Free chapter · Read without an account

HIS JEALOUSY EYES

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN


*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER EIGHTY SIX:86*

* HIS JEALOUSY EYES*

*JIDDAAH BARKUM*

———

Hancin Zayd babu abinda yake kwaso masa sai azababben kamshin Raihana da ya gama gauraye ko’ina a cikin falon, hankalinsa ya kasa kwanciya kan wayarsa, kawai pressing yake ba tare da ya san abinda yake ba, yatsunsa na yawo akan screen ɗin ba tare da ko ɗan fahimtar abin da yake dannawa ba. Ita kuma, kasancewarsa a wajen ya sa yanayin falon ya canza mata gaba ɗaya, kawai dauriya take da bata tashi ta bar wajen ba, a hankali ya ɗan ɗago idanunsa ƙasa-ƙasa, ya sauke su kan Raihana inda take zaune kusa da Suhaila, tana ɗan janyo gefen mayafinta dake sake zamewa daga gashinta mai bala’in sulbii. Kai, kana ganin yanayin zaman kasan a takure take, dan tsaff take jin nauyin idanunsa dake bin jikinta da kallo, wanda karyane kace wai Zayd ya ma san akwai ta a wajen.

Shiru ne ya biyo bayan lamarin, babu mai magana a tsakaninsu, shi da ita kowa yayi pretending as if yana danna wayar hannunshi, while neither of them had the slightest idea what the other was actually doing with the phone, sai dai kawai Imran da Suhaila da suke magana suna dariya.

Amma hanzarin katse wannan yanayin ya zo ne lokacin da Ummie ta sauko ƙasa da misalin ƙarfe 7:00 na dare, sanye take da wata kyakkyawar doguwar abaya baƙa, tare da wani mayafi mai girma da ta yafa, wanda ya fito da cikakkiyar kalamarta, a hannunta tana ɗauke da ƙaramar jaka da kuma wayarta, ta ɗan tsaya tana kallonsu a falon. Imran ya ɗan sosa kai, ya gyara zamansa, sannan ya yi murmushi, “Barka da dare, Ummie,” ya faɗa yana murmushi, Ummie ta yi murmushi tana kallonsa, “Kazo kenan?” Ya ɗan saki ƙaramin dariya, “Eh wallahi, yunwa ce ta yar da ni a nan wajen, shi yasa ban karaso mun gaisa ba, dama ina cewa zan gama sai nazo…” Ta ɗan jinjina kai, “Toh, ya mutanen gida?” “Lafiya lau suke wallahi,” ya amsa yana wannan dariyar tashi. Ummie ta kalli Zayd, wanda ya ɗan langwabe kai yana kallonta ƙasa-ƙasa, ta girgiza kai kaɗan, “Sai yanzu kenan ka shigo? Ko tare kuke da Imran ne?” Zayd ya girgiza kai a hankali, “No, I just came back, a nan ma na sameshi.” “Okay.”

Ummie ta kalli su Suhaila da Raihana, “Ba nace muku zamu fita bane? Ku tashi mu tafi dan ina son mu dawo da wuri.” Suhaila ta miƙe tana dariya, “Wallahi Yaa Imuu ne ya tsaya yana sa mu dariya, shine ma ya mantar damu fita gaba ɗaya,” ta faɗa tana gyara mayafin kanta domin ta yafa shi sosai. Raihana ma ta miƙe a hankali, “Bari na ɗauko hijab,” ta faɗa da wata sanyayyar murya, Ummie ta kalleta da rigar jikinta, sai ta girgiza kai, “Wannan mayafin ma is okay, yayi, ku muje kawai.” Raihana ta ɗan yi gaba, Suhaila na biye da ita har suka wuce gaban Ummie.

