannan maganar a gaba.” “Yanda ka yi ta kai da Baffa…” Ta ɗan dakata, “Ka bar ta a wajen.” “Idan ma wata ƙaryar za ka sake masa, ni dai ka janye maganar ka.” Ta ƙara sauri, “Ko kuma ma kar ka sake zuwa, balle har ya ganka.” “Ba sai idan ka zo ne zai nemi ka turo ɗin ba.” Ta yi shiru tana huci.
A ɗayan ɓangaren kuwa Zayd ya ɗan lumshe idanunsa ya yi shiru kamar wanda yake sauraron wani abu mai matuƙar nishaɗi, sai a hankali ya buɗe bakinsa, “Wa ke magana, please?”
Raihana ta wani buɗe ido, “Kuttt…” Ta furta a hankali. Cikin zuciyarta kuwa ta ce, Amma guy ɗin nan ba na biyunsa a rainin hankali. Cikin uban takaici ta ce, “Dama ya za a yi ka gane ni? Ai ba za ka gane ba.” Ta ja numfashi, “Wallahi ka fita a sabgata, ni ba zan iya da wannan halin naka ba na rainin wayau.”
A ɗayan ɓangaren, wani murmushi ya subuce wa Zayd. Ba ƙaramin murmushi ba, har haƙoransa suka bayyana. Ya ɗaga hannu ya shafa fuskarsa a hankali, sai ya ɗan gyara kwanciyarsa ya jingina da headboard. Ya ɗan lumshe idanunsa sai ya buɗe su a hankali, “Ohhh…” Muryarsa ta fito cikin cikakkiyar nutsuwa, “Yanzu na gane.” Ya yi shiru na ƴan seconds sai ya ƙara, “Me magana…” Ya ɗan dakata, “Ke idan ba ni ɗin ba…” Ya ɗan yi murmushi, “…ma wa zai iya aurenki?”
Raihana ta yi shiru. Zayd ya ci gaba cikin wannan sanyin nasa, “Ke da hotunanki na abin da kika aikata…” Ya ɗan karkatar da kansa, “…suke ta yawo a yanar gizo, wa zai fara kuskuren aurenki?”
Raihana ta buɗe bakinta amma babu kalma da ta fito.
Zayd kuwa bai tsaya nan ba, “Ni kaina…” Ya ɗan yi murmushi, “…zan yi jihadi ne…” Ya ɗan dakata, “…da fatan Allah Ya ba ni ladan abin da na yi.”
Raihana ta wani buɗe baki, idanunta suka ƙara faɗaɗa kamar ba ta fahimci abin da kunnenta suka ji ba. Wani gagarumin uban mamaki ne ya rufe ta. Zayd ya yi wata ‘yar dariya ƙasa-ƙasa, amma Raihana ba ta ma ji sound ɗin ba. Tunaninta ya yi nisa, nisan da ya sa ta kasa motsi, ta kasa magana, ta kasa ko ƙiftawa.
Zayd ya sake kallon wayar sai kawai ya kashe, ya ajiye ta gefe ya koma ya jingina da headboard. A fuskarsa wani irin calmness ne kawai.
Amma a ɗayan ɓangaren, Raihana tana nan tsaye, wayar har yanzu a hannunta, idanunta a buɗe kamar kalmar da ya faɗa ta ɗauke mata dukkan tunaninta. “Hotunanki na abin da kika aikata…” Sai ta haɗiye yawu.
Zayd kuwa da ya ajiye wayar a gefe, sai ya juya a hankali ya kwanta. Ya janyo pillow ɗin ya gyara shi ƙarƙashin kansa sannan ya lumshe idanunsa, a fuskarsa kuwa wani irin nishaɗi ne ya bayyana. Nishaɗin da shi kansa ba zai iya cewa mene ne ya kawo shi ba, wataƙila maganganun Raihana ne, ko kuma yadda ta yi ta masifa tana tunanin tana magana da shi, ko kuma kawai yadda ta kasa gane cewa tun farko shi ne wanda take nema. Ya ɗan yi murmushi sai ya sake juya jikinsa ya samu comfortable position. Bai ƙara tunanin komai ba, kawai ya kwanta cikin wani irin yanayi na nishaɗi da ya kasa ɓoye, kamar mutumin da ya samu wani abu da bai san yana nema ba.
