Free chapter · Read without an account
A NEW CHAPTER BEGINS
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER SIXTY EIGHT:68*
A NEW CHAPTER BEGINS
*JIDDAAH BARKUM*
————-
Motar ta fara barin layin su Baffa a hankali, tana zamewa cikin wani irin salo mai cike da tsari da kasaita, tana ninkaya a kan shimfiɗaddiyar kwalta ta birnin Kaduna.
A cikin motar, kukan Raihana ya dawo sabo, wani irin sanyi da fargaba suka mamaye zuciyarta. Maman Ihsan ta ɗan jawo ta jikinta a hankali, tana shafa bayanta cikin wani irin tausar zuciya mai cike da sanyi da kuma kulawa ta musamman, tana goge mata hawayen da ke ci gaba da ambaliya a kan kumatunta.
Raihana ta ƙara matsawa jikinta, tana ɓoye fuskarta cikin lafayyar da aka naɗa mata. Kafadunta suna rawa a hankali duk lokacin da wani sabon kuka ya taso mata.
Amarya rayy fa bata da wani baki a yanzu da ya wuce kuka da kuma ƴa nodding masu nuna saƙon da zuciyarta ke aika mata a duk lokacin da akayi wata magana.
Maman Ihsan ta ɗan sunkuya kusa da ita,
“Shhh… ki yi haƙuri, my dear.”
Raihana ta yi ƙaramin nodding ba tare da ta ɗago kanta ba.
Maman Khausar da ke kusa da su ta kalleta da tausayi, sannan ta miƙa hannu ta ɗan gyara mata lafayyar da ta fara zamewa daga kafadarta,
“Ki daure, Raihana.”
Raihana ta sake nodding.
Bayan wani ɗan lokaci na tafiya, motocin suka karkata suka shiga babban layin da zai sada su da Arman Mansion.
Tun kafin ma motar ta tsaya cak, gidan ya nuna alamar cewa an yi shiri na musamman don tarbar sarauniyar da ke shigowa.
Girmamawa da nuna isa na gaske suka fara bayyana.
Manyan fitilu sun haskaka harabar gidan.
Kafin ma su ɗora ƙafunsu a ƙasa, Inno, Ummie, da sauran sisters ɗin Ummie sun riga sun fito harabar gidan don tarbar su da mutuntawa mai girma.
Maman Khausar ta buɗe ƙofar motar ta sauko, tana kokarin taimakawa Raihana ma ta sauko.
Ummie ta matso da sauri, fuskarta cike da wani irin farin ciki da annushuwa.
Ta kamo hannun Raihana a hankali cike da wani irin so da kulawa, ta fito da ita a hankali daga cikin motar, sannan ta rungume ta tsam a ƙirjinta.
“Welcome, my daughter…” Ummie ta faɗa da wani irin farin ciki wanda ya kasa ɓoyuwa a fuskarta.
Raihana kuwa, duk da zafin kukan da ke maƙogwaronta, sai ta yi nodding kawai a hankali, tana mai jin yadda kuka ke son ƙara kubce mata.
Ummie ta shafa bayanta a hankali,
“Shhh… you’re welcome.”
Raihana ta lumshe idanunta, wani sabon hawaye ya zubo mata.
Ba ta iya cewa komai ba.
Nan take Inno da Ummie suka kalli ɓangaren da Baffa da Malam Sammani ke zaune a cikin mota, suka fara ƙoƙarin nuna musu lallai dole ne shi da Malam Sammani su shigo ciki su huta.
Amma Baffa ya girgiza kai yana murmushi,
“A’a, Hajiya, ba komai, za mu juya ne tunda dare ya fara yi…”
ya faɗa cikin nutsuwa, yana gyara zaman sa, kamar wanda baya son ya wahalar da su.
Kafin ma Baffa ya rufe bakinsa, Inna ta yi saurin matsowa gefe tana gyara zaninta,
“A’a wallahi, shiga zamuyi! Ya za a yi mu kawo ɗan mutum guda, ka ce ba za mu shiga ba? Kai da Sammani dai ku tafi, amma mu kam za mu shiga, bayan ga uban motoci a gidan nan, nasan ba a rasa wanda zai mayar da mu gida ba!”
ta faɗa tana mai kama hannun Maryam da ƙarfi.
