Free chapter · Read without an account

THE OTHER WIFE

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN



ZAYD ARMAAN

CHAPTER SIXTY ONE: 61

THE OTHER WIFE

JIDDAAH BARKUM

————

Motsin ficewarsa daga parlour’n ya bar wurin gaba ɗaya cikin wani irin shiru mai nauyin gaske, sai kawai sautin numfashin Raihana da ke fitowa da ƙyar. Tana tsaye a wurin, ƙafafunta suna karkarwa yayin da take jin tamkar ba za su iya ɗaukar nauyin jikinta ba. Idanunta suka cika da ƙwalla, ta lumshe su na ɗan lokaci tana ƙoƙarin haɗiye abin da ya tokare mata maƙogwaro.
Ta kalli tafin hannunta da ke riƙe da damin dalar $100 wacce ya ɗamƙa mata a hannu. Wani sabon ɓaɓɓacin rai da tsantsar kishin kai ya taso mata, ta ji tamkar ta yar da kuɗaɗen a ƙasa ta taka su da takalmin ƙafarta. Ta matse damin kuɗin sosai a tafin hannunta, yatsunta suka ɗan yi rawa saboda haushi. Amma amsawa da barazanar da ya yi mata tana nan tana yawo a kanta: “Wallahi idan kika zubar, za ki sha mamaki na.”
Wata uwar muguwar harara ta jefa wa ƙofar da ya fita ta cikinta, tana haɗiye wani zafaffen yawu mai cike da baƙin ciki. Ta ɗan girgiza kanta a hankali, fuskarta ta nuna tsananin takaici da rashin yarda da abin da ya faru.
Ta matsa a hankali zuwa kan kujera ta zube a kai, gaba ɗaya jikinta a sake, as if her entire strength had been drained. Ta sauke kanta a kan bayan kujera, idanunta suka lumshe. Yawo da hannunta ta yi a kan fuskarta tana goge sauran gumin da ƙwallar da ke jike a kumatunta. Lips ɗinta har yanzu suna yi mata wani irin mugun zafi saboda saƙon da ya bar mata a kai, ɗan wlh har lokacin ji take kamar bakinsa na wajen, hakan ke sake tuna mata yadda ya mamaye ta gaba ɗaya a ’yan mintocin da suka gabata. Ta ɗan taɓa leɓenta da yatsunta cikin rashin yarda, nan take ta janye hannunta kamar zafin ya ƙara dawo mata.
“Ashe ya iya iskanci… Mugu… azalumi…” ta furta a hankali cikin rawar murya da tsantsar raɗaɗi, tana sake matse idanunta ruf. Ƙwallar da ta taru a gefen idanunta ta sake zubo mata, ta share ta da bayan tafin hannunta cikin fushi.
Da ƙyar ta shawo kanta, ta ɗan tsaya a parlour’n Baffa ɗin don ta yi settling kanta. Ta sami wuri ta lafe a gefen kujera na ’yan mintuna, tana sauke numfashin mai ƙarfi. Ta sanya tafin hannunta tana goge sauran yawunsa da ke kyalli a kumatunta da bakinta, tana haɗiye wani zafaffen yawu na haushi. Ta ɗan yi ƙasa da kanta, tana ƙoƙarin dawo da nutsuwarta, kafin daga bisani ta share fuskarta da sauri.
Ganin cewa nutsuwarta ta ɗan dawo jikinta kuma numfashinta ya saitu, sai ta miƙe cikin hanzari. Ta murɗa ƙofar parlour’n Baffa, ta fito kamar wata munafuka gwanin tausayi, fuskarta cike da firgici, idanunta na yawo a tsakiyar gidan ko za ta hango wani. Ta ɗan tsaya na seconds ɗaya tana sauraron ko akwai wanda ya lura da ita, sannan ta runtse idanunta tana ƙoƙarin haɗiye sauran kukan. Yaƙi take yi da numfashinta don kar a jiyo sautin kukan da yake neman sake ƙufce mata.
Allah ya taimake ta, har a lokacin Umma tana cikin ɗaki ba ta fito tsakar gida ko parlour ba. Raihana ba ta tsaya yin shawara ba; ta ruga da wani irin mugun gudu, ta faɗa cikin ɗakinta direct, sannan ta tura ƙofar ta sa mata sakata da ƙarfi! Hannunta ya ɗan tsaya a kan sakatar na ƴan seconds, kamar tana tabbatar da cewa babu wanda zai iya shigowa.
Tana sa sakatar, sai kawai ta zube gaba ɗaya a jikin ƙofar, ta maƙale kanta a gwiwoyinta sannan ta fashe da wani zafaffen kuka mai matukar sauti da ban tausayi. Kafadunta suka fara rawa sosai, tana ƙoƙarin danne sautin kukan amma hakan ya gagare ta.
