Free chapter · Read without an account
THE SECOND WING İİ
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER SEVENTY THREE:73*
*THE SECOND WING II*
*JIDDAAH BARKUM*
————-
Amarya Seeyama kuwa, tunda garin Allah ya yi, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Kallo ɗaya zaka yi mata ka san cewa hankalinta gaba ɗaya yana kan lokacin da za a daura auren. Gani take kamar lokacin da aka saka za a daura auren ba zai zo ba.
Few of her friends dake tare da ita a ɗaki kuwa, sai tsokanarta suke yi, suna dariya suna zuga ta, amma ita sam bata biye musu ba. Duk lokacin da suka yi wata magana, sai dai ta basu wani kallo ko ta tabe baki, sannan ta koma gyara wani abu a jikinta.
Domin a wajenta, ko da ace ba wani taro za a yi ba, ba ta damu ba. Kuma Inno ta dage ba wani shagali saboda yadda bikin ya zo ma haka kawai, tace babu adalci ayi shagali ana Seeyama bayan na Raihana baayi komai ba, so, daura aure kawai is okay. Ba ta damu da wani abu ba, ita dai indai ta auri Zayd, magana ta kare, shi ne kawai burinta.
Yanzu ma, kawarta Safina ce ta ɗago kanta tana kallon yadda Seeyama take ta faman gyara dankwalinta karo na ba adadi. Seeyama ta riga ta gyara shi sau da dama, amma duk da haka sai ta sake ɗaga hannu ta gyara gefensa. Safina ta kalleta na ƴa seconds, sai ta ɗan cije leɓenta tana ƙoƙarin hana kanta dariya, daga ƙarshe ta kasa, “Seema!”
Seeyama ta ɗago ido ta kalleta. Safina ta ɗaga gira, ta ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, sannan ta yi wata irin murmushi na zolaya, “Wai ni wannan rawar kan da kike duk akan mijin da yake da wata matar?” Seeyama ta ɗan ja numfashi, ta sake gyara dankwalinta kamar bata ji ta ba.
Safina ta ci gaba, tana ƙara matsowa kusa da ita, “Ni wallahi ina sonki da Mr. Armaan, but when I remember that he is already married…” Ta ɗan dakata, ta kankance idanu, “…and he married somebody else?” Ta yi wani irin facial expression na mamaki, sannan ta girgiza kai, “A very low-class girl from a poor background? Wallahi duk sai na ji abin ya fice min a kai.”
Seeyama ta ɗan tsaya, a hankali ta sake ɗago kai ta kalli Safina. Safina kuwa kamar ta samu abin da take so, sai ta ƙara cigaba da zuga ta, “Yanzu da irin wannan local yarinyar zaki haɗa miji? Gosh!” Ta ɗan dafe goshinta, ta runtse ido, “Very unfortunate, wallahi.”
Seeyama ta tabe baki, ta ɗan ɗaga gira, sannan ta maida kanta gefe kamar maganar ba ta shafe ta ba, “Ina ruwana? Da wata yar iskan yarinya wai ita matarshi.” Ta yi wani ɗan murmushi mai ɗauke da raini, “Please.” Ta ɗan yi ƙaramar dariya ta gefen baki, “Kinsani ai kinsan what I’m capable of doing.” Ta ɗaga gira, “Ba komai.” Sai ta ɗan karkata kanta, idanunta suka bude cike da assurance, “Wallahi da ƙafafunta sai ta bar gidan nan ta bar min shi.”
Seeyama ta ƙara matsawa baya, ta janyo stool din mirror ta zauna cikin wani irin confidence kamar wadda ta riga ta mallaki abin da take magana akai, “Sabida nice kaɗai.” Ta nuna kanta da yatsa, “Ni ce kawai ta shi.” Sai ta ɗan yi murmushi, tana cije leɓenta, “He belongs to me, alone.” Safina ta fashe da dariya, Seeyama kuwa ko ajikinta, “Lokaci kawai zan bata.” Ta ɗaga yatsa guda ɗaya, “Dan kadan kuma zaku gani.” Ta ɗan lumshe ido, sannan ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya, ta jikin mirror din dake bayanta cikin wani irin izzah, “This is just the beginning.”
Nan take ’yan matan suka hau ihu, “Ehhhh!” Suna tafawa suna dariya. Ɗaya daga cikin friends dinta Sophie tace, “Go Seema!” Shema’u tace, “That’s our girl!” Safina ta ɗaga hannunta tana dariya, “Exactly! Mrs. Armaan!” Seeyama ta yi murmushi cike da pride, ta ɗan ɗaga haɓarta sama, sai ta fara hura hanci a hankali, tana kallon su ɗaya bayan ɗaya kamar sarauniyar da aka tabbatar mata da nasara. Ta kuma ɗan girgiza ƙafarta da ke sama, tana ƙara reassuring na abinda ta fada.