Maryam ta yi wata ƙaramar dariya, tana kallon Inna.
Baffa kuwa ya ɗan tsaya cak, ya kalli Inna, sai ya kalli Malam Sammani.
Wani ɗan murmushi ya bayyana a gefen bakinsa, mai kama da yake, amma a fuskarsa ana iya ganin yadda maganar Inna ta ɗan ba shi kunya.
Malam Sammani ya lura da hakan, sai ya sunkuyar da kansa yana ɓoye murmushi.
Ummie ta danyi yar dariya tana kallon Baffa,
“Hakane ai, ba komai, ku je kawai Malam, za a kawo su.”
Baffa ya ɗan girgiza kansa a hankali, ya san dai babu yadda zai yi da Inna.
Ya sauke numfashi sannan ya ce,
“To ba komai, bari mu jirasu a mota su gama, sai mu juya.”
Inna ta yi murmushi cikin nasara,
“Shi kenan.”
Ta ja Maryam kusa da ita.
Haka suka juya suka nufi cikin babban lounge ɗin mai cike da zubi da tsari na alfarma.
Inno ta karɓi hannun Raihana daga hannun Ummie, ta ja ta har zuwa kan wata sassauƙa kuma lafiyayyar sofa ta zaunar da ita a hankali.
Raihana ta zauna cikin nutsuwa, kanta a ƙasa, hannayenta a kan cinyarta.
Zuwa yanzu, sautin kukanta ya tsaya, sai dai ajiyar zuciya da take saukewa lokaci-lokaci, yayin da idanunta suka yi jazir saboda kuka.
Inno ta zauna kusa da ita, ta ɗan kalleta na ƴan seconds, sannan ta shafa mata kafada a hankali,
“Easy, my dear.”
Raihana ba ta ɗago kanta ba, sai kawai ta yi ƙaramin nodding.
Kowa ya samu wuri ya zauna, inda aka fara gaishe-gaishe cikin walwala, ƙananan dariya da hirarraki, na dan tashi kadan, amma duk da haka hankalin Ummie yana yawan komawa wajen Raihana.
Ba ta daina kallonta ba.
Ba a daɗe ba, Kubura da sauran maids suka fito ɗauke da manyan trays na abinci da kayan zaki kala-kala, suka jera a kan Centre table ɗin dake tsakiyar falon.
Ƙamshin abincin ya cika falon.
Inno ta kalli su Maman Ihsan da sauran mutanen da suka kawo Raihana tana cewa,
“Ku sauko ku ci wani abu mana! Don Allah ku ci ko kaɗan ne.”
ta faɗa tana murmushi, sannan ta nuna musu kayan da aka jera.
Maman Ihsan ta yi ƴar ƙaramar dariya, tana girgiza kai,
“Wallahi Kaka mun ƙoshi, ai daga gida ma muke kuma mun ci abinci, kuma gaskiya tafiya ma za mu yi, su Baffa na jira kar mu bata lokaci. Allah ya basu zaman lafiya.”
Ummie, wadda tun da aka zauna hankalinta ke kan Raihana tana kallonta da wani irin murmushi a fuskarta, ta juyo wajen Maman Ihsan.
Har yanzu murmushin bai gushe ba a fuskarta,
“Haba, ya za ku zo ku tafi ba ku ci komai ba?” Ummie ta faɗa cikin sigar lallami,
“Don Allah ku ci ko kaɗan ne, wallahi ba za mu ji daɗin hakan ba.”
Inna ta yi dariya,
“Wallahi ba komai, Hajiya, ai yanzu an zama ɗaya, babu wani bako a tsakaninmu.”
Daga nan Inna ta juya tana kallon Inno,
“To Hajiya ga jikata, mun kawo ta amana gidan naku,”
muryarta ta ɗan yi sanyi,
“Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a masu tarin albarka. Allah ya haɗa kanta da mijinta da kuma abokiyar zamanta.”
ta ɗan kalli Raihana,
“Don Allah idan tayi wani abu ba dai-dai ba, a tsawatar mata, duk da dai Raihana ba ta da matsala.”
Inna ta ɗan yi murmushi,
“A duk jikokina, wallahi babu ruwanta da lamarin duniya, ita ba mai zafi bace.”