Sanda Zayd ya fice daga parlour’n Baffa, takunsa na fitar da wata irin ƙasaita da kwarjini na tsantsar cikakken namiji. Ba tare da ya waiwaya baya ba, ya taka a tsanake har zuwa inda motarsa ke fake a ƙofar gida. Fuskarsa a haɗe take, amma a cikin idanunsa akwai wani irin tunani mai zurfi da ba a iya karantawa.
Ya buɗe ƙofar motar, ya shiga sannan ya rufe da ƙarfi. Ƙarar ƙofar ta sake amsawa a cikin shiru.
Yana zama a kan sitiyarin motar, ya karkata kansa baya ya jingina da headrest, sannan ya lumshe idanunsa kaɗan. Sautin tsananin kukan da Raihana ke yi da kuma irin fuskarta da ke cike da ƙwalla suna ta faman dawo masa daki-daki a brain ɗinsa. Girarsa ta ɗan motsa, kamar wani ɓangare na zuciyarsa ke ƙin amincewa da abin da ya bari a baya. Ya fitar da wani dogon numfashi mai ɗumi da nauyi daga bakinsa, his chest rising and falling slowly.
Gaba ɗaya ya kasa fahimtar kansa; yanda yake jin kuka da raunin yarinyar na samun matsugunni a tsakiyar zuciyarsa abin mamaki ne a gare shi. Ya ɗan buɗe idanunsa yana kallon gaba cikin tunani. Deep down, ba ya son ganin hawayenta, amma taurin kanta da tsiwar bakinta suke ƙara tunzura shi wajen nuna mata ikon da yake da shi a kanta.
Ya ɗaga hannunsa guda ɗaya, na dama, yana kallo inda yake jin har yanzu akwai dumin da ya matsa mata a hannu da kuma laushin fatar jikinta. Yatsunsa suka ɗan motsa a hankali, sannan ya sauke hannun zuwa kan steering. Ya buɗe idanunsa masu nauyin gaske, ya tsare steering wheel ɗin da kallo.
Wani ɗan gajeren murmushi na kasaita da mugunta ya sake bayyana a gefen bakinsa lokacin da ya tuna yadda ta rikice ta fara ya tsaya za ta faɗa masa. Gira ɗaya ta ɗan ɗaga, kamar yana sake ganin expression ɗinta a gabansa.
“Stubborn girl,” ya furta a hankali kafin ya tashi engine ɗin motar cikin wani irin sanyi, ya murɗa steering tare da cilla motar zuwa kan hanya. A ransa yana sake faɗa cewa: this is just the beginning… Dole ki koya zama a ƙarƙashin dokoki na.
Lokacin da Zayd ya isa gida, ana gab da kiran sallar La'asar. Yana yin parking, ya fito daga motar, straight ya nufi part ɗinsa, ya wuce kai tsaye zuwa babban ɗakinsa ba tare da ya tsaya ko’ina ba.
Kai tsaye ya shiga bathroom, ya sakar wa kansa ruwan sanyi na showerhead gaba ɗaya. Ruwan na dukan ƙafaɗa da bayansa, ya rage saurin numfashinsa tare da lumshe idanunsa. Ya ɗan karkatar da kansa ƙasa, yana barin ruwan ya wanke masa fuskarsa kamar yana ƙoƙarin kawar da tunanin da ya cika masa kai.
Amma duk da ruwan da ke zuba a kansa, har yanzu hoton Raihana ya ƙi ɓace masa; swollen lips ɗinta da suka yi jawur saboda yadda ya matsa su da tsotsa, gami da wannan azababben, daddaɗan ƙamshin gyaran jikinta da ya shaƙa a wuyanta ne ke sake ruruwa a hancinsa da kwakwalwarsa. Fuskarsa ta ɗan ƙara tsukewa, kamar yana jin haushin yadda tunanin nata ya ƙi barin kansa.
A hankali ya sa hannu ya shafa fuskarsa tare da buɗe idanunsa da suka sake canja launi da nauyi. Ya sauke numfashi mai zafi, ya fito daga ƙasan shower ɗin yana amfani da towel don goge jikinsa.
Bayan ya gama goge jikinsa da towel, Zayd ya buɗe wardrobe ɗinsa ya ɗauko casual home outfit mai sauƙi, ya sanya shi ba tare da wani shiri na musamman ba. Ya gyara rigarsa a jikinsa, ya ɗauki agogon hannunsa ya sanya, sannan ya fesa ɗan turare kaɗan.