Daga bayane Safina ta sake cewa, “Wai Suhaila ba zata zo ba?” Seeyama ta ɗan dakata. Safina ta ƙara tambaya, “Tunda dai nasan ba wai taro ake yi a can gidan ba, ni na zata ma zan zo na tadda ita a nan.” Seeyama ta tabe baki, nan take fuskarta ta ɗan sauya, ta kalli Safina da gefen ido, sannan ta sauke numfashi, “Ni wallahi yanzu ƙaf yan gidansu kallon munafukai nake musu.” Ta ɗan ɗaga gira, “Har uwarsa ke, har kakar tamu maa.” Ta ɗan girgiza kai, “Kuma wallahi zasu sha mamaki.” “Na rantse da Allah, sai sun zama su dashi sai hange daga nesa.”
Safina ta yi dariya. Seeyama ta ɗan yarfe hannunta, “Kar Allah ya sa ta zo.” Ta faɗa cikin nutsuwa, amma sautin muryarta cike yake da tsantsar jin haushi, “Ni bana buƙatar ta a nan.” Ta maida kanta gefe, ta sake gyara dankwalinta, sannan ta kalli madubi, ta yi murmushi ga reflection ɗinta.
Bayan Jumu’a prayer aka daura auren Zayd da Seeyama. Kowa ya shaida, few of his friends ma sun halarta, musamman bayan Imraan ya sanar da su. Kuma dama cycle ɗinsu ɗaya ne, don haka wasu daga cikinsu sun samu damar zuwa. Wasu kuwa tun kafin a gama daurin auren suka fara masa tsiya, “ARMAAN!” Ɗaya daga cikinsu ya danna kafadarsa yana dariya, “Yanzu ka auri mata biyu a sati ɗaya?” Wani ya fashe da dariya, “Bro, you don’t waste time!” Wani ya ƙara da cewa, “Two wives in one week? Kai, wannan record ɗin naka fa ba duk kaii ba!” Suka yi dariya gaba ɗaya.
Zayd kuwa, sam bai bi ta kansu ba, fuskarsa babu wani sabon expression, calm, still, kamar ba shi ake magana akai ba. Wani ya kalleshi ya girgiza kai, “Look at him, wallahi kamar ba shi aka daura wa aure ba.” Imraan ya yi dariya, “Ku bar shi, kun san wannan guy ɗin baya bayyana kansa.” Zayd ya ɗan kallesu kawai, bai ce komai ba.
Daga ƙarshe ma, kafin hayaniyar ta ƙaru, sai ya silale, ya gudu guest house, ya shiga ciki, ya zauna a gefen gadon, sannan ya cire wayarsa daga aljihu, ya kalli screen ɗin na ƴan seconds, daga nan ya kashe wayar gaba ɗaya, ya ɗora ta a gefe, ya sauke numfashi mai nauyi, ya jingina da headboard, ya lumshe idanunsa. A zuciyarsa, ya san abu ɗaya kawai, idan ya koma gida yanzu… Ummie na iya saka shi wani abu da ba ya so, musamman a kan harkar wannan auren. Saboda haka, a wannan karon, Zayd ya yanke shawarar ya ba kansa ɗan space, sai ya kwanta kawai ya lumshe idanunsaa.
A ARMAAN MANSION kuwa, babu wani abu da ya nuna kamar ana biki, babu komai, gidan yana nan yadda yake, babu wani abu sabo, babu decorations, babu hayaniya, babu wani abu da zai sa mutum ya ce yau ɗin nan an daura wani aure a gidan, kamar dai ranar ce ta yau da kullum.
Suhaila da Raihana kuwa suna ɗakin Suhaila, lokacin wajen ƙarfe huɗu na yamma, bayan Asr, Suhaila ta yi dariya tana kallon Raihana wadda take zaune a gabanta, “Bari na miki kwalba a kanki kinji.” Raihana tayi murmushi tana cire dankwalin. Suhaila ta fara, “Wai ya kike yi da wannan gashin? Idan zaki yi combing ɗinsa, dazu da ƙyar na dinga ja, sai na ji kamar zaki ji zafi a kowane lokaci.” Ta yi dariya, tana girgiza kai yayin da ta sake ɗaukar comb ɗin ta ɗan gyara wani ɓangaren gashin.
Raihana ta ɗan yi murmushi mai faɗi, ta ɗan taɓa gashin da hannunta, “Kuma ba zafin kawai combing ɗin nake.” Suhaila ta sake fashewa da dariya, “Amma dai ku ba ƴan Nigeria bane.” Raihana ta ɗan gyada kai, “Ummah ce yar Niger, amma Baffanmu ɗan nan ne, Makarfi to be precise.” Suhaila ta ɗan tsaya tana kallonta, sai ta ɗaga gira, “Wow.” Ta sake ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, sannan murmushi ya bayyana a fuskarta, “No wonder.” Ta ɗan yi dariya, “Shiyasa wallahi baki ganki ba, ina ganin farin Akhie, amma idan na ganki…” Ta ɗan leqa Raihana tana kallon fuskarta da kyau, “…sai naga shi ba komai bane a inda akwai ki.”
Raihana ta ɗan lumshe idanunta cikin jin kunya, murmushi mai sanyi ya bayyana a fuskarta, ta sauke idanunta ƙasa, bata ce komai ba. Suhaila kuwa ta ɗan yi murmushi tana kallonta, kafin ta koma gyara gashin nata.
A daidai lokacin ne wayar Suhaila ta fara ringing, ta ɗan kalli screen ɗin, ta ɗan ɗaga gira, sannan ta ɗaga wayar, “Feenah, ya kike?” Muryar Feenah ta fito daga ɗayan ɓangaren cikin gaggawa, “Wai da gaske ne an daura auren Zayd da Seeyama? I just got the news right now, nace bari na kiraki na yi confirming, please tell me it’s a prank.”
Suhaila ta yi shiru, murmushin da ke fuskarta ya ɓace a hankali, idanunta suka sauka kan Raihana. Raihana tana kusa da ita, kanta a ɗan sunkuye, hannunta yana wasa da Dayan comb din. Ko shakka babu, ta san ta ji abinda aka faɗa. Suhaila ta ɗan haɗiye yawu, ta sake kallon Raihana na wasu seconds, kamar tana ƙoƙarin karanta reaction ɗinta. Raihana bata ɗago kai ba, fuskarta kuwa ta yi shiru sosai.
Suhaila ta maida hankalinta kan wayar, “I will get back to you, Feenah, akwai abinda nake yi yanzu.” Feenah ta fara sake magana daga can, amma Suhaila bata jira ta gama ba, ta yanke call ɗin, ta ajiye wayar a gefe. Shiru ya ratsa ɗakin.
Suhaila ta ɗan kalli Raihana, Raihana kuwa har yanzu tana kallon ƙasa, ba ta ce komai ba. Suhaila ta yi shiru na ƴan seconds tana kallon Raihana, guilt ɗin da ke ranta yana ƙara bayyana a fuskarta, ta san wannan ba irin labarin da ya kamata Raihana ta ji haka kwatsam bane, duk da tasan yau zaa daura auren.
A hankali ta kira sunanta, “Anty Rayy…” ta fara a hankali, “Please kar ki bari wannan abin ya dame ki sosai.” Raihana ta ɗago ta dan kalleta kawai, sannan ta sake sauke idonta. Suhaila ta ci gaba, “Na san ba abu bane mai sauƙi, especially after everything… har yanzu ba ki gama settling a nan ba, yanzu kuma wannan labarin, amma please, ki yi haƙuri. Kada ki yi tunanin cewa saboda ya yi wani aure to hakan yana nufin wani abu ya canza game da ke.”
Raihana ta yi shiru. Suhaila ta ɗan matsa kusa da ita, “Anty Rayy, wannan auren…” ta ɗan yi shiru tana neman kalmomin da suka dace, “Inna ce ta haɗa shi.” Kuma gaskiya ita ma bata san da ke ba lokacin da ta fara haɗa auren nan, ban san ko da ta sani da wuri da ta yi wani abu daban ba, but you know Inna… idan ta yanke shawara a kan abu, ba kasafai take barin wani ya tsaya a gabanta ya ce mata a’a ba, tana da nata ra’ayin kuma idan ta riga ta ɗaura kanta da wani abu, it’s very difficult for anyone to change her mind.”
Raihana ta yi shiru tana sauraron ta. Suhaila ta ci gaba da sauri kamar tana son ta tabbatar Raihana ta fahimci abin, “Ba wai ina cewa wannan zai rage miki zafi bane, na san ba abu bane mai sauƙi, especially yanzu da ke ma har yanzu ba ki gama tarewa a ɗakinki ba, amma please, ki yi haƙuri, kada ki bari wannan labarin ya sa ki ji kamar an yi wani abu ne a kanki. Ni dai na san Brother dina, sometimes baya faɗa mana komai, he just does whatever he thinks is right, kuma sai daga baya mu ji, but da ace yana neman Seema da soyayya, wnn kam ba zai boya ba, believe me, wlh ba son auren yake ba, so please kar ki ɗauka cewa kin yi wani abu ne ko akwai matsala a tare da ke.”