Ummie ta yi murmushi tana kallon Raihana, Inno ma ta kalleta, kafin kallonta ya dawo kan Inna,
“Karki ji komai Hajiya, ki dauka yarinyar nan na gabanku ne, In Shaa Allah zamu kula da ita iyakar iyawarmu, Allah dai ya basu zaman lafiya.”
“Amin, Amin,” kowa dake wajen ya amsa.
Sai Inna ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta,
“To, ku tashi mu tafi mana.”
Ummie ta miƙe da sauri, tana nuna disapproval,
“Don Allah Hajiya, ku zauna mana!”
Inna ta yi dariya,
“To ai Baffa yana jira.”
“Toh, bari a yi packaging kayan sai ku tafi da su gaba ɗaya,” Ummie ta faɗa tana kiran Kubura.
Nan da nan aka haɗe komai cikin kulawa ta musamman.
Kubura da sauran maids suka fara tattara kayan cikin trays da bags masu kyau, suna tabbatar da komai yayi dai dai.
Amma a dai-dai lokacin da Raihana, wadda ke zaune kanta a ƙasa, ta ji ana shirin tafiya da gaske, sai tsoro da kaɗaici suka lulluɓe ta.
Ta ɗago hannunta da sauri, ta riƙe hannun Inna sosai, kamar ba ta son ta tafi.
Sai ta saki wani sabon kuka mai tsuma zuciya.
Inna ta dakata, nan take ta juya gare ta, ta rusuna ta rungume ta tsam a jikinta tana lallashinta,
“Ki yi haƙuri, Raihana, girman kenan, kin ji ko?”
ta shafa kanta a hankali,
“Kowacce mace da haka ta fara rayuwarta, ke dai ki bi mijinki, ki yi haƙuri, kuma ki girmama kowa, zaki ga ribar hakan.”
ta sumbaci goshinta,
“Allah ya baku zaman lafiya.”
Raihana ta ƙara fashewa da kuka.
Maryam kam tuni ta fara kuka itama, ta matso da sauri ta rungume Raihana sosai,
“Rayy I will miss you…”
muryarta ta karye saboda kuka.
Raihana ta rungumeta da ƙarfi, kamar ba za ta sake ta ba.
Inna ta shafa bayansu,
“Ku yi haƙuri, kema saura ke…”
sannan a hankali ta janye Maryam.
Maryam ta share hawayenta da bayan hannunta, tana ci gaba da kallon Raihana da jajayen idanu.
Inna ta cigaba da rarrashin Raihana, tana shafa kanta kafin ta sake ta a hankali.
Ummie da sauran mutanen wajen duk suka miƙe tsaye domin raka baƙin.
Maman Ihsan ta matso kusa da Raihana, ta shafa kanta a hankali,
“Allah ya baku zaman lafiya, be a good wife, kin ji ko?”
Raihana ta gyada kai, amma wannan nodding ɗin ya zama sanadin sabon kuka, hawayenta suka sake zuba.
Maman Ihsan ta ɗan matse kafadarta,
“Ki yi haƙuri, my dear.”
daga haka itama ta juya ta bi bayan su.
Idanunta suka bi Maman Ihsan har ta kai bakin ƙofa, sai ta fara share hawayen da suka cika fuskarta.
A hankali mutane suka fara fita, ɗaya bayan ɗaya, sai aka bar Raihana da Inno kaɗai a babban falon.
Shiru ya sauka, wani irin shiru mai nauyi.
Inno ta kalli Raihana na ɗan lokaci, ta ga yadda take ƙoƙarin riƙe kanta, amma zuciyarta ta kasa.
Nan take Inno ta matso, ta rungumeta sosai, hannunta ya fara shafa bayanta a hankali.
Raihana kuwa ta manne jikinta, kamar wadda ta samu wurin da za ta sake sakin duk abin da ke zuciyarta, ta fara rizgar sabon kuka kuwa, kuka mai zurfi.
Kuka wanda ba wai na rabuwa da mutane kaɗai bane… kukan mace ce da take jin kamar rayuwarta ce ta canja gabadaya.
Inno ta ƙara rungumeta,
“Shhh… Raihana.”
amma wannan karon… ba ta ce ta daina kuka ba, ta bar ta ta yi kukan.
