Free chapter · Read without an account

THE SECOND WING

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN



ZAYD ARMAAN 

CHAPTER SIXTY FIVE:65

THE SECOND WING

JIDDAAH BARKUM

————
Haka suka ɗauki hanya; Mama Indo, Mama Sabuwa, Maman Ihsan, Maman Khausar, da Khausar ɗin kanta—dama can kawar Ray ce, kawai dai bata cika zama a Malali ba, ta fi zama a gidan kakarta. Sai kuma Amara, ƙirjin biki, Hajiya Merry. Duk suka dunguma aka ɗeɓi rankataf kayan Raihana, komai da komai, zuwa gidanta.
Bayan tafiyarsu ne Umma ta ji shiru, domin dama tunda suka dawo daga kasuwa, Raihana ko labulen ɗakinta bata taɓa ba, bare kuma ta leƙo ta ga wani abu a cikin abin da aka siya. Tana kwance, dan ita jin ana ta hidima ma ƙara mata rashin jin daɗin jikinta yayi. Da kuwa ta ji Maryam na cewa an zo kwasar kaya, wallahi karkarwa jikinta ya fara take a wajen, wani uban zazzabi yayi mata rubdugu!
Ta ɗan ja bargon jikinta sama, jikinta na rawa kaɗan, sannan ta lumshe idanunta da ƙarfi.
Umma ta shiga ɗakin da sallama, ta sameta a wannan halin. Ita kam ta rasa wacce kala ce Raihana, kamar akanta aka fara aure ba shiri, sai kace ba itace ta kawo mijin ba! Ta ɗan tsaya a bakin ƙofa tana kallonta na ƴan seconds, fuskarta cike da mamaki da damuwa. Sanin idan ta biye mata da tambayar me ya faru zata lafke mata ne, kila ma har da kuka ya sanya, bata tsaya tambayar abinda ya faru ba. Strictly ta kalleta:
“Kina ta kwance kamar ruwa, ki tashi ki nemi abinci ki ci, kuma ki fara haɗe kayanki waje ɗaya! Kina sane da cewa gobe ne zaki bar gidan nan, amma kina wani abu kamar wata yarinyar goye? Ki tashi yanzu ki biyoni kizo ki samu wani abu ki ci, haba, na gaji da ganinki a haka wallahi!”
Ta ƙare maganar tana ɗan girgiza kai, kamar patience ɗinta ya kusa ƙarewa.
Daga nan Umma ta juya ta fice.
Raihana ta tashi ta zauna akan gadon, ta harde ƙafafunta sannan ta ɗora kanta aka gwiwar ta, ta fashe da kuka:
“Kina ina wai?!”
Muryar Umma ta sauka a kunneta.
Da sauri ta miƙe tana share hawayenta da bayan hannunta, sannan ta gyara hular kanta ta fito. Ta ɗan ja numfashi kafin ta zauna a inda Umma ta ajiye mata abincin favorite ɗinta ne rice and stew amma wallahi ko san kallon abincin bata yi.
Ta kalle shi na ƴan seconds, ta ɗauki spoon ɗin, sannan ta sauke idanunta ƙasa.
Haka nan ta haƙura ta sa spoon ta fara cakala kamar wata mai ciwon hannu.
Sai ta ɗauki ɗan abin kaɗan, ta kai bakinta, amma ko kaɗan bata ji wani appetite ba.
“Yaa Allah…” ta furta a ranta, tana jin ƙirjinta ya na ƙara nauyi.
Suna zaune a falon Umma, suka ji sallama daga tsakar gida.
Umma ta miƙe ta isa tsakar gidan, nan da nan ta washe baki, fuskarta ta haska da excitement:
“Sannunku da zuwa!”
Muryarta ɗauke da farin ciki.
“Yauwa, sannunku. Ba kowa a gidan ne muna ta sallama.”
Umma ta karasa ta karɓi jakar Inna Salamatu, mahaifiyar Baffa.
“Muna ciki, wallahi ban ji sallama ba ne. Ku karaso!”
