Free chapter · Read without an account

A NEW LIFE AWAITS

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN


ZAYD ARMAAN

CHAPTER FIFTY EIGHT: 58

A NEW LIFE AWAITS

JIDDAAH BARKUM 

——-

Haka Raihana ta ɗinga laƙe-laƙe da jan ƙafa, tana tafiya kamar wadda aka ɗora mata wani nauyi a kafaɗa, amma daga ƙarshe ta shirya tsaf. Ita da Maryam suka fito daga gidan. Exactly as they stepped outside, wata mota tana ƙoƙarin yin parking a ƙofar gidan. Bintu ce da saurayinta, wanda zuwansu ke nan ya dawo da ita gida daga fitar da suka yi.
Har su Raihana suka wuce ta gefen motar, idanun saurayin nata suka bi su cikin wani irin intense stare. Ya ɗan karkatar da kansa, idanunsa suna bin su Maryam da Raihana har suka ɗan yi nisa. Bintu ta lura da hakan. Nan take ta ƙanƙance idanu, ta haɗe gira, fuskarta ta sauya zuwa wata irin rashin jin daɗi. “Wai me kake kallo ne?” Muryarta ta fito cikin ɗan tsuke rai.
Ya juyo da sauri yana ɗan yaƙe, kamar wanda aka kama yana aikata abin da bai kamata ba. Amma duk da haka, ya sake ɗan leƙa rear mirror kafin ya maida idanunsa kanta. “Waɗannan da suka fito daga gidanku, ƙannenki ne?”
Bintu ta ɗan yi shiru. Ta juya kai a hankali, ta kalli su Maryam da ke tafiya a gaba, sannan ta sake juyowa gare shi, wannan karon idanunta cike da zargi. “Ehh… me ya faru?”
Ya ɗan ɗaga kafaɗarsa, yana ƙoƙarin nuna kamar babu wani abu mai muhimmanci. “No, ba komai…” Ya ɗan yi murmushi. “I just noticed them because ban taɓa ganinsu ba, kuma ban taɓa jin kin yi zancen su ba ma.” Ya ɗan tsaya, idanunsa suka sake komawa kan mirror. “Though I realized almost same feature kuke da su.”
Bintu ta ɗan buɗe baki cikin rashin yarda. Sai ta saki wani guntun tsaki, ta juya fuskarta gefe. “Ka ga matsalata da kai ko?” Ta haɗa hannayenta a ƙirjinta, fuskarta cike da takaici. “Sam ba ka ba ni respect! Muddin za ka ga mace za ka tsaya kallo, ko da kuwa ina tare da kai! Wallahi wannan ne kaɗai abin da ba na so a halinka!” Ta ƙarasa maganar tana ɗauke kanta gefe, kamar ba ta son ƙara kallonsa.
Ya ɗan yi murmushi, yana ƙoƙarin rage tension ɗin da ya tashi. “Sorry, babe.” Ya ɗan matsa jikinsa kusa da steering, yana kallonta da idanun neman afuwa. “Kin san dai ba wata mace a gabanki. Ni fa ba abin da nake nufi… I just asked because na so na gane ɗayar ne.”
Bintu ta juyo da sauri, idanunta suka buɗe sosai. “Ka gane ɗayar?” Ta ɗan matso gaba, fuskarta cike da mamaki da zargi. “Wacce a cikinsu ke nan?!”
Ya ɗan buɗe baki, sannan ya rufe shi. Ya shafa gefen kansa a hankali, yana kallonta kamar wanda ya gane cewa maganarsa ta ƙara ɗaga mata hankali. “Kar ki damu, tunda ba ki son maganar.” Ya ɗan gyara zamansa, sannan ya yi murmushi mai sanyi. “Yanzu sai yaushe ke nan?”
Bintu ta ɗan rolling idanunta, kafin fuskarta ta ɗan lafa. “Maybe next tomorrow. Don gobe ina da inda zan je, kuma ban jin zan dawo da wuri.”
Ya ɗan ɗaga kai, fuskarsa ta sake sakin murmushi. “It’s alright, babe.” Ya kalle ta na ƴan seconds, sannan ya furta cikin wata irin murya mai ɗauke da ɗan shagwaɓa: “I will miss you throughout tomorrow.”
Bintu ta ɗan yi murmushi, tana girgiza kai. “Gobe ne kaɗai fa, kar ka damu. Bari na shiga gida…” Sai ta kalle shi kai tsaye, murmushi ya ƙara bayyana a fuskarta. “I love you!”
“And I love you too,” ya amsa mata cikin murmushi. Daga haka ta sauka daga motar, ta kwashi shirginta ta yi cikin gida. Ya bi ta da kallo na ƴan seconds, har sai da ta ɓace daga ganinsa, sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali. Ba tare da ɓata lokaci ba, ya ja motarsa cikin sauri ya bi bayan su Raihana.
Raihana da Maryam suna barin ƙofar gidansu, ba su ɗauki wani dogon lokaci ba suka ɓace daga kan layin. Shi kuwa saurayin Bintu, bin bayan da ya yi bai ba shi damar ganinsu ba; kawai ya rasa inda suka yi. Ya ɗan rage gudun motarsa, idanunsa suna yawo ta cikin gilashin motar, yana ƙoƙarin gano inda suka ɓace. Sai ya sauke glass ɗin motarsa, ya ɗaga kai ya tambayi wani mai ruwa da ke ɗauke da ƙurar sa a gefen titi: “Ɗan Allah, ka ga wasu ƴan mata guda biyu sun wuce yanzu?”
Mai ruwan ya ɗago kansa, ya kalle shi, sannan ya amsa: “Ehh.” Ya miƙa hannunsa yana nuna masa hanyar da suka bi. “Can suka bi.”
“Okay, thank you.” Ya ɗaga glass ɗin motarsa, ya ja motar da sauri zuwa hanyar da mutumin ya nuna masa. Amma duk da ya bi layin har ƙarshe, bai gansu ba. Ya rage gudu, ya kalli gaba babu su, ya kalli gefen titi babu ko alamar su. Sai ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici, ya juya motar ya dawo gefe guda ya yi parking. Ya kashe engine, amma bai fita ba. Kawai ya zauna a cikin motar, hannunsa ɗaya a kan steering, yana kallon hanyar da suka bi kamar mai jiran ko za su sake ɓullowa ta wani wajen.
Su Maryam kuwa, zagayawa ta baya kawai suka yi zuwa gidan Maman Ihsan. A lokacin, Maman Ihsan ta gama shirinta tsaf tana ta faman jiransu. Da Raihana ta tura ƙofa ta shiga da sallama a bakinsu, Maman Ihsan ta miƙe tsaye da sauri, fuskarta cike da ɗan takaici. “Sai yanzu ke nan?!” Ta ɗaga hannayenta biyu kaɗan. “Duk abin da na ce a kan ki zo da wuri nan… Yau ne fa kaɗai gare mu, sai gobe! Ba a samu an yi miki komai ba, yanzu ta ina za mu fara? Da kin zo da wuri da ba wannan maganar ake yi ba, maybe tuni mun ci ƙarfin abun!”
Ita dai Raihana ba ta ce komai ba. Ta ɗan sauke idanunta ƙasa, ta janyo wata ƙarama kujera ta tsuguno ta zauna, sannan ta fara gaida Maman Ihsan cikin sanyi: “Ina kwana…”
Maryam ma ta gaishe ta. Maman Ihsan ta amsa musu cike da kulawa, sannan ta yi wa Raihana alamar ta tashi. “Zo, mu shiga.” Ta nuna mata ɗakinta extra da ke tsakar gida wanda a can ta haɗa duk wani abu na gyaran jiki. Babu wani abu na artificial a wajen; komai pure natural organic components ne. Daga kurkur, haɗin dilka, halawa (sugar wax), sai kuma wata babbar roba da aka haɗa lalle na musamman da sauran kayan aromatics waɗanda za a shafa a duk jikinta.
Raihana ta tsaya a bakin ƙofar tana kallon kayan. Idanunta suka yi gefe guda, fuskarta ta ɗan haɗe cikin takaici. Kamar ba kayan gyaran jiki take kallo ba, sai dai wani sabon nauyi da aka ƙara ɗora mata. Tunaninta ya koma kan mutumin da za a yi mata duk wannan saboda shi. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali.
Maman Ihsan ta lura da yadda ta ja gefe, sai ta juyo gare ta ta saki baki cikin ɗan mamaki. “Toh Raihana…” Ta ɗan ɗaga gira. “Ni zan biyo ki na cire miki kayan ne ko Maryam ce za ta cire miki?”
Raihana ta ɗan kalli Maryam, Maryam kuwa ta riga ta fara murmushi. Raihana ta haɗiye yawu, ta karɓi zanin da Maman Ihsan ta mika mata. Ta fara cire kayanta a hankali tana ajiye su a gefe, sannan ta ɗaura zanin a ƙirjinta ta gyara shi sosai. Ta kuma gyara hular kanta kafin ta ƙarasa ta zauna a kan kujerar da aka nuna mata.
Da ta zauna, sai ta jefa wa Maryam wata muguwar harara. Maryam ta yi saurin kawar da fuskarta, tana ƙoƙarin ɓoye dariyar da take yi ƙasa-ƙasa. Raihana ta ƙara tsuke fuska, Maryam ta cije leɓenta, amma murmushin bai gushe ba.
Yayin da Raihana ke gidan Maman Ihsan ana mata wannan traditional spa session ɗin a sauƙaƙe, a fannin Seeyama kuwa abin daban yake gaba ɗaya. Gidan Mommy Hauwa ya kaɗe da wasu uban su ƙamshi na ƴan gayu irin ƙamshin da tun daga ƙofar gidan yake sanar da kai cewa ba ko ina ba ake samun irin wannan ba. Mommy Hauwa ta gayyato guda cikin fitattun masana gyaran jiki all the way from Maiduguri, Falmatta da tawagar staff ɗinta.
Falmatta da mutanenta suka buɗe manyan luxury kits ɗinsu na alfarma. Komai na wajen classy and ultra-luxurious ne: tun daga sanannun man shafa na Khumrah, dilkar Halwa mai haɗe da man Chandan, turaren fata na Duhnal Oud, har zuwa na’urorin da ake fitar da dafaffen turaren jiki mai shiga har cikin ƙashi.
Seeyama kuwa tana zaune a tsakiyar ɗakin kamar sarauniya. Ƙafarta ɗaya a kan ɗaya, bayanta a jingine sosai da kujera, hannunta ɗaya na wasa da wayarta. Fuskarta babu wata alamar damuwa, sai dai wani irin isa da ƙwarjini da ke bayyana a kowane motsinta. Suka fara gyara Seeyama ciki da waje, cike da ƙwarewa da tsantsar kissa ta mutanen Borno. Seeyama na zaune cike da isa, lokaci-lokaci tana kallon yadda ake mata aikin, tana nuna musu yadda take so a yi mata komai perfectly.
“Slowly… ba haka nake so ba.” Ta ɗan ɗaga hannunta tana nuna musu yadda take so. “Make sure komai ya zama perfect.” Wata daga cikin staff ta gyara mata zanin da ya rufe bayanta tana massaging wajen da dilke, Seeyama ta kalli kanta a mirror sannan ta ɗan ɗaga kai cikin gamsuwa, ta yadda duk wanda ya kalle ta sai ya sake dawowa ya kalle ta.
Mommy Hauwa kuwa ta haɗe hannayenta tsakiya, tana tsaye a gefe kamar wata mace da ke kallon abin alfahari mafi girma a rayuwarta. Murmushin girman kai da alfahari ya kwanta a fuskarta. Ta kalli Seeyama daga mirror, sannan ta fara magana. “Ki kwantar da hankalinki, Seeyama.” Muryarta ta fito cike da confidence. “Gyaran da za a yi miki, ina mai tabbatar miki ba a yi wa wata mace irinsa ba!”
Seeyama ta ɗan yi murmushi a cikin mirror. Mommy Hauwa ta ƙarasa kusa da ita, ta ɗan sunkuya, sannan ta sauke muryarta ƙasa cikin lallami. “Tell me the truth…” Ta ɗan kalli Falmatta, sannan ta dawo da idanunta kan Seeyama. “A gaban Falmatta, daughter, kin tabbatar you are a virgin?”
Seeyama ta ɗago kai da sauri, fuskarta ta sauya nan take. Mommy Hauwa ta ci gaba ba tare da ta damu da expression ɗin da ya sauya a fuskar ɗiyarta ba: “Saboda Falmatta ta san irin gyaran da za ta miki. Kin ga dai babu lokaci, idan kuma kin san akwai wani abu, ba babbar matsala ba ce… Falmatta za ta san dabarun da za ta yi miki a wuce wajen.”
Seeyama ta kalle ta da wani irin mugun kallo. A take ta haɗe girar sama da ta ƙasa, leɓenta ya matse, fuskarta ta cika da tsantsar takaici. “Kin ga ke irin abinki, Mommy!” Ta ɗan juya jikinta gefe. “Duk abina wallahi ni ba ƴar iska ba ce!” Ta sake kallon Mommy Hauwa kai tsaye, idanunta cike da fushi. “Ban taɓa bawa wani shege kai na ba, ki daina ɗanganta ni da wannan! Mijina ne kaɗai zai fara kusanta ta!” Ta ƙare maganar tana kawar da kanta gefe gaba ɗaya, tana huci a hankali saboda haushin tambayar.
Mommy Hauwa ta kalle ta na ƴan seconds. Sai wani ɗan murmushi ya bayyana a gefen leɓenta, kamar amsar ta tabbatar mata da abin da take son ji. Ta sake gyara tsayuwarta, ta ɗaga kanta sama cikin wata irin gadara, sannan ta juyo wajen Falmatta. “Ki tabbatar Seeyama ta fita kunya!” Muryarta ta ɗauki ɗakin. “Ki gyara min ita sosai da kyau, Falmatta.” Ta ɗan kalli Seeyama daga gefe, sannan ta sake maida idanunta kan Falmatta. “Don’t mind how much it will cost… Ni kawai ƴata ta fito fesss tasss!”
Falmatta ta yi murmushi na ƙwarewa, ta gyara zamanta sannan ta amsa cikin nutsuwa: “Kar ki damu, Hajiya… Just trust me.”
Mommy Hauwa ta jinjina kai cikin gamsuwa, sannan ta sake kallon Seeyama. A fuskarta akwai cikakken confidence na macen da ta riga ta yanke shawarar cewa komai zai kasance yadda take so. Seeyama kuwa ta maida kanta kan mirror, kamar ba tajin me suka ce ɗan har lokacin haushin tambayar Mommy take ji. 

——-
Daga ya shigo daga masallaci sallar Magrib, Zayd kai tsaye ɗakin Ummie ya wuce. Ƙamshin hadadden turaren wuta na oud da bakhoor mai sanyi ke tashi a cikin ɗakin. Ummie tana zaune a kan prayer mat ɗinta bayan ta idar da sallar Magrib, tana jiran kiran Ishe’i. Da sallama ya shigo, ya ƙarasa a nutse ya zauna a gefenta. “Barka da dare, Ummie,” ya faɗa, muryarsa na fitar da gajiyar da ke ɗauke a ransa.
Ummie ta ɗan kalle shi, idanunta suka tsaya a kan fuskarsa na ƴan daƙiƙoƙi, kamar tana ƙoƙarin fahimtar irin yanayin da yake ciki. Sai da ta ƙarasa addu'arta ta shafa, shi ma ya shafa tare da ita, sannan ta juyo gare shi. “Baka tsaya ka yi Ishe’i ba ka shigo?”
Ya ɗan ɗaga kansa, sannan ya sauke numfashi a hankali. “Ehh… ba na jin daɗi ne, Ummie. I just want to head back and rest.”
Ummie ta zuba masa ido na ƴan daƙiƙoƙi. Ta lura da yadda yake zaune cikin nutsuwa, amma idanunsa suna ɗauke da gajiya da wani irin nauyi da bai faɗa mata ba. Sai kuma ta gyara zamanta ta fara magana cikin nutsuwa: “Yanzu ya kamata a haɗa musu lefe. Mun yi magana da Inno, sai ka tura ƙudin komai. Sannan ta fannin Raihana, na ga zai kasance guda biyu ne saboda abokiyar zaman da za a yi mata.”
Zayd ya lumshe idanunsa da ƙarfi. Ya Allah… Wallahi ya rasa ma me zai ce! Shi ba wai yi wa Seeyama lefe ba ne damuwarsa ba, a’a, gaba ɗaya abin da ke yawo a kansa shi ne yadda da gaske za a haɗa shi da mata biyu a lokaci guda. Toh wai ya zai yi da su ne?! Ya ɗan sauke kansa ƙasa, ya shafi gefen goshinsa da yatsunsa na ƴan seconds, kamar yana ƙoƙarin tsara tunaninsa. Daga ƙarshe a hankali ya buɗe idanunsa ya kalli Ummie, sannan ya fito da wayarsa daga aljihu.
After a few seconds, wayar Ummie da ke gefe ta yi vibrating alamun shigowar saƙo. Ta ɗauka ta duba. Da idanunta suka sauka kan adadin ƙudin da ya turo, sai ɗan ɗaga gira cikin mamaki. Sannan ta ɗaga kai ta kalle shi. “Wannan ƙudin bai yi yawa ba, Zayd?”
Zayd ya ɗan langwaɓe kansa gaba, idanunsa a kan wayarta. “Just use it to get whatever is necessary, Ummie. Ayi abin da za a yi kawai.”
Ummie ta yi shiru tana kallonsa na ƴan daƙiƙoƙi, kamar tana son tabbatar da cewa da gaske ba zai ƙara bayani ba. Sai kuma ta jinjina kai cikin gamsuwa da tausayawa. “Allah ya yi albarka, ya ƙara buɗi mai albarka.”
“Amin,” ya amsa a ƙasan makogwaronsa.
Ummie ta sake cewa: “Yanzu ina so ka tambayi Raihana ko akwai wani abu da take buƙata. Sannan ni ma na bada order kayan ɗakinta da su kitchen items ɗinta, don gaskiya it wouldn’t be fair mu bar mahaifinta da wannan nauyin tunda mu muka ɗauko auren nan. Amma duk da haka, ya ƙafe a kan sai ya yi mata nashi. Don haka ina so ka tambaye ta ko da akwai abin da take so na shirin biki wanda za ta ɗan yi hidima da ƙawayenta duk da babanta ya ce ba wani taro, amma ka san ƴan mata ko ya ya ne ba za a rasa wani abu ba… har Seeyama ma ka tambaye ta idan akwai abin da take so, ka ji ko?”
“In sha Allah,” ya amsa. Muryarsa ta fito cikin nutsuwa, amma zuciyarsa ba ta tare da su gaba ɗaya. Ba wai don ya so ba, ɗan wallahi kansa har ya fara ciwo saboda waɗannan zantukan gaba ɗaya ba wata fahimta yake yi musu ba. Shi dai kawai ba ya so ya ɓata ran Ummie ne. Ya ɗan jingina bayansa da kujerar, ya sauke ajiyar zuciya a hankali, kafin ya maida hankalinsa gare ta.
Daga ƙarshe, Ummie ta sake kallonsa tare da jefa masa wata muhimmiyar tambaya: “Yanzu maganar wajen zama… ina ka shirya ajiye su? Za ka haɗa su waje ɗaya ne ko kowacce da gidanta?”
Zayd ya yi shiru. Kalaman suka tsaya a kansa. Don har ga Allah ya manta cewa ashe fa gida ɗaya zai koma ya zauna da su! Idanunsa suka yi nisa na ƴan seconds, kamar tunaninsa ya gudu zuwa wani wuri. Sai ya sauke numfashi a hankali, ya ɗan dafe gwiwarsa da hannunsa. Shi fa wannan auren gaba ɗaya zuwar masa ya yi ba shiri, ba tare da ya tsara komai da hankalinsa ba.
“Kai nake sauraro,” muryar Ummie ta katse masa tunani.
Ya ɗan lumshe idonsa sannan ya buɗe. “Zasu zauna tare ne… a can Malali Park View Estate.”
Ummie ta yi shiru. Ta ɗaga gira domin ba ta zaci hakan zai ce ba. Ta kalle shi na ƴan daƙiƙoƙi, sannan daga baya ta jinjina kai a hankali. “Babu laifi.” Sai ta ɗan gyara zamansa. “Sai dai kuma Seeyama za ta fara tarewa, ita Raihana za ta zauna da mu a nan har zuwa lokacin da kayanta za su ƙaraso a je a gyara mata gida. Don na san ba lallai su zo kafin ranar ba, kuma gaskiya ba za ta tare ba tare da sauran abubuwanta ba. Idan ya so daga baya, idan komai ya kammala, sai ta tare.”
Zayd ya ɗaga kansa cikin sanyi da zurfafa nutsuwa, his overall composure completely relaxed yet respectful. Ya ɗan karkata kansa gefe kaɗan, ya duba Ummie da waɗancan zurfafan idanunsa. Fuskarsa ta yi laushi kaɗan, duk da cewa nauyin maganar yana nan a zuciyarsa. “Kamar yadda kika tsara, Ummie. Whatever you decide is completely fine with me… shi za a bi.”
A soft, subtle smile crossed Ummie’s face, satisfied with his calm attitude da kuma irin biyayyar da yake nuna mata duk da halin da yake ciki. Ta ɗan ɗaga hannunta ta shafi gefen kafaɗarsa a hankali, kamar wata uwa da ke nuna wa ɗanta cewa ta fahimci abin da yake ciki.
Daga nan, suka ci gaba da tattaunawa a tsanake a kan sauran abubuwan da ke gabansu har zuwa lokacin da aka kira sallar Ishe’i.



Not edited

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.