Free chapter · Read without an account

THE REVELATION

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN


ZAYD ARMAAN

CHAPTER FIFTY FIVE:55

THE REVELATION

JIDDAAH BARKUM

———
A cikin falon Baffa kuwa, shiru ya sake ratsawa bayan kalmar da ta fito daga bakinsa.
Idanun Raihana a rufe suke ruf, zuciyarta kuwa tana bugawa da wani irin mahaukacin daf-daf saboda kusancin da ke tsakaninsu, da kuma sanyin hannunsa da ke riƙe da nata. Ta ji tamkar numfashinta zai ɗauke gaba ɗaya.
Zayd kuwa ya kafa mata idanunsa, yana kallon yadda fuskarta ta tattare waje ɗaya saboda tsoro da fargaba. Wani ƙaramin murmushi mai wuyar ganewa ya kubuce a gefen leɓensa, amma muryarsa ta fito tsaf, cikin sanyi da zurfi.
“Ba cewa kika yi in shafa in ji ba?”
Ya ɗan matso da fuskarsa kusa da tata.
“Tambayarki nake… ina zan shafa ɗin?”
Raihana ta matsar da kanta baya da sauri, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga riƙon da ya yi mata. Amma riƙon nasa na nutsuwa ne, mai ƙarfi, wanda bai bar ta ta subuce ba cikin sauƙi.
“Malam, ka ƙyale ni mana! Sakar min hannu!”
Muryarta ta fito a shaƙe, fuskarta na bayyana tsagwaron haushi da kuma tsoron da take ƙoƙarin ɓoyewa.
“Wallahi idan ba ka sake ni ba, zan kwalla maka ihu a gidan nan, kowa ya shigo!”
Zayd bai firgita ba, bai kuma saki hannunta ba. Maimakon haka, sai ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya sake buɗe su a hankali.
Kallon da ya yi mata yana ɗauke da wani irin nauyi da ya sa Raihana jin tamkar tana neman madafa.
“Ki yi ihunki.”
Muryarsa ta fito a hankali.
“Ki tara wa kanki mutane. A ƙarshe kuma a haɗa miki kayanki a kore ki.”
Ya faɗa cikin nutsuwa, yana ɗan rage tazarar da ke tsakaninsu.
Raihana ta sake zabga masa uwar harara, har sai da ta ji tamkar idanunta za su faɗo.
Sai Zayd ya yi wani ƙaramin murmushi.
“Kin san dai akwai aurena a kanki.”
Ya ɗan karkatar da kansa.
“Ki kula da yadda za ki dinga magana da ni.”
Raihana ta ɗan buɗe baki, ta ƙalle shi cikin mamaki, kafin ta saki wata dariyar takaici.
“Wanne auren?”
Muryarta ta canza.
“Auren da ban zaɓa ba!”
Ta ɗan ja numfashi, idanunta suka cika da ƙwalla saboda takaici da fushin da suka haɗu mata lokaci guda.
“Ka nace sai da ka aure ni.”
Ta harare shi.
“Kuma kai ma ba wacce kake so ba ce!”
Zayd ya yi shiru.
Raihana ta ci gaba, kalamanta suna fitowa daga can ƙasan zuciyarta, ba tare da ta sake samun damar tace su ba.
“Ka sani sarai. Kuma tunda Inno ta riga ta shirya maka taka matar, me zai sa ka dame ni da wani zancen matarka a kaina?”
Da kalmar ta fito daga bakinta ne kawai, sai shiru ya sake mamaye falon.
Zayd ya tsaya cak.
Idanunsa suka sauka sosai a kan fuskarta.
Wacce mata?
Wannan shi ne karo na biyu da Raihana ta ambaci wannan maganar tun daga lokacin da ta shigo falon.
Tabbas akwai wani abu.
Wani abu da shi bai sani ba.
Ya yi shiru yana nazarin fuskarta, yana ƙoƙarin haɗa kalmomin da take faɗa da abin da ya riga ya sani.
Amma kafin ya samu damar tambayarta…
“Ka cika min hannuna…”
Muryar Raihana ta fito a hankali.
