Free chapter · Read without an account
THE BRIDE’S NEW HOME
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER SIXTY FOUR: 64*
THE BRIDE’S NEW HOME
*JIDDAAH BARKUM*
————
A ARMAAN mansion kuwa, tun wajen ƙarfe goma na safe bayan an gama breakfast, Suhaila ba ta sake bata lokaci ba, ta haura sama zuwa ɗakin Ummie.
Ummie ta fito a wanka kenan, tana zaune a gaban tafkeken mirror ɗin ɗakinta tana ƙoƙarin shirya kanta.
Suhaila ta shigo da sallama, ta nemi waje ta zauna gefen gadon Ummie, sannan ta fara magana da sauri:
“Ummie, wai haka za a yi siyayya ba a san size din underwear’s ɗinta ba da takalmi?
Kayan ma ya kamata ace an yi magana da ita ta zaɓi abunta da kanta, tunda dai yanzu haka ake yi.”
Ummie ta ɗan tsaya tana kallonta ta cikin mirror, ta ɗaga gira ɗaya kafin ta maida hankalinta kan abin da take gyarawa a gabanta.
“Toh, kije wajensa ki karɓi phone number ta, ni kam shaf manta wa na yi da ban karɓa a wajenta ba, amma yanzu ma ba ta baci ba.
Kije ya ba ki, sai kuyi magana da ita, idan yaso zaki iya tura mata kayan ta riƙa selecting to her color of preference.”
“Tooh,” Suhaila ta amsa a taƙaice, tana ɗan jinjina kai.
Ta miƙe ta nufi ɗakin Zayd.
Ita kuwa Seeyama, dama tunda aka fara maganar lefe tace a bata kuɗinta, ta san abin da take so zata siya da kanta, kar a je a debo mata abinda ba shi take so ba—shiyasa aka tura mata kuɗinta.
Yanzu kuma suka maida hankali kan siyayyar ta Raihana.
Suhaila ta isa ƙofar ɗakin Zayd, ta ɗan yi knocking.
Shiru.
Ta ɗan karkatar da kanta, ta sake saurare na ƴan seconds, bata ji motsi ba, sai kawai ta tura ƙofar.
Idanunta suka ɗan fara yawo a ɗakin, komai clean tsaf!
Gadon nan kamar ɗan Adam bai kwana a kai ba.
Ta ɗan dafe ƙofar tana kallon gadon, sannan ta ɗaga gira.
Bata ganshi a ciki ba, kuma bata ji alamun yana toilet ba, don haka sai kawai ta juya ta nufi study room ɗinshi.
Dama kwana biyu baya fita office, a nan study room ɗin yake komai, sai dai ya aika musu da komai ta email.
Ilai kuwa, sai ta hango shi ta transparent glass door ɗinshi.
Yana nan a zaune a nutse, fingers ɗinsa na yawo kan keyboard ɗin system cikin ƙwarewa, fuskarsa a sake kadaran-kadahaan kamar babu wani abin da yake damunshi a rayuwar nan.
Suhaila ta yi murmushi, ta ɗan girgiza kanta kamar wadda ta riga ta san inda za ta same shi.
Ta tura ƙofar ta shiga.
Jin motsinta ya sa Zayd ɗago kanshi, ya sauke idanunshi akan Suhaila na ƴan seconds kafin ya ɗauke, ya maida hankalinshi kan abinda yake yi.
Babu wata magana, babu wata tambaya.
Ta ƙaraso, ta ja kujera ta zauna.
“Well done, akhi.”
“Uhm,” kawai yace ba tare da ya ɗago ko ya kalli inda take ba.
Suhaila ta ɗan turo baki, ta kalle shi na ƴan seconds kafin ta fara magana:
“Uhm dama fa cewa nayi ka tambayi anty Raihana size din ta, sabida siyayyar da zaayi kar a siya mata wani abu yayi kaɗan ko yayi yawa,”
ta ƙarasa tana kallon fuskarshi, tana jiran ya ɗago ya kalleta.
Zayd bai ɗago ba, bai kuma dakatar da abin da yake yi ba, kamar ba zai amsa ba.
Can cikin nutsuwarshi yace:
“Like?”
Suhaila ta turo baki sosai, ta ɗan daga hannunta kamar wadda take ganin tambayar ta obvious ce:
“Akhi, idan an ce size ba dai underwear’s bane ko takalmi?
Sai abaya, tunda dai kowa da size dinshi!”
Zayd yayi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ya ɗan ɗago ya kalleta.
“Ki sa mata kowanne.”
Daga haka ya maida kanshi kan abinda yake yi.
Suhaila ta saki baki tana kallonshi, idanunta suka ɗan ƙara buɗewa cikin disbelief.
“Every size?” ta tambaya a ranta, kafin ta girgiza kanta.
Ganin dai ba zai ce komai ba, tace:
“Toh tunda ba zaka kirata ba, ni bani number ta na tambayeta da kaina, dan Allah!”
Zayd ya yi mata banza.
Suhaila ta ɗan jira ko zaiyi magana, amma still babu response.
Ta sauke numfashi ta ɗaga hannayenta sama kaɗan cikin surrender.
Da ta ji ta fara gajiya da zama, sai ta miƙe tana turo baki:
“Toh wallahi Ummie ce tace dama nazo ka kirata, tunda ba zaka kirata ba, bari naje na faɗa mata!”
Ta yi kamar za ta fita, amma tana ɗan kallonshi ta gefen ido.
Ilai kuwa sai yace:
“Wallahi kika fita, I will give you a dirty slap!”
Suhaila ta tsaya cak, ta juyo tana zaro ido:
“Toh kaƙi kira kuma ka hanani number!”
Zayd bai ce komai ba, sai kawai ya ɗauki wayarshi a hankali, ya danna number Raihana sannan ya sa a speaker.
Ya turo ma Suhaila ita a gaban desk dinshi.
Suhaila ta yi dariya a hankali, ta girgiza kanta.
Ai ta san in dai ba Ummie tace masa ba, ba zai taɓa kiran nata da kansa ba.
Raihana kuwa tana kwance inda su Maryam suka barta, basu daɗe da fita ba.
Wayarta ta fara ringing a hankali.
Ta ɗan motsa daga kwancen, ta miƙa hannu ta ɗago wayar, ta kalli screen din, zuwa lokacin kam ta riga ta haddace number Zayd a ranta.
Ta ɗan harari screen din, lebenta ya ɗan matse, kamar ba za ta ɗauka ba.
Saidai kuma ta sake kai hannu ta ɗauka yana gab da katsewa.
Ta ɗauka ta sa a kunneta tayi shiru.
Suhaila kuma, ganin an daga amma ba a yi magana ba, ya sa ta ɗauki wayarshi da excitement, tana shirin cire ta daga speaker.
Amma Zayd ya fincike wayar a hankali ya maida ita kan desk dinshi, yana nufin wato a yi maganar a haka yana ji.
Suhaila ta ɗan kalli Zayd, sannan ta lumshe ido ɗaya cikin amusement.
Sanin halinshi ya sa kawai ta fara magana:
“Assalamualaikum, Anty Raihana! Nice, Suhaila ce, ina kwana?”
Raihana ta jiyo muryar Suhaila tana amsawa daga ɗayan ɓangaren wayar.
Jin hakan ya sa ta ɗan gyara daga kwancen da take, ta tashi a hankali tana jingina bayanta da jikin gadon.
Fuskarta cike da wani irin sanyi, ta ɗan ja bargon jikinta ta gyara zamanta, sannan ta bude baki zata amsa, amma Suhaila ta cigaba da magana cikin sakin fuska da wani irin excitement, ganin cewa Raihana ta yi shiru bata ce komai ba:
“Ina fatan kina lafiya?
Dama wajen siyayyar lefenki ce, Ummie tace a tambaye ki sizes ɗinki da kuma abubuwan da kike so musamman underwear’s, takalmi da abubuwa masu muhimmanci, saboda kar a tafi a siyo wani abin da ba za ki so ba ko kuma wanda ba zai miki fitting ba.”
Zayd na zaune a wurin, fuskarsa ɗauke da wancan cool da nutsuwar tasa, amma idanunshi na kan screen din laptop dinshi.
Yatsunsa na ci gaba da motsawa kan keyboard kamar ba ya cikin wata tattaunawa,
sai dai duk da haka, yana sauraron abin da Raihana za ta ce, duk da cewa baya nuna hakan a fili.
Raihana ta ɗan ja numfashi, tana jin wani irin nauyin Suhaila da kuma ta san tabbas Zayd yana nan kusa da ita.
