Free chapter · Read without an account
TWO CALLS TWO WORLDS
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER EIGHTY THREE: 83*
*TWO CALLS, TWO WORLDS*
*JIDDAAH BARKUM*
————
Zayd ya tsaya cak, idanunsa na kan Seeyama wacce murmushin fuskarta ya ɗan fara dusashewa saboda yadda ta lura da irin kallon da yake watsa mata. Hannunta da ke riƙe da nashi ta fara janyewa a hankali, yayin da fara’ar da ke fuskarta ta ci gaba da janyewa kaɗan-kaɗan, “Babe…” Ta sake cewa, wannan karon muryarta ta fito da wata irin uncertainty, tana kallon fuskarsa wacce ta yi wani irin blank, amma ga wani tsantsar coldness da yake fitarwa da kowanne kallo.
Zayd bai amsa mata ba, kawai sai ya fizge hannunsa daga nata gaba ɗaya, ya yi folding ɗin hannayensa a chest ɗinsa, ya ɗan kalli bedroom ɗin da gadon da Safina ta tashi na wasu seconds, sannan ya dawo da idanunsa kanta. Muryarsa ta fito a hankali, amma tana da wani irin nauyi da zafi da sai da ya sa zuciyarta ta yi wani irin mugun sanyi, “Who gave you the permission to bring trash into my house?” Seeyama ta buɗe baki da sauri, “Ha… trash? Wace ce kuma trash, babe? Safina fa kake nufi?” Ta yi wani ɗan yaƙe, tana son ta mayar da abin wasa, “Ita ce kake cewa—” “Shut up.” Ya dakatar da ita a sanyaye, amma da wata irin tsawa a ciki wacce ba ta buƙatar ɗaga murya don ta shiga ranta.
Zayd ya matsa gaba kaɗan, ya na tuno yadda falon yake a watse, kayan da suka bazu, takeaways da suke nan harda ragowar abinci, da kuma takalman da suka jefa ko’ina, ya saki wata guntun tsaki na takaici, “Wannan wane irin rashin hankali ne?” Ya tambaye ta, idanunsa suna kallon cikin nata kai tsaye, “Kin zo gidana, kin maida shi gidan marasa galihu? Kin bar gidan nan a watse kamar ba mace ce take rayuwa a ciki ba?” Ya ɗan dakata, “Sannan ki kawo min kawarki har kan gadona, ba ma a dakinki ba. Dakina! Are you in your right senses?!”
Seeyama ta fara jin zuciyarta na bugawa, ta saba da Zayd yana da zafi idan ya yi fushi, amma wannan karon yanayin nashi ya fi na kowane lokaci ban tsoro, and she didn’t even see anything bad in what she had done, tunda akwai dakuna da yawa a gidan, ba sai ya canja wani ba, sai dai ta daure, ta fara magana tana ɗan langwabe kai, “Babe, kasan fa ba ni na ɓata wajen haka ba. Safina ce ta—” “I don’t give a damn about Safina!” Ya katse ta a zafafe, a karo na farko da muryarsa ta ɗan ɗago, “Wace ce ita da za ta zo gida na har ta samu damar da za ta watsa kaya?” Sannan kuma… ya ɗan tsaya, idanunsa suka kankance yana kallonta kasa kasa, “…na ji labarin mai gadina. Kin mare shi saboda ya yi abin da na saka shi?” Fuskarsa ta sake haɗewa fiye da da.
Seeyama ta haɗiye yawu da ƙyar, yanzu kam tsoro ya fara bayyana a idanunta amma ta daure, “Anya babe, lafiya kuwa? Saboda wani ɗan iskan mai gadi ne zaka zo kana min magana haka?” Ta ɗan ɗaga murya cikin kuka, “I’m your wife, for God’s sake!” “Wife?” Zayd ya maimaita kalmar da wani irin sarcastic tone, ya saki wani ɗan murmushi mara daɗi, “Matar da ba ta san mutuncin gidan mijinta ba?” Ya matsa kusa, “Matar da ta zama headache a duk inda ta taka?” Ya sake matsowa har sai da Seeyama ta yi baya, tana tuntuɓe da bakin gado, “Wai dan Allah me haka kake min ihu!” Seeyama ta fashe da kuka, tana mai da numfashi da sauri, “Tun ɗazu nake ta jiran ka dawo a matsayinka na mijina, kuma ni a matsayina na Amarya ka barni na kwana ni ɗaya!” Hawaye suka fara zuba a fuskarta, “Sannan yanzu ka dawo amma abin da zaka fara faɗa min kenan? Saboda kawai na kawo ƙawata?”