Inna da sauran matan kusan su huɗu suma suka jibge uban buhunhuna da suka zo da shi a gefe, sannan suka bi bayan Umma da Inna zuwa ɗakin Umma.
Umma ta ajiye jakar Inna a gefe, sannan ta karasa gaban Inna wacce tayi wa kanta masauki a kan kujera.
Umma ta fara gaisheta:
“Ina yini, Inna? Ya hanya?”
Inna ta ɗan kalleta, idanunta suna komawa kan Raihana:
“Lafiya kalau Hajara, ya hidima? Kuma ashe haka biki yazo ba shiri!”
Umma ta ɗan yi murmushi, ta gyara zamanta:
“Wallahi Inna, haka Allah ya kawo abun.”
Sai kuma ta miƙe:
“Bari na kawo miki ruwa da abinci.”
Bata jira amsa ba, ta juya da sauri zuwa tsakar gida.
Raihana ta ɗago kanta ta kalli Inna wacce itama kallonta take, tana jiran taga Raihana za ta gaisheta ne ko jira take ita ta fara gaida ta.
Raihana ta ɗan haɗiye yawu, ta gyara zamanta, sannan ta ce a hankali:
“Ina yini, Inna?”
Muryarta ta fito a hankali. Bata jira Inna ta amsa ba, ta juya wajen sauran matan, duk ta gaishe su.
Su kam suka amsa mata a sake.
Inna kam kallon Raihana kawai take, kamar ma ta ga ta rame mata a ido. Ta ɗan karkatar da kanta gefe, tana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, kafin ta ce:
“Ita Raihana mai ƙaudin bala’i, itace wannan kamar an zubawa fulawa ruwa? Ke, ko auren dole ubanki ya shirya miki ne?”
Raihana ta ɗago ta kalli Inna.
Fuskarta ta ɗan canza, idanunta suka nuna irritation, amma ta daure ta yi shiru.
A daidai lokacin Umma ta shigo, ta ajiyewa Inna abinci da ruwa, sannan ta ajiyewa matan da suka zo tare ma.
Inna ta kalli Umma:
“Hajara, ba dai auren dole ku ka yi wa yarinyar nan ba? Shi yasa kuka tashi da aure gaggagaga, ayi a gama kafin mutane su ankara.”
Umma ta kalli Raihana, sannan ta kalli Inna tana zama a gefe. Cikin ladabi Umma ta fara magana:
“Auren dole kuma, Inna? Wallahi ba auren dole bane, itace da kanta ta kawo shi tace ta amince ya turo.”
Inna ta katse Umma nan take, ta ɗaga hannu kamar ba ta son ƙarin bayani:
“Wallahi ban yarda ba! Toh, tana son auren tayi wannan mahaukaciyar rama? Fuskarta sai idanuwa kamar an jijjiga bera a buța! Ke, Raihana! Wannan irin aure ne akayi miki? Kin tabbatar kina son shi?”
Raihana ta yi shiru.
Kirjinta na bugawa da ƙarfi, lips ɗinta suka ɗan matse. Ta ɗan kalli Inna, sannan idanunta suka sauka ƙasa.
Umma kam ta zuba mata idanu.
Haka Inna ma.
Raihana ta ji kamar idan ta buɗe baki yanzu, hawayen da take ƙoƙarin riƙewa za su sake zubo mata.
Inna ta zabga wani salati kamar irin wani mugun abu ya faru:
“Wallahi daga ganin yarinyar nan bata son auren nan! Mu dake dama can irin auren da aka mana kenan, sai dai idan an kai ka ka ga mijin shiyasa nan da nan na gane halin da yarinyar nan take ciki. Toh wallahi bata saɓuwa, bari uban nata yazo! Tunda ba tarewa tayi ba, wallahi gwara ya sallame ta tun wuri. Yo, a gidan ubanta ma tayi wannan ramar sabida tunanin aurensa, inaga an kaita can gidanta?”
Umma dai tayi shiru ta kasa magana, dan ta san tunda Inna ta fara maganar nan, toh sai kuma ta Allah.
Raihana kamar wacce aka shaƙe ta kalli Inna. Fuskarta ba yabo ba fallasa, ta ɗan dafe gefen kujerar da take zaune, sannan ta ce:
“Ni ce miki nayi bana son sa? Daga kin zo kin tarar na tashi a bacci, sai kice wai auren dole akayi min?”
Muryarta ta ɗan yi rawa a ƙarshen maganar.
Umma ta kalli Raihana wacce ta ɗauke kanta taƙi kallon Umma.
Inna ta saki baki:
“Kan ubancan! Ni zaki mayar wata yar iska bayan uwarki naga ta kūreki da kallo? Yo, wa ya sani ko wata inkiya tayi miki taku ta can yan Niger ki nuna min kina so? Ke kuwa ga jarababbiya tazo! Wallahi karya kike, kowa ya kalleki ya san auren nan ba son shi kike ba!”
Raihana ta ɗan rufe idanunta, ta ja wani numfashi mai ƙarfi tana ƙoƙarin ganin baya fashe da kuka ba.
Sai ta miƙe—dama so take ta bar wajen, wallahi tunda axu ba son cin abincin take ba. Ta ɗan harari Inna ta gefen ido jin tace wai halinsu na yan Niger, fuskarta ta ɗan nuna wani irin disbelief.
Sai ta ɗan girgiza kai, ta share gefen idonta da sauri kafin tace:
“Toh wallahi ni dai ina son shi, ki barni kuma ki barmin Ummataa!”
Muryarta ta fito da ƙarfi fiye da yadda ta saba, kamar wadda ta gama gajiya da kare kanta.
Kafin Umma ta buɗe baki zatayi magana, Raihana har ta shige ɗakinta.
Umma ta kalli hanyar da ta bi, ta sauke numfashi mai nauyi.
Inna kuwa ta zauna tana kallon Umma, sannan ta ɗan girgiza kai.
“Hmm… yanzu kin ji?”
Umma bata amsa ba.
Ta ɗan ɗora tafin hannunta a gwiwarta, tana kallon ƙofar ɗakin Raihana cikin shiru.
A ranta kuwa, abu ɗaya ne kawai yake ta maimaituwa: Something is definitely wrong with this girl.
Masu jere kuwa kai tsaye aka nufi rantsattsiyar unguwar da gidan Ray yake.
Tun daga kwaltar da zata kai mutum zuwa gate ɗin estate ɗin, Mama Sabuwa ke haɗiye yawu da ƙyar, saboda wani azababben kullutu da ya tokare mata maƙoshi. Idanunta kuwa sai zarewa take, tana kallon wajen ta tagar motar kamar wadda aka kai ta wani sabon duniya.
A hankali motar ta ƙara kusantar gate ɗin estate ɗin.
Sai Mama Sabuwa ta ɗan gyara zamanta.
Ta ɗan leƙa gaba.
Sai kuma idanunta suka tsaya cak.
Ashe a bakin gate ɗin shiga estate ɗin ma akwai wani security post mai girma, inda security officers suke tsaye suna duba mutanen da suka shigo da kuma motocin da suke ciki kafin a bar su su wuce.
Motar da suke ciki ta tsaya.
Ɗaya daga cikin security ɗin ya ƙaraso cikin ladabi, ya yi magana da direban, sannan ya duba motar da mutanen da ke ciki. Bayan an tabbatar da komai, aka basu damar wucewa.
Mama Sabuwa ta haɗiye yawu.
“Tabdi…”
Ta furta a hankali, idanuwanta har yanzu suna yawo.
Wannan ba irin estate ɗin da take zato bane.
Bayan sun wuce security post ɗin, sai motar ta ci gaba da tafiya a cikin estate ɗin.
Komai ya kasance neatly arranged.
Manyan gidaje masu tsayi suna jere cikin natsuwa, kowanne da irin tsarin architecture ɗinsa na musamman. Titunan suna da faɗi, tsafta ta ko’ina, lawns ɗin gidaje suna kore kamar an shafe su da paint, yayin da manyan bishiyoyi da flowers aka tsara su cikin perfect symmetry.
Amma ba su daɗe da tafiya ba, sai motarsu ta yi horn a gaban wani uban sun gate!
Sai Mama Sabuwa ta sake zare ido take.
Ta ɗaga kanta sama tana kallonsa.
Wallahi za a rantse da Allah ba da hannu aka ƙera shi ba saboda irin girma da tsayin da yake da shi.
Babban gate ne mai tsayi, an yi shi da thick metallic panels masu tsari na zamani, yana da wani irin dark luxury finish wanda hasken rana ke ɗan bugawa ya ba shi classy shine. Gefensa kuma akwai manyan stone pillars guda biyu, kowannensu an gina shi da duwatsun ado masu tsada, suna ɗauke da fitilun da aka saka a ciki cikin salon da yake nuna modern luxury.
A saman bangaren gate ɗin kuwa akwai cameras da security lights da suke kallon ko’ina.
Ba gate kawai bane. It looked more like the entrance to a private mansion than an ordinary house.
Mama Sabuwa ta yi shiru.
Bakinta ya ɗan buɗe.
Maman Ihsan wadda ke zaune gefenta kuwa sai murmushi take yi, musamman da ta ga yadda Mama Sabuwa ta kasa ɓoye reaction ɗinta.
Ta ɗan juyo ta kalle ta.
Amma ba ta ce komai ba.
Kawai murmushin ta ƙara faɗaɗa.
Sameer ya danna horn ɗin motar sau biyu.
Sai security ɗin dake bakin gate ya fito.
Da ya ga wanda yake cikin motar Sameer ne ya san shi sai ya juya bayan ɗan lokaci sai aka fara buɗe gate ɗin a hankali.
A hankali…
Harabar gidan ta fara bayyana a idanunsu.
Mama Sabuwa ta saki baki.
Ba ita kaɗai ba.
Maryam ma ta ɗan matsa kanta gaba tana kallon wajen.
Maman Ihsan kuwa murmushin da ke fuskarta ya ƙara bayyana.
Gidan ya kasance babban luxury mansion wanda aka gina shi cikin wani irin sophisticated architectural design.
Ba gida ɗaya ne kawai a compound ɗin ba.
Akwai manyan parts guda biyu na gidan.
Bangaren farko yana da babban façade mai hawa biyu, manyan glass windows masu tsawo daga ƙasa har sama, da manyan balcony railings masu kyau. An yi front ɗin gidan da haɗin smooth cream stone da dark wood finishing, wanda ya ba gidan wani irin expensive, timeless look.
A gabansa akwai babban lawn mai faɗi, cike da flowers da aka tsara cikin neat lines. A tsakiyar lawn ɗin akwai wani ƙaramin fountain mai kyau, ruwan yana fitowa a hankali yana komawa cikin wani zagayen basin da aka kewaye da white stones.
A gefen gidan kuma akwai dogayen palm trees da wasu ornamental trees waɗanda suka ƙara wa harabar gidan girma da class.
Hasken rana yana bugawa a jikin manyan glass ɗin, yana sa gidan ya yi wani irin haske mai nutsuwa.
Akwai kuma security cameras kusan a dukkan strategic corners, yayin da wani ƙaramin security post yake kusa da babban entrance ɗin gidan.
Amma abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda gidan yake da parts biyu.
Ɗayan bangaren gidan yana da ƙofar da aka kulle sosai.
An rufe entrance ɗin da babban wooden door mai kauri, wanda daga yadda aka tsara shi za ka rantse cewa akwai mutane a ciki—kamar wani separate wing ne na gidan da ba kowa ke shiga ba.
A ɗayan bangaren kuwa, ƙofar tana rufe, amma an shirya wajen da kyau sosai. Akwai pathway da aka yi da marble-like stones daga lawn har zuwa entrance ɗin, tare da manyan flower pots a gefe-gefe.
Mama Sabuwa ta ɗan ɗaga gira.
Idanunta suka fara yawo daga wannan bangaren zuwa wancan.
