Free chapter · Read without an account
THE GAME CHANGED
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER EIGHTY-FOUR: 84*
*THE GAME CHANGED*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Seeyama ta tsaya cak, wayar na makale a kunnenta, amma gaba ɗaya ta rasa abin da za ta ce. Kwakwalwarta ta yi blank na ɗan lokaci saboda tsananin mamaki, ta gwalo idanu waje, tana kallon bango kurrrr, yayin da kalaman Mommy suka ci gaba da amsa-kuwa a cikin kanta, “Ashe baki da hankali? Har kin yi wayon da za ki yi abu irin wannan ba ki yi shawara da ni uwar ki ba?!” “Mommy…?” Seeyama ta ambaci sunan a hankali, muryarta na rawa saboda tarin mamaki al’ajabi da baƙin ciki, “Me kike cewa haka ne? Saboda na ce miki na je wajen boka ne yake baki haushi? I thought ke ce za ki fi kowa goyon bayana wajen ganin mun ga bayanta! Ai ko kasheta na yi, ina tunanin kece zaki kama min ita mu binne, kuma na san za ki fi kowa farin ciki da hakan. Don me yanzu zaki riƙa yi min wannan fadan kamar wata yarinya?”
A ɗayan ɓangaren, Hajiya Hauwa ta saki wani nauyayyen numfashi, ganin yadda Seeyama take magana a buɗe ya sa ta fahimci cewa kamar ta saki layi da yawa, don haka sai ta gyara zamanta, a hankali ta sauko daga kan bacin ran da take yi, sannan ta saki wani irin murmushi da babu wanda yake gani, murmushin da ke ɗauke da wani abu daban, ta fara magana da wata sanyayyar murya wacce ta nuna tsananin basira da ƙwarewa, “Seeyama…” Hajiya Hauwa ta kira sunanta a hankali, “Ki saurari abin da zan gaya miki da kyau, ke yarinya ce baki da wayo, waye ya faɗa miki haka ake yi wa kishiya? Daga farawa da Bismillah? Hanyar da za ki bi ba ta zubar da jini ko ta wajen bokaye ba ce wacce za a gano ki a sauƙaƙe.”
Seeyama ta haɗiye wani yawu mai ɗaci, tana sauraron Mommy ɗinta wacce ta canza salo gaba ɗaya, “Kishiya ba a fitar da ita ta hanyar sakarci,” Hajiya Hauwa ta ci gaba da cewa cikin nitsuwa da lissafi, “Dabaru za ki koya, da kissa da kisisina! Ita mace mai hankali ba ta yaƙar kishiya da yaƙin zafi ko tsinuwa, a’a! Da wayo ake cinye ta har sai ta fitar da ita daga gidanta da ranta ba ko kwarzane, ba tare da mijinta da sauran jama’a sun zarge ki da komai ba.” Ta ɗan yi shiru, sannan ta ƙara da cewa, “Amma ke, da za ki kama hanya ki yi tafiyarki wajen boka kamar wacce ba ta da tunani—idan Zayd ya gano hakan, kin san abin da zai faru da ke kuwa? Zai kore ki ne cikin wulaƙanci ba tare da ya kalli fuskar kowa ba! Ke tunda kike kin taɓa ji ance yau gani a wajen wani katon mashirki wai boka da sunan naje ya bani wani sihiri.”
Seeyama ta dafe kanta da ɗayan hannunta, hawaye suka sake cika mata idanu, amma wannan karon ba na tausayi ba ne, na bacin rai ne, na rashin fahimta, “Amma Mommy…” ta fara magana cikin ruɗani, “Ni ya kike so na yi? Naga mata ai haka suke yi mostly, kuma naga Safina ce ta rakani.” “Amma ba irin naki na rashin hankali da son kai ba!” Hajiya Hauwa ta katse ta a tsawace, amma har yanzu muryarta cike take da nutsuwa, “Yanzu dai ki saurari abin da zan gaya miki.” Seeyama ta yi shiru, “Ki ajiye duk wata maganar boka a gefe, ki koma ki zama ‘yar gari mai natsattsiyar zuciya, ki gyara gidan nan yanzu kafin Zayd ya dawo ya sake tarar da shi a watse.” Ta ja numfashi, “Sannan ki nuna masa cewa ke matar kirki ce mai lura da gidan mijinta, ki sauke kai, ki ajiye duk wani uban girman kai da kike ji, ki je ki ba shi haƙuri, kinji ni da kyau.” Muryarta ta ƙara yin ƙarfi, “Duk girman kai da jiji da kai da taƙamar mace, toh bata yi wa mijinta macen da tasan wacece ita maida kanta take ba kowa ba a gaban mijinta ko da kuwa ubanta sarki ne, ki bi shi sau da ƙafa idan yace kiyi ki yi, idan yace bari ma ki bari, ba rashin kunya ba, ba nuna masa ke mace ce kuma kina da right ba.”
