Free chapter · Read without an account
THE WEDDING FATIHA
ZAYD ARMAAN
CHAPTER FORTY NINE:49
THE WEDDING FATIHA
JIDDAAH BARKUM
—————-
Da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana, Baffa yana ɗakinsa tare da Aminu, yana ɗan danna masa ƙafa. Mama Indo da Mama Sabuwa ma duk suna cikin ɗakin, sai Yusuf ya zo ya tsaya a ƙofar ɗakin Baffa.
“Assalamu alaikum.” Aka amsa daga ciki, “Wa alaikumus salam.” Sai yaron ya ɗan sunkuyar da kai, “Baffa, na shigo.” “Shigo mana.”
Yusuf ya ɗaga labulen falon Baffa a hankali ya shigo, ya ɗan risina. “Baffa, kana da baƙi a waje.”
Baffa ya yi shiru na ƴan seconds, yana kallonsa. “Baƙi?”
Yusuf ya gyada kai, “Eh, Baffa. Sun zo a mota, suna waje su huɗu ne.”
Baffa ya sake yin shiru, kamar yana nazarin ko akwai wani daga cikin mutanen da yake tsammanin zai zo. Daga ƙarshe ya miƙe, ya ɗauki hulawarsa dake gefensa ya saka, dama bai jima da shigowa gidan ba. Sai ya kalli Mama Indo da Mama Sabuwa, “Ku koma ciki ku ɗan ba mu waje, ina ganin zasu shigo ne.”
A hankali suka miƙe su ma. Baffa ya juya tare da Yusuf, suka nufi ƙofar gidan.
Da Baffa ya fito bakin ƙofar gidan, abin farko da ya fara cin karo da shi shi ne wata hamshakiyar mota da ta tsaya a gefen gidan. Imraan ne kaɗai a waje, ya jingina da motar, hannayensa a aljihun wandonsa. Sauran kuma—Alhaji Minzali da kuma sauran mutum biyu—suna cikin motar suna jiran izini.
Baffa ya tsaya na ɗan lokaci. Da idanunsa suka sauka kan Imraan, sai ya gane shi ne wanda ya zo da Zayd a karon farko. Nan take wani irin fahimta ta ratsa zuciyarsa, toh… baƙin nan kenan mutane Zayd ne.
Imraan ma a daidai lokacin ya hango Baffa, sai ya miƙe daga jikin motar. Fuskarsa ta sauya zuwa cikakkiyar girmamawa, ya matso gaba kaɗan, ya ɗan sunkuyar da kansa. “Assalamu alaikum, Baffa.”
Baffa ya amsa da fara’a, “Wa alaikumus salam.” Murmushi ya bayyana a fuskar Baffa, akwai wani irin farin ciki da ke bayyana a idanunsa saboda girmamawar da Imraan ya nuna masa.
Sai Imraan ya juya wajen motar ya yi musu magana, dukkan mutanen suka fara saukowa. Manyan mutane ne, dattijan arziki. Kowanne ka kalla, za ka san Allah Ya rufa masa asiri a gidan duniya. Tufafinsu, nutsuvarsu, yadda suke tafiya da yadda suke murmusawa tun kafin su ƙaraso inda Baffa yake, komai yana nuna dattako. Sai dai fatan irin wannan suturar asirin ta same su a gidan ƙiyama.
Da suka ƙaraso inda Baffa yake, fuskokinsu duka suka washe da farin ciki. Baffa ma ya tarbesu da fara’a, ya yi musu maraba, ya gaishe su ɗaya bayan ɗaya, sannan ya musu izinin shigowa ciki.
“Bismillah.” Ya nuna musu hanyar shiga, “Ku shigo mana.”
Suka fara shiga, Imraan ma ya bi su a baya. Dama shi ne ya kawo su, kuma yana son ya kasance a wajen, yana son ya ji da kunnensa yanda zai ji daɗin ba Zayd labarin abin da ya faru.