⸻
Raihana ta tsaya cak, wayar har yanzu a manne da kunnenta amma Zayd ya riga ya kashe. Ta sauke wayar a hankali ta kalli screen ɗin, ta sake kallonsa sai ta sake kallon screen ɗin kamar wataƙila wayar ce ta yi mata ƙarya. “…” Bakin ta ya ɗan buɗe, idanunta suka buɗe, wani irin shock ya rufe ta. Sai a hankali abin da ya faru ya fara dawowa mata ɗaya bayan ɗaya.
“Bawan Allah, yaushe na ce maka na amince da wani aure?” Ta lumshe ido. Sai kuma— “Wallahi ba na sonka.” Ta ɗan buɗe ido. “Ban taɓa sonka ba.” Ta sake rufe idanunta da ƙarfi. “Ya Allah, yanzu sai ya ce son nashi nake…” Ta dafe goshinta, amma sai kalmar da ya faɗa ta dawo mata. “Wa ke magana, please?”
Raihana ta zaro ido, “Kuttt!” Ta furta cikin ƙaramin murya. “Na gama masa lecture na kusan minti goma…” Ta tsaya, sai ta tuna yadda ta yi masa magana, ta kuma tuna yadda shi kuwa ya mata shiru. Sai wani sabon wave na takaici ya rufe ta, “Rainin hankali!” Ta faɗa cikin haushi, “Uban rainin hankali!”
Ta yi wasu steps a ɗakin sannan ta tsaya, “Yana ji na ina ta masifa…” Ta ɗan tsaya, sai ta runtse idanunta, “‘Ba na sonka wallahi!’” Ta sake dafe kanta, “Na shiga uku…”
Amma abin da ya fi bata mata rai shi ne, ya san ita ce tun farko. Ya sani, ya bar ta ta yi magana, ya bar ta ta dinga zuba amma daga ƙarshe ɗan tsabaragen rainin hankali wai, “Wa ke magana?”
Raihana ta buɗe baki cikin mamaki, “Wannan mutumin…” Ta kasa ƙarasa maganar. Ta sake kallon wayar sai ta harari screen ɗin kamar Zayd yana tsaye a cikinta. Ta ja numfash, “Ni zai cewa ba mai aurena? Toh uban me na aikata?”
Sai ta yi shiru kamar yanzu ne ta gane mafi munin ɓangaren abin. Ta kira shi da kanta, da daddare, tana neman shi, kuma ita ce ta fara yi masa magana. Raihana ta lumshe idanunta, “Subhanallah…” Ta ɗan juya gefe, “Da kaina na je na nemo number ɗinsa…” Ta yi shiru na seconds, sai ta ɗaga hannu ta dafe fuskarta, “Yanzu kuma shi zai kwanta yana dariya.” Kamar ta karanta abin da ke faruwa a wani wuri dabam, ta ƙara fusata, “Yana can yana dariya!” Ta yi wani irin tsaki, sai ta ajiye wayar a gefenta ta naɗe hannayenta a ƙirji.
————-
WASHEGARI DA SAFE — ARMAAN MANSION
Wajen ƙarfe goma sha ɗaya na safe Seeyama ta sauko daga sama. Kusan duk mutanen gidan suna falon, amma yau fuskarta ba ta ɗauke da walwala ko kaɗan, kamar wadda aka yi wa wani gagarumin laifi. Tana cika, tana ɓatsewa, har tafiyarta kanta tana nuna cewa yau babu wanda ya isa ya kusance ta. Ta tsaya tana gaishe da mutanen falon, amma muryarta babu ƙarfi a cikinta.
A ɗai-ɗai lokacin Kubura, mai aikin Ummie, ta ɗago daga gaban Inno hannunta ɗauke da tray ɗin da Inno ta yi breakfast. Tana cikin sauri, ba tare da ta lura ba sai hannunta ya ɗan shafi kafadar Seeyama. Kuskure ne kawai, amma Seeyama ta juya kamar an kunna mata wuta. “Ke!”
Kubura ta tsaya cak. Seeyama ta harare ta, “Ba ki da hankali ne?”
Kubura ta buɗe baki, “Anty…”
“Banza!” Seeyama ta katse ta, “Shashasha!” Ta ɗan matsa kusa da ita, “Na tsani hauka wallahi!” Kubura ta sunkuyar da kai. “Mutum ya dinga tafiya kamar…” Seeyama ta kalli jikinta daga sama har ƙasa, “…kamar idanunsa suna tsakiyar kansa!” Ta ɗan ja tsaki, “Dalla, kalli yadda kika wani bangaje ni kamar ba kya gani!”
