Free chapter · Read without an account

CONTINUATION FROM THE ARMAAN FAMILY

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN


*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER EIGHTY NINE:89*

*CONTINUATION THE ARMAAN FAMILY*

*JIDDAAH BARKUM*

————

Abie da Ummie sun yi matuƙar jin haushin abin da suka gani, bayan wannan surprise visit ɗin, Zayd ya sha warning sosai daga mahaifinsa da Ummie, musamman saboda irin yadda suka tarar da Felicia a gidansa da kuma yadda kusancinsu ya fara zama abin da mutane za su iya fahimta ta wata hanya daban. Zayd kuwa ya yi musu bayani cewa Felicia ba kowa ba ce a wajensa, ba kuma budurwarsa ba ce, amma Abie da Ummie ba su gamsu da hakan gaba ɗaya ba, kafin su bar New York, Zayd ya yi musu alkawarin cewa zai sa Felicia ta bar gidan, ya ce ba zai sake barinta ta zauna a wajensa ba.

Amma da Abie da Ummie suka tafi, Felicia ta koma gidan kamar babu abin da ya faru, Zayd kuwa wannan karon ya fusata sosai, ya gaya mata a fili cewa ba za ta ci gaba da zama a wajensa ba, sai Felicia ta fashe da kuka, ta ce ba ta da kowa a New York yanzu, ba ta da wanda za ta iya komawa wajensa, kuma har yanzu tana jin tsoron mutanen da suka yi mata barazana a wancan daren, a cewarta, Zayd ne kaɗai mutumin da ya tsaya mata lokacin da kowa ya juya mata baya, Zayd ya yi shiru, ba don yana son ya ci gaba da zama da ita ba, amma saboda ya san cewa idan ya kore ta kawai ba tare da ya tabbatar da inda za ta je ba, zai bar ta cikin wani hali da bai kamata ta shiga ba.

Daga ƙarshe, sai ya nemo wata yarinyar yar Najeriya da take karatu a school ɗinsu, mutuniyar shi ce sosai da ya sani kuma ya yarda da ita, ya yi magana da ita, ya tabbatar da cewa Felicia za ta iya zama a wajenta, daga nan aka shirya mata wