Free chapter · Read without an account

WHEN FATE DECIDED FOR ME

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN


ZAYD ARMAAN 

CHAPTER FIFTY TWO:52

WHEN FATE DECIDED FOR ME!

JIDDAAH BARKUM

————
Raihana ta jingina jikinta a hankali da kofar ɗakinta. A hankali ta sulale ƙasa, ta zauna a bakin ƙofar, ta ɗora kanta kan gwiwoyinta, sai kuka ya kubce mata. Ba irin kukan da ake yi domin kawai a ji ana kuka ba, kuka ne da ya fito daga can ƙasan zuciyarta—mai nauyi, mai zafi, kamar an tsaga mata wani abu a cikin ƙirjinta.
Ta riƙe kanta da hannayenta. Hawayen suka fara gangarowa ba tare da tsayawa ba. Ta yi kuka sosai, kuka har numfashinta ya fara rikicewa, kuka har kirjinta yana tashi yana sauka da ƙarfi.
Ba ta san tsawon lokacin da ta ɗauka a zaune a wajen ba. Lokaci ya wuce, amma ita kamar ba ta san da shi ba.
Daga baya ta fara rarrafe a hankali, ta kai kanta wajen daddumarta, ta kwanta. Har yanzu hawayen suna zuba daga idanunta, sai dai wannan karon babu sautin kuka, kawai tana faman sauke ajiyar zuciya a hankali.
Ta lumshe idanunta, sai ta buɗe bakinta da murya mai rawa, “Ya aureni…” Ta yi shiru, hawaye guda ya sake zubo mata, “Ba da yardata ba…” Ta share fuskarta da sauri, “Ba da amincewata ba.”
Ta yi wata ƙaramar dariya mai ɗaci, “Kawai ya yi amfani da ikonsa…” Ta haɗiye wani irin kuka, “Ya aure ni.”
Sai ta juya jikinta a hankali, tana kallon silin, “Na fada masa…” Muryarta ta ƙara rawa, “Na fada masa bana son sa.” Ta lumshe idanunta, “Na ce ba zan iya zama da baƙin halinsa ba.”
Ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, amma kamar tana ganin Zayd ɗin a gabanta ne, sai ta sake magana, “Amma ya aure ni.” Ta ja numfashi mai nauyi, “Why?” Kalmar ta fito da rauni, “Me ya sa?”
Sai ta tashi a hankali, ƙafafunta suna rawa. Ta ƙarasa gaban mirror ɗin ɗakinta, ta jingina da shi, ta kalli kanta. Idanunta sun kumbura, fuskarta cike da hawaye. Ta ɗan yi shiru tana kallon kanta kamar ba ta gane mutumin da ke tsaye a gabanta ba.
“Na gaya maka bana son ka…” Ta yi magana kamar Zayd yana tsaye a gabanta, “Na gaya maka ba zan iya da kai ba.” Ta ɗan share hawaye, “Amma ka aure ni.” Muryarta ta ɗan ƙara ƙarfi, “Kamar abin da nake ji bai da muhimmanci.”
Ta yi shiru, sai ta ɗan daga kai, kamar tana ƙoƙarin tara ƙarfin zuciya, “Wlh… za ka yi da-na-sanin wannan auren.” Ta goge fuskarta da tafin hannunta, “Ba zan taɓa ɗaukar ka a matsayin mijina ba…” Ta tsaya, numfashinta ya ɗan tsaya, sai ta ƙara da ƙudurin da take ƙoƙarin shukawa a cikin zuciyarta, “Kamar yadda da kanka ka ƙulla wannan auren… da kanka za ka warware shi.” Ta ɗan gyada kai, “Na rantse.”
Sai ta sauke numfashin mai zurfi, amma da ta juya daga mirror ɗin, ƙarfin da ta tara ya fara dusashewa. Ta sake komawa kusa da daddumarta, a hankali ta zame ƙasa, ta kwanta a wajen, ta rungume kanta. Idanunta suka kafe kan wuri daya.
Komai ya yi mata kamar mafarki, kamar wannan duniyar ba ita ce duniyar da ta saba rayuwa a cikinta ba. Kamar an ɗauke ta daga rayuwarta a cikin ƴan sa’o’i kaɗan… aka jefa ta cikin wata sabuwar rayuwa da ba ta shirya mata ba.
Ta tashi da safe tana tunanin komai yana nan yadda yake, amma yanzu… an ce ta zama matar wani. Kuma ba wani ba, Zayd! Mutumin da ta taɓa gaya masa a fili cewa ba za ta iya rayuwa da shi ba, mutumin da zuciyarta ta ƙi tun kafin ma ta san cewa wata rana za a kira shi mijinta.
Ta runtse idanunta, hawaye suka sake zubo mata. Ta ɗan matsa jikinta cikin daddumarta, “Ya Allah…” Muryarta ta fito ƙasa-ƙasa, “Me zan yi?”
Babu amsa, sai shirun ɗakin da sautin numfashinta kawai.
Ta share hawayen da ke kan kumatunta, amma wasu suka sake fitowa. A wannan lokacin, Raihana ba ta san abin da gobe za ta kawo ba, ba ta san yadda za ta fuskanci Zayd ba, ba ta san yadda za ta iya zama cikin wannan auren ba. Ta san abu ɗaya kawai—rayuwar da ta sani ta ƙare a wannan daren.
Ta runtse idanunta sosai. Wani mummunan tunani ya ratsa zuciyarta, kamar dai mutuwa ce kawai za ta kawo mata hutu. Ta ƙara matse idanunta, sai ta yi shiru… tana jiran dare ya ƙare, ko kuma zuciyarta ta samu wata hanyar da za ta iya jure abin da kaddara ta ɗora mata.
————-
Washegari, gidan ya tashi kamar babu wani abu da ya faru. Kowa ya fito, ya kama sabgarsa kamar kullum. Sai dai duk da haka, idan mutum ya duba sosai, zai gane cewa akwai wani abu da ya sauya a cikin gidan.
Mama Sabuwa ta fito da fuskar nan a dinke, kamar hadarin gabas. Kai tsaye ta fito da radio, ta kunna shi ta kure uwar ƙara, sannan ta ɗora shi kan window ɗin ɗakin Baffa. Daga nan ta ɗauko mangal ɗinta, ta haɗa wuta, ta jawo kujera ta zauna a wajen. Tana rura wutar, tana kuma bin wakar da ke tashi daga rediyon kai tsaye, fuskarta cike da wani irin annuri, kamar babu abin da ya dame ta.
Mama Indo dake gefe tana haɗa abun ƙari ta ɗan kalleta, sai kawai ta tabe baki, ba ta ce komai ba, ta cigaba da sabgarta.
Umma kuwa dama ba ta fito ba. Ba ita ce da girki ba, saboda haka ta yi zamanta a ɗakinta.
Ba a daɗe ba sai Bintu ta fito, ta sha gayu sosai. Daga gani kawai ka san yau akwai inda take shirin zuwa, kamshin turarenta kuwa ya cika wajen.
Sai ta kalli Mama Sabuwa, “Mama, na shirya.”
Mama Sabuwa ta ɗago kai ta kalleta, sai murmushi ya bayyana a fuskarta, “Ma Shaa Allah!” Ta ɗan kalli Bintu daga sama har ƙasa, “Idan ba ka yi ban guri, kin fito kenan.”