“Dankariii…”
Ta furta a hankali, kusan ba tare da ta san ta faɗa ba.
Maman Ihsan ta ji, sai ta ɗan yi murmushi.
Maryam kuma ta kasa riƙe murmushinta.
“Wow…”
Ta furta a hankali, tana kallon gidan kamar wadda aka kai ta wani five-star hotel.
Sameer ya shigar da motar cikin harabar gidan.
Sai Mama Sabuwa ta ƙara juyar da kanta.
Gidan yana da wani irin quietness wanda ya bambanta da girman sa. Babu hayaniya, babu tarin mutane, babu wani abu da ke nuna gidan yana cike da jama’a amma komai yana nuna cewa akwai security da proper management a ko’ina.
Sameer ya ci gaba da driving a hankali har suka isa wajen da aka tanadar da parking.
Sai ya juya motar zuwa wani bangare na gidan—part ɗin da ƙofar ke kulle. Ya tsaya, ya danna birki, ya yi parking a hankali.
A bayan motar kuwa, sauran motocin suka shigo ɗaya bayan ɗaya, suka tsaya a bayansu.
Mama Sabuwa kuwa har yanzu tana zaune cikin motar.
Bakinta a ɗan buɗe.
Idanunta a kan gidan.
Kamar wadda har yanzu take trying to process what she had just seen.
Maman Ihsan ta ɗan kalle ta daga gefen ido.
Murmushi kawai ta yi.
Ba ta ce komai ba.
Domin reaction ɗin Mama Sabuwa ya riga ya faɗi komai.
A ranta kuwa, abu ɗaya kawai ke ta maimaituwa: “Wannan ne gidan Raihana?”
Ta sake haɗiye yawu. This was definitely not what she had expected.
Kuma a karon farko tun da suka bar Malali, Mama Sabuwa ta rasa abin da za ta ce.
Sameer ya yi musu jagoranci har zuwa inda bangaren Raihana yake. Bangaren ma wani part daban ne a cikinshi mai zaman kansa wanda aka ware shi daban da sauran sassan gidan.
Ya tsaya a bakin ƙofar, sannan ya nuna musu wajen: “A nan za a saka kayan.”
Suka shiga.
Kowa na baza idanu, yana bawa idonshi abinci, domin wajen gaba ɗaya ya yi musu wani irin sabon salo.
Mama Sabuwa kuwa wallahi kawai binsu take da kallo. Tun shigowarta take kallon komai da wani irin yanayi na disbelief, amma wallahi zuwa yanzu ita sam bata gane komai.
Ta ɗan juyo tana kallon bangaren da aka kawo su, sannan ta sake kallon Sameer da sauran mazan da suke ta motsi.
Da gaske dai wannan uban bangaren duk na Raihana ne?
Ta furta a ranta, tana ɗan matse leɓenta.
Sauran drivers ɗin suka fita, suka sake shigowa da kayayyakin da suka zo da su. Wasu suka ɗauko cartons, wasu suka ɗauko kayan furniture, wasu kuma suka riƙe abubuwan da aka tanada don aikin.
Mama Indo da Maman Ihsan sai Maman Khausar suka zage, suka fara aiki.
Ɗaya na buɗe cartons, ɗaya na ɗaukar kaya, ɗaya na tsara su yadda ya kamata.
Maryam da Khausar kuwa suna kitchen, suna gyara abubuwan can da aka siya, suna ware kayan kitchen ɗin ɗaya bayan ɗaya.
Maryam ta ɗaga wani abu tana kallon Khausar: “Wannan fa ina za mu ajiye shi?”
Khausar ta nuna mata gefe: “Ki sa shi can, daga baya sai mu tsara komai properly.”
“Toh.” Ta juya ta ci gaba da aikinta.
Mama Sabuwa kuwa ita kam ta tsaya gefe.
Hannunta ɗaya a haɗe da ɗayan, idanunta sai yawo suke yi.