Zayd ya zuba musu ido kawai yana kallonsu, bai ce komai ba, Ummie ma ta juya zata bi bayansu kenan, sai muryar Zayd ta dakatar da ita, amma abin mamaki, ya yi maganar ne da wata irin shagwaɓa ta yara kanana, kamar wani yaro ɗan goyo, “Ummieeee…” Ya ja sunan yana wani turo baki, ba Ummie kaɗai ba, har su Suhaila da Raihana sai da suka juyo da sauri wallahi, Raihana ma ta tsaya cak, idanunta suka buɗe kaɗan, Ummie ta kalleshi tana dage gira, “Uhn? Ya akai?” Sai ya fara magana da wata irin shagwaɓa, “Ban ci komai ba fa since morning, zuwa na kenan, kuma zaki fita baki bani abinci ba!”

Ummie ta tsaya kawai tana kallonshi, kamar tana ƙoƙarin tabbatar da cewa shi ɗin ne da gaske yake wannan maganar, Raihana kuwa ta saki baki da uban mamaki wanda ya kusa kashe ta, wannan babban mutumin sangameme da shi, ya buɗe baki wai zai yi shagwaɓa kamar wani ƙaramin yaro?! In front of everyone?! Ko kunyar jama’ar dake wajen ma bai ji ba! Kafin Ummie ma tayi magana, Imran ya riga ta farawa, “Kai! Rascal, wallahi kaji tsoron Allah!” Sai ya juya ya kalli Ummie yana nuna mata plate ɗin da ya gama cin abinci, “Kinga, Ummie, sai da na ce masa yazo mu ci, Suhaila ma tace masa ko ta zubo masa abinci, wallahi babu wanda ya kalla a cikinmu! Amma yanzu ganinki shine wai zai ci abinci?” Zayd ya wani zuba masa wata uwar harara kamar mace, kafin ya ce, “Abincin da ka gama ci kana zubawa yawu, ka buɗe baki kana magana akai, shine zan ci?” Sai ya sake kallon Ummie da idanu cike da pleading, amma bai ƙara cewa komai ba.

Ummie ta sauke numfashi, ta girgiza kai, “Toh, bari Kubra ta zubo maka.” Sai ya make kafaɗa, “Ah-ahh, Ummie, ni kee…” Raihana takaici ya isheta, ta ji kamar ta rufeshi da duka, ta dan lumshe idanunta, ta haɗiye abin da zata faɗa, tana tunanin what is wrong with this man? Ummie ta girgiza kai kawai bata ce komai ba, ta juya ta nufi kitchen ɗin dan ta hado masa abinci da kanta. Zayd ya kalli Raihana da fuska a haɗe, kamar ba shi ne ya gama chalikanci ba yanzu-yanzu, ya miƙa mata wayarshi, “Go and plug it in to charge for me in my room.”

Raihana ta kalli wayar, sannan ta kalleshi da wani irin kallo, Suhaila da Imran kuwa sai suka baki suna kallon ikon mai sama, amma babu wanda ya iya cewa komai, Raihana ta haɗiye yawu saboda tsananin uban kallon da yake jefa mata, dole ta ƙarasa ta karɓa, ba wai don tasan abin da zata yi ba, dan gaskiya ita har yau ma bata san ina ne ɗakin nasa ba, kawai dai tasan akwai wani corridor da yake bullowa daga cikinshi a upstairs, nan kaɗai ta sani, haka ta nufi hanyar sama, jama’ar falon suka bita da kallo. Tana gama bace wa daga ganinsu, Zayd ya miƙe ba tare da ya kalli kowa a cikinsu ba, ya bi bayanta, sai da ya bace bat da gani, Suhaila ta kalli Imran wanda har lokacin yana kallon stairs ɗin da uban mamakin rainin hankalin da Zayd ya dankara musu.

Suhaila ta tafa hannayenta tana zama a kujerar gefenta, “Yaa Imuu!” Sai Imran ya juyo, “Ka ga abinda na gani ko?” Sai lokacin Imran ya samu dama, aikuwa ya fashe da wani irin dariya mai balain ƙarfi, ya riƙe cikinsa yana girgiza kai, “Waton rascal duk ya maida mu yan iska…” Ya kasa ƙarasa maganar saboda dariyar ta ƙi bari. Suhaila ta ja uban numfashi, tana zuba tagumi da hannaye biyu, amma har yanzu idanunta na kan upstairs ɗin kamar Zayd da Raihana za su sake bayyana a gabanta, Imran kuwa yana kallonta yana murmushi, yana girgiza kai dan ba karamin goge mai hadda Zayd yayi ba.