A wannan karon ba fushi ne ya mamaye ta ba, sai dai kunyar abin da ta faɗa da kuma tsoron yadda Zayd zai ɗauki kalamanta.
Yanzu ne ma take fara gane irin abin da ta furta.
“Ka ƙyale ni in fita…”
Zayd ya kalle ta na ƴan daƙiƙu.
Sai a hankali…
Ya sake hannunta.
Raihana ba ta jira komai ba. Nan take ta ja baya, ta gyara hijabinta cikin sauri, sannan ta kalle shi da ƙyar ta gefen ido.
Har yanzu fuskarsa fes take.
Babu alamar damuwa.
Babu alamar fushi.
Kawai tsayuwarsa cike take da aji da kwarjini, kamar babu abin da ya faru.
Raihana ta murguda baki.
Ba tare da ta sake cewa komai ba, ta juya ta fice daga ɗakin Baffa zuwa tsakar gida.
Tana tafiya, tana jin kamar ta fito daga wani wuri mai zafi zuwa wajen da iska ke ɗan sanyi.
Ta ci gaba da tafiya da sauri zuwa ɓangaren ɗakin Umma, tana ƙoƙarin kwantar da zuciyarta.
Amma kalaman da ta faɗa a cikin falon suka ci gaba da dawowa mata a rai.
Ta ɗan lumshe idanunta.
“Me ya sa na faɗa haka?”
Ta furta a ranta, tana cizon leɓenta cikin takaici.
A waje kuwa, Inno da Ummie har sun fito daga falon Umma, suna shirin fita zuwa compound.
Suhaila tana tsaye a gefe, murmushi kwance a fuskarta.
Da ta hango Raihana tana zuwa, sai murmushin da ke fuskarta ya ƙara bayyana.
Raihana kuwa tana zuwa ne da sauri, kanta a sunkuye, kamar wadda take ƙoƙarin guduwa daga wani abu da take jin yana bi ta a zuciyarta.
Da kanta a sunkuye haka, Raihana ba ta lura da inda take takawa ba har sai da ta kusa cin karo da Inno da Ummie a bakin ƙofar shiga babban tsakar gidan, wato daga inda ake barin falon Baffa.
Inno ta tsaya, idanunta suka sauka a kanta cike da ƙauna da kulawa. Ta kalli yadda Raihana ta fito daga falon, fuskarta a tattare, idanunta sun yi ja kamar wadda take gab da yin kuka.
“Raihana…”
Inno ta kira sunanta cikin muryarta mai cike da karamci da sanyi.
Raihana ta tsaya cak.
Zuciyarta ta sake yin wani irin harbi guda saboda ba ta tsammaci kiran ba. Ta ɗago kanta a hankali, idanunta masu cike da ɗal-ɗalin ƙwalla suka sauka kan Inno.
Sai ta juya ta kalli Ummie wadda ita ma take tsaye kusa da Inno, tana mata wani irin murmushi mai cike da kwantar da hankali.
“Na’am…”
Ta furta a hankali, muryarta a lafe, sannan ta sake sauke idanunta ƙasa.
Inno ta matsa kusa da ita, ta ɗaga hannunta ta dafa kafaɗarta a hankali, cikin tsantsar kulawa.
“Muna shirin tafiya ne,” Inno ta faɗa, tana kallon fuskarta fes. “Gashi mun gama magana da Baffanki.”
Ta ɗan yi murmushi.
“Muna roƙon Allah Ya albarkaci wannan zamantakewa taku.”
Ta ɗan matsa hannunta a kafaɗar Raihana.
“Ki kwantar da hankalinki, Raihana. A wurinmu ke ba suruka ba ce kawai…”
Inno ta ɗan dakata, idanunta cike da tausayawa.
“Ke ƴar mu ce.”
Kalaman suka sauka a ƙirjin Raihana tamkar ruwan sanyi a kan wutar da ke ruruwa a zuciyarta.
Ta yi shiru.
Na wasu seconds kaɗan, ba ta iya samun kalmar da za ta amsa ba. Kawai ta haɗiye yawu, tana ƙoƙarin hana ƙwallar da ta cika idanunta zubowa.
ƴar mu ce…
Wata irin magana ce mai sauƙi, amma ta taɓa wani wuri a zuciyarta da ba ta shirya ba.