Because sometimes, silence was the only comfort words could not give.
Ba a daɗe da barin Raihana da Inno kaɗai a babban falon ba, sai suka fara jin sautin takun ƙafa daga saman bene.
Suhaila ce ke saukowa daga stairs ɗin a hankali, tana rike da wayarta, fuskarta ɗauke da wani irin farin ciki da excitement.
Da idanunta suka sauka kan Raihana, nan take murmushinta ya ƙara faɗaɗa,
“Anty Raihana!”
ta kira cikin murna.
Raihana ta ɗago kanta a hankali, har yanzu idanunta sun cika da hawaye, fuskarta kuma ta yi ja saboda kukan da ta yi.
Suhaila ba ta jira komai ba, ta ƙaraso da sauri ta rungume ta,
“Welcome, Anty Raihana! Sannu da zuwa.”
ta matse ta sosai kamar wadda ta daɗe tana jiran wannan ranar.
Raihana ta ɗan yi murmushi cikin hawaye, ta rungume Suhaila a hankali, sannan ta sake sunkuyar da kanta.
Suhaila ta janye kaɗan tana kallonta da farin ciki,
“Anty Raihana kin zo mana finally, wlh I am very happy.”
ta yi dariya.
A dai-dai lokacin ne mutanen da suka dawo daga raka baƙin, Ummie da sauran sisters ɗinta suka sake bayyana a falon.
Suhaila kuwa kamar ta tuna wani abu, nan take ta matso kusa da Raihana,
“Anty Raihana, bude fuskarki mana.”
Raihana ta ɗago kai kaɗan.
Suhaila ta riƙe gefen lafayyar,
“Dan Allah Anty, bude fuskarki, Anty Mariya ta ganki.”
ta kalli Raihana da pleading eyes,
“Dan Allah.”
Raihana ta yi ɗan murmushi cikin kunya.
Suhaila ta ɗaga lafayyar a hankali daga fuskarta, fuskar Raihana ta bayyana.
Idanunta har yanzu sun yi ja saboda kuka, amma kyawunta bai ragu ba ko kaɗan.
Suhaila ta tsaya tana kallonta na ƴan seconds, sai ta juyo da sauri wajen ɗaya daga cikin sisters ɗin Ummie,
“Anty Mariya, kin ganta?”
ta yi dariya,
“Ba nace miki kyakkayawace ba? Wallahi ki duba ta sosai.”
Anty Mariya ta matso kusa, ta kalli Raihana, sannan ta yi dariya,
“Ai na yarda.”
Suhaila ta ɗaga gira cikin satisfaction,
“Kin gani ko? Na faɗa miki tun farko.”
Anty Mariya ta yi murmushi tana kallon Raihana,
“Wallahi gaskiya ne, kyakkyawa ce sosai, zamu ga beautiful kids a wajensu itada Zayd.”
Raihana ta ƙara sunkuyar da kanta cikin kunya.
Suhaila kuwa ta sake rungumeta,
“Welcome again, Anty, I’m so happy kin zama matar Akhie wlh.”
Sai dai kafin Suhaila ta sake fara wani sabon bayani, Ummie ta yi murmushi tana kallonta,
“Suhaila!”
Suhaila ta juya,
“Hmm?”
Ummie ta girgiza kai tana dan hade rai,
“Wai meye haka? Ki kyale min yarinya ta huta daga zuwanta,”
ta nuna Raihana da hannunta,
“Come on, matsa a wajen.”
Suhaila ta yi dariya,
“Ai kawai ina son na ganta ne.”
Ummie ta sake girgiza kai,
“Kin gan ta ai.”
ta matso kusa da Raihana, ta gyara mata lafayyar da Suhaila ta ɗaga,
“Yanzu ku kyale ta, ta gaji, kuma ta yi kuka sosai.”
Suhaila ta ɗan yi shiru, ta kalli Raihana, sai ta yi ƙaramin murmushi, amma batace komai ba sai ta koma gefe, amma har yanzu fuskarta cike take da excitement.
Ummie ta kalli Raihana sannan ta yi mata murmushi,
“Zo daughter,”
ta miƙa hannunta.
Raihana ta kama hannunta a hankali, kuma a wannan karon…
ko da har yanzu zuciyarta cike take da missing home, akwai wani ƙaramin abu da ya fara sauka a zuciyarta.