Raihana ta ɗan yi murmushi kaɗan, “Kai ki daina magana haka mana.” Suhaila ta kalleta. Raihana ta cigaba cikin nutsuwa, “What’s there?” ta faɗa a hankali, “Idan yayi aure ai ya halatta.” Suhaila ta yi shiru na ɗan lokaci, tana kallonta da mamaki, “Anty Rayy, I know ya halatta… ba wai ina cewa bai halatta ba ne, amma kin sani, ba wacce zata so a yi mata kishiya bayan ko tarewa a ɗakinta batayi ba.”
Raihana ta ɗan kalli Suhaila cikin nutsuwa. Suhaila ta cigaba, “Shi yasa nake cewa ki yi haƙuri, kada ki bari maganar mutane ko wannan abin ya shiga ranki, and please, kar ki yi ƙoƙarin nuna cewa komai ba komai bane idan a zuciyarki akwai abin da ke damunki, you can talk to me.” Raihana ta yi shiru na ƴan seconds, sai kawai ta girgiza kai a hankali, “Babu komai.” Suhaila ta kalleta sosai, “Anty Rayy…” Raihana ta ɗan yi murmushi, “I’m fine, Suhaila.” Ta sake komawa da idonta ƙasa, cikin cikakkiyar nutsuwa.
Suhaila ta yi shiru tana kallonta, amma har yanzu guilt ɗin bai bar fuskarta ba, “Okay…” ta faɗa a hankali, duk da cewa har yanzu bata gamsu ba. Raihana kuwa bata ƙara cewa komai ba, ta zauna cikin nutsuwa kamar labarin bai sa ta rasa hankalinta ba—ko da kuwa Suhaila tana ganin akwai wani abu da ta ɓoye a cikin wannan shirun nata.
Bintu sun karaso gidan Haj Hauwa ita da Haj Balaraba. Da suka shiga, Haj Hauwa ta kalli Bintu sannan ta ce, Bintu, taje wajen su Seema a ɗakinta. Bintu ta gyada kai ba tare da wata magana ba, sannan ta wuce zuwa ɗakin Seeyama. Da ta shiga, sai ta tsaya a bakin ƙofar na ƴan seconds. Abin mamaki, ko kallon inda take babu wanda yayi, kamar Allah bai yi ruwanta a wajen ba.
Bintu ta ɗan kalli ɗakin gaba ɗaya, sannan ta kalli Seeyama wacce ita ma bata nuna wata alama ta ta san cewa akwai wani mai rai a wajen ba. Har sai da ɗaya daga cikin mutanen da ke ciki ta kalli Bintu sannan ta tambayi Seeyama, “Who’s this?” Seeyama bata ko kalli Bintu ba, sai dai kawai ta amsa cikin raini, “Maid ɗin Mommy ce.” Bintu ta ɗan tsaya cak, fuskarta ta sauya na ɗan lokaci, amma bata ce komai ba, ta sauke idonta ƙasa, sannan ba tare da shiri ba ta juya ta koma ɗakin Haj Hauwa.
Da misalin ƙarfe biyar, Haj Hauwa ta zauna ta ɗauki wayarta, ta ɗan yi shiru kafin ta nemo lambar Ummie, sannan ta kira ta. Bayan an gaisa, Haj Hauwa ta ɗan gyara zamanta, ta ɗora wayar a kunnenta, “Hajja Fatee, ina so na ji yanda za ayi da kai amarya ne zaku aiko ne ko nice zan kawota da kaina ko kuma mijinta ne zai zo ya ɗauketa?” Ta ɗan yi shiru, sannan ta ci gaba ba yabo ba fallasa, “Nifa wannan aure kamar wani na marasa galihu ne, irin gaisuwar sirikan nan ma da ake zuwa bayan daurin aure, banga ƙafar Zayd ba bare abokansa, shi kanshi Imran tunda ya fice da sunan daurin auren ban sake ji daga gare shi ba.” Haj Hauwa ta ɗan matsa wayar da kyau a kunnenta, fuskarta a hade, “Yana da kyau a dinga kwabar Zayd akan abin da yakamata, yanzu shi ba yaro bane, mace biyu ya ajiye, idan bai san abin da yakamata ba, me kenan zai faru bayan ya haɗe su gida ɗaya?”