Ummie kuwa ta rage tazarar da ke tsakaninsu, ta kama hannun Raihana ɗaya, ta matse shi cikin nata.
“Addu’armu ita ce Allah Ya ba ku zaman lafiya, Raihana.”
Ta yi mata murmushi.
“Idan akwai wani abu da kike buƙata, kar ki ji shakka ko ɗaya wajen sanar da mu. Don Allah, don Allah ki ɗauke mu kamar mutanen gidanku.”
Raihana ta ɗago idanunta a hankali.
Ummie ta ci gaba:
“Ranar Alhamis na nan tafe, in sha Allahu.”
Murmushinta ya ƙara faɗaɗa.
“Muna jiran ranar shigowarki cikin aminci.”
Ta ƙare maganar cikin wata irin nutsuwa, sannan ta ɗan juyo ta kalli Suhaila da ke gefe.
Suhaila kuwa tun farko take kallon Raihana da wani irin murmushi.
Sai ta ɗan ɗaga gira.
“Very soon…”
Ta faɗa cikin wasa, tana murmushi.
Raihana ta ji kunya ta kama ta nan take.
Maryam kuwa da ke kusa da su, bakinta ya ɗan buɗe, kamar wadda aka yi wa albishir da abin da take jira tun daɗewa.
“Allah Ya kai mu ranar lafiya,” Inno ta ƙara faɗa.
“Amin,” Ummie ta amsa.
Raihana ta ji ƙwalla ta sake taruwa a idanunta.
Ta maida kanta ƙasa da sauri, tana ƙoƙarin ɓoye fuskarta.
Inno ta shafi kanta a hankali.
“Good girl.”
Sai ta ɗan matse kafaɗarta kafin ta janye hannunta.
Raihana ta kasa ɗago kai.
Ba don maganar aurenta ba…
Sai don yadda suka karɓe ta.
Cikin sauƙi.
Cikin ƙauna.
Kamar ta riga ta kasance ɗaya daga cikinsu.
Amma a can wani wuri a cikin zuciyarta, wata tambaya ta sake tasowa.
Alhamis kuma? Me za a yi Alhamis?
Ta ɗan runtse idanunta.
Har suka isa gida, babu abin da ke tashi a cikin motar face muryar Inno da ke ta jaddada irin mutunci da karamcin Baffa. Ummie kuwa tana ta murmushi cikin tsagwaron farin ciki, musamman saboda yadda Inno ta amshi al’amarin hannu biyu-biyu.
Suhaila da ke zaune a mazaunin gaba kuwa, kawai kallon Zayd take tana ta faman zabga murmushi.
Shi kam, tukinsa kawai yake yi cikin nutsuwa. Duk da kunnuwansa suna sauraron hirar da suke yi, amma gaba ɗaya tunaninsa yana can wajen Raihana.
Kalaman da ta jefa masa a ɗakin Baffa suka kasa barin kansa.
“Inno ta riga ta shirya maka taka matar…”
Da kuma yadda ta faɗa masa cike da takaici:
“Wanne auren? Auren da ban zaɓa ba!”
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali, sannan ya ƙara maida hankalinsa kan tukinsa.
Ba a ɗauki dogon lokaci ba suka ƙaraso Armaan Mansion. Ya yi horn, a take gateman ya buɗe musu ƙofa, suka shigo cikin compound.
Bayan ya yi parking, Ummie da Inno suka fito daga motar.
Suhaila ma ta buɗe ƙofar tana shirin fitowa, sai muryarsa mai sanyi, amma cike da iko, ta dakatar da ita.
“Tsaya.”
Suhaila ta tsaya.
“Za ki raka ni.”
Ta ɗan juyo ta kalle shi cikin mamaki, sai kuma ta koma ta zauna tare da rufe ƙofar.
Zayd ya bi Ummie da Inno da kallo ta rearview mirror, yana kallon yadda suke dosar main entrance na lounge ɗin gidan.
Ya sauke wani deep breath.
Sai ya juyo gaba ɗaya ya fuskanci Suhaila.
Ya zuba mata waɗancan lumsasshun idanunsa masu zurfi da kwarjini. Bai ce komai ba da farko, kawai yana kallonta cikin wani intense gaze da ya sa murmushin da ke fuskarta ya fara gushewa.