Ta ɗan haɗiye yawu, ta gyara muryarta, sannan ta ce cikin sanyi, tana ƙoƙarin danne wata fargaba da ta zo mata ba zato ba tsammani:
“Ina kwana, Suhaila… Lafiya lau, ba sai an wahala ba, komai dai wanda aka kawo zai yi.”
Suhaila ta turo baki kaɗan tana kallon Zayd, kamar wadda ta ƙi amincewa da wannan answer ɗin,
sai ta sake cewa:
“Haba Anty Raihana! Ai dole a tambaye ki, kar aje a siyo abu amma daga baya a ga bai dace da choice ɗinki ba.
Ko da yake… at least yanzu mun fara magana, zan iya tura miki hotunan wasu abubuwan ta WhatsApp sai ki zaɓi wanda kike so according to your color of preference.”
Zayd ya ɗan dakatar da yatsunsa na ɗan second a kan keyboard, sai ya ci gaba da typing, fuskarsa unchanged.
“Ba komai, Suhaila, ko wanne color ne zai yi, ba sai kin wani wahala kin zaɓa ba.”
Suhaila ta girgiza kai tana ɗan kallon Zayd, ta ɗan yi murmushi kamar wadda ta fahimci stubbornness ɗin Raihana.
Ta dage sosai akan gwara ta tura mata ta zaɓa ta WhatsApp:
“Haba Anty Raihana, dole a zaɓi wanda ya dace mana!”
Amma Raihana ta sake cewa:
“A’a, kawai na ba ki zaɓi, duk wanda ya yi miki, nima ya yi min.”
Suhaila ta saki dariyar farin ciki, ta ɗan gyada kai:
“Toh shikenan, tunda dai kin dage.
Yanzu fa sizes ɗinki na shoe da underwear’s sai abaya?”
Tana faɗar haka, jin ambaton underwear’s a gaban Zayd ya sa Raihana jin wani irin zafi yana ratsa jikinta.
Take ta yi shiru, idanunta suka buɗe kaɗan, sannan ta lumshe su cikin tsananin kunya.
Ta ɗan matse wayar da ke hannunta, zuciyarta tana bugawa da sauri.
Kamar ƙasa ta buɗe ta nutse saboda tsananin kunya, domin tasan tabbas Zayd na zaune a wajen Suhaila kuma yana jin abin da ake ta cewa!
Ta ɗan ja numfashi, ta kasa cewa komai na ɗan daƙiƙa.
Suhaila ta yi murmushi ta sake cewa:
“Toh kawai ki tura min ta SMS kin ji?”
Raihana ta ɗan buɗe baki kamar za ta amsa, amma kalmar ta makale, ta sake haɗiye yawu.
A ɓangaren Zayd kuwa, yana zaune yana ci gaba da danna laptop ɗinsa.
Idan ka gan shi zaka rantse da Allah bai ma san suna tattauna wani abu ba saboda yadda ya nuna total indifference da nutsuwa a kan aikinsa.
Sai dai ƙasan fuskarsa ya ɗan yi wani ƙaramin movement na ɗan second—kusan wanda ba za a iya ganewa ba.
Ya ci gaba da typing, calm, unbothered, as if the entire conversation meant absolutely nothing to him.
Raihana ta amsa a sanyaye, sannan suka yi sallama da Suhaila.
Suhaila ta yi wani murmushi, tana neman waje domin ta zauna ta jira Raihana ta turo mata da SMS ɗin.
Amma tana zama, Zayd ya ɗago kai ya kalleta da wani irin kallon da ya nuna a fili cewa patience ɗinsa ya fara ƙarewa.
“Me kuma ya rage? Get out, my friend.”
Suhaila ta miƙe tsaye tana turo baki, ta ɗan ɗaga hannunta sama kamar wadda take ƙoƙarin kare kanta:
“Cewa fa tayi za ta turo! Jira nake ta turo mana na ɗauka na tafi.”
Zayd ya kalleta up and down, fuskarsa completely blank, sai ya ɗan jingina bayansa da kujerar, kafin ya faɗa a cikin serious tone:
“Dismiss.”
Suhaila ta turo baki sosai, sai ta juya ta fice, tana jan ƙafafunta da ɗan ɓacin rai, ta bar masa ɗakin.