Wata irin fahimta cewa…
perhaps, this new home wouldn’t be as frightening as she had imagined.
Ummie ta matso kusa da ita da wani irin murmushi a fuskarta, ta ɗan sunkuya kusa da ita, sannan ta rike mata hannu da kyau,
“Daughter mu je ɗakina ki huta, ki yi wanka, sannan ki yi sallah, sai a kawo miki abinci ki ci, kin ji ko?”
muryarta a hankali take, cike da wani irin warmth da kulawar uwa.
Raihana ta ɗan ɗago kanta a hankali, ta kalli Ummie na ƴan seconds, ta cikin lafayyar, sannan ta gyada kai ba tare da ta ce uffan ba.
Har yanzu idanunta sun yi ja saboda kukan da ta yi, fuskarta kuma tana ɗauke da alamun gajiya.
Ummie ta ɗan matse hannunta cikin nata,
“Good,”
tana shirin su fara tafiya kenan.
Amma kafin ta yi wani mataki, sai Suhaila ta daga murya daga gefe,
“Ummie, dan Allah ki barta mu je ɗakina! Wallahi ba zata sake da ke ba,”
ta faɗa cikin saurin magana, tana matsowa gare su.
Ta ƙaraso da sauri, tana kama ɗayan hannun Raihana da wani irin warm smile, ta ɗan ja ta kusa da ita kamar wadda ta riga ta ƙuduri aniyar dole dole sai ta Kai ta ɗakinta,
“Wallahi ba zan dameta da surutu ba, I promise!”
Raihana ta ɗan kalleta, sai ta sake sunkuyar da kanta cikin kunya.
Ummie ta kalli Suhaila da ɗan wani irin kallo mai cike da shakku, kamar bata yarda ba, ta ɗan ɗaga gira.
Suhaila ta fahimci kallon, nan take ta langwabe kai cikin shagwaba,
“Wallahi Ummie da gaske nake, kin ji dan Allah?”
ta ɗan matse hannun Raihana,
“Just let me take care of her.”
Ummie ta yi mata kallon wanda har yanzu bai nuna cewa ta gamsu ba.
Inno, wadda ke zaune tana kallonsu, ta sa baki,
“Hajja Fati, barta mana! Ki bar su su zauna tare, yaushe ɗama Raihana za ta sake a ɗakinki? Ai sai a ɗakin Suhaila din, ki barta kawai, idan can ɗin ma bai yi mata ba, sai a kai ta ɗakin mijinta tunda shima yana gidan ai.”
ta faɗa cikin sauƙi, kamar magana ce kawai bawani abu ba.
Amma kalmar ta ƙarshe ta tsaya a zuciyar Raihana.
Jin an ambaci “ɗakin mijinta” yasa gaban Raihana faɗuwa matuka, a tsaye take amma ji tayi kamar kafafunta zasu gaza tallafarta kamar zata fadi.
Wani irin sanyi ya ratsa jikinta, hannunta da ke cikin na Suhaila ta ke ya yi sanyi.
Ta haɗiye yawu a hankali, sannan ta danne duk abin da ke tashi a zuciyarta, amma ta daure ta danne, har yanzu kanta na sunkuye ƙasa.
Numfashinta ya ɗan rikice, kalmar ta sake ratsawa a zuciyarta, ta ƙara matse gefen lafayyar da dayan hannunta.
Ummie ta juyo da kallonta kansu, sannan ta amince da sharadi,
“To ku je, amma wallahi Suhaila kika dameta da surutu sai ranki ya baci!”
ta faɗa tana kallon Suhaila da warning look.
Suhaila ta saki yar dariya farinciki,
“Ba zan yi ba, Ummie, I swear!”
ta ɗaga hannu kamar wadda take rantsuwa.
Ummie ta girgiza kai tana murmushi,
“Ki kula da ita.”
Suhaila ta yi saurin gyada kai,
“Yes, Ummie.”
Daga nan, suka fara haurawa stairs ɗin a hankali, inda Suhaila ke riƙe da hannun Raihana.
Raihana ta bi ta ba tare da ta ce komai ba, kanta har yanzu a sunkuye.
Kowane step da take hawa kamar yana ƙara tabbatar mata da cewa babu sauran komawa baya.