Zayd ya tsaya a kanta, ya zuba mata idanu sosai, “Karki kuma kiran kanki matar aure a gaba na.” Muryarsa ta yi sanyi, amma wannan sanyin ya fi tsawa tsoratarwa, “Saboda baki san ciwon kanki ba.” Ya nuna mata hanyar falon da hannunsa, muryarsa tana rawa saboda tsananin ɓacin rai, “Awa ɗaya na baki. Ki gyara gidan nan tsaf ya koma yadda yake in less than an hour!” “Sannan kuma…” Ya nuna ta da yatsa, “Wallahi, ko da wasa kika sake daga hannu kika taɓa mai gadina, zaki sha mamaki na!” Seeyama ta zaro idanu waje, tana kallonsa tana rawar baki, “Zayd, saboda mai gadi zaka—” “Ba na son jin ko kalma ɗaya daga gare ki!” Ya katse ta da wata uwar tsawa, har sai da ta ja da baya da sauri, “Ki gama abin da na saka ki kafin lokaci ya cika. Idan ba haka ba kuma…” Ya ɗan sunkuyar da kansa, “…zaki ga abin da zan miki.”
Sai Seeyama ta sake fashewa da kuka da ƙarfi sosai, “Saboda waccan yarinyar ce?” Ta yi numfashi da ƙyar, “Saboda Raihana ce take sa kake min haka ko?!” Jin sunan Raihana a bakinta ya sa Zayd ya daka mata wata uwar tsawa, har sai da ta saki wani ƙara ta dafe ƙirjinta, “Karki kuskura ki kuma ambaton sunanta a wannan bakin naki!” Ya nuna ta da yatsa, muryarsa tana qara kaushi, “Idan na sake ji ko na gani kina sakata a maganar da muke yi ni da ke…” Ya yi ɗan shiru, “…wallahi zan nuna miki ba ki san wane ne ni ba!” Idanunsa suka cika da wani irin tsananin fushi, “Get out of my sight. Now!” Ba tare da ya jira ta ce komai ba, ya juya da sauri ya fice daga ɗakin, ya bar ta a tsaye tana kuka da huci kamar za ta shiɗe da baƙin ciki.
Seeyama ta kalli ƙofar da ya fice ta cikinta, hawaye na zuba mata ba kakkautawa, amma a ƙarƙashin wannan kukan… takaici, kiyayyar Raihana, da kuma azabar kishi, duk suka gama cika mata zuciya. A wannan karon, ba wai kawai ta ji an wulaƙanta ta ba, ta fara fahimtar cewa akwai wani abu game da Raihana da Zayd ba zai bari ta taɓa ba, and that realization hurt her more than anything.
Gidan Baffa Musa kuwa, jama’ar gidan na zaune a tsakar gida saboda yanayin zafin garin, hadari ya taru a sama, amma bai kai ga zubar da ruwa ba, hakan ne ya sa garin ya ƙara yin zafi sosai, iska ma kamar ta tsaya cak. Umma da Mama Indo suna zaune a tsakar gidan, kan veranda, a kan tabarma, Bintu kuma tana gefe, wajen ɗakinsu, tana haɗawa almajiri kayan wanki da zai musu. Mama Sabuwa na zaune a ƙofar ɗakinta a kan tabarma, ta sha ɗaurin kirji, tana ta fifita kanta da mafici, tana jan numfashi lokaci-lokaci saboda zafin. Maryam kuma tana gefen kitchen, zaune a kan wata ƙaramar tabarma tana tankaɗe garin tuwo.