⸻
Bayan gaishe-gaishe da ƴan kalaman maraba, Alhaji Minzali ya gyara zamansa, ya kalli Baffa cikin ladabi. “Toh, Alhaji Musa…” Ya ɗan yi murmushi. “Ni dai kamar yanda na sanar maka a kwanakin baya, ni da mahaifin Zayd uwa ɗaya, uba ɗaya muke. Ɗan a lissafi ma, shi ne ya cika nono na ƙama.” Ya nuna mutumin dake gefensa, “Wannan kuma shi ne Alhaji Sa’idu Matawalle, aminin marigayi mahaifin Zaydu ne.” Sai ya juya ya nuna mutumin dake gefen Baffa, “Shi kuma wannan ɗan’uwanmu ne, sunanshi Alhaji Rabiu.” Ya ɗan yi dariya kaɗan, “Yan maza zarr muke.”
Ya ɗan dakata, sai ya kalli Baffa kai tsaye. “Saboda haka mun zo neman iri, da fatan zamu samu.”
Baffa ya ɗan jinjina kai, fuskarsa ta nuna gamsuwa. “Madallah… madallah.” Sai ya ɗan kalli mutanen, “Sai dai ban san zaku zo ba, ban sanar da kowa ba sai ni kaɗai kuka tadda.” Ya ɗan yi shiru kamar yana son ya tabbatar musu cewa ba wai rashin tarba ba ne. “Kun san sha’anin aure yana da kyau ace ta ɓangarena ma akwai wani.”
Dukkansu suka jinjina kai cike da fahimta. “Tabbas.” “Wannan haka yake.”
Baffa ya sauke ajiyar zuciya. “Saboda haka bari zanyi wa maƙocina amintacce na magana ya shigo.”
Alhaji Minzali ya gyada kai, “Ba matsala, hakan ma yayi kyau.”
Baffa ya ɗan yi musu excuse ya fita. Bayan ƴan mintuna sai ga shi ya dawo tare da maƙocinsa, Malam Sammani. Ya shigo, suka gaisa, sannan suka zauna. Aka ɗan yi bayanai da suka kamata.
Imraan kuwa yana gefe, idanunsa suna rabuwa tsakanin Baffa da Alhaji Minzali, kamar wanda yake son ya tabbatar da cewa komai yana tafiya yadda ya kamata. Kuma a cikin zuciyarsa, yana jin wani irin farin ciki da ya kasa ɓoyewa.
Daga ƙarshe Alhaji Minzali ya gyara zamansa, ya kalli Baffa. “Wlh ba ƙaramin farin ciki na ji ba jiya da ya zo min da maganar nan…” Ya ɗan yi murmushi, “Cewa kun amince masa ya turo. Shi yasa na kasa haƙuri, na ce tabbas yau ɗin nan zan zo.”
Baffa ya girgiza kai yana murmushi. “Wlh haka abin ya zo.” Ya ɗan dakata, “Haka Allah Ya tsara.”
Sai Alhaji Matawalle ya ɗan matsa gaba. A wannan karon, yanayinsa ya sauya, maganar ta fara ɗaukar nauyi. Ya kalli Baffa kai tsaye. “Ɗan Allah Alhaji…” Ya ɗan yi shiru, “Idan ba zamu matsa maka ba…” Ya sake yin shiru na ɗan lokaci, kamar yana auna kalmomin da zai zaɓa. “Kuma idan abun ba zai zama akwai takura ba…” Ya ɗan sunkuyar da kai cikin girmamawa, “Muna neman alfarma a ɗaura auren yanzu, a nan.”
Wajen yayi shiru, maganar ta sauka a cikin falon kamar wani abu mai nauyi. Alhaji Matawalle ya ci gaba cikin murya mai ɗauke da roƙo. “Idan ya so daga baya duk wani shiri da za a yi sai a yi.” Ya kalli Alhaji Minzali na ɗan lokaci, sannan ya dawo da kallonsa kan Baffa. “Wlh yaron nan muna ta so mu ga yayi aure amma abun ya ci tura.” Ya ɗan girgiza kai, “Shi yasa yanzu da ya zo da lamarin, duk muke ta Allah-Allah mu ga komai ya wakana.” Muryarsa ta ɗan yi sanyi, “Kar wani abu ya gifta a samu matsala.”