Seeyama ta ɗan ɗaga gira, Hajiya Hauwa ta ci gaba, “Kin ga wannan? Shi ne zai sa ya fara kyamar waccan Raihanar ta zama wata aba a idanunsa, ke kuma ya fara ɗaukaka ki a samanta.” Maganar ta shiga zuciyar Seeyama sosai, ta cije leɓenta na ƙasa, fuskarta a murtuke, ta yi shiru na ɗan lokaci tana tunanin maganganun Mommy, duk da cewa ranta bai gama cika da amincewa ba, amma ta san babu yadda za ta yi da hukuncin Mommy—musamman da take neman mafita ido biyu a buɗe, “Toh… na ji, Mommy,” ta faɗa a raunane, “Yawwa, ‘yar albarka,” inji Hajiya Hauwa, “Ki yi abin da na ce miki, kuma karki kuskura ki sake yin wani motsi ba tare da kin nemi shawarata ba, anjima zan kiraki.” Daga nan ta kashe wayar, kat! Layin ya yanke.
Seeyama ta cire wayar daga kunnenta, ta dube ta na wasu seconds biyu kamar tana ƙoƙarin fahimtar abin da ya faru, “Why me…?” Ta fashe da wani sabon irin kuka na takaicin yadda duniya ta juya mata baya a lokaci guda, amma duk da haka, ta san dole ta miƙe, dole ta fara aikin da Zayd ya sa ta, domin lokaci yana tafiya, kuma idan ya dawo ya sake fitowa batayi ba maybe haukan da zai mata sai ya fi na dazu, ta goge fuskarta da tafin hannunta, amma a cikin zuciyarta, maganar Mommy ta tsaya a wuri guda, “Da wayo ake cinye ta…” Seeyama ta ɗan lumshe idanu, Raihana, wannan karon, ba za ta yi gaggawa ba, ba za ta yi hayaniya ba, za ta yi yadda Mommy ta ce, amma ba don ta zama matar kirki ba, a’a, don ta samu abin da take so, sai ta jefa wayar kan gado, ta saki wani tsaki mai cike da takaici da zafin rai, amma tuno cewa Zayd ya ba ta takaitaccen lokaci ya sa ta miƙe da ƙyar, tana jan ƙafafunta tamkar wacce aka yi wa mugun duka.
Ita fa Seeyama ba yar wahala ba ce, ba ta taɓa sanin mece ce wahala ba a rayuwarta, malalaciyar mace ce mai son jiki balai, ‘yar gata ta gaske wacce a gidansu ko cokali ba ta san ta ɗauka ta wanke ba, ko kaya ta cire, watsarwa kawai take yi, ba ta san inda suke ba, sai dai idan tana nemansu bayan kwana biyu ta same su a wanke, a goge, an shirya su cikin tsari a closets ɗinta, hatta undies ɗinta maids ne ke wanke mata su a gida, ba ta ko san yadda ake share gida ko wanke abu ba, balle har ta iya share gida ko ta gyara wuri mai uban girma irin wannan.
Ta fito falon da ke cike da uban shirgin da ita da Safina suka bari, ta tsaya cak tana kallon halin da wajen yake ciki, bacin rai ya sake lullube fuskarta, “This is ridiculous!” Ta faɗa a fili, tana zagaye idanunta da suka kumbura saboda kuka, ta kai hannu ta fara jan ledojin takeaway ɗin ɗaya bayan ɗaya, tana jan wani tsaki duk lokacin da hannunta ya taɓa ɗaya, ita da Safina ne suka tsaya a hanya suka sayi abincin, suka shigo da shi gidan suna dariya suna magana kamar babu wata matsala a gabansu, ba tare da sanin cewa yau ita ce za ta tattara duk wani abin da suka bari ba.
Ta fara tattara ledojin da tana yi tana yatsina fuska kamar wacce ta ɗauki wani abu mai ƙyama, “Look at this mess…” Ta furta a hankali, ta cusa komai a cikin wata babbar leda, ta ɗaure ta sosai, sannan ta fito da ita zuwa compound, da ta buɗe ƙofar compound, ta jefa ledar cikin dustbin da ƙarfi, “Finally,” ta faɗa tana sauke numfashi, sannan ta dawo falon, amma da ta dawo… sai ta tsaya, ta kalli sauran pillows ɗin da suke watse a ƙasa, ta ɗaga gira, “Duk waɗannan ni zan ɗaga?” Amma babu wanda zai amsa mata, ta ja numfashi, ta sunkuya a hankali, ta fara ɗaukar su ɗaya bayan ɗaya.