Ya tsaya a gaban mirror na ƴan seconds, ya kalli kansa, fuskarsa har yanzu babu wani expression na musamman. Sai ya ɗauki wayarsa ya fito daga ɗakin.
A hallway ɗin ya yi tafiya cikin nutsuwa, takunsa steady. Da ya isa downstairs, bai tsaya wata doguwar magana da kowa ba. Kawai ya cewa Ummie zai je wajen Imraan, daga nan ya wuce.
Sai kawai ya nufi ƙofar gida, ya fito, ya kalli lokacin a wayarsa sannan ya nufi masjid domin sallar La’asar.
Daga masallaci, Zayd kai tsaye gidan Mommy Hauwa ya nufa. A lokacin, Alhaji Bashari—baban Seeyama—yana compound tare da Imraan suna magana da shugaban jami'an tsaron gidan (security leader).
Zayd ya yi parking ɗin motarsa ya fito, ya ƙarasa inda suke sannan ya risina cikin tsantsar ladabi ya gaishe shi:
“Barka da dawowa, Daddy.”
Alhaji Bashari ya saki gajeren murmushi yana kallonsa, sannan ya ɗan gyara tsayuwarsa cikin nutsuwa.
“A’ah, kai ne a gidan, Zayd? Barka dai.”
Muryarsa cike take da nutsuwa, kamar babu wani abu a duniya da yake da ikon tayar masa da hankali.
Sannan ya juyo wajen shugaban tsaron:
“You can take your leave.”
“Yes, sir,” jami’in ya amsa cikin hanzari ya juya.
Dukansu uku—Zayd, Imraan, da Alhaji Bashari—suka nufi ƙofar shiga falon.
Mommy Hauwa na zaune a kan babbar sofa, ta sha ƙwalliya cikin wani ɗan ubansun lace mai matuƙar tsada. Sai sheƙi take, wuya da hannayenta duk gwalagwalai ne ke ƙyalli da adon da ke bayyana iko da takama. Ga wani azababben ƙamshi da ke tashi, kamar mai ƙoƙarin zuwa gasar sarauniyar ƙyau.
Ta ɗago kanta a lokacin da su Zayd suka shigo.
A take fuskarta ta haskaka da murmushi mai cike da alfahari, musamman ganin yanda Zayd ya shigo cikin nutsuwa irin tasa.
“Son, kai ne a tafe?”
Zayd ya ɗan shafa ƙeyarsa a hankali, ya ƙarasa gefenta.
“Good evening, Mommy.”
“Evening, son. How are you?”
“Lafiya ƙalau.”
Mommy Hauwa ta ɗan kalle shi tun daga sama har ƙasa, fuskarta ɗauke da wani irin murmushi wanda ƙarya ne ka ce ga abin da ke ranta.
“Toh, ina uwargidan taka? Hope kana zuwa duba ta akai-akai? Duk da ba ta tare ba yanzu, ai haƙƙin kula da ita yana kanka.”
Zayd ya ɗan yi murmushi yana ƙoƙarin ƙauda maganar, kamar ba ya son a tsawaita batun.
“Eh, ina zuwa.”
“Good, hakan ya yi kyau.”
Ta juya wajen Alhaji Bashari da ke zaune yana murmushi.
“Daddy, an ɗaura auren nasa fa! Duk da na faɗa maka a waya, gashi nan abu kamar wasa… Zayd da ya ƙi yin aure, sai gashi Allah ya ba shi mata biyu a tare.”
Alhaji Bashari ya sake gajeren dariya yana gyaɗa kai, amma yanayin fuskarsa ya nuna kamar maganar ba ta dame shi ba ko kaɗan.
“Ai da gaskiyarsa! Ni wallahi ya burge ni. Kana namiji ba ka yi mace sama da ɗaya ba, ai ka rako maza duniya ne. Zayd, ka ji ɗaɗinka… a Aljannah ma mata saba’in za ka samu!”
Mommy Hauwa ta ɗan ɓata rai sakamakon wasan mijin nata. Ta jefa masa wata ƙaramar harara, kamar tana cewa “please, enough,” kafin ta sake kallon Zayd.
A ƙoƙarinta na sauya akalar zancen, ta ce:
“Seema na upstairs a ɗakinta. Wallahi she’s sick tun jiya da dare, ta ƙi cin komai. An kai mata abinci tun ɗazun ta ƙi ci… Ko za ka shiga duba ta? Maybe kai ka sa ta iya ci.”
Zayd ya ji wani zafaffen takaici ya ɗamƙe shi a take, har ya fara ɗan danasani takowa gidan.
Ya ɗan lumshe idanunsa na ƴan seconds, kamar yana tara patience ɗinsa.
Amma ganin Daddy na zaune a wurin, ya daure ya ɗan shafa kansa a hankali.
“Ok.”
Muryarsa babu wani nauyi a cikinta, sai dai wannan calm ɗin nasa da yake sa mutum ƙasa gane ainihin abin da yake tunani.
Ya miƙe tsaye.
Imraan ya kashe masa ido ɗaya yana dariyar ƙasa-ƙasa.