Raihana kuwa, tun da ta sauke wayar take contemplating ko za ta turo ko ta kyale.
The fact that a wayar Zayd za a turo shi ne abinda ke daga mata hankali.
Ta ɗan cije leɓenta, idanunta suka kafe a kan screen ɗin wayarta.
“Dama ina da number Suhaila,” ta faɗa a hankali, tana ɗan matse wayar a hannunta,
“ko na tambayeshi ne ya turo min?”
Sai ta girgiza kai a hankali, ta runtse idanunta na ɗan seconds,
ganin yadda duk ta dinga dragging da Suhaila, ba ta so ta sake kiranta a kan maganar.
Kawai ta runtse idanunta, ta rubuta sizes ɗinta.
Yatsunta suka tsaya a kan send button na ƴan seconds, tana kallon saƙon kamar wanda ke gab da aikata wani abu mai girma.
Kafin ta danna send, ta ja numfashi mai nauyi.
“Ya Allah…”
ji ta yi kamar wani uban mugun abu za ta aikata, zuciyarta ta soma bugawa da sauri,
ta ɗan ɗora tafin hannunta a ƙirjinta tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta.
Daga ƙarshe dai ta daure kawai ta tura.
Nan take ta ajiye wayar gefe, ta dafe ƙirjinta da hannu biyu-biyu saboda tsananin faɗuwar gaba,
ta lumshe idanunta, tana jan numfashi a hankali kamar wadda take jiran wani abu da ba ta san yadda zai kasance ba.
But somehow, the embarrassment was still there.
Jin ƙar notification ya shigo, Zayd ya ɗan dakata,
yatsunsa suka tsaya a kan keyboard.
Ya juya ya kalli wayarshi dake gefe na kusan seconds biyar, fuskarsa unchanged, kafin ya miƙa hannu ya ɗauka.
Ya buɗe SMS ɗin Raihana, ya ɗan kafe screen ɗin da idanunsa.
Ya tsaya yana duba abinda ta turo, kamar wanda aka turawa wani uban kuɗin da yake ganin ba haka ya zaci gani ba.
Girarsa ɗaya ta ɗan motsa sama, sannan ya ɗan karkatar da kansa gefe.
For a brief second, expression ɗinsa ya nuna mild.
Sai dai bai ce komai ba, ya taɓe baki a hankali, ya sake kallon message ɗin na ƴan seconds,
kafin kawai ya danna forward ya tura wa Suhaila.
Ya ajiye wayar a gefe ba tare da wata magana ba, ya koma kan laptop ɗinsa,
yatsunsa suka sake komawa kan keyboard kamar babu wani abu da ya faru,
yana ci gaba da aikinshi cikin irin waccan nutsuwar tasa ta absolute indifference.
Sai ga su Maryam sun dawo daga kasuwa misalin ƙarfe biyu na rana.
Amma ba su daɗe da shigowa gidan ba, aka aiko da sako cewa mota na jiransu a waje domin su tafi da kayan ɗakin Raihana.
Maryam ce ta leka waje, da ta fito, sai ta tadda Imran tsaye tare da Sameer.
Akwai babbar motar ɗaukar kaya da kuma wasu normal cars guda biyu a waje da za su ɗauki mutanen da za su je tare.
Ta ɗan tsaya tana kallonsu na ƴan seconds, sannan ta gaisa da su cikin fara’a:
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumussalam,” Imran ya amsa, yana mata ɗan murmushi.
Maryam ta juyo ta koma ciki, da ta shiga, ta sanar wa Umma, Mama Indo, harda Maman Ihsan waɗanda suke zaune a ɗakin Umma suna baje kayan kitchen da suka siyo ana gani.
Umma ta ɗago kai da sauri, ta kalli Maryam da ɗan murmushin tausayawa a fuskarta:
“Gashi kuma dawowarku kenan ba ku huta ba.”
Maman Ihsan ta taɓe baki da murmushi, tana ɗaga ɗaya daga cikin kayan da ke gabanta tana dubawa:
“Haba dai, wane hutu kuma?
Mu da muke da hidima a gabanmu!
Ai tunda mun yi sallah mun ci abinci, kawai tafiya za mu yi.”
Ta faɗa cikin wani irin cheerful tone, kamar ba ta ma jin gajiyar tafiyar kasuwar.