Raihana ta ƙarasa corridor ɗin upstairs ɗin a hankali, wayar Zayd a hannunta, ta ɗan tsaya tana kallon gabanta, rooms ɗin suna gefen corridor ɗin, amma ita ba ta taɓa zuwa nan ba, ta ɗan kalli gefe da gefe kafin idanunta su tsaya kan wata ƙofa guda ɗaya, “Maybe nan ne…” ta faɗa a ranta, ta matso kusa da ƙofar, sannan ta tura ta buɗe. Da ta shiga, sai ta tsaya cak, idanunta suka fara yawo cikin ɗakin, room ɗin ya kasance neat sosai komai yana a inda ya dace, babban bed ɗin yana gyare sosai, pillows ɗin suna a jere, curtains ɗin an ja su da kyau, yayin da kayan da ke cikin room ɗin suke simple amma expensive-looking, babu wani abu da ya yi yawa, komai clean ne, organized kuma yana bada irin wannan serious CEO aura ɗin Zayd, Raihana ta ɗan tabe baki, “Hmm…” Sai ta fara neman inda charger ɗin yake, ta kalli bedside table, babu, ta kalli ɗayan gefen, babu, ta ɗan matsa kusa da desk ɗin tana dubawa, hannunta har ya fara motsawa kan wasu abubuwan da ke saman desk ɗin, “Where is this charger?” ta faɗa a hankali.

A lokacin ne karar ƙofar ta sa zuciyar Raihana bugawa, sai ta tsaya cak a hankali, ta juya, Zayd ne, ya shigo a hankali, ya maida ƙofar ya rufe, sai ya tsaya a jikin ƙofar na ɗan lokaci, ya ɗaga hannayensa ya haɗe su a kirjinsa, kansa ya ɗan karkace kaɗan, yana watsa mata wai shegen kallo, wani irin kallo yake mata, Raihana ta kasa motsi na seconds kaɗan, idanunta suka sauka ƙasa immediately, yaushe ya biyo ni? Zayd bai ce komai ba, sai kawai wannan kallon nan nasa yake yi mata quiet, steady, kuma kamar yana jin daɗin ganin yadda ta rikice. Raihana ta haɗiye yawu, “Charger…” ta faɗa a hankali, kamar tana yi wa kanta bayani, sai ta juya da sauri ta cigaba da war gaza kayan wajen kamar tana neman charger din, Zayd har yanzu yana tsaye shiru yana cigaba da watsa mata wannan kallon, sai kawai ya ɗan ɗaga gira.

Raihana ta ƙara sunkuyar da kanta, tana neman charger ɗin kamar ita ce abu mafi muhimmanci a duniya a wannan lokacin, amma a zuciyarta… ya Allah, why did he follow me? A hankali Zayd ya fara takowa gabanta, one step, sai kuma wani, the more ya tako, the more tashin hankalin Raihana ya ƙaru, ta kasa kara ɗaga kai ta juyo balle ta kalleshi, heart ɗinta ya cigaba da bugawa da sauri, yatsunta suna motsi a hankali kamar tana ƙoƙarin nemo wani abu da zai rage mata wannan nervousness ɗin, domin har yanzu bata manta da haduwarsu ta safe ba, kowane irin tunani game da abin da ya faru yana dawowa mata a hankali daki daki, wanda tuno hakan kadai na sa taji kamar ta saki fitsari a wajen.