Bayan wasu seconds, muryarsa ta fito a hankali, cikin wannan deep, husky voice ɗinsa mai cike da haiba da iko.
“Suhaila…”
Ta ɗan ɗago gira.
“Tell me everything.”
Suhaila ta zaro idanu waje guda.
“Akhie… ni ban gane me kake cewa ba.”
Ta faɗa tana turo baki cikin sigar shagwaɓa.
Zayd bai ce komai ba.
Kawai ya ci gaba da kallonta.
Wannan kallon nasa ya isa ya sanar da ita cewa wannan karon ba wasa yake yi ba.
Sai a hankali ya ce:
“Wanne auren ne za a yi Juma’a?”
A take Suhaila ta zaro idanu.
“Waye ya faɗa maka?”
Zayd ya ɗan kalle ta.
Kallo guda kawai.
Mai nauyi.
Mai gargaɗi.
Mai cewa kar ki ɓoye min komai.
Suhaila ta haɗiye yawu, sannan ta sauke idanunta ƙasa.
“Ummm…”
Ta ɗan yi shiru kafin ta fara magana.
“Dama Inno ce ta ce Friday za a ɗaura aurenka da Seemaa.”
Ta ɗan ɗaga idanunta ta leƙo fuskarsa.
“Shi ne ta faɗa wa Baffan Raihana… kuma a gabanta ta faɗa.”
Zayd bai motsa ba.
Suhaila ta ci gaba da sauri, kamar wadda take son ta gama bayanin kafin ya katse ta.
“And honestly, Akhie…”
Ta ɗan sauke numfashi.
“Na ga kamar Raihana ba ta ji daɗin maganar nan ko kaɗan ba.”
Ta ɗan turo baki.
“Ai ba ƙaramin abu ba ne. A ce har ba a kai ta ɗakin mijinta ba, amma an riga an fara zancen ƙara mata kishiya.”
Ta ɗan girgiza kai.
“Wace mace ce za ta ji daɗin irin wannan?”
Wani irin mugun shiru ne ya sauka a cikin motar nan take.
Zayd ya daskare. Wani irin nauyi ya sauka a ƙirjinsa yayin da kwakwalwarsa ta fara sake sarrafa kalaman Suhaila.
Seemaa.
Aure.
Juma’a.
A hankali kalaman Suhaila suka fara haɗuwa da waɗanda Raihana ta faɗa masa.
Komai ya fara haɗuwa.
Yanzu ya fahimci dalilin da ya sa kalaman Raihana suka fito da wannan irin zafi.
Inno ta riga ta yanke masa hukunci.
Ba tare da ta sanar da shi ba.
Ba tare da ta tambaye shi ba.
Ba tare da ta san ko yana son wannan auren ko a’a ba.
Seemaa?
Shi sam ba ya son ta.
Ba ya da wani ra’ayi a kanta.
Ko na second ɗaya.
Amma Inno har ta kai maganar zuwa gidan Baffa, ta faɗa a gaban Raihana, har ma da ranar da za a ɗaura auren.
Idanunsa suka sauya.
Fuskarsa ta yi tsauri.
Ya ɗauke kansa daga kan Suhaila, ya zuba wa dashboard ɗin motar idanu, zuciyarsa na cika da wani irin takaici da mamakin dalilin da zai sa Inno ta yi masa wannan ɗanye hukuncin. Me ya sa Inno za ta masa haka? Me ya sa za ta nemi ruguza masa lissafi?
Ya dafe goshinsa da hannu ɗaya, ya lumshe idanunsa gam.
Sai tunanin Raihana ya sake dawo masa.
Ko da kuwa Raihana ba ta son shi…
Ko da kuwa wannan auren ba ita ta zaɓa ba…
Ba za ta ji daɗin jin cewa wata mace tana zuwa a kanta ba.
Wace mace ce za ta ji daɗi?
Ya sauke numfashi mai nauyi.
Sai ya buɗe idanunsa.
Muryarsa ta fito a tsaurare, cikin wani irin sanyi mai ɗauke da fushi.
“Get out, Suhaila.”
Suhaila ta yi shiru.
Ta kalle shi na ƴan seconds, amma ganin yadda fuskarsa ta canza ya sa ba ta ƙara tambaya ba.
Ta buɗe ƙofar motar, ta fito da sauri, sannan ta rufe ƙofar a hankali.
Bayan ta fita…
Zayd ya sake jingina kansa da kujerar.
Ya lumshe idanunsa.