Bayan mintuna kaɗan, hannunta ya fara gajiya, ta tsaya ta ɗan dafe bayanta, “Why is this thing so hard?” Ta furta cikin takaici, sai ta sake ɗaukar wani pillow, ta kai shi kan sofa, ta dawo, ta ɗauki wani, ta koma, haka ta ci gaba, bayan wasu mintuna, ta fara share ƙasa, a wannan lokacin, fuskarta ta riga ta cika da gumi, ta riƙe mop ɗin da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma tana ɗan dafa bayanta lokaci zuwa lokaci, “Allah na…” Ta yi ƙasa da murya, amma babu wanda ya ji, babu wanda ya zo ya taimaka mata, babu wanda ya ce ta huta, kuma babu wanda ya damu da cewa ita ba ta taɓa yin irin wannan aikin ba.
Tsawon mintuna talatin masu tsanani ta kwashe tana ta kai-komo cikin gidan, tana sharewa da mopping da ƙyar, tana jan numfashi kamar wacce ta yi gudun gaske, hannunta ya fara yin jajir, fatarta mai laushi wacce ta saba da kulawa ta fara nuna mata cewa yau ta shiga wani sabon rayuwa na aure, ta kalli tafin hannunta, ta yi shiru, “Look at my hands…” Ta faɗa cikin murya mai rauni, hawayen da suka taru a idonta suka sake zubowa, wannan karon ba wai saboda Zayd ne kaɗai ba, saboda gajiya ce, saboda takaici ne, saboda baƙin cikin yadda rayuwarta ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci, ta share hawayen da ke zuba a fuskarta da bayan hannunta, amma kafin su bushe, wasu suka sake gangarowa, ta haɗiye kukan da ke neman fito mata, sai suna guda ya fara yawo a cikin ranta, Raihana, ta sake ɗaukar mop ɗin, Raihana, ta ci gaba da sharewa, Raihana, kamar ita ce tushen duk abin da ke faruwa da ita, kamar da ba a aurar da waccan yarinyar ba, da ita Seeyama ba za ta taɓa sanin irin wannan ranar ba, dan tana ganin duk wulakancin da Zayd yake mata yanada alaƙa da auren Raihana da yayi.
Ta dafe baki, tana ƙoƙarin hana sabon kuka fitowa, amma zuciyarta ta ƙi yin shiru, a karo na farko a rayuwarta… Seeyama ta san abin da ake nufi da wahala, ta san yadda gajiya take shiga jiki, ta san yadda hannuwa ke ciwo sabida wani dan aiki da ita awajenta ba za a kirashi da kadan ba, ta san yadda mutum yake ji idan babu wanda zai yi masa abin da ya saba samu a shirye, kuma maimakon wannan wahalar ta sa ta koyi darasi… sai ta ƙara mata tsantsar baƙin ciki, da ƙiyayya, da kuma wani sabon ƙuduri, Raihana, sunanta ya sake ratsawa a zuciyarta, ta share hawaye, ta ɗan ɗaga kai, “Ke ce kika kawo ni nan,” ta furta cikin raɗa, “Ke ce sanadin duk wannan,” ta sake kallon gidan.
A ɗaya daga cikin ɗakunan gidan kuwa, Zayd yana kwance a kan wata kujera mai tsawo, bayansa a jingine da cushion, hannunsa ɗaya a kan goshinsa, shiru ne ya gauraye ɗakin, sai ƙarar air conditioner kawai da ya cika wajen, ba a san ko yana hutawa ba ne ko kuma kawai yana son ya samu ɗan sarari daga duk hayaniyar duniya ba. Sai ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali, Seeyama ce, ta tsaya a bakin ƙofar na ɗan lokaci, kallon da take yi masa ya sha bamban da na farkon lokacin da ta shiga gabansa, kamar ba ita ce waccan matar da yake yi wa ihu ɗazu ba, babu ko alamun fushi ko bacin rai sai ma kalar shagwaba da tayi da fuskar ta tana kallonshi kasa kasa, ta langwabe kanta kaɗan, “Babe…”
Zayd ya ɗago kansa, idanunsa suka sauka kanta, ya kalleta, bai ce komai ba, Seeyama ta matso a hankali, ta sake yarfe hannayenta, sannan ta tsaya gabansa, “I’m done,” har yanzu Zayd bai ce komai ba, “Duk abin da ka ce na yi… na yi.” Ta yi wani irin murmushi, ta ɗan ɗaga hannunta, “Harda mopping… duk na yi.” Zayd ya ci gaba da kallonta, Seeyama ta yi tsammanin zai fara mata magana, ko ya tambaye ta wani abu, ko kuma ya nuna ya ji dadi tayi abinda yace, amma babu komai, kawai ya cigaba da kallonta.