Ta kalli Mama Indo dake kokawa da mirror ita da Maman Khausar, tana ƙoƙarin ganin inda ya fi dacewa a ajiye shi. Ta taɓe baki sosai, ta ɗan ɗaga gira, sannan ta fara magana cikin wani irin yanayi na raini: “Gida dai har gidaaaa…”
Ta ja maganar, tana kallon wajen. “Amma wallahi ni duk sai kunya ta kamani ma da naga kalar wulakantattun kayan da ubanta ya yi mata! Wannan wanne irin kaya ne? Ai inaga ko mai gadin gidan bai kamata ace wannan sune kayan ɗakinsa ba, bare kuma matar gidan!”
Ta yi kwafa, ta sake kallon kayan da aka jere. “Kuma gashi harda kishiya ce gareta ko?”
Mama Indo ta tsaya cak.
Ta ɗago kanta a hankali, sannan ta juyo ta kalli Mama Sabuwa cike da bala’i. “Ke Sabuwa!”
Muryarta ta fito da ƙarfi. “Ja gefe! Bakincikinki ne ya motsa shine zaki mana hauka a nan?”
Mama Sabuwa ta jefa mata wani mugun kallo ta buɗe baki zata mayar mata, amma Mama Indo ba ta bata damar shiga ba. “Toh Billahillazi Lailaha illahuwa, zamu ba da ke yanzun nan a maida ke! Dama uwarme kika haɗa da Raihana da zaki kwaso kafa kizo?”
Ta ɗan matsa gaba, tana nuna mata yatsa. “Banda baki da zuciya, caa nake ubanta kike aure kuma ya sawwake miki tun tuni! Ke, idan mai hankali ce ma, da aka cike kizo ka zo, toh wallahi tallahi ki iya bakinki!”
Fuskarta ta cika da tsananin fushi. “Dan ni na jibge mace a nan ba wani abu bane! Bar ganin da ina kyale ki. Wallahi yanzu kika min wani shirme, wallahi jikin mata ne zai faɗa mata, dan ni babu ruwana da girmanta!”
Mama Sabuwa ta zabura.
Ta karaso gaban Mama Indo da sauri, kamar wadda aka watsawa wuta a fuska. Ta tako gaba tana shirin mayar da martani. “Ke—”
Maman Ihsan ta yi tsalle ta shiga tsakaninsu nan take. “A’a! Wallahi mu nan farin ciki muke! Babu wanda zai bata mana sabga yau.”
Ta ɗaga hannayenta biyu, tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya. “Yauwa, me haka?”
Sai ta juya wajen Mama Sabuwa. “Kinga Sabuwa. Idan kinsan bala’i ne ya sa kika biyo mu, toh wallahi kawai ki koma. An ce dama kizo ne dan a fita haƙkin zaman tare ne. Ban ga dalilin da zaki dinga watsa mana zantuka marasa daɗi ba.”
Ta ɗan sauke numfashi, sannan ta ci gaba da kallonta. “A dai daure a dinga boye halin da zuciya take ciki, dan Allah. Meye wani ‘wulakantattun kaya’?”
Ta nuna kayan da aka jera. “Iya ƙarfin ubanta kenan! Kuma wallahi kayan nan na Raihana babu gidan uban da ba za a kai su ba.”
Ta juyo da sauri wajen Mama Indo: “Yauwa Maman Maryam, ɗauko zannuwan gadon a shinfida.”
Mama Indo kuwa ta sake kallon Mama Sabuwa na ɗan second, sannan ta juya ta ɗauki zannuwan.
Maman Ihsan ta sauke numfashi, ta kalli Mama Sabuwa na ƴan seconds. “Mu dai mun zo ne don farin ciki. Please, karki bata mana mood.”
Daga nan ta koma wajen kayan, ta ci gaba da abinda ke gabanta.
Mama Sabuwa ta tsaya a wurin, tana kallon bayan Mama Indo da wani irin haushi. Ta yi kwafa. “Hmm!”
Sai ta juya kanta gefe.
Kamar ba ta gama jin haushin abin ba, ta fara hura hanci, tana ta wani girgize-girgize da kai, jikinta na motsawa kamar wadda take gab da kai duka.
