Free chapter · Read without an account

WHAT LAY BENEATH

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN


ZAYD ARMAAN 

CHAPTER FIFTY THREE:53

WHAT LAY BENEATH

JIDDAAH BARKUM

—————

Ba a ɗauki dogon lokaci ba, sai takun sawunsa da ƙamshin turarensa suka cika falon.
Suhaila ta ɗago kai, idanunta suka sauka a kansa.
“Fatabarakallahu ahsanal khaliqeen…”
Shi kaɗai ne abin da bakinta ya iya furtawa, domin wani irin mugun kyau ne ta ga ya bayyana a gabanta, kamar dai a yau ne ainihin hasken angonci ya fara bayyana a jikinsa.
Zayd ya fito cikin nutsuwa, sanye da yard ash-coloured riga da wando masu sauƙin kyau. Rigarsa ta zauna daidai a jikinsa, ba matsewa, ba kuma sakaki, tana ƙara fito da tsayin jikinsa da faɗin kafadunsa.
Babu hula a kansa. Gashinsa kuwa a gyare yake cikin sauƙi—ba wai mai yawa ba ne, amma an yi masa neat ɗin da ya dace da yanayinsa. Wasu ’yan gashin sun ɗan tsaya a goshinsa, suna ƙara masa wani irin fresh da youthful look.
A wuyan hannunsa kuwa akwai Tissot PRX, agogon da ya zauna a hannunsa cikin nutsuwa, yana ƙara masa classy appearance ba tare da ya yi yawa ba. Ƙafafunsa kuwa suna sanye da black leather sandals masu tsabta.
Amma uwa uba… ƙamshin da ke tashi daga jikinsa. Wani irin daddadan ƙamshi ne da ya cika falon tun kafin ya ƙaraso sosai. Turare ne mai zurfi, mai ɗan ɗumi, amma fresh a lokaci guda—irin wanda idan mutum ya wuce kusa da kai, sai ka ci gaba da jin ƙamshinsa bayan ya wuce.
Fuskarsa kuwa… fresh, fess fess, kamar wanda a ka yi wa wankan madara. Babu wani expression mai yawa a fuskarsa. Kawai nutsuwa ce wacce ta saba kasancewa tare da shi, amma a yau akwai wani ɗan sauyin da ba a saba gani ba, kamar dai da gaske angonci ya fara screaming a jikinshi, ko da shi kansa bai nuna shi ba.
Suhaila ta sake murmushi, idanunta suka ci gaba da binsa. Ta so ta faɗi wani abu, amma kalmomin suka tsaya mata a maƙogwaro. Subhanallah… Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci kamar wadda take ƙoƙarin haɗiye murmushinta. Ummie tana nan, Inno ma tana nan, don haka ta kasa yin abin da zuciyarta take so.
Zayd kuwa bai ce komai ba. Kawai ya ɗan kalli kowa, sannan ya gyara hannun rigarsa a hankali. Daga nan ya karasa stool din gefen vase din flower ya ɗauki keys ɗinsa.
Suhaila ta lura. Murmushin da ke fuskarta ya ƙara faɗaɗa. “Hmm…” Ta furta a ranta. A yau dai Akhi ya fi kyau fiye da kullum.
Sai ta mike. Ummie da Inno ma suka mike, suka nufi compound ɗin.
Da suka isa wajen motar, guards ɗin Zayd suka taso da niyyar yi musu rakiya. Amma Zayd ya ɗaga musu hannu kawai—alamar a’a. Kallon da ya yi musu ya isa su fahimci abin da yake nufi: shi da kansa zai yi driving. Wannan kuwa ba ƙaramin abu ba ne, domin ba kasafai yake driving da kansa ba.
Suhaila ta sake murmushi, ta kalle shi daga gefe, “Akhi…” Kamar za ta ce wani abu, amma ta sake yin shiru.
Zayd ya yi kamar bai lura da ita ba. Ya shiga wajen direba. Ummie da Inno suka shiga baya, Suhaila kuwa ta zagaya ta zauna a front passenger seat.