Bintu ta gyada kai, “Eh, Mama.” Ta ɗan gyara jakarta, “Na fito. Yau da wuri zan fita sabida anjima zan dawo, ba daɗewa zan yi ba.” Ta ɗan yi shiru, “Akwai baƙin da zan yi.” Sai ta buɗe jakarta, ta ciro ₦5,000 ta miƙa wa Mama Sabuwa, “Gashi, ki yi cefanen rana. Ba ma sai kin yi girkin da ni ba.”
Mama Sabuwa ta washe baki, “Ahhh…” Ta karɓi kuɗin da sauri, “Toh, sai kin dawo.” Ta ɗan yi mata kallon ƙauna, “Ki kula da kanki, ki ya la haula, sabida miyagu da kuma ’yan hana ruwa gudu.” Ta ɗan daga hannunta, “Allah Ya tsare. Maza jeki, Bintu.”
Bintu ta yi murmushi, “Toh, sai na dawo.” Ta mike ta nufi ƙofa.
Mama Sabuwa ta bita da kallo, sai ta yi shewa, “Kaiii! Allah, na gode!” Ta kalli kuɗin da ke hannunta, “Dan baƙinciki sai ya mutu.” Ta ɗan yi wata dariyar alfahari, “Wallahi na gaba dai ya yi gaba… Ahto, na baya sai labari!”
Mama Indo ta ja wani uban tsaki. Ta yi kamar ba ta ji komai ba, ta cigaba da sabgarta. Can sai ta kwalawa Maryam kira, “Maryam!”
Ba a daɗe ba Maryam ta fito tana ɗan miƙa jikinta.
Mama Indo ta girgiza kai, “Yanzu Maryam…” Ta ɗan kalleta, “ina nan ina fama da aiki, ke kina ɗaki kina kwance.” Ta ɗan ɗaga gira, “Ko kuma aikin danna wayar kike? Oho!”
Maryam ta ƙaraso tana murmushi, “Wlh Mama, na zata kin gama.” Ta ɗan yi dariya, “Ke ce ba kya so na miki aiki, sai ki ce bai miki ba. Yanzu kawo na ƙarasa.”
Mama Indo ta janye flask ɗin, “A’a, barshi. Na gama.” Ta ɗan mika mata, “Dauki abincinku ke da Raihana.” Sai ta miko mata wata cooler, “Dauki wannan na Umma ne, ki shigar mata da shi.”
“Toh.” Maryam ta ɗauki abincinsu, sai ta ɗauki na Raihana, ta kuma riƙe na Umma, ta nufi ɗakin.
Sai Mama Indo ta kalli Mama Sabuwa, “Ga, abincinku.”
Mama Sabuwa ta ɗago kai, sai ta zuba mata wata uwar harara, “Allah Ya sawake! Wlh ko mayyace ni, ba zan ci abincinku ba.” Ta ɗan ɗaga gira cikin girman kai, “Kuma ai abin da ya haɗa ya raba. Daga yau…” Ta ɗan tsaya, ta kalli Mama Indo sosai, “kar wata kinibabbiyar mata ta sake bani abincinta. Ba na so, ku ci tsiyarku.”
Mama Indo ta fashe da dariya tana mikewa, “Ah…” Ta girgiza kai, “toh, ba shakka. Ya ɗada auki kenan.” Ta ɗauki na Baffa ta nufi ɗakinsa.
Mama Sabuwa kuwa ta bita da wani uban harara, ta ja tsaki, “Hmm!” Sai ta koma kan mangal ɗinta, kamar babu abin da ya faru.
———
Maryam ta shiga ɗakin Umma, ta ajiye abincin Umma a kan ƙaramin teburin gefe, sannan ta ƙarasa cikin bedroom ɗin. Ta ɗan yi sallama, “Assalamu alaikum, Umma.”
“Wa alaikumus salam.” Umma ta amsa cikin sanyin murya.
Maryam ta ƙarasa kusa da ita, “Umma, ina kwana?”
Umma ta ɗago kai da murmushi, “Lafiya. Ya kika tashi?”
Maryam ma ta yi murmushi, “Alhamdulillah.” Ta ɗan kalli wajen falon, “Ga, abincinki yana falo. Ko na shigo miki da shi nan?”
Umma ta girgiza kai, “A’a, barshi. Yanzu zan fita falon. Sannu da ƙoƙari.”
