Free chapter · Read without an account
JUST HIS PRESENCE
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER EIGHTY FIVE:85*
*JUST HIS PRESENCE*
*JIDDAAH BARKUM*
———
Yammacin ranar ya sauya salo lokacin da Anty Sadiya, fitacciyar mai gyaran jikin nan da Ummie ta tanada, ta isa gidan. Tsarin gyaran jikin zai ɗauki kwanaki uku ne kacal, amma ko a wannan ranar ta farko da aka yi mata, jikin Raihana ya riga ya fara nuna wani irin glow mai ban mamaki, duk dai dama akwai ragowar na Maman Ihsan, hakan ya sa fatarta ta ɗauki wani irin radiant look, tana sheki da kyallawa, tana na bada wani stunning effect a tare da ita.
Raihana da farko tana ta faman overthinking, tana hiding kanta, tana ganin kamar kowa ya lura da abinda ya faru a tsakaninsu. Duk lokacin da ta ga wani yana kallonta, sai ta ɗan sunkuyar da kanta, heart ɗinta ya ɗan buga, tana tunanin ko akwai wani abu da ke bayyana a fuskarta, gani take kamar a rubuce yake a goshinta, everyone knows.
Amma yadda ta ga kowa a gidan ya natsu, babu wanda ya yi mata wata awkward question, babu wanda ya tambaye ta inda suka je da Zayd, kuma babu wanda ya damu da ko ina Zayd ɗin yake, kowa ya ci gaba da rayuwarsa a normal yadda suka saba, kamar babu wani abu da ya faru, hakan ya sa ta saki ranta gaba ɗaya. A hankali ta fara breathing normally, ba tare da wannan tension ɗin da ta kasance da shi tun dawowarta gidan ba, wannan peace of mind ɗin ne ya ba ta damar sakewa sosai, har ta fara jin kamar komai zai iya komawa normal.
Har ta kai ga can yamma, bayan fitar Anty Sadiya daga gidan, Raihana ta fito daga ɗaki ta nufi kitchen, sanye take da wata simple lawn gown da ɗan ƙaramin veil da ta rufe kanta da shi, fuskarta ta yi haske, babu wannan tiredness ɗin da ke tattare da ita tunda ta shigo gidan, sai wani irin calmness da freshness suka bayyana a tare da ita, sai ta nufi wajen Kubura, tana kokarin taimaka mata wajen haɗa abincin dare, “Anty Kubura, bari na taimaka miki,” ta faɗa a hankali, tana ɗaukar wasu daga cikin kayan girkin. Kubura ta ɗan kalleta, murmushi ya bayyana a fuskarta, “Anty Rayy, ki zauna mana, kin yi gyaran jiki yau me za kiyi a kitchen kuma.” Raihana ta ɗan yi dariya, ta girgiza kai, “No, it’s okay zanyi pls bari na taimaka miki.” A dole Kubura ta barta, dan ta san Raihana idan ta riga ta shigo kitchen din nan duk abinda zata ce ba zai sa ta fasa abinda tazo yi ba.
Yanayin yadda ta ke moving cikin kitchen ɗin cike yake da wani irin freshness da walwala, ta na motsi cikin sauƙi, tana ɗaukar abu ɗaya bayan ɗaya, wani lokacin ma ta yi ɗan humming a hankali ba tare da ta sani ba, hakan ya nuna cewa a yanzu ta fara mantawa da stress ɗin da ta fuskanta a baya, tana kuma maido da kanta a hankali, for the first time that day, Raihana looked genuinely at peace.
Bayan Magrib suna zaune a lounge ɗin, ita Suhaila ta cire mayafin daga yafen ta daura shi a kanta, tana zaune a ƙasan carpet ita da Suhaila suna kallon abu a wayar Suhaila, suna ɗan dariya lokaci-lokaci, wani lokacin Suhaila ta ɗan matsa wayar kusa da fuskarsu, wani lokacin kuma ta yi dariya tana girgiza kai, sai kawai Suhaila ta yi zooming wani hoton wata model, “Kingaa wannan gown ɗin? Irinta za a ɗinka miki da wannan material ɗin naki.” Raihana ta zaro ido, ta ɗan matsa kusa da wayar tana kallon hoton sosai, “Kaii! Ai bazan iya sawa na fito ba.” Suhaila ta kyalkyale da dariya, har ta dafe cikinta, “Haba Anty Rayy! Meye da wannan rigar toh da bazaki iya sawa ba?” Ta sake zooming ɗin hoton, tana kallon Raihana da murmushin zolaya kamar wadda ta riga ta san amsar.