Numfashinsa yana hawa yana sauka a hankali, amma zuciyarta ta riga ta ɗauki wani sabon salo.
Bayan sun yi sallama a Malali da su Inno, Mommy Hauwa ta doshi gida, ranta cikin wani yanayi mai gauraye—farin ciki da kuma wani irin nauyi da ita kanta ba ta san takamaiman dalilinsa ba.
Duk tsawon tafiyar, babu wani tunani da ya fi dawowa mata a rai kamar fuskar Raihana da kuma irin tashin hankalin da ta san yana jiran ta a gida.
Ta sauke ajiyar zuciya.
Bayan ta yi parking a compound ɗin gidanta, ba ta ma gama kashe motar ba sai ta ji ƙarar buɗe ƙofa da sauri.
Seeyama ce.
Ta fito daga cikin falon da gudu-gudu, idanunta sun kumbura gaba ɗaya saboda kuka, fuskarta babu ko alamar nutsuwa. Kamar dai da ta ji motsin motar Mommy Hauwa ne kawai ta kasa ci gaba da zama a cikin gidan.
Maimakon ta tsaya, sai ta ƙaraso da gudu wajen motar, ta buɗe ƙofar ɓangaren Mommy Hauwa kafin ma ta samu damar fitowa sosai.
“Mommy!”
Muryarta na rawa.
“Da gaske ne?!”
Ta haɗiye yawu, idanunta suka ƙara cika da ƙwalla.
“Ya yi aure?! Ya auri wata da gaske ne, Mommy?!”
Mommy Hauwa ta sauke wani numfashi mai nauyi.
Fuskarta ta nuna tausayi da damuwa. Ta fito daga motar, sannan ta kama hannayen Seeyama biyu.
“Let’s get inside, darling…”
Ta yi ƙoƙarin murmushi.
“Come inside first.”
Ta ja ta a hankali zuwa cikin gidan.
Amma Seeyama ta fisge hannunta da sauri.
“A’a, Mommy!”
Hawaye masu ɗumi suka sake wanke mata fuska.
“Just tell me the truth!”
Muryarta ta ƙara rawa.
“Da gaske ne kenan ya yi auren?!”
Ta girgiza kai, tana kallon Mommy Hauwa da wani irin tashin hankali.
“Shirun da kika yi… shi ne amsar kenan?”
Kallon yadda Seeyama ke fita daga nutsuwarta ya sa Mommy Hauwa jin wani irin ɗaci a zuciyarta.
Ta san ba za ta iya ɓoye mata gaskiyar ba har abada.
Amma ba ta so ta faɗa mata komai a tsaye, a cikin wannan yanayin.
Sai ta sake takawa kusa da ita, ta kama kafaɗunta a hankali.
“Come on, sweetheart…”
Ta lallaba ta zuwa cikin falon.
Bayan sun shiga gidan, ta ƙarasa da ita wajen doguwar sofa, ta zaunar da ita a hankali, sannan ita ma ta zauna daf da ita.
Ta ɗaga hannayenta biyu, ta riƙo fuskar Seeyama, tana goge mata hawayen da ke bin kumatunta.
“Look at me, princess…”
Muryarta ta yi laushi sosai.
“Ki kwantar da hankalinki, kin ji ko?”
Ta shafa gefen fuskarta a hankali.
“I know how you feel, but you need to calm down first so we can talk—”
“Mommy!”
Seeyama ta hayayyako mata kafin ta ƙarasa.
Ta ɗan matsa gaba, fuskarta na sheƙi da takaici, ciwo da zafin kishi.
“Ni ki daina min wani ƙwana-ƙwana!”
Ta share hawayenta da bayan hannunta.
“Kawai ki faɗa min gaskiya!”
Muryarta ta sake rawa.
“Ya yi auren ko bai yi ba?!”
Ta kafa mata idanu.
“Is he married to another woman or not?!”
Muryar Seeyama ta amsa kuwwa a cikin tsaftataccen falon.
Shiru ya biyo baya.
Mommy Hauwa ta kasa magana na ƴan seconds.
Seeyama kuwa ta ci gaba da ƙafe ta da idanunta masu cike da hawaye, tana jiran amsa guda ɗaya kacal…
Amsar da tun fitar Mommy Hauwa take tsoron ji.



Not edited

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.