Kubura ta rikice, “Ki yi haƙuri, Anty. Wallahi ban san na goge ki ba. Ɗan Allah…”
Seeyama ta sake harararta, amma wannan karon fushin nata ya ƙara hawa. “Dalla ni! Daina ba ni haƙuri!” Ta ɗan ɗaga hannu, “Allah Ya sa ba ki shafa min baƙin talaucinku ba.”
Kubura ta yi shiru, fuskarta ta sauya, idanunta suka fara cika da hawaye. A gefe guda Inno tana kallon su, Ummie ma ta yi shiru. Suhaila ta ɗan kalli Kubura sannan ta kalli Seeyama. Amma kafin kowa ya ce komai, sai muryar Inno ta yanke shirun, “Seeyama.” Muryarta ta fito da kaushi.
Seeyama ta ɗago kai, idanunta suka sauka kan Inno. Inno ta kalle ta kai tsaye, “Ba ta haƙuri.”
Seeyama ta zaro ido, sai kuma ta kalli Inno, ta kalli Kubura. Kubura ta riga ta sunkuyar da kai, hawaye sun fara zubo mata. Seeyama ta ɗan haɗiye yawu amma fushin bai sauka ba. “Na ba ta haƙuri…” Ta furta a sanyaye.
Inno ta katse ta, “Eh.” Ta ɗan dakata, “Ki ba ta haƙuri.”
Seeyama ta lumshe idanunta sai ta kalli Kubura, “Sorry.” Muryarta ta fito a tsuke.
Inno ta ɗan kalli Kubura, “Yi haƙuri ki tafiyarki.”
Kubura ta share hawayenta da bayan hannunta, ta gyaɗa kai sai ta juya, ta nufi kitchen a hankali.
Seeyama kuwa ta tsaya na wasu seconds, fuskarta cike da ɓacin rai. Sai ta ɗan ja numfashi, kafin ta juya— fuuuu! Ta fice daga falon. Ummie ta bi ta da kallo, ta sauke ajiyar zuciya a hankali.
Kai tsaye Seeyama ta nufi gidansu. Da ta isa baƙin gate sai ta danna horn ɗin motar da wani irin mugun ƙarfi har mai gadin ya firgita. Ya fito da sauri duk ya rikice, amma wannan ɗan jinkirin da ya yi kafin ya buɗe mata gate ɗin ya isa ya ƙara hura mata wutar da ke ƙona zuciyarta.
“Wai gidan na ubanka ne da ba za ka buɗe ba!” Ta faɗa cikin tsawa.
Mai gadin ya yi saurin buɗewa. Da gate ɗin ya buɗe ta shigar da motarta ciki, ta yi parking ba tare da kula da komai ba. Ta fito fuuuu! Ta nufi cikin gidan kai tsaye cikin tsananin fushi, fuskarta babu walwala ko kaɗan.
Kai tsaye ta nufi ɗakin Mommy. A kan hanyar shiga sai ta yi karo da Bintu wadda take ƙoƙarin fita. Seeyama ta tsaya, idanunta suka sauka kan Bintu daga sama har ƙasa, ta ja tsaki. Bintu kuwa ta ɗan ɓaɓe baki kawai, ba ta ce komai ba ta wuce abinta. Seeyama ta bi ta da kallo na ƴan seconds.
Ta saba ganin ’yan mata iri-iri suna zuwa wajen Mommy. Wasu ma masu mugun kyau wanda Bintu ba za ta iya tsayawa a waje idan suna nan ba, wasu kuma suna da kuɗi, wasu suna da matsayi. Amma babu wadda ta taɓa damunta sai Bintu. Tun ranar da suka fara haɗuwa a gidan Hajiya Balaraba kawai ta ji wani irin ƙyama gare ta, ba don Bintu ta taɓa yi mata wani abu ba, kawai… haka zuciyarta ta ɗauka.
Ta ci gaba da tafiya, ta haura matakala sannan ta isa baƙin ƙofar ɗakin Mommy. Ta tura ƙofar. A ɗai-ɗai lokacin Hajiya Hauwa ta ɗago kai sai ta ɗan zaro ido. Sai ta gyara towel ɗin da take ɗaure a jikinta kamar wadda ta fito daga wanka yanzu-yanzu, “Sweetheart?” Ta kalli Seeyama da mamaki, “What happened? Lafiya kika zo da sassafen nan?”