Raihana ta sake kallon rigar, sannan ta ɗan ɗaga gira tana girgiza kai a hankali, fuskarta ɗauke da murmushi, amma a fili take cewa ba ta da niyyar amincewa, “Allah, bazan iya ba.” Suhaila ta sake fashewa da dariya, “Anty Rayy, you’re too shy wallahi!” Raihana ta yi murmushi kawai, ta sunkuyar da kanta tana kallon wayar, kamar ba ta son ci gaba da wannan maganar, “Ni fa irin waɗannan rigunan ba na iya sawa, no way.” Suhaila ta ɗan yi mata kallon gefe, tana murmushi, “Hmm… we’ll see about that.” Raihana ta ɗaga kai da sauri, “Me za ku gani?” Suhaila ta kyalkyale da dariya, ta sake komawa kan hoton tana zooming ɗin gown ɗin, “Nothinggg, Anty Rayy.” Raihana ta girgiza kai tana murmushi, sannan ta ci gaba da kallon hotunan da Suhaila ke nuna mata.
Suna can suna dariyarsu har Imran ya shigo, basu sani ba, ya tsaya a bakin lounge, ya riƙe kugunsa yana kallonsu da dariya a fuskarsa, yana girgiza kai a hankali, Raihana kam instinct ɗinta ne ya bata cewa akwai mutum, a hankali ta ɗago kanta, sai idonta ya sauka kan Imran, Suhaila ma ta dago kai, “Yah Imuuu! Kaine? Kawai ka tsaya kana kallonmu?” Suhaila ta faɗa tana tashi zaune, tana kallonsa da ɗan harara, Imran ya sake faɗada dariyar da ya ke yi, yana takowa inda suke, “Toh, yaushe zaku ji kun haɗa kai ku na ta dariya a waya?” Ya faɗa yana kallonsu da murmushi, kamar ya kama su da wani secret. Raihana ta ɗan yi murmushi, “Ina yini.” Sai ya juyo gareta, “Lafiya kalau, Amarya, ya gida?” “Alhamdulillah,” ta amsa a hankali, tana ɗan sunkuyar da kanta, sai ya kalli Suhaila, “Me kuka dafa ne? Yunwa kamar an yashe min kayan cikina.” Suhaila ta yi dariya, “Jollof rice ne,” sai ta kalli Raihana da murmushi, “Amarya ce ta dafa.” Imran ya yi dariya, ya ɗan ɗaga gira, “Toh, a sammin Amarya, ranar nazo zan sha, kunu mijinki ya min rowa.” Suhaila ta fashe da dariya, “Yaa Imuu bakayi niyyar sha ba dai!” Raihana kuma kawai tayi murmushi, ta sunkuyar da kanta, sannan ta miƙe a hankali ta nufi kitchen, Suhaila kuma suka ci gaba da magana da Imran.
A kitchen kuwa, Raihana ta fara haɗa masa abincin cikin nutsuwa, ta ɗebo jollof rice ɗin cikin plate mai kyau, ta gyara shi neatly, ta saka salad a gefe, sannan ta ƙara masa juice da bottled water, komai ta shirya shi sosai, cikin clean and well-arranged presentation, tray ɗin ya yi kyau sosai, bayan ta gama, ta ɗauki abincin ta fito da shi a hankali, ta kalli Imran, “Nan za’a kawo maka ko a dining?” Imran ya yi dariya, ya ɗaga hannu kamar mai dakatar da wani abu, “Ai Amarya, kawo nan kawai, wannan hawa dining ɗin duk wahala ce.” Ya faɗa yana dariya.
Raihana ta ɗan yi murmushi, ta karaso kusa da shi dauke da tray din, sai ta juya ta janyo stool, ta ja shi kusa da Imran, sannan ta ɗan rankwafa a hankali, tana shirin ɗora masa plate ɗin abincin a kai, a dai-dai lokacin ne… ƙofar lounge ɗin ta sake buɗewa, Zayd ne ke shigowa a nutse, takun sawunsa a hankali yake, fuskarsa kuma a nutse take, kamar yadda ya saba, amma da ya shigo, idanunsa suka sauka kan Raihana, ta ɗan rankwafa, tana ƙoƙarin ɗora wa Imran abincin akan stool, veil ɗinta yana ɗan zamewa daga kanta, frontage hair dinta gashi nan tass a bude, bata ma lura ba dan gabadaya ta mai da hankali kan abin da ke gabanta.