Sai Umma ta ɗago kai ta kalli Maryam cikin sanyin murya, “Maryam, kun yi magana da yar uwarki kuwa kwana biyu? Ban ji ta ba, bata kira ba.” Maryam ta ɗan girgiza kai tana ci gaba da aikinta, “Wallahi Umma, kusan kwana biyu, tun shekaran jiya dai ba mu yi ko chat ba. Dazu ma na mata magana a WhatsApp, naga bai tafi ba, kamar bata kunna data ba, gashi kuma ba ni da number mijin nata ko kuma ta Suhaila, bare na ji. Amma dai ban mata waya ba, iya chat WhatsApp ne, sai dai ko a kira ta ta waya, ko za a sameta.”
Umma za ta yi magana kenan, Mama Sabuwa ta karɓe zancen da wani irin tone na shagube, tana fifita kanta da mafici, “Ke kuwa Hajara, don kin aurar da diya kin yi kwana ɗaya biyu ba wai ma kwana biyun malam Bahaushe ba ba ki yi magana da ita ba, shi ne abin tashin hankali?” Ta ɗan tsaya, ta sake fifita fuskarta kafin ta ci gaba, “Yo ni Allah na tuba! Sai na yi wata ban yi waya da kowacce a cikin su ba, ba dai suna zaune lafiya a dakinsu ba? Me ye na wani kiraye-kiraye? Ai lafiya ita ke buya, ba wani abu ba.” Ta ɗaga gira, “Idan ba lafiya, ai duk runtsi dole a kira iyayenta a sanar.” Bintu ta watsa wa Mama Sabuwa wani kallo a sace, ta yi tsaki ƙasa-ƙasa, amma ba ta ce komai ba.
Mama Indo kuwa ta dubi Umma kai tsaye, fuskarta babu wasa, “Maman Aminu…” Umma ta ɗauke kanta daga kallon Mama Sabuwa, ta kalli Mama Indo, sai Mama Indo ta ci gaba da magana da wani irin direct approach, “Dauki wayarki ki kira yarki kiji ya lafiyarta.” Ta ɗan yi shiru, sannan ta cigaba, “Kira abarki! Tunda ba uban wani ne ya haifa miki ba, bare a ce sai kin yi shawarar yadda za ki yi da abarki.” Umma ta yi shiru na ɗan lokaci, tana kallon Mama Indo, sai ta ɗan sauke numfashi, sannan ta fara magana cikin sanyin murya, “Ai dake tana gidan surukanta ne, ba na so na yi ta kiranta ne wallahi…” Amma Mama Indo ta girgiza kai, kamar ba ta yarda da hujjar ba, “Wallahi ki kira abarki! Yo me ye? Ba dai gaisuwa ba ce kawai ki kirata, ki ji muryarta, ki tabbatar tana lafiya, me ya fi haka?” Umma ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta ɗaga wayarta da ke gefenta, Mama Sabuwa kuwa babu abin da take yi sai zabga musu harara daga inda take zaune, kallon nan nata na gefe-gefe, kamar tana so ta nuna musu cewa duk wannan abin babu wani muhimmanci, sai ta ja uban tsaki, amma babu wanda ya bi ta kanta.
Umma ta ci gaba da neman number Raihana, Maryam ta koma ga tankaɗe garin tuwonta kamar ba ta ji komai ba, Bintu kuma ta sunkuyar da kai tana cigaba da haɗa kayan wankin almajirin, Mama Indo ta gyara zamanta, ta sake kallon Umma, “Kira ta kawai, Hajara, kada ki damu da wani abu.” Umma ta ɗan murmusa, “Toh, bari na kira ta.” Ta danna number ɗin Raihana, ta ɗaga wayar zuwa kunnenta, a tsakar gidan kuwa, kowa ya ci gaba da abin da yake yi, sai dai Mama Sabuwa har yanzu tana can tana harare-harare, ta sake jan wani dogon tsaki, amma kamar ba ta nan, babu wanda ya bi ta kanta.
A ɗayan ɓangaren kuwa, wayar Raihana ce ta fara ringing a kan bedside table, ta yi ringing sau ɗaya, sau biyu, Raihana da take kwance cikin bacci mai nauyi, ta ɗan motsa kanta a kan pillow, amma kamar ba ta san abin da ke faruwa ba, wayar ta cigaba da ringing, a hankali ta buɗe idanunta, har yanzu baccin bai gama sakinta ba, ta miƙa hannu cikin kasala tana neman wayar, amma hannunta ya fara yawo a kan bedside table kafin daga ƙarshe ta taɓa wayar, ta kalli screen ɗin, UMMA CALLING… Nan take bacci ya ɗan gushe daga idanunta, “Umma…” Ta ɗaga wayar da sauri, “Assalamualaikum?” Muryarta a ɗan raunane saboda bacci.