Ummie tayi shiru. Haj Hauwa ta jira amsar, tana kallon Haj Balaraba wacce ke zaune kusa da ita. Sai bayan ƴan seconds Ummie ta ce a hankali, “Zan kirashi, yanda ake ciki zan sake kiranki.” “Toh, ya dai fi,” Haj Hauwa ta amsa. Ta katse wayar a hankali sannan ta ajiye ta gefenta. Haj Balaraba ta dubeta, ta ɗan ɗaga gira, “Ya kukayi?” Haj Hauwa ta yamutse fuska, ta jingina bayanta da kujerar, “Zata kirashi, yanda sukayi zata kirani.” Haj Balaraba ta ɗan yi shiru, tana kallon fuskarta, “Da ban kira ba kenan? Haka zata barmu a gantale a nan? Ba zata masa magana ba?” Ta girgiza kai a hankali, fuskarta cike da takaici, “Dan wannan yaron idan ta barshi haka, sai Seeyama ta rube a gidan nan, dan wallahi ba ta kanta zai bi ba.” “Duk an bar yaro ya lalace, baya ganin uban kowa da gashi sai uwarsa.”
Haj Balaraba ta yi shiru tana kallon Haj Hauwa kafin tace, “Kece ai kika dage Seeyama ta aureshi bayan uban samarin da suke sonta, ni na rasa wanne irin dalili ne dake akan auren nan.” Haj Hauwa tayi murmushi tana girgiza kafafunta amma batace komai ba.
Ummie tana sauke wayar, bata bata lokaci ba ta shiga neman Zayd. Ta kira layinsa, amma kaf layinsa, har wanda idan ta kira second ɗaya yayi yawa Zayd ya ɗauka, yau sai ta ji wayar a kashe. Ta ɗan yi jimmm tana kallon screen ɗin wayar, kamar tana mamakin me ya sa zai kashe wayoyinsa. Bayan ƴan seconds, sai ta canja akalar kiran zuwa ga Sameer. Bayan sun gaisa, Ummie ta tambaya cikin nutsuwa, “Zayd fa?” Sameer ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya amsa cikin girmamawa daga can, “Wallahi Ummie, tun wajen daurin auren ban sake ganinsa ba.” “Okay,” ta amsa kawai, sai ta kashe wayar.
Ba tare da bata lokaci ba, ta sake danna kiran Imraan. Bayan sun gaisa, sai ta tambaye shi, “Imraan, Zayd fa?” Imraan ya amsa daga can, “Tun a mosque rabona da shi, Ummie.” Ummie ta yi shiru na ƴan seconds, ta sauke wayar a hankali tana kallon gabanta, sai ta mike, ta nufi ɗakin Suhaila.
Da ta shiga, ta tarar Suhaila da Raihana suna zaune, Raihana na taimakawa Suhaila gyaran kayanta. Ummie ta shiga ta zauna a gefen gadon, idonta ya tsaya kan Raihana na ƴan seconds. Raihana kuwa tana zaune cikin nutsuwa, ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da gyaran kayan. Ummie ta juya dubanta zuwa wajen Suhaila, “Waton kin fara bata aiki ko? Dan raini, ita ma zata gyara miki kayanki?” Suhaila ta ɗan langwabe kai, tana kallon Ummie da innocent expression, “Wlh Ummie, nace ta bari ta dage a lalle sai ta tayani, nayi-nayi ta bari ta ƙi.”
Ummie ta ɗan kalli Raihana, Raihana haryanzu kanta na ƙasa, babu abin da ta ce. Sai kawai Ummie ta ɗan yi murmushi, ta sake mayar da dubanta ga Suhaila, “Kun yi magana da Yayanki?” Suhaila ta girgiza kai, “A’a, bamuyi waya ba.” Suhaila ta ɗan tsaya, sannan ta tambaya, “Akwai wani abu ne?” Ta faɗi hakan cikin murya mai sauƙi, amma idanunta suna kan Ummie kamar tana son fahimtar wani abu.
Ummie ta girgiza kai a hankali, “Babu komai.” Daga haka sai ta mike, bata ƙara cewa komai ba, ta fita daga ɗakin, sannan ta ja ƙofar ta rufe musu a hankali. Suhaila ta kalli ƙofar na ƴan seconds, sannan ta juya ta kalli Raihana. Raihana kuwa har yanzu tana zaune cikin nutsuwa, kanta a sunkuye, tana ci gaba da gyaran kayan kamar babu wani abu da ya faru.