Zayd ya tsaya na ɗan lokaci, idanunsa suka tsaya a kanta, ba tare da ya ce komai ba, Raihana kuwa har yanzu bata san ya shigo ba, Imran da yake zaune kujerar dake facing kofa ya ɗago kai, sai ya ga Zayd a tsaye kawai, Imran kuwa, being the jovial cousin that he was, sai ya fashe da wata muguwar dariya, ya kalli Zayd, ya kuma kalli abincin da Raihana ta kawo masa, sai ya girgiza kai yana murmushi, “Rascal! Yau duk baƙincikinka zan ci abincin matarka, ai banso ka shigo yanzu ba, na so sai na cinye abincin tas, sai na baka labari.” Ya faɗa yana dariya, kamar da gangan yake ƙara tsokanar Zayd. Suhaila ta fashe da dariya, tana kallon Zayd da gefen ido, kamar tana jiran reaction ɗinsa.
Raihana kuwa, tunda kamshinsa ya sauka a falon, gabanta ya fara mugun bugawa, tana jin kamar kowa dake wajen na iya jiyo sautin bugawar zuciyarta, amma ta dake ta ƙi ɗagowa, ta ci gaba da abin da take yi kamar bata lura da shi ba, tana ƙoƙarin controlling ɗin reaction ɗinta, sai ta ƙarasa abinda za tayi, sannan a hankali ta juya tana gyara veil ɗin da ya zame mata, ba ta kalli inda yake ba, ta koma kusa da Suhaila, tayi zamanta a hankali, Zayd ya bi bayanta da kallo, idanunsa suka sauka kan veil ɗin da ta gyara, sannan suka tsaya na ɗan lokaci, yanda mayafin ko gadon bayanta bai sauko ba balle ya rufe duwawunta, har ta zauna, bai daina kallonta ƙasa-ƙasa ba, fuskarsa kuwa babu kowanne expression just cold, quiet, as if nothing had happened.
Lokacin da ya shigo gidan zuciyarsa, niyyarsa shi ya wuce sama kawai dan ya balain gajiya, bai shirya zama a lounge ɗin ba, ballantana ya shiga wata magana da kowa, amma haka kawai… sai ya ga kansa ya zo ya zauna a gefen Imran, har lokacin bai ce komai ba, Imran ya kalle shi, murmushi yana ƙoƙarin ɓoyewa a fuskarsa, Suhaila kuwa ta kalli Zayd, sannan ta kalli Raihana, sai ta ɗan cije leɓenta tana hana kanta dariya, Raihana kuwa ta sunkuyar da kanta, hannunta yana wasa da gefen veil ɗinta, heart ɗinta kuwa, wani mahaukacin bugu take, tana so ta bar wajen amma ta rasa ta ina, addua kawai ta fara, Allah ya kawo mata sanadin da zata bar wajen nan, sai ta juya a hankali ta dauki wayar dake gefenta, ta yi kamar tana kallon abin da ke wayar Suhaila, amma ko kalma ɗaya daga cikin abin da take kallo ba ta shiga kanta ba, because she could feel his presence right there, idanunshi na yawo a kanta, and somehow, that was enough to make her nervous.
Suhaila ta ɗan maze, tana maida dariyarta, sannan ta kalli Zayd, “Akhie, a kawo maka abinci ne?” Zayd bai ko kalli inda take ba, kamar bai ji ta ba, kawai sai ya zaro wayarsa daga aljihu ya fara dannawa, idanunsa suna kan screen ɗin, ya musu banza gaba ɗaya, Imran kuwa ya cika bakinsa da abinci, ya ɗan tsaya yana taunawa kafin ya kalli Suhaila, sai ya ce, “Kawai barshi Suhaila, zan rage masa.” Ya faɗa cikin raha, yana ɗan murmushi, sannan ya kalli Zayd, “Rascal, a ɗauko maka spoon ne mu ci tare?” Zayd ya ɗago idanunsa daga wayarsa a hankali, ya kalli Imran na ɗan lokaci, fuskarsa babu ko ɗan alamun dariya, sai ya ce a sanyaye, “You eat yours. Allah has already decided your share.” Imran ya fashe da dariya, ya girgiza kai, “See this guy ko dake Allah ka ce amma ai idan ta kaine saidai na mutu da yawa!” Suhaila ma ta kasa riƙe dariyarta, ta rufe bakinta da hannu, Raihana kuwa ta yi murmushi kaɗan ba tare da ta ɗago kai ba, Zayd ya sake komawa kan wayarsa, kamar babu abin da ya faru.