Baffa bai amsa ba, kawai ya yi shiru. Idanunsa suka sauka ƙasa kamar yana auna maganar sosai. A gefe guda, Alhaji Minzali ma ya yi shiru, Imraan kuwa ya tsaya kallon Baffa. A wannan lokacin babu wanda ya sake magana, kowa yana jiran kalmar mutum ɗaya: Baffa.
Baffa ya ɗago idanunsa a hankali, ya kalli Alhaji Matawalle, sai ya juya ya kalli Malam Sammani. Kallon da ya yi masa ya ɗauki ƴan seconds, kamar yana neman amsar da zai dogara da ita kafin ya furta abin da zai iya sauya makomar Zayd da Raihana gaba ɗaya. Malam Sammani ya kalleshi, shi ma bai yi magana ba, kawai ya ɗan gyada masa kai a hankali.
Baffa ya sauke ajiyar zuciya, sai ya koma da kallonsa kan baƙin da suke gabansa. A wannan lokacin, falon ya yi shiru sosai, kamar kowa yana jiran hukuncin da zai fito daga bakinsa. Ya ɗan ɗauke numfashi a hankali, sai ya maida dubansa kan Alhaji Matawalle. Wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarsa, ba tare da ya yi saurin amsa ba.
“Tabbas zan so hakan ya kasance.” Ya ɗan dakata, “Zaydu yaran kirki ne, na san haka.” Sai ya sauke idanunsa na ɗan lokaci, kafin ya sake kallonsu. “Sai dai kuma…” Muryarsa ta ƙara nutsuwa, “Ba ni kaɗai ke da haƙƙin yanke hukunci a kan rayuwarta ba.” Ya ɗan jinjina kai, “Yana da kyau na tattauna da mahaifiyarta, na ji ra’ayinta.”
Maganar ta sauka a tsakaninsu cikin natsuwa. Dukkan dattijan suka jinjina kai cike da gamsuwa, babu wanda ya nuna rashin fahimta. A maimakon haka, fuskokinsu suka ƙara washewa, domin sun fahimci cewa maganar tana tafiya ne a hanya mai kyau.
Baffa ya ɗan gyara zamansa. “Bari na shiga ciki.” Ya kalli kowa ɗaya bayan ɗaya, “Bari na ji abin da muka tattauna, in Shaa Allah zan fito in sanar da ku.”
“Ba laifi.” “Madallah.” “Allah Ya sa a dace.” Amsoshin suka biyo juna.
Baffa ya ɗan jinjina kai, sai ya miƙe, ya juya ya nufi cikin gida. Imraan kuwa ya tsaya a gefe, murmushi ne kawai yake ta zagaye fuskarsa. Da ka kalle shi, za ka rantse da Allah shi za a karɓa wa auren. Ya ɗan girgiza kai yana murmushi, “Allah Ya sa…” ya furta ƙasa-ƙasa.
⸻
Kai tsaye Baffa ya nufi cikin gidan. A veranda, Mama Sabuwa da Mama Indo suna zaune a kan tabarma, dukkansu sun kasa haƙuri. Sun tsare idanunsu kan hanyar da Baffa ya bi, suna jiran dawowarsa. Tun lokacin da Yusuf ya ce manyan mutane ne suka zo da babbar mota, hankalinsu ya tashi. Wane ne? Me ya kawo su? Kuma me suke nema da tsakar rana haka?
A cikin gidan kuwa, Umma tana kitchen tana fama da shirya abincin rana. Raihana da Maryam kuwa suna gidan Fauziyya, yayar Maryam, tun safe. Bintu kuma tana cikin ɗaki, ana aikin da aka saba na ɗanna waya.