Zayd ya juyo ya kalle shi na second ɗaya kawai.
Imraan ya ɗan matse leɓensa yana ƙoƙarin hana dariyarsa fitowa sosai.
Zayd ya yi kamar bai gansa ba, ya fuskanci stairs ɗin da za su kai shi ɗakin Seeyama, yayin da idanunsu gaba ɗaya suka bi shi da kallo.
A lokacin da ya ƙarasa ƙofar ɗakin, ya ɗan yi knocking mai sauƙi kamar ba ya son yi.
Daga ciki, muryar Seeyama ta fito cikin harzuƙa:
“Who is that?!”
Zayd ya ɗan tsaya.
Fuskarsa ta nuna wani ɗan ƙaramin expression na rashin haƙuri, amma bai ce komai ba.
A ransa, har ya fara tunanin ko dai ya juya kawai.
Amma ganin Daddy na gidan, sai ya daure ya sake knocking kawai.
Seeyama ta taso a fusace cikin gaggawa:
“And who the fuck is—”
Ba ta ƙarasa maganar ba.
Idanunta suka sauka a kan Zayd.
A take ta zaro idanu waje.
Shock ya bayyana a fuskarta kafin murmushi mai sauri ya maye gurbinsa.
Ta buɗe masa ƙofar tana ba shi hanya.
Zayd ya shiga ɗakin a hankali ya tsaya daga gefe, idanunsa suka fara yawo yana kallon yadda ta baza uban shirgi a ɗakin kamar mutum hamsin ne ke kwana a ciki.
Ya ɗan ɗaga gira.
Kallo ɗaya kacal ya yi wa ɗakin, sannan ya dawo da kallonsa kanta.
Ta juyo tana ɗan ɗingishi gami da laṅgwabe kai:
“Yaya… kai ne? Sannu da zuwa…”
Ta karkatar da kanta cike da kissa.
Zayd ya ɗan bi ta da kallo ƙasa-ƙasa, expression ɗinsa har yanzu calm, amma idanunsa sun tsaya a kanta na ƴan seconds.
Wata farar white vest ce kawai a jikinta wadda ta matse ta sosai, ta matse ƙirjinta har ’yan ƙananan nonowanta suka bayyana masu kamar tangerine! Ƙasanta kuma gaba ɗaya wani matsattsun bumshorts ne a ɗan siririn ƙugunta wanda ya matse ta sosai kamar an saka wa sauro belt. Ta sake gashinta mai mugun tsawon gaske har baya ya kwanta da kyau.
Ta matso kusa da shi tana wata tafiyar kissa:
“Ba ni da lafiya fa…”
Ta faɗa cikin wata shagwaɓa, tana ƙoƙarin ƙama hannunsa.
Zayd ya janye hannunsa cikin sauri ya jefa su a pocket ɗin wandon jikinsa.
Seeyama ta tsaya cakkk tana kallonsa.
Ta ɗan buɗe baki, sannan ta rufe shi.
Sai ta yi baya cike da kissa kamar za ta faɗi.
Da ma niyyar Zayd barinta ta faɗi ɗin, ya tsaya kawai yana kallonta da wannan sanyin fuskarsa.
Amma ganin yadda fuskarta ta koma daga kallon farko da ya shigo kamar da gaske ba ta da lafiyar, sai ya miƙa hannu ya riƙo ta cikin sauri.
Ya ƙarasa da ita gefen gadonta.
Ta sauke wani sanyayyan numfashin kissa, sannan ta ɗan kalle shi daga ƙarƙashin ido.
Zayd ya ɗan kalli abincin da ke gefen stool ɗin kusa da sofa, sannan ya dubeta da fuskarsa a tsaye ba tare da wani expression ba.
“You haven’t eaten?”
Ta yamutsa fuska sosai tana lafe kanta:
“Ban jin yunwa… amai ke damuna.”
Zayd ya lumshe idanunsa a hankali.
“Okay…”
Ya buɗe idanunsa ya sake kallonta.
“What’s wrong with you?”
Muryarsa a natse kuma a bushe.
Seeyama ta ƙankance idanunta tana kallonsa ta ƙarƙashin ido gami da sauke ajiyar zuciya mai sauti.
“Ciwon mara nake yi… period ke wahalar da ni.”
Ta ɗan karkatar da kanta, fuskarta ta nuna shagwaɓa.
“Ko yaushe dama haka nake yi. Amma doctor ɗin da ke duba ni ya ce ina aure… maybe my first or second encounter with my husband, zan daina.”
Zayd ya yi shiru na ƴan seconds.
Fuskarsa ba ta canza ba.
Sai dai yadda idanunsa suka ɗan tsaya a kanta ya nuna cewa ya fahimci inda maganarta ta dosa.
Seeyama kuwa ta ɗan yi murmushi mai laushi, tana kallonsa da wani irin kissa kamar tana jiran reaction ɗinsa.





Not edited

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.