Seeyama ta ɗan motsa a wurin, tana kallonsa da wani irin rashin fahimta, “Babe…?” A zuciyarta ta fara tunanin ko ma ba zai ce komai ba ne, sai bayan wasu seconds, Zayd ya ɗan gyara zamansa, “Good,” kalma ɗaya kawai, Seeyama ta ɗan zaro idanu, ta tsaya tana kallonsa, amma kafin ta fahimci me hakan yake nufi, Zayd ya sauke ƙafafunsa daga kan kujera, ya miƙe, cikin nutsuwa ya zura takalmansa ba tare da ya ƙara cewa komai ba, Seeyama ta tsaya tana kallonsa baki bude, ya wuce kusa da ita, ya buɗe ƙofar, ya fita, Seeyama ta juya kanta tana binsa da ido, amma ya riga ya fice ma ya rufo mata kofar, kafin ma ta fahimci abin da ya faru, sai ta ji ƙarar motarsa daga compound, ta tsaya cak, “Wait…” Ta juya da sauri ta nufi window, ta yaye curtain ɗin da hannu ɗaya, tana kallon compound ɗin, motar Zayd ta riga ta wuce, maigadin ya kama gate ɗin yana mayar da shi a hankali, Seeyama ta tsaya a window tana kallon gate ɗin da aka rufe, fuskarta ta sauya, ta kasa fahimta, “Ya tafi?” Ta furta a hankali, bayan duk wahalar da ta sha… bayan ta yi duk abin da ya ce… kalmar da ya ba ta ita ce kawai— “Good,” sannan ya tafi, ta sauke curtain ɗin a hankali, ta tsaya a wurin tana kallon ƙofar da ya fita, wani irin yanayi ya cika zuciyarta wanda ba ta iya fassarawa ba.
Zayd na fita daga gidan, ba tare da ɓata lokaci ba, ya ɗaga wayarsa ya kira Sameer, ya ba shi umarnin na ya tafi ya siyo duk wani abin amfani na gida, kama daga foodstuffs, veggies, fish, meat, har da duk wani abu na bukata da za a iya buƙata a gida, sannan ya kai wa Seeyama, kamar ko yaushe, Sameer bai bata lokaci ba wajen cika umarnin ogan nashi, ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba, ya tattara komai tsaf, ya cika motarsa da kayan abinci kala-kala, sannan ya nufi gidan, da isarsa, ya yi sa’a mai gadi ya buɗe masa, Sameer ya shigo da kayan ciki, yana ta kwaso su ɗaya bayan ɗaya yana jera su a store din dake manne da kitchen din, ya yi ta kaiwa ba tare da gajiyawa ba, yana duba komai da kyau domin tabbatar da cewa babu abinda bai saya ba.
Sai dai a maimakon ya sami ko kalmar godiya ko ta ‘sannu’ daga matar gidan wacce har a lokacin take nan, fuskar nan kamar wacce ta rasa uwa da uba lokaci ɗaya, abin da ya tarar da shi kawai shi ne tsarabar harara mai cike da huci da mugun kallo da Seeyama ta watsa masa daga nesa, Seeyama kuwa ta ci gaba da kallonsa yana shigo da kayan kamar shi ne ya jawo mata duk abin da ya faru tun safe, Sameer ya ɗan ɗaga gira, ya sauke numfashi a hankali, “Okay… tough crowd,” ya furta a ƙasan ransa, sannan ya koma kan aikin da ya zo yi, Seeyama ta sake yi masa wani kallon gefe, ta yi tsaki, kafin ta juya ta bar wajen rai a bace, Sameer ya bi bayanta da ido na ɗan lokaci, sai ya girgiza kai kawai, amma bai ce komai ba, ya gama aikin da aka sa shi, ya tabbatar da komai yana nan yadda ya kamata, daga nan ya fita daga gidan hankalinsa kwance, ya bar Seeyama da kayan da aka kawo mata da kuma halin da take ciki.