A ɗayan ɓangaren, Umma ta yi murmushi da jin muryar ɗiyarta, “Raihana?” “Ummaaa taaa…” Sai muryar Raihana ta canza gaba ɗaya, wani irin farin ciki ya bayyana a fuskarta, “Umma ina yini?” “Lafiya lau, Raihana ya kike?” Raihana ta ɗan gyara zamanta, ta jingina da pillow, sannan ta murmusa, “Ni ma lafiya lau nake, Umma.” Umma ta yi shiru na ɗan lokaci, “Kina lafiya dai?” Raihana ta ɗan yi murmushi, “Eh Umma, lafiya lau nake.” “Kin tabbata?” “Wallahi Umma, lafiya lau.” Umma ta sake tambaya cikin kulawa, “Babu wani abu dai?” Raihana ta ɗan yi shiru, sannan ta sake wani murmushin kaɗan, “Babu komai Umma, me zai faru?” “Ban sani ba ne, kawai kwana biyu ban ji muryarki ba.” Raihana ta ɗan sauke numfashi, “Wayyo ummanaaa banso na cika damunki ne ki dauka ko akwai wani abu shiyasa ban kira ki ba jiya da yau amma bakomai.”
Umma ta sauke numfashi cike da gamsuwa amma sai ta sake tambaya, “Kin ci abinci?” Raihana ta kalli plate ɗin abincin da ke gefe wanda ta kasa ci tun da aka kawo mata shi, “Eh…” Sai ta tsaya, ta gyara maganar cikin sauri, “Zan ci yanzu.” Umma ta yi shiru, “Raihana…” “Hmm?” “Kin tabbata dai ba wata matsala?” Raihana ta yi murmushi, amma wannan karon murmushin ya ɗan yi rauni, “Umma, wallahi babu matsala, ina lafiya lau, ki daina damuwa.” Umma ta yi ajiyar zuciya, “Toh, Allah ya sa haka, ni dai na ce bari na ji muryarki.” Raihana ta ƙara murmushi, “Awwn Umma…” Muryarta ta yi laushi, “Na yi missing ɗinki sosai, ina su Aminu da Yusuf.” Umma ta yi dariya a hankali, “Ni ma na yi missing ɗinki, kowa yana lafiya, shi ya sa nace sai na ji muryarki da kaina.” Raihana ta rufe idanunta na ɗan lokaci, tana murmushi, jin muryar Umma kaɗai ya sa wani irin kwanciyar hankali ya sauka mata a zuciya.
Amma Umma har yanzu ba ta gama gamsuwa ba, “Raihana…” “Na’am Umma?” “Kin tabbata babu abin da kike ɓoye min?” Raihana ta buɗe idanunta, “Umma!” Ta yi dariya kaɗan, “Wallahi babu komai, lafiya lau nake.” “Hmm…” Umma ta ja numfashi, “Toh shikenan, amma ki sani, idan akwai wani abu, ki gaya min, kada ki ce kina gidan surukinki shi ya sa ba za ki iya magana da ni ba.” Raihana ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta murmusa, “Toh Umma, zan gaya miki.” “Yauwa.” Raihana ta sake murmushi, “Allah ya ƙara miki lafiya Umma ta.” “Ameen, ke ma Allah ya tsare ki, ya sa ki zauna lafiya a duk inda rayuwa zata kai ki, Allah yayi miki albarka.” Raihana taji hawaye ya taru a idanunta, muryarta ta kara sanyi ta amsa a hankali, “Ameen,” sai ta lumshe ido tana murmushi, a wannan karon, zuciyarta ta ji wani irin sauƙi, kamar dai jin muryar Umma kadai ya isa ya sa wani nishadi da farinciki sauka a zuciyarta nan take…
Bayan Seeyama ta ci uban kuka, ta gode Allah har saida idanunta suka yi ja suka dan kumbura, ta share fuskarta da bayan hannunta, ta ɗan yi shiru tana jan numfashi, zuciyarta still na wani tuqiqin bakinciki da bacin rai, a ƙarshe ta zauna a gefen gado, ta ɗauki wayarta da ɗan sauri, ba tare da ɓata lokaci ba, ta fara neman Mommy a cikin contacts ɗinta, bugu biyu kacal, Haj Hauwa ta ɗaga, “Hello…?” Muryarta ta fito sama-sama, kamar wadda aka tashe ta daga bacci.