Maryam ta yi murmushi, “Toh. Bari na je mu ci namu.”
Umma ta gyada kai, “Toh.”
Maryam ta juya ta nufi ɗakin Raihana. Da ta tura ƙofar, sai ta tarar da Raihana tsaye gaban mirror tana gyara kayan wajen. A zahiri, ta kasance cikin nutsuwa, kamar babu wani abu da yake damunta. Amma duk wanda ya kalli fuskarta na ƴan daƙiƙu kaɗan zai gane cewa wannan ba nutsuwar gaskiya ba ce, akwai wani babban abu da yake ci mata zuciya.
Maryam ta karasa ta ajiye abincin, sai ta dawo wajen Raihana, “Ga abincinmu. Ki zo mu ci.”
Raihana ba ta ko kalleta ba, “Na koshi.”
Maryam ta tsaya, ta buɗe ido, “Kin koshi?” Ta ɗan kalleta da mamaki, “Me kika ciii?”
Raihana ta ci gaba da gyara kayan kwalliyarta.
Maryam ta ƙara matsowa, “Yanzu fa gari ya waye.”
Raihana ta ɗago idanunta ta kalleta, “Wlh… na koshi.”
Kallo ɗaya kacal da Maryam ta yi mata ya isa ya sa zuciyarta ta buga. Nan take ta matso kusa, ta kama hannunta, “Rayy…” Muryarta ta sauya, “me ya faru?” Ta ƙara matse hannunta, “Me aka miki? Wani abu ya faru ne?” Ta kalli fuskarta sosai, “Kin ga yadda fuskarki ta yi? Me aka yi miki?”
Raihana ta ɗauke kanta gefe, ba ta ce komai ba.
Maryam ta ƙara kallonta, “Rayy…” Amma shiru.
Sai Maryam ta kasa jurewa, ta fisgo ta a hankali suka zauna gefen gadon Raihana, “Wai meye?” Ta ɗan daure fuska, “Ni ba za ki ce bakomai ba, don Allah ki faɗa min kafin jinina ya hau.”
Raihana ta yi shiru, hawaye suka fara cika idanunta, ta sunkuyar da kanta.
Maryam ta kalleta, “Rayy…”
Sai Raihana ta ɗago kanta, kalamanta suka fito cikin murya mai rawa, “Baffa…” Ta yi shiru, hawaye suka zubo, “Baffa ya daura min aure jiya.”
Maryam ta zuba mata ido.
Raihana ta goge hawaye da sauri, “Ya bada aurena…” Muryarta ta ƙara karyewa.
Maryam ta zuba mata ido, “Baffa ya daura miki aure jiya?”
Raihana ta gyada kai a hankali, “Ya ba da aurena ga wanda ban so…” Muryarta ta karye, “Wlh, Maryam… mutuwa kawai nake so.” Hawaye suka sake cika idanunta.
Amma kafin ta sake furta wata kalma, Maryam ta fashe da dariya, “Wayyo Allah! Nagode maka!”
Raihana ta ɗago idanunta a hankali, Maryam kuwa ta kasa riƙe dariyarta, “Wannan abu da daɗi yake kuwa!” Ta riƙe cikinta tana dariya, “Ashe yanzu ke ba sa’ar mu bace?”
Raihana ta kalleta babu ko alamun dariya a fuskarta.
Maryam ta ƙara dariya, “Yo ashe ni tun jiya nake zaune da matar aure?” Ta ɗan matsa kusa da ita, “Rayy, you kept this from me fa!”
Raihana ba ta amsa ba, kawai ta sauke idanunta. Hawayen da suka taru a gefen idonta ta ɗauke su da yatsunta a hankali, ɗaya bayan ɗaya.
Maryam ta ɗan tsaya, dariyar ta ragu, sai ta kalli fuskarta sosai, “Rayy…”
Raihana ta ci gaba da share hawaye, “Ki daina mana…”
Sai Raihana ta kalli Maryam, muryarta ta fito ƙasa-ƙasa, “Ban da ƙarfin jin wannan yanzu.”