Zayd ya zauna a driver seat, ya saka key, ya ɗan daidaita mirror. Daga nan ya ja seat belt ya ɗaure. Kamar yadda ya saba, babu wani gaggawa a motsinsa. A hankali ya kunna motar. Sautin engine ɗin ya cika wajen. Ya saka gear, ya yi reverse a hankali. Gateman ya garzaya ya buɗe gate.
Sai dai… daidai lokacin da motar Zayd ke shirin fita, sai ga wata mota tana ƙoƙarin shigowa. Wanda ke cikin motar ya lura da motar Zayd, nan take ya ɗan ja baya, ya ba su dama su fara fita. Zayd ya ɗa rage gudu ya fito kofar gidan yana kokarin daukar direction dinsa.
Amma kafin ya yi nisa, sai aka sauke glass ɗin motar da ke wajen. Fuskar Mommy Hauwa ta bayyana. Fuskarta babu yabo, babu fallasa, kawai wani irin yanayi ne da ba zai iya sa mutum gane abin da ke cikin zuciyarta ba.
“Ina zuwa.” Ta furta a hankali, idanunta suka sauka kan Suhaila.
Suhaila ta kalleta, ba ta ce komai ba.
Sai Inno ta ɗan buɗe glass ɗin gefenta, “Ki yi reverse ki juya.” Ta ɗan nuna mata hanya, “Ki biyo mu a baya.”
Mommy Hauwa ta gyada kai, “Toh.”
Inno ta maida glass ɗin sama. Zayd kuwa ya ci gaba da driving. Sai ya ɗan kalli mirror ɗin gefensa, ya ga motar Mommy Hauwa tana binsu. Bai ce komai ba, kawai ya maida idanunsa kan hanya.
Ummie ta sauke ajiyar zuciya. A gaskiya, ba ta so Inno ta ce Mommy Hauwa ta biyo su ba—ba yanzu ba, ba a lokacin da suke shirin zuwa gidan sirikan Zayd ba, musamman da Raihana bata ko tare ba. Amma ta san babu yadda za ta iya hana abin da ya riga ya faru, sai kawai ta yi shiru. Ta jingina da kujerarta, idanunta suka tsaya kan hanya. A zuciyarta kuwa… ta fara addu’a, domin wani abu a cikin ranta yana gaya mata cewa wannan tafiyar ba za ta kasance kamar yadda ta fara ba.
Mintuna kaɗan kacal suka ɗauka kafin suka isa Malali. Zayd ya nemi gefe ya yi parking a hankali. Motar Mommy Hauwa ma ta bi bayansa, ta yi parking a ɗan nesa. Ta kashe motarta, amma ba ta sauko nan take ba.
Idanunta suka fara yawo a wajen. Ta kalli layin, ta kalli gidajen, sai ta sake kallon gabanta ta wani yatsine fuska. A ranta ta ce, Wannan wace irin unguwa ce kuma? Unguwar ta yi mata kama da irin tsofaffin unguwannin Jakara—ƙananan tituna, ƙura a gefe, gidaje jere kusa da juna, da kwata da ta ratsa gefen layukaa. Ta ɗan murɗe bakinta. To, me kuma suka zo yi a nan?
A hankali Zayd ya buɗe murfin motarsa ya fito. Kafin ya yi wani motsi, Suhaila ma ta sauko daga ɗayan gefen. Inno da Ummie suka fito daga baya.
Suhaila ta rufe murfin motar, ta gyara mayafinta sannan ta kalli Zayd. Shi kuwa ya tsaya a gefe yana kallonsu cikin nutsuwa. Fuskarsa babu wani expression, amma idan aka duba sosai, akwai wani irin nutsuwa a tare da shi—irin nutsuwar mutumin da ya riga ya san dalilin zuwansa kuma ba ya buƙatar ya bayyana wa kowa.
Mommy Hauwa ta buɗe murfin motarta a hankali, ta fito. Sai ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon wajen kamar an sauke ta a wani wuri da ba ta taɓa tsammanin za ta taka ba. Ta dauko handbag ɗinta, ta ɗan ɗaga haɓa sama sannan ta nufi inda suke.
Ta fara zuwa wajen Hajja, “Assalamu alaikum, Hajja.”
Hajja ta amsa mata.
Mommy Hauwa ta juyo wajen Ummie. Kallon da ta yi mata ya kasance na sama-sama, kamar dai gaisuwar kawai take son kawarwa daga kanta, “Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumussalam,” Ummie ta amsa a sanyaye, ba ta ƙara komai ba.
Mommy Hauwa ta ɗan taɓe baki, sannan ta juyo wajen Inno, “Hajiya…” Ta ɗan kalli hanyar da suka zo, “wai ina ne nan muka zo?” Ta sake kallon gidajen da ke gabansu, “Gamu mun tsaya a nan kamar muna jiran wani abu.”
Inno ta ɗago idanunta a hankali. Kallon da ta yi wa Mommy Hauwa ya sa ta yi shiru na ɗan lokaci. Muryarta ta fito cikin nutsuwa, amma cike da authority, “Za ki gani yanzu.”
Mommy Hauwa ta ɗan buɗe baki. Amma kafin ta sake tambaya, Inno ta juya kai tsaye wajen Zayd, “Zayd.”
Zayd ya ɗago kansa.
“Ina gidan nasu ne?” Muryar Inno ba ta da tambayar da ake tsammanin amsa mai tsawo, umurni ne kawai, “Ka bar mu a tsaye a nan? Ka nuna mana gidan mu shiga.”
Zayd bai yi saurin amsawa ba. Ya ɗan kalli Inno, sai ya juya idanunsa zuwa gidan da ke gabansu.
Amma kafin ya yi magana, Suhaila ta riga ta yi gaba, “Ga gidan fa…” Ta juya tana kallon su, “Inno, ku taho mu je.” Ta fara tafiya.
Inno ta bita ba tare da wani ƙarin bayani ba. Ummie ma ta bi bayanta cikin nutsuwa.
Mommy Hauwa ta tsaya, ta zuba wa gidan ido. Gidan ba irin gidajen da ta saba gani ba ne. Ta ɗan karkatar da kanta, ta sake yatsina fuska, kamar wacce aka tilasta mata shiga wani wuri da ba ta so. Ta ɗan ja dogon numfashi, sai ta gyara mayafinta, ta kalli bayansu. Dukkansu sun riga sun fara shiga.
Ta tsaya na ƴan daƙiƙu kamar tana son ta ƙi bin su. Amma daga ƙarshe… ta ɗan ɗaga kafaɗa, “Kalli wani hut dan Allah…” Ta yi maganar a ƙarƙashin murya, sai ta bi bayansu da tafiyar da ke nuna ba ta jin daɗin komai.
A waje kuwa… Zayd ne kaɗai ya rage. Ya tsaya kusa da motarsa yana kallonsu har Inno, Ummie, Suhaila da Mommy Hauwa suka ɓace a bakin ƙofar gidan. Ya sauke ajiyar zuciya a hankali, sai ya haɗe hannayensa a ƙirji. Kallon gidajen dake layin ya yi na ƴan daƙiƙu, daga nan idanunsa suka koma kan ƙofar da suka shiga. Fuskarsa har yanzu babu wani expression, amma daga yadda ya sauke ajiyar zuciyar… kamar ya san cewa abin da ke gabansu ba zai kasance tafiya mai sauƙi ba.
———
Da sallama Suhaila ta shigo gidan, fuskarta ɗauke da murmushi.
Maryam da ke zaune tana tsife kitsonta ta ɗago kai tana amsawa. Amma da idanunta suka sauka kan yawan mutanen da suka shigo tare da Suhaila, nan take ta yi saurin jawo ɗankwalinta ta rufe gashinta. Fuskarta ta washe da murmushi, sai ta mike. A take ta gane Suhaila, “Sannunku da zuwa.” Ta ƙaraso tana ɗan sunkuyar da kai cikin girmamawa, “Ina yini.”
Inno ta amsa tana kallonta, “Lafiya kalau, Alhamdulillah.”
Maryam ta ƙara murmushi, “Bismillah ku shigo.”
A dai-dai lokacin Mama Sabuwa ta ɗaga labulen ɗakinta, ta fito. Ta bi mutanen da kallo ɗaya bayan ɗaya, amma ba ta ce musu komai ba.
Mama Indo kuwa ta fito daga ɗakinta, fuskarta cike da fara’a, “Barka dai! Lale, sannunku da zuwa!” Ta buɗe hannuwanta, “Ku shigo mana, ya kuke tsaye a waje?” Nan take ta nufi hanyar ɗakin Umma, tana cewa su shigo ciki.
Ummie, Suhaila da Inno suka biyo bayanta.
Mommy Hauwa kuwa ta tsaya a tsakar gidan. Idanunta suka fara yawo ko’ina. Ta kalli tsakar gidan, ta kalli ɗakunan, ta kalli kayan da ke wajen. Ta kalli komai kamar wacce aka kawo inspection. Amma duk da irin qurillar da take yi a zuciyarta, ba ta ga wani abu da za ta iya kira datti ko rashin tsari ba; komai yana cikin tsafta. Ba ta kuma ga wani abu na musamman da za ta iya kushewa ba, sai dai… ba luxury life ɗin da ta saba gani ba ne. Ta ɗan tabe baki, Hmm.
Sai ta bi bayansu a hankali. Har yanzu ba ta san gidan uban wa aka kawo ta ba. Ta ɗaga labulen ɗakin Umma ta shiga.
Inno kuwa har ta zauna cikin falon tare da Ummie da Suhaila, bisa jagorancin Mama Indo, wadda ta riga ta shiga ɗakin Umma ta yi mata magana.
Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba sai ga Mama Indo ta dawo tare da Umma. Ta zauna tana murmushi, idanunta cike da fara’a. Da ta ga Ummie, sai fuskarta ta ƙara haske. Suka gaisa cikin mutunci.
Daga nan ta juya wajen Mommy Hauwa, “Hajiya, ina yini?”
Mommy Hauwa ta fara bin ta da kallo, kallon da ta yi mata ya kasance sama-sama. Ta kalle ta daga sama har ƙasa. A ranta ta yarda cewa matar tana da kyau, amma sai ta ɗan tabe baki, “Ina gajiya.” Ta maida kanta gefe.
Umma da ke zaune ta yi ɗan jim, kamar ba ta ji daɗi ba. Shiru ya ratsa tsakanin su na ƴan daƙiƙu.
Sai Maryam ta sake bayyana da sallama. Ta ajiye ruwan da ta kawo a gefe cikin girmamawa, “Sannunku da zuwa.” Ta sake sunkuyar da kai, sai ta shige ɗakin Raihana.
Inno ta ɗan dubi Umma, murmushi ya bayyana a fuskarta, “Maigidan baya nan ne?”
Umma ta ɗago kai, “Yana ɗakinsa.” Ta ɗan yi shiru, “Baya jin daɗi ne, bai daɗe da kwanciya ba.”
Inno ta gyada kai, “Wayyo Allah sarki.”
Sai Umma ta cigaba, “Bari a yi magana da shi.” Ta yi ƙoƙarin tashi.
Amma kafin ta miƙe sosai, Mama Indo ta yi saurin tashi, “Ki zauna.” Ta ɗan murmusa, “Bari ni na masa magana.” Ba tare da ta jira amsa ba, ta nufi ƙofar falon ta fice.
Inno ta bita da kallo, sai ta sake juyowa wajen Umma. Murmushin da ke fuskarta ya ƙaru, “Toh, ina amaryar take?” Ta ɗan karkatar da kai, “Ko dai saboda na zo ne take tsoron fitowa ta gan ni?” Ta faɗi hakan cikin wasa.
Amma kalmar ta sa Mommy Hauwa ta ɗago kai. Ta kalli Inno, sai ta kalli Umma. A hankali… wani abu ya fara haɗuwa a cikin tunaninta. Gidan nan… gidan matar da aka aura wa Zayd ne.
Ahh… Ta ɗan runtse idanunta. Ba shakka. Wani ɗan murmushi mai sanyi ya bayyana a gefen bakinta. Ashe ma yar matsiyata ce. Ta sake kallon gidan, sai ta dubi Umma sama-sama, wani irin raini ya bayyana a idanunta. Ashe saboda wannan ne aka kawo mu nan?
Umma kuwa ta ɗan yi ƙaramar dariya, kamar ta fahimci abin da Inno take nufe—wato ita ce kakarsa kenan. Sai ta mike a hankali, “Bari na mata magana.” Ta juya ta nufi ɗakin Raihana.
A lokacin… Maryam ta riga ta fara fesawa Raihana labarin baƙin da suka zo.
Umma ta shiga, ta samu Raihana a zaune. Ta kalleta cikin nutsuwa, “Raihana.”
Raihana ta ɗago kai.
“Ki tashi ki saka hijabi.” Ta ɗan yi shiru, “Ki fito ku gaisa da baƙin.”
Raihana ta sauke idanunta, ba ta ce komai ba, kawai ta ɗan gyada kai.
Umma ta kalleta na ƴan daƙiƙu, sai ta juya ta fita, ta koma falon ta zauna a inda take.
Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba… sai suka ji sallamar Baffa daga bakin ƙofar. Sun dawo, tare da Mama Indo.
Inno ta ɗago kai, Ummie ma ta kalli ƙofar. Mommy Hauwa ta gyara zamanta. A hankali… yanayin falon ya sauya.
Bayan zaman Baffa, sai aka fara gaishe-gaishe cikin mutuntawa.
Inno ta ɗan murmusa, sannan ta dubi Baffa, “Mungode fa, Malam Musa. Allah Ya saka da alheri. An mutunta mu daga zuwa neman auren yarinya sai daurin aure. Allah Ya saka da alheri.” Ta ɗan sauke numfashi, “Allah Ya haɗa kawunanmu, Ya kauda sabani da rashin fahimta, Ya sa wannan zumunci ya zama na alheri.”
Baffa ya ɗan yi dariya a hankali, “Haba, Hajiya, ba komai.” Ya ɗan gyara zamansa, “Ai matar mutum kabarin sa ce. Abin da Allah Ya rubuta maka a Lauhul Mahfuz, shi za ka samu. Haka Allah Ya tsara, haka kuma zai gudana.” Ya ɗan yi murmushi, “Allah dai Ya ba su zaman lafiya.”
“Amin,” kowa ya amsa kusan a lokaci guda.
A dai-dai lokacin… Raihana ta fito, kanta a sunkuye. Tafiyarta a hankali take, cike da kunya da nutsuwa. Tana taku ɗaya… sai ɗaya. Amma da ta shiga falon, sai ta ji kamar dukkan idanun da ke wajen sun sauka kanta. Kuma tabbas hakane, kowa ya zuba mata ido, kowa kuma da irin tunanin da ke yawo a zuciyarsa.
Raihana ta ƙara sunkuyar da kai.
Inno ce ke zaune a gefen da Raihana take, saboda haka kai tsaye Raihana ta ƙaraso gabanta, ta durƙusa, kanta har yanzu a ƙasa.
Inno ta zuba mata ido, ta duba fuskarta sosai. A take ta lura da kamalar yarinyar: kunya, natsuwa, tawali’u—duk sun haɗu a tare. Wata irin nutsuwa ta ratsa zuciyar Inno, ta ji wani abu mai taushi ya sauka a zuciyarta. Ba tare da ta yi wata magana ba, ta miƙa hannu a hankali, ta rungume Raihana.
“Matso wajena.”
Raihana ta ɗan matsa kusa.
Inno ta sake rungumeta, “Ni ce nan kishiyarki.” Ta ɗan ja da baya tana kallonta, “Kin ganni?” Ta yi murmushi, “Har yanzu da ƙarfi na!”
Ƙaramar dariya ta tashi a falon.
Suhaila ta ɗan girgiza kai tana murmushi, “Toh, Inno… kar dai kishi ya sa ki karya ta mana.”
Inno ta ɗan yi dariya, ta sake kallon Raihana.
Raihana kuwa kanta har yanzu a ƙasa take, ta ɗan yi murmushi cikin kunya, sai ta fara gaishe da Inno cikin sanyin murya, “Barka da yamma.”
“Barka dai, amarya.” Inno ta amsa cikin fara’a.