Khausar ta ɗan kalli Maryam wanda hayaniya ta fito da su daga kitchen.
Maryam ma ta kalleta. Suka yi shiru. Kawai sai suka juya suka ci gaba da aikinsu.
Domin sun san Mama Sabuwa ba ta zo ne da zuciyar yin farin ciki ba, ta zo ne da abin da ke ƙuna a cikin zuciyarta tun kafin su bar gida.
Mai saka curtains ma ya zo ya saka a duk inda ya kamata windows da sauran wajaje da ake buƙatar a gyara, ya gama komai cikin tsari sannan ya tattara kayansa ya tafi.
Ba a jima ba, Sameer ya dawo ɗauke da manyan warmers na abinci, juice, sai bottled water. Akwai varieties daban-daban na abinci, fried rice, fried spaghetti wanda ta sha kayan lambu, sai fried chicken.
Maryam ta ƙarasa ta karɓa tana murmushi. “Thank you.”
Ta koma ciki ta ajiye musu .
Ba tare da wani kunya ko wata magana ba.
Mama Sabuwa, da ta ga abincin, sai ta ɗauki plate ta shake shi dam-dam da abinci da kaji. Ta zauna ta fara ci, tana kora abincin da chilled juice abinta.
Babu wanda ya ce mata kala. Kowa ya ci abincinsa a nutse, kowanne yana mayar da hankalinsa kan abinda ke gabansa.
Daga ƙarshe, suka ƙarasa sauran abubuwan da suka rage. Gidan ya fito fesss tasss, an gama shirya shi tsaf domin amarya.
Gaskiya Baffa ya yi ƙoƙari wajen siyawa Raihana kayan da suka dace da ita. Komai ya kasance cikin tsari da kyau, har babu wani abu da zai sa mai hankali ya samu abin kushewa.
Akwai babban plasma TV, fridge mai ɗan girma, kayan ɗaki masu kyau, da sauran muhimman abubuwan da amarya za ta buƙata. Komai ya yi sosai.
Sai dai kamar yadda ake cewa, ba kowa ke ganin alheri da ido ɗaya ba.
Wasu suka dinga kallon gidan da mamaki—kamar dai Mama Sabuwa—wasu kuma suka yi shiru suna jin daɗin yadda komai ya kasance.
Daga ƙarshe, sai aka dinga cewa: “Allah ya sa albarka.” “Allah ya bada zaman lafiya.” “Allah ya sanya alheri a cikin auren.”
Basu fito daga compound ɗin da shirin tafiya ba sai gab da Magariba.
A lokacin kuwa, ɗayan part ɗin dake kallon na Raihana ya cika da uban music da hayaniya. Sautin kiɗan yana tashi har zuwa inda suke, yana sa mutum ya san cewa can ma ana wani shiri na musamman.
Maman Ihsan ta kasa haƙuri. Ta kalli wani yaro daga cikin ma’aikatan gidan, wanda yake yin alwala a gefe. “Sannu fa.”
Yaron ya ɗago kansa ya kalleta. “Yauwa. Ina yini?” “Lafiya kalau,” ta amsa da ɗan murmushi, sannan ta ɗan nuna masa ɗayan part ɗin da hannunta. “Ahm… dan Allah, me ake can ne?”
Yaron ya ɗan bi hannunta da kallo kafin ya dawo da kallonsa kanta. “Bangaren ɗayar matar ne. Suna jere ne su ma, saboda jibi ne ɗaurin aurensu.”
Maman Ihsan ta ɗan yi shiru. Sai ta jinjina kai a hankali. “Toh, nagode.” “Babu komai,” ya amsa.
Daga haka ta juya, tana ɗan kallon bangaren Seeyama na ƴan seconds. Ta sauke numfashi a hankali, sannan ta nufi motar da ta zama ta mayar da su.
Motocin da suka zo da su suka fara tashi ɗaya bayan ɗaya. A haka suka fice daga gidan a hankali, suna barin gidan cikin wani irin yanayi mai cike da shiri da hayaniya kafin dare ya rufe komai.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.