Mama Indo ta yi dariya tana girgiza kai:
“Wallahi abin da za yi kenan kam.”
Ta juya ta kalli Maryam, sannan ta ɗaga hannunta kaɗan:
“Je ki kira Maman Khausar, matar Malam Sammani ce, maƙocin Baffa wanda ya yi waƙilin auren Raihana, sai mu haɗu mu tafi gaba ɗaya.”
“Toh,” Maryam ta amsa, ta juya ta fita don kiran ta.
Umma ta kalli Maman Ihsan, ta ɗan yi murmushi:
“Ko za ki yi magana da Sabuwa itama ku je tare ko?”
Mama Indo ta ɗago kanta da sauri, ta kalli Umma cikin mamaki sosai:
“Wace Sabuwa kuma ana zaune kalau?
Haba Hajara!”
Ta faɗa tana ɗan buɗe idanunta, kamar maganar Umma ta ba ta mamaki.
Umma ta girgiza kai tana murmushi, fuskarta cike da sanyin hali:
“A’a, gwara dai a faɗa kawai, ku je gaba ɗaya ai ba wani abu bane.”
Maman Ihsan ta miƙe tsaye nan take, ta gyara mayafinta tana ɗan murmushi:
“Ko don ma ta ga abin da zai hana ta bacci, wallahi sai na kirata.”
Ta faɗa cikin wani ɗan teasing tone, kafin ta juya ta fice daga ɗakin ta nufi ɗakin Mama Sabuwa.
“Gafaran ku dai,” ta faɗa tana ɗaga labulen ɗakin.
Mama Sabuwa da Bintu dake zaune suna cin abinci suka ɗago kai lokaci guda ba tare da sun amsa ba, idanunsu suka sauka kan Maman Ihsan, suna kallonta cikin shiru.
Ita kuwa Maman Ihsan ko a jikinta, ta ɗanyi murmushi, sannan ta ce:
“Dama mijin Raihana ne ya aiko da motoci zuwa jere, shi ne na ce bari na miki magana ki fito mu tafi tare ko?”
Mama Sabuwa ta yi still, kamar an daskarar da ita a wurin,
ta kafe Maman Ihsan da idanu cike da al’ajabi, lebenta ya ɗan buɗe, sannan ta ɗan karkatar da kanta gefe kamar tana ƙoƙarin tabbatar da abin da ta ji.
Bintu ma ta bi Mama Sabuwa da kallo, tana jiran amsar da za ta fito daga bakinta.
“Yanzu za a tafi?” Mama Sabuwa ta tambaya, tana tsame hannunta daga kwanon abincin.
Maman Ihsan ta ɗan ɗaga gira, ta yi murmushi:
“Yo wane yanzu kuma?
Sabuwa, ga motoci a waje!
Ai kawai ki taso bari mu jira ki.”
Daga haka Maman Ihsan ta saki labulen ta juya, ta koma tsakar gidan.
Mama Sabuwa kuwa ta ɗan tsaya na ƴan seconds, tana kallon hanyar da Maman Ihsan ta bi da wani irin nazari.
Sai ta miƙe tsaye tana side hannunta.
Bintu ta kalleta da mamaki sosai, har ta ɗan ajiye cokalin da ke hannunta:
“Mama, wai zuwa za ki yi?”
Mama Sabuwa ba ta ma kalle ta ba, ta ɗauki hijabinta tana gyara shi a jikinta, sannan ta amsa cikin wani irin tone mai cike da takaici da ƙudirrin zuciya:
“Eh!
Da a ba ka labari gwara ka bayar, zan je naga inane gidan, da kuma wane ne wannan mijin da aka sakeni sabida an aura masa Raihana!”
Ta ƙare maganar da wani ɗan tsaki, sannan ta jawo hijabinta ta zura a kanta ba tare da wani babban kintsi ba.
Bintu ta tsaya cak, idanunta suka zaro:
“Mama…”
Amma Mama Sabuwa ba ta saurare ta ba, ta fice daga ɗakin zuwa tsakar gidan, ta bar Bintu baki buɗe hangangan tana kallonta cike da mamaki.
Bintu ta girgiza kanta a hankali, tana kallon ƙofar da Mama Sabuwa ta bi:
“Is she really going there?”
ta furta a ranta cikin rashin yarda, kafin ta sauke numfashi mai nauyi ta cigaba da cin abincinta…
Not edited