Behind her…
sabuwar rayuwa ce take jiranta, kuma a yau ne ta fara shiga cikinta.
Suhaila ta rufe ƙofar ɗakinta da key, tana mai tabbatar da cewa sun samu complete privacy.
Ta juya daga ƙofar, ta kalli Raihana.
Raihana na tsaye a gefe shiru, hannayenta a haɗe a gabanta, kamar tana jiran Suhaila ta ba ta izinin zama.
Ganin haka, Suhaila ta yi sauri ta ƙaraso wajenta, ta kamo hannunta cike da kulawa,
“Muje,” ta faɗa cikin murmushi.
Ta ja ta a hankali suka karasa gefen gadon.
Raihana ta zauna a hankali, tana gyara lafayyar da ke jikinta.
Suhaila ta zauna kusa da ita, ta kalleta na ƴan seconds kafin ta ci gaba da cewa,
“Bari na haɗa miki ruwa kiyi wanka, Anty Raihana, dan Allah ki saki jikinki, kin ji? Ki ɗaukeni kamar ‘yar uwarki Anty Maryam, please.”
muryarta ta kasance mai laushi, ba tare da wata alamar wasa ba a wannan karon.
Raihana ta ɗan yi murmushi, sannan cikin sanyin murya tace,
“To.”
Suhaila ta saki murmushi mai daɗi,
“Na gode!”
ta ɗan matse hannun Raihana,
“Ki cire kayan, bari na kawo miki towel.”
Ta miƙe tsaye ta juya ta nufi bathroom.
A lokacin ne Raihana ta mike ta fara warware lafayyar da ke jikinta a hankali, hannunta yana motsawa a hankali, kamar har yanzu jikinta bai saba da yanayin gidan ba.
Kafin ta gama, sai ga Suhaila ta dawo ɗauke da babban towel mai laushi ta miƙa mata,
“Gashi.”
Raihana ta karɓa tana faɗin,
“Thank you.”
ta ajiye lafayyar a gefen gadon, sannan ta cire ɗankwalinta ma ta ajiye.
A daidai lokacin da ta cire shi, Suhaila ta zaro ido cike da matsananciyar mamaki.
Ta tsaya tana kallon gashin Raihana kamar wadda ta manta da abin da take shirin yi.
Wani haɗaɗen gashi da ya sha gyara, yake wani sheƙi mai ban mamaki, ga kuma jelar da aka daure ya sauko har bayan Raihana.
Suhaila ta ɗan buɗe baki cikin mamaki,
“Wow, Anty Raihana!”
sai ta ɗan matso kusa,
“Maa shaa Allah Tabarakallah!”
ta faɗa da ƙarfi, idanunta sun cika da sha’awa,
“Kalli gashin nan wallahi kamar ba ‘yar Nigeria ba! I swear, you are so gorgeous!”
ta ɗan yi dariya,
“Allah kinada kyau!”
Raihana dai murmushi kawai ta yi, tana ɗan sunkuyar da kanta saboda kunya, amma ba ta ce komai ba.
Suhaila ta kalleta na ɗan lokaci, sannan ta ɗan saki murmushi,
“To, kiyi wanka, bari na sauka na haɗo miki abinci, okay?”
Raihana ta kalleta na ɗan lokaci,
“To,” ta amsa a hankali.
Suhaila ta gyada kai,
“Okay, take your time.”
Amma duk da hakan, ta ga kamar ba za ta iya cire kayanta a gaban Suhaila ba saboda wani irin kunya.
Ta ɗan ja towel ɗin jikinta kusa da ita.
Don haka, sai kawai ta ɗauki towel ɗin ta juya ta nufi toilet ɗin a hankali.
Suhaila ta kalli bayanta yayin da take tafiya, sai ta yi ƙaramin murmushi, ta fahimci kunyar da Raihana ke ji.
Ba ta sake cewa komai ba, ta nufi closet ɗinta ta ciro mata kayan baccin da hula, ta ninke su cikin tsari ta ajiye a kan gadon.
Ta ɗan kalli kayan,
“Hopefully za su yi mata.”
ta gyara su a gefen pillow.
Daga nan ta juya ta fice zuwa ƙasa don haɗo mata abincin da za ta ci.