Seeyama ta ɗan yi jim, ta kalli screen ɗin wayarta, 17:45, ta sake maida wayar a kunnenta, “Mommy… bacci kike ne?” A ɗayan ɓangaren, Haj Hauwa ta gyara muryarta a hankali, tana kuma janye hannun Haj Balaraba daga jikinta, “No, sweetheart, ina kwance ne, mura ke damuna,” ta ɗan yi tari a hankali, “Ya kike? Ya gidan? Zayd din ya zo kuwa nan?” Nan take fuskar Seeyama ta canza, ta haɗe rai, ta ɗan ja numfashi, “Mommy…” “Na’aam?” “Wallahi ba zan bar yarinyar nan ta zauna lafiya ba.” Muryarta ta fara cika da fushi, “Kin ga ihun da yayi min sabida ita? Don kuma yace gateman, kar ya buɗe ƙofa, na sa an buɗe min, don kawai na fita sai—”
Haj Hauwa ta ɗan haɗe rai, “Kin fita kuma?” Muryarta ta sauya gaba ɗaya, “Ina kikaje?” Ta tambaye ta, Seeyama ta ɗan ɗaga gira, snn cikin wani irin I don’t care attitude ta fara magana, “Na fita da Safina.” Ta ɗan yi shiru, sannan ta ƙara da ƙiyayya a cikin muryarta, “Neman mafita ne akan shegiyar yarinyar nan ne.” Haj Hauwa ta yi shiru, sai ta ɗan gyara zamanta, “Wai Seeyama…” “Wace shegiya da kike magana a kai? Ni fa ban gane ba.” Seeyama ta haɗe rai sosai, ta goge hawayen da suka sake taruwa a gefen idonta, “Toh Mommy, akwai wata shegiya gantalalliya da ya wuce Raihana ne?” Ta ɗan cije leɓenta, “Ita nake nufi.” Nan take Haj Hauwa ta tashi da kyau ta zauna, fuskarta ta sauya, Haj Balaraba da take kusa da ita ta zuba mata ido, ba tare da ko kiftawa ba, Haj Hauwa ta riƙe wayar da kyau, muryarta ta fito da seriousness, “Ina kika je? Maganinta wajen boka ko ina??”
Seeyama kuwa ba ta yi ƙoƙarin ɓoye komai ba, kai tsaye ta amsa, “Ehh mana.” Haj Hauwa ta zabura kamar an zuba mata ruwan sanyi, “Ke Seeyama!” Ta ɗaga murya, “Ashe baki da hankali?!” Haj Balaraba ta ƙara zuba mata ido, “Mahaukaciyar gidan uban waye ke? Ki ji, yarinya mara hankali!” Ta ɗan ja numfashi, cike da fushi, “Har kin yi wayon da za ki yi abu irin wannan ba ki yi shawara da ni uwar ki ba?!” Seeyama ta yi shiru, fuskarta ta ɗan nuna mamakin fadan Mommy, dan she sees nothing wrong with what she did da Mommy ke wannan kumfar bakin.
Haj Hauwa ta ci gaba, “Toh wallahi, idan ma ba ki aiwatar da abin da yace ba, kar ma ki fara, kina ji na ko?!” Ta ɗan tsaya, ta kalli Haj Balaraba na ɗan lokaci, sannan ta dawo da hankalinta kan wayar, “Kuma sannan…” Muryarta ta yi ƙasa, amma seriousness ɗin ya ƙara fitowa fili, “Kar ki taɓa yin komai ba tare da kin sanar da ni ba.” Seeyama ta yi still kawai tana sauraronta, Haj Hauwa ta girgiza kai cikin takaici, “Shashasha! Mahaukaciyar da ba ta shawara da uwarta sai wasu ’yan iskan kawaye da za su kai ki su baro…”