Seeyama ba ta amsa ba, kawai ta shiga. Idanunta suka fara yawo a cikin ɗakin, kaya sun bazu a ƙasa, wasu kuma suna kan gadon. Ta ɗan ɓaɓe baki sai ta nufi kujera ta zauna.
Hajiya Hauwa ta kalle ta na ƴan seconds, “Mommy, wai me yarinyar nan ta zo yi gidan nan ne?” Ta ɗan ɗaga gira.
Hajiya Hauwa ta yi ƙaramar dariya, “Laa, ki niga… Hajiya Balaraba ce ta aiko ta ta kawo min kayana da na siya.” Ta ɗan gyara towel ɗin, “Toh shi ne fa na ce kawai ta haura sama, ni kuma yanzu nan na fito daga wanka, na ce ta shigo ta ajiye min.” Ta ɗan dakata, “Ai yanzu nan ma ta zo, ba ta wani daɗe ba.” Ta kalli Seeyama kamar tana son kashe zancen, “Amma ke fa? Me ya same ki?”
Seeyama ta kau da kai, ta yi shiru na ɗan lokaci kamar tana ƙoƙarin tattara kalaman da za ta faɗa. Daga ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya, “Mommy…” Muryarta ta fito ƙasa-ƙasa amma akwai fushi a cikinta, “Ummie ce ba ta son Zayd ya aure ni.”
Hajiya Hauwa ta ɗan ƙanƙance idanunsa, ta daina motsi, ta maida hankalinta gaba ɗaya kanta, “Me kika ce?”
Seeyama ta kalle ta, “Da kunnena na ji.” Ta ɗan matsa gaba, “Tana waya da wata.” Ta yi shiru na ɗan seconds sannan muryarta ta ƙara ɗaukar zafi, “Tana zagina, ta ce ba ni da tarbiyya.” Ta ɗan yi dariya mai cike da takaici, “Ta ce ni ba irin matar da ta dace ɗanta ya aura ba ce.”
Hajiya Hauwa ta sauke ajiyar zuciya, amma Seeyama ba ta gama ba, “Yanzu ƙila ma a yi auren… ta hana ni zaman lafiya.” Ta ƙanƙance idanunsa, “Ko ta dinga juya min miji.” Ta girgiza kai da ƙarfi, “Ni wallahi ba zan yarda ba. Idan ta ce za ta ɗaga min hankali…” Ta ɗan yi shiru, sai ta furta da cikakken tabbaci, “Na rantse da Allah, maganinta zan yi.”
Hajiya Hauwa ta kalle ta na ƴan seconds sai ta sauke ajiyar zuciya mai zurfi, “Ai ni dama… na daɗe ina tunanin haka.”
Seeyama ta ɗago gira. Hajiya Hauwa ta ɗan yi murmushi, “Amma ki daina damuwa.” Ta ɗaga mata hannu kamar tana ƙwantar mata da hankali, “Idan ta san wata, ba ta san wata ba.”
Seeyama ta yi shiru. Hajiya Hauwa ta ci gaba, “Bari dai a yi auren.” Ta ɗan kalli agogo, “Yau Lahadi ne.” Sai ta maida kallonta kan Seeyama, “Cikin kwanaki biyar masu zuwa… kin zama matar Zayd.” Murmushi ya bayyana a fuskarta, “Daga lokacin ne Hajja Fati za ta dawo abar tausayi.”
Seeyama ta ɗan ɗago gira. Hajiya Hauwa ta ƙara da cewa, “Wallahi ko ganin Zayd take son yi, sai ta fara neman izini a wajenki.” Ta ɗan yi murmushi mai cike da mugunta, “Ki zuba min ido kawai, za ki ga abin da zai faru.”
Seeyama ta yi shiru, amma wannan karon ƙaramin murmushi ya fara bayyana a gefen bakinta kamar kalaman Mommy sun ɗan dawo mata da ƙarfin gwiwar da ta rasa tun daren jiya. Ta jingina da kujerar, idanunta suka lumshe na ɗan lokaci. A zuciyarta kuwa ta fara ganin ranar da komai zai sauya, ranar da za ta zama— Mrs. Zayd Armaan.
Not edited