Maryam ta yi shiru, ta gane wannan karon ba lokacin tsokana ba ne. Ta kama hannun Raihana, “Who is he?”
Raihana ta yi shiru na ƴan daƙiƙu kamar tuna wanda aka aura mata din yana mata wani uban ciwo a zuciya, da kyar tace, “Zayd.”
Maryam ta ɗan zaro ido, “Zayd?”
Raihana ta gyada kai.
Maryam ta buɗe baki kamar za ta sake yin magana, amma ganin yadda Raihana take share hawayenta ne ya hana ta. Ta matso sosai kusa da ita, “Rayy …”
Raihana ta ɗago idanunta.
Maryam ta yi murmushi mai laushi, “Na san ba wannan kika shirya wa rayuwarki ba.” Ta ɗan matse hannunta, “Amma ki saurare ni.”
Raihana ba ta ce komai ba.
Maryam ta ci gaba, “Wani lokaci… abin da muke so ba ya zuwa lokacin da muke so, wanda zuciyarmu take so ba ya kasancewa a gare mu. Amma idan abin da muke so ya gagara…” Ta ɗan kalleta, “ba yana nufin rayuwa ta ƙare ba.”
Raihana ta runtse idanunta, hawaye guda ya sake gangarowa, ta share shi da yatsanta.
Maryam ta ci gaba cikin natsuwa, “Ki ba kanki lokaci, ki fara sanin mutumin, ki san halinsa, ki san yadda yake tunani. Maybe…” Ta ɗan yi murmushi, “maybe ba zai zama yadda kike tunaninsa ba.”
Raihana ta ɗan girgiza kai, “Maryam, ni bana son sa.”
“Na sani.” Maryam ta amsa nan take, “Amma yanzu ba za mu iya canza abin da ya faru jiya ba.” Ta ɗan matsa kusa, “Don haka, for now… ki yi amfani da abin da yake gabanki, ki kare zuciyarki, ki bar lokaci ya nuna miki inda komai zai dosa.”
Raihana ta yi shiru.
Maryam ta ɗan taɓa kumatunta, “Kar ki yi wa kanki illa saboda abin da bai faru yadda kika so ba. Ki yi addu’a, ki roƙi Allah idan akwai alheri a cikinsa, Ya sanya ki gani. Idan kuma babu…” Ta ɗan yi shiru, “Allah Ya buɗe miki wata ƙofa.”
Raihana ta sauke ajiyar zuciya, ta ɗan gyada kai.
Maryam ta ɗan murmusa, “Amma gaskiya…” Ta kasa riƙe murmushin da ya sake bayyana a fuskarta, “wai ke fa matar aure ce yanzu?”
Raihana ta kalleta a hankali.
Maryam ta yi dariya, “Okay, okay! Na daina!”
Raihana ta sake dauke kanta, “Yanzu zo mu ci abinci.”
Raihana ta kalli abincin, sai ta girgiza kai, “Ba na jin yunwa.”
Maryam ta kalleta, “Ko da ba za ki ci ba, ki zauna tare da ni.”
Raihana ta yi shiru, daga ƙarshe ta miƙe a hankali.
Maryam ta kama hannunta, suka nufi wajen abincin. Amma kafin su zauna, Raihana ta sake kallon kanta a madubi. Fuskarta ta yi shiru, idanuwanta sun nuna abin da bakinta ya ƙi faɗa.
A jiya… ta kasance Raihana kawai. Yau… ta farka da sabon suna a rayuwarta, matar aure.
Sai ta sauke idanunta, “Ya Allah…” Ta furta a hankali, “ka taimake ni.”
Maryam ta kalleta, ba ta ce komai ba, kawai ta matse hannunta domin ta san… wannan shi ne farkon wani sabon babi da babu ɗayansu da ya shirya shi.

——————

ARMAAN MANSION


Wayewar garin Litinin kuwa, a ARMAAN MANSION, Inno ta sauko downstairs inda Ummie da Suhaila suke zaune suna jiranta. Sanye take da atamfar Super Holland, dinkin riga da zani, tare da yalwataccen mayafi da ya dace da atamfar. Medical glasses ne suka manne a idanunta, wanda suka ƙara bayyana kamala da tsantsar nutsuwa da ke tattare da shigarta da suffarta.
Da ta sauko, idanunta suka fara yawo a falon, kamar tana neman wani.
Ummie da ta lura da ita sai ta mike, “Kin sauko, Hajiya?”
“Eh.” Inno ta gyada kai, “Za mu iya tafiya.” Sai ta ɗan tsaya, idanunta suka sake yawo, “Amma kuma… Zaydu fa?” Ta kalli Ummie, “Ina yake? Shi ne zai kaimu, ko mu kaɗai za mu je mu yi musu godiyar auren ne?”
Ummie ta ɗan kalli Suhaila, “Je ki kira shi, ki ce ya shirya ya fito ya kaimu.”
“Toh.” Suhaila ta amsa tana murmushi, sannan ta nufi stairs.
Inno kuwa ta karasa kan kujera ta zauna, “Mu jira su dawo.”
Ummie ta gyada kai tana komawa kujerarta.
Suhaila ta karasa ƙofar ɗakin Zayd, ta ɗan yi knocking.
A lokacin kusan ƙarfe uku na rana ne. Zayd yana zaune a kan sofa, laptop ɗinsa ajiye a gabansa kan ƙaramin stool. Yatsunsa suna yawo a kan keyboard, yana aiki cikin nutsuwa, fuskarsa babu wani expression.
Sai aka sake knocking. A hankali ya ɗago kansa, “Yes, come in.”
Suhaila ta turo ƙofar ta shigo, murmushi a fuskarta, “Akhi…”
Zayd ya ɗaga gira, bai ce komai ba.
Suhaila ta ƙaraso, “Inno ta ce ka shirya.” Ta ɗan yi shiru tana ƙoƙarin hana kanta dariya, “Za mu je gidansu matarka.”
Zayd ya ɗan kalleta.
Suhaila ta ci gaba, “Ta ce ka yi sauri.”
Zayd ya sake kallonta, fuskarsa ta kasance a yadda take. Amma kallon da ya yi mata ya isa ya sa Suhaila ta ɗan buɗe ido.
“Wallahi da gaske nake!” Ta ɗan daga hannunta, “Tace mu dawo kafata kafarka.” Sai ta yi murmushi, “Don Allah, Akhi… ka yi sauri, kaji?”
Zayd ya buɗe baki zai yi magana. Amma kafin ya samu damar cewa komai… aka turo ƙofar, Ummie ta shigo.
Da ta ga Suhaila har yanzu tana nan, sai ta kalli su biyun, “Kun bar mu muna jira?” Ta ɗan daure fuska, “Ku hanzarta mana.”
Zayd ya ɗan langwabe kai, kamar yana shirin kawo wani excuse. Amma Ummie ta riga ta fahimci abin da yake shirin yi.
“Ke, Suhaila, fito ki barshi ya shirya.” Sai ta kalli Zayd, “Five minutes.” Ta ɗaga yatsa, “Ka same mu downstairs.” Ta juya ta fita.
Suhaila ma ta biyo bayanta, tana dariya ƙasa-ƙasa.
Zayd ya bi su da kallo na ƴan daƙiƙu, sai ya sauke ajiyar zuciya. Ya kalli laptop ɗinsa, daga nan ya rufe shi a hankali, ya mike ya nufi closet dinsa.




Not edited

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.