Zayd kuwa bai yi sauri ba, a hankali yake takowa, idanunsa a kanta, har ya zo dai-dai inda take, Raihana ta ɗan sake sunkuyawa still scattering the items on the desk pretending tana neman charger, sai Zayd ya sa hannu ya finciko hannunta, a razane ta saki wata ƙaramar ƙara, kafin ta ankara, ta fado jikinsa ta dire kai tsaye a kan faɗadden kirjinsa, tana zaro manyan idanunta waje saboda tsananin tsoro da ruɗani, hannunta ya makale a kirjinsa, numfashinta ya tsaya na ɗa seconds, yayin da Zayd ya riƙe ta sosai yana kallon fuskarta kurrrr.

Raihana ta ɗaga idanunta a hankali, su biyu suka haɗa ido, ta yi saurin sauke nata, “Charger…” Kamar charger ɗin nan ne kaɗai zai iya kawo mata agaji a wannan lokacin, muryarta ta fito ƙasa-ƙasa, cike da kunya da tashin hankali, shi kuwa Zayd bai ce komai ba, kawai yana kallonta ne da wannan mayun idanun nashi masa sakata rawar sanyi a take. Raihana ta ƙara haɗiye yawu, ya Allah… ta so ta ja hannunta ta koma baya, amma yadda yake tsaye gabanta ya sa ta kasa sanin abin da za ta yi, gashi kuma bayanta desk ne, Zayd kuwa ya ɗan matsa fuskarsa kusa da ita, still wearing that unreadable expression, bai ce komai ba, kawai idanunsa suka sauka daga fuskarta zuwa gashinta, mayafinta ya ɗan zame, diye da rabin gashinta ya fito a fili a bayyane.

Zayd ya tsaya yana kallon yadda gashin ya fito, nan take wani scene na dazu ya dawo masa a rai, haka mayafin nata ya zame a gaban Imran, ya tuna yadda ta yi saurin gyara shi bayan ta lura, ya dan lumshe idanunshi yana jin yanda zuciyarshi ke wani azababben bugawa, Raihana kuwa bata san me yake tunani ba, tana tsaye a gabansa cikin rikicewa, hannunta har yanzu yana hannunsa, sai ta sake motsa baki a hankali, muryarta tana rawa, “Charger…” Amma Zayd bai motsa ba, ya kalleta kai tsaye, fuskarsa babu ko ɗan murmushi, sai ya ce a hankali, “Is Imran your mahram?” Raihana ta ɗago idanunta a firgice, Zayd ya ɗan sunkuyo gare ta, “Da za ki je inda yake a haka…” ya dakata na ɗan second, idanunsa suka sauka kan mayafinta da ya sake zamewa, “…kina da hankali kuwa?” Raihana ta kasa magana, Zayd ya ƙara matsowa kusa, sai ya ɗan sunkuyo, kamar yana tabbatar da wani abu, kamshin dake jikinta ya sake bugar cikin hancinsa, wannan kamshin, kamshin da ya cika falon gidan kenan tunda ya shigo gidan, abinda yayi masa maraba kenan, ya tsaya na ɗan moment, so it was on her, aikuwa ita ce ke wannan azababben kamshin, a hankali ya dago kansa, idanunsa da suka dan rine suka koma kan nata, “Har da wannan kamshin kika je wajen shi?” Muryarsa ta sauya, ta yi ƙasa, ta yi nauyi, Adam's apple ɗinsa ya motsa yayin da ya haɗiye yawu.

Raihana ta fara girgiza kai da sauri, “A’a… a’a wallahi!” Ta fara magana cikin sauri, “Muna falon ne… yazo, shine yace—shine yace zai ci abinci… wallahi a nan ya same mu.” Ta kasa tsara maganar sosai saboda tashin hankalin da take ciki, Zayd ya cigaba da kallonta kawai, Raihana ta ƙara girgiza kai, “Ni ban je wajensa ba… wallahi…” Sai ta ɗan ja hannunta a hankali, tana son ta samu space, amma Zayd bai saketa ba, kawai ya cigaba da zuba mata wannan lumshashun idanun nasa wanda su kadai ba tare da kowacce kalma ba sun isa su ladabtar da ita.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.