Da Baffa ya shigo, Mama Sabuwa da Mama Indo suka ɗaga idanunsu lokaci guda, suka bishi da kallo, kamar kowannensu yana jiran ya ji kalma ɗaya daga bakinsa. Amma Baffa bai tsaya ba, kai tsaye ya nufi kitchen, sannan ya tsaya a bakin ƙofar. “Hajara.”
Umma ta juyo. Da ta hango shi, sai ta ɗan tsaya. Baffa kuwa bai ƙara cewa komai ba, ya juya ya nufi ɗakinta. Umma ta ɗan kalleshi, sai ta ɗan goge hannunta da towel ɗin dake kan ƙofar kitchen ɗin, ta bi bayansa. Mama Sabuwa da Mama Indo kuwa suka bita da ido, baki a buɗe, zuciyarsu cike da tambayoyi.
“Me ya faru?” Mama Sabuwa ta furta ƙasa-ƙasa.
Mama Indo ta ɗan girgiza kai, “Idan kin tambayeni ni kuma na tambayi wa Sabuwa?” Mama Sabuwa ta ɗan taɓe baki kawai, sai suka ci gaba da jira.
⸻
Umma ta shiga ɗakin. Baffa ya riga ya zauna, ta zauna a gabansa, amma bata ce komai ba kawai ta saurara taji me zai ce.
Baffa ya ɗan ƙalleta, sai ya sauke ajiyar zuciya. “Yanzu-yanzu na karɓi baƙuncin wasu mutane.”
Umma ta yi shiru. “Su wanene?”
“Mutanen gidan Zayd.”
Nan take idanun Umma suka ɗan buɗe. Baffa ya lura, ya ɗan yi murmushi. “Alhaji Minzali ne ƙanin mahaifinshi ya zo.” Ya ɗan dakata, “Tare da wasu dattijai biyu.”
Umma ta kasa cewa komai, kawai ta tsaya sauraren shi.
Sai Baffa ya fara bayyana mata komai: yadda suka zauna, yadda Alhaji Minzali ya gabatar da kansa, yadda ya ce shi da mahaifin Zayd uwa ɗaya uba ɗaya suke, ya kuma gaya mata yadda ya gabatar da Alhaji Sa’idu Matawalle da kuma Alhaji Rabiu. Ya bayyana mata abin da suka zo nema. “Sun ce sun zo neman iri.”
Umma ta ɗan sauke numfashi. Baffa ya ci gaba, “Sun kuma ce sun yi farin ciki sosai da jin cewa na ba Zayd dama ya turo magabatansa.” Sai ya ɗan yi shiru. “Amma…”
Umma ta kalleshi, “Sun nemi wata buƙata?”
“Wace irin buƙata?”
Baffa ya ɗan gyara zamansa. “Sun ce idan ba za su matsa mana ba… sun fi so a ɗaura auren yanzu.”
Umma ta zaro ido kaɗan, “Yanzu?”
“Eh.” Ya jinjina kai, “A nan. Sun ce daga baya duk wani shiri da ya kamata a yi, sai a yi.” Ya sauke ajiyar zuciya, “Sun ce sun daɗe suna son ganin yaron nan ya yi aure, amma abin yana ta ci tura. Shi yasa yanzu da ya zo da wannan maganar… suke son komai ya wakana cikin sauƙi, kafin wani abu ya gifta a samu matsala.”
Umma ta yi shiru, ta sunkuyar da kanta na ƴan seconds. Baffa kuwa ya ƙalleta, sai ya tambaya cikin nutsuwa, “Toh… yanzu menene ra’ayinki? Me kike gani?”
Umma ta ɗago kai, ta ɗan yi murmushi, murmushin mace wadda ta san matsayinta. “Ni?” Ta ɗan girgiza kai, “Ai tun da ka yanke hukunci… ni da Raihana muna bayanka.” Ta ɗan dakata, “Mu masu biyayya ne a gareka. Kaine kake da dukkan dama na zartar da kowanne hukunci a kan rayuwarta. Idan ka ga hakan ya fi dacewa da ita… ni ba zan ce komai ba.”
Baffa ya yi shiru, kalaman sun yi masa daɗi, ba don kawai ta amince da shi ba, amma saboda yadda ta fahimci matsayinta a matsayin matar da ta san wanda Allah Ya ɗora wa alhakin iyalinsa. Sai ya sauke ajiyar zuciya, wani irin gamsuwa ya bayyana a fuskarsa. “Madallah, Hajara.” Ya ɗan jinjina kai, “Wannan shi ne abin da nake so in ji daga gare ki.” Ya yi murmushi, “Allah Ya saka miki da alheri.”
Umma ta sunkuyar da kanta, “Amin.”
Baffa ya ɗan yi shiru, sai ya sake cewa, “Allah Ya sa abin ya zama alheri.”
Umma ta amsa a hankali, “In Shaa Allah.”
A wajen ɗakin kuwa, Mama Sabuwa da Mama Indo har yanzu suna jiran su ji abin da ya faru. Baffa ya sake wucewa ta gabansu, ya nufi falonsa. Umma kuwa ta koma kitchen, ta cigaba da aikin da ta bari. Amma zuciyarta… tana cikin wani irin yanayi da ita kanta ba za ta iya fassara shi ba. Ba za ta iya cewa farin ciki ne kai tsaye ba, haka kuma ba za ta iya cewa baƙin ciki ba ne. Kawai… wani abu ne da ya tsaya mata a ƙirji. Sai ta ci gaba da aikin hannunta a hankali, tana ta ambaton Allah a ƙarƙashin bakinta. “Subhanallah… Alhamdulillah… Allah Ya sa alheri…” Kamar tana neman nutsuwa ne daga kalmomin da take furtawa.
⸻
Baffa ya dawo bayan ƴan mintuna, fuskarsa a washe. Da ya shigo, sai ya ɗan tsaya kafin ya ƙarasa ya zauna inda ya tashi. Nan take dukkan idanun da ke wajen suka koma kansa. Musamman Imraan… wanda tun lokacin da Baffa ya shiga yake ji kamar shi ya janyo maganar bakin Baffa. Kowa yana jiran kalmar da za ta fito daga bakinsa.
Baffa ya ɗan kalli kowa, sai a hankali ya buɗe baki. “Mahaifiyarta ta amince.” Nan take fuskokin mutanen suka canza. Baffa ya cigaba, “Idan kun shirya, sai mu ƙarasa masallaci.” Ya ɗan kalli agogo, “Lokacin Zuhr ya kusa. Idan an idar da sallah, sai a ɗaura, ko ɗan ma a samu ƙarin shaidu.”
Sai ya yi shiru, amma wannan karon… shiru ne mai cike da amsa.
Imraan ya washe baki, “Alhamdulillahi!” Muryarsa ta fito da tsananin farin ciki. “Alhamdulillahi…”
Sauran ma suka amsa, “Allah Ya sa alheri.” “Allah Ya sanya albarka.”
Ba tare da ɓata lokaci ba, suka dunguma suka nufi masallacin.
Da kowa ya shiga masallacin, Alhaji Minzali ya ɗan tsaya a waje, bai shiga nan take ba. Sai ya zaro wayarsa, kai tsaye ya ɗanna number Ummie.
A ɗayan ɓangaren kuwa, Ummie tana ɗakinta tare da Inno. Da wayar ta yi ringing, ta ɗaga. “Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.” Suka gaisa.
Ummie ta ɗan yi murmushi, “Ai dama ina cewa zan kira ka na sanar maka.” Ta ɗago idanunta ta kalli Inno da gefen ido, sai ta cigaba. “Gidan da Zayd yake zuwa neman aure ne, sun ce ya turo magabatansa.” Ta ɗan dakata, “Toh jiya yake sanar da ni, shi ne na ce zan faɗa maka… amma sai ga shi kai ka kira ni kafin ma na kira.”
Inno ta ɗan juyo, ta kalli Ummie, amma ba ta ce komai ba, kawai ta zuba mata ido.
A ɗayan ɓangaren, Alhaji Minzali ya yi ƙaramar dariya. “Toh ai ni ma abin da ya sa na kira kenan. Tun daren jiya ya zo har gida ya sanar da ni. Yanzu haka ma…” Ya ɗan juya ya kalli ƙofar masallacin, “…ga mu nan.” Sai ya cigaba, “Muna can gidan iyayen yarinyar, ni da Alhaji Matawalle da Rabiu.” Ya yi ɗan murmushi, “Yanzu haka ma na kira na sanar da ku.” Sai muryarsa ta ƙara nuna farin ciki, “Mun yanke shawarar za a ɗaura auren yanzu, bayan an idar da sallah.”
Ummie ta yi shiru. Alhaji Minzali ya cigaba, “Saboda haka ki sanar da Inno dai…” Ya yi ɗan dariya, “…ta yi kishiya.”
Ummie ta yi shiru, wayar har yanzu manne a kunnenta, ta kasa cewa komai. Inno kuwa, ganin yadda Ummie ta tsaya ba tare da ta motsa ba, sai ta fahimci cewa akwai wani abu da ke faruwa a wayar. Ta matso kusa, ta miƙa hannu. “Bani.”
Ummie ta ɗan ƙalleta, sai ta miƙa mata wayar. Inno ta sa a kunnenta.
Da Alhaji Minzali ya ji muryarta, sai murmushinsa ya ƙara faɗaɗa. “Hajiya…” Ya sake jaddada mata abin da ya faɗa wa Ummie, “Yanzu haka muna gidan iyayen yarinyar. Mahaifinta ya amince, yanzu bayan sallar Zuhr za a ɗaura.”
Inno ta yi shiru, kalaman sun sauka a kunnenta ɗaya bayan ɗaya. Ta san Hajja Fati, ta san ba macen da za ta shirya wani abu a ɓoye ba ce, ba kuma munafuka ba ce. Idan ba haka ba… da ta ce an shirya wannan ne kawai saboda tace za’a haɗa Zayd da Seeyama. Amma wannan? Auren Zayd da wata yarinya? Kuma yanzu? A wannan lokacin?
Inno ta kalli Ummie. Ummie kuwa tana kallonta cike da mamaki da wani irin tunani da ya hana ta nuna farin cikin da ke neman bayyana a fuskarta.
Sai muryar Inno ta dawo da ita daga tunanin. “Minzali…” Ta yi shiru na ɗan lokaci, “Tun yaushe Zaydu ya fara neman yarinyar nan?” Ta tambaya cikin nutsuwa, “Tsakaninka da Allah, zaka faɗa min?”
Alhaji Minzali ya yi ɗan murmushi, ba tare da wani zato ya shigo ransa ba. “Hajiya… ai ina ganin kusan wata biyu kenan, ina ganin tun lokacin ne abin ya fara. Jiya ya zo min da maganar, ya ce iyayenta suna son ganinmu, shi yasa yau muka zo.” Ya ɗan dakata, “Toh kuma kin ga…” Ya kalli masallacin, “Allah ne. Cikin ikonSa, abinda Ya rubuta shi ne yake faruwa.”
Inno ta yi shiru. Alhaji Minzali ya sake kallon masallacin. “Bari na je, na ji an fara kiran sallah. Da an idar, za a ɗaura auren.” Sai ya yi wata ƙaramar dariya, “Shikenan… kin yi kishiya.”
Inno ta ɗan jinjina kai. “Madallah.” Muryarta ta fito a nutsuwa, “Allah Ya sa albarka.”
“Amin.” Alhaji Minzali ya amsa, “Amin, Hajiya.” Sai kiran ya katse.
Inno ta sauke wayar a hankali, ta kalli Ummie. Ummie ma ta ƙalleta, amma… babu wadda ta ce komai, kamar kowaccensu tana ƙoƙarin fahimtar irin abin da Allah Ya juya musu cikin dare ɗaya.
————-
Bayan an idar da sallar Zuhr, liman bai tashi daga wajen nan take ba, sai ya ɗan gyara zamansa. Masallacin ya yi shiru, muryoyin mutanen da suka gama addu’a suka ragu a hankali, har sai da nutsuwa ta mamaye wajen.
Sai liman ya ɗago kai. “Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.”
Mutane suka amsa.
Liman ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “Yan’uwa Musulmi… yanzu za mu yi wani ɗan gajeren bayani. Akwai ɗaurin aure da za a yi yanzu.” Ya ɗan kalli mutanen da ke gabansa.
A wannan lokacin, Alhaji Matawalle ya gyara zamansa, Baffa kuwa ya ɗan sunkuyar da kai. Malam Sammani, maƙwabcin Baffa, ya zauna cikin nutsuwa. Imraan kuwa… murmushi kawai yake yi, kamar har yanzu bai yarda da irin yadda komai ya faru cikin sauƙi ba. Amma duk da haka sai ya ɗan buɗe camera zai fara daukan video.
Liman ya cigaba. “Wakilin angon yana nan?”
Alhaji Matawalle ya ɗaga hannu. “Ni ne.”
Liman ya jinjina kai. “Sunanka?”
“Alhaji Sa’idu Matawalle.”
“Wakilin Ahmad Abdulrahman?”
“Eh.”
Liman ya ɗan gyara zamansa. “Za ka karɓa masa auren?”
Alhaji Matawalle ya jinjina kai. “Eh, In Shaa Allah.”
A hankali aka fara shirya duk abin da ya dace. Baffa ya kalli Malam Sammani, “Shi ne zai ba da auren.” Malam Sammani ya ɗan gyada kai, sai ya matsa kusa.
Liman ya kalli Alhaji Matawalle. “Alhaji Sa’idu…” Ya ɗan dakata, “Za ka karɓa wa Ahmad Abdulrahman auren Raihana Musa Maiturare?”
Alhaji Matawalle ya zauna cikin cikakkiyar nutsuwa. “Na karɓa.”
Liman ya sake maimaitawa domin tabbatarwa. “Ka karɓa?”
“Na karɓa.”
Sai ga ɗan ɗago ƙudin da Alhaji Matawalle ya ajiye na sadakin. “Da sadaki dubu ɗari biyar… na karɓa.”
Liman ya jinjina kai, sai ya juya wajen Malam Sammani. “Malam Sammani…”
Malam Sammani ya ɗan ɗaga kai.
“Za ka ba da auren Raihana Musa Maiturare ga Ahmad Abdulrahman bisa ga abin da aka amince da shi?”
Malam Sammani ya ɗan kalli Baffa. Baffa ya amsa masa da ɗan jinjina kai. Sai Malam Sammani ya dawo da kallonsa kan liman. “Na ba da.”
Liman ya kalli Alhaji Matawalle. “Ka karɓa?”
Amsar ta fito nan take. “Na karɓa.”
Liman ya ɗan dakata, sai ya kalli mutanen da ke wajen. “An samu shaidu?”
“Eh.” Muryoyin suka amsa.
Liman ya ɗan yi murmushi. “Allah Ya sanya albarka.” Sai ya ɗaga hannayensa. “Allah Ya sanya wannan aure ya zama sanadin alheri, soyayya, rahama da kwanciyar hankali tsakanin ma’auratan. Allah Ya haɗa zukatansu a kan alheri.”
“Amin.” “Amin.” Muryoyin suka cika masallacin.
Baffa ya sauke ajiyar zuciya. A gefensa, Alhaji Minzali ya lumshe idanunsa na ƴan seconds, fuskarsa cike da farin ciki. Alhaji Matawalle kuwa ya kalli Baffa, murmushi ya bayyana a fuskarsa, sai ya ɗaga hannunsa suka gaisa.
“Maa Shaa Allah. Mungode, mungode.”
Imraan kuwa ya kasa ɓoye farin cikinsa, ya ɗan girgiza kai. “Finally!”
Not edited