Raihana ta sake sunkuyar da kai, daga nan ta cigaba da gaishe da sauran mutanen da ke falon ɗaya bayan ɗaya, har ta isa wajen Ummie.
Da idanun Ummie suka sauka kan Raihana… wani irin annuri ya bayyana a fuskarta. Ta ɗan tsaya tana kallonta. Yanzu wannan ita ce matar Habibina? Matar Zayd… Matar ɗanta. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali, zuciyarta cike da godiya ga Allah. A ƙarshe kafin ta bar duniya ta samu damar ganin wacce aka haɗa rayuwarta da ta ɗanta. Ta kalli Raihana cikin wani irin tausayi da ƙauna da ba ta ma san lokacin da suka fara shiga zuciyarta ba. Ya Allah… Ka sa ta zama alheri a gare shi.
Amma Mommy Hauwa… tun daga lokacin da idanunta suka sauka kan Raihana, wani abu ya buga mata zuciya. Ita kanta ba ta san menene ba, amma ta ji cewa ba ƙaramin abu ba ne. Ta kafeta da idanu kamar zata cinyeta, daga fuskarta… zuwa yadda take tafiya, zuwa yanda hannunta ke motsi cikin hijabinta, har zuwa yadda take sunkuyar da kanta, kamar tana ƙoƙarin karanta wani abu a jikinta.
Da kyar ta iya amsa gaisuwar Raihana, “Yauwa.” Muryarta ta fito a sanyaye, amma idanunta… ba su bar Raihana ba. Suna bin duk wani motsinta, duk wani sauyin da ke bayyana a fuskarta, kamar wacce aka ɗora wa aiki na musamman na tsare duk wani motsin Raihana.
Raihana kuwa ba ta san komai ba, kawai ta ci gaba da sunkuyar da kanta cikin kunya, ba ta san cewa ba kowa ne yake kallonta da irin idon da ta zata ba.
Inno ta sake gyara zamanta, sai ta kalli Raihana, ta kalli Umma, daga nan ta koma da dubanta kan Baffa. “Yanzu…” Ta ɗan yi shiru, “Ina ɗauke da wata magana mai muhimmanci.” Ta sauke ajiyar zuciya, “Kuma ban san da wanne ido za ku kalli wannan maganar ba.” Ta ɗan yi murmushi mara ƙarfi, “Amma ina roƙon ku ku fahimce ni.”
Falon ya yi shiru, kowa ya maida hankalinsa kanta.
Inno ta ɗora magana a hankali, “Gaskiya… ban san da maganar Raihana ba lokacin da na zo wannan garin ba.” Ta ɗan kalli Raihana, “Abin da ya kawo ni shi ne… ganin wannan yaron ya ƙi aure.” Ta ɗan girgiza kai, “Abin ya zama kamar wanda aka yi wa baki. Saboda haka na tashi daga can na zo nan ne da niyyar in haɗa shi aure da ‘yar uwarsa.” Ta ɗaga hannunta ta nuna Mommy Hauwa, “Wannan ita ce mahaifiyar yarinyar da na so haɗa shi da ita.”
Mommy Hauwa ta ɗan gyara zamanta.
Inno ta ci gaba, “Ɗiyar cikina ce, ƙanwar mahaifin Zayd.” Ta sauke ajiyar zuciya, “Gaskiya ma… na riga na fara fitar da maganar.” Ta yi shiru, “Har maganar ta shiga kunnen ita yarinyar. Ni ma na shiga tunanin cewa idan komai ya tafi yadda nake so, wannan Juma’ar za a ɗaura musu aure.”
Shiru ya sake mamaye falon. Inno ta kalli kowa ɗaya bayan ɗaya.
“Amma…” Ta ɗan dakata, “Allah yana da nasa tsarin. Abin da Allah Ya tsara shi ne ya faru. Abu ya taso ba mu shirya ba, kuma aka yi abin da ya dace.” Ta haɗe hannayenta a kan cinyarta, “Saboda haka…” Ta kalli Baffa, “Na zo ne in ba ku haƙuri, domin gaskiya, ban san ko ya dace a sanar da ku tun farko ko a’a ba. Amma ganin ba a sanar da ku cewa akwai wata magana ba…” Ta ɗan sauke kai, “Na ga ya dace ku sani, domin kada ku taɓa ganin kamar an ɓoye muku wannan magana ne da gangan.”
Ta ɗan yi shiru, “Minzali da ya zo neman auren Raihana ma bai san da wannan maganar ba. Da ya sani…” Ta ɗan girgiza kai, “da na tabbata zai sanar da ku. Saboda haka na ga ya fi kyau ku sani daga bakina.” Ta sauke numfashi, “Don Allah ku fahimce ni, ban zo da niyyar na ɓoye komai ba, Allah ne Ya tsara abin da ya faru.”
Falon yayi shiru, wani irin shiru mai nauyi.
Zuciyar Raihana ta buga da ƙarfi. Sau ɗaya, sai kuma ta sake buguwa, kamar zuciyarta ta kasa ɗaukar abin da kunnuwanta suka ji. Ta sunkuyar da kanta, hannunta ya ɗan matse gefen hijabinta.
Umma kuwa ta yi shiru, jikinta ya ɗan yi sanyi. Ta ɗago kai a hankali ta kalli Baffa, amma ba ta ce komai ba.
Baffa ya lura da kallonta, sai ya sauke ajiyar zuciya. Ya kalli Inno cikin nutsuwa, “Haba Hajiya…” Muryarsa ta kasance cikin nutsuwa irin ta mutumin da bai son abu ya rikide ya zama matsala, “Na fahimci abin da kika ce.” Ya ɗan gyara zamansa, “Kuma babu wani abu da ya sa na ga ya kamata mu ɗauki maganar da zafi.”
Ya kalli Raihana na ɗan lokaci, sai ya koma kan Inno, “Zayd Musulmi ne, Allah Ya ba shi damar auren mata huɗu. Saboda haka kasancewar an yi magana a kan wata mace kafin wannan auren…” Ya ɗan dakata, “ba abin mamaki ba ne, ba kuma abin da zai sa mu ce an cuce mu ba ne.” Ya ɗan yi murmushi, “Da Allah Ya ƙaddara ya auri waccan ma, da ita ce Raihana za ta samu. Amma Allah Ya ƙaddara Raihana ita ce farko.”
Ya kalli Inno, “Abin da ya fi muhimmanci shi ne… ya yi adalci, ya kiyaye haƙƙoƙin kowacce mace, ya kuma tsare mutuncin gidansa.” Ya ɗan sauke numfashi, “Idan har Allah Ya ba mutum ikon ɗaukar nauyin mata huɗu, to nauyin adalci yana tare da wannan ikon. Ba auren mace da yawa ne abin tsoro ba, abin tsoro shi ne zalunci.”
Kalaman suka sauka cikin falon. Inno ta yi shiru.
Baffa ya ci gaba cikin natsuwa, “Saboda haka Hajiya, ki kwantar da hankalinki. Ba mu ɗauki wannan a matsayin laifi a gare ku ba. Abin da ya faru, ya faru, Allah ne Ya tsara shi.”
Sai ya kalli Raihana. Fuskarta har yanzu a sunkuye take, “Ke kuma…” Muryarsa ta yi laushi, “ki daina saka abin da kika ji yau a zuciyarki kamar an rage darajarki. Ba a rage darajarki ba, ke matar Zayd ce.”
Raihana ta ɗan runtse idanunta. Ta ji wani abu ya tokare maƙogwaronta, ba ta san ko saboda Baffa yace ke matar Zayd ce ko kuma saboda wani abun ne daban ba, ba ta sani ba.
Baffa ya sake duban Inno, “Mun gode da kika faɗa mana. Allah Ya sa wannan zumunci ya kasance na alheri.”
Inno ta ɗan jinjina kai, “Amin.”
Ummie kuwa ta sauke ajiyar zuciya. Suhaila ta kalli Raihana a hankali.
Mommy Hauwa kuwa… ta yi shiru, amma idanunta suna kan Raihana darammm. A wannan karon… ba wai kawai kallon amaryar Zayd take yi ba, ta fara kallonta da wani ido da har yanzu ba ta ba shi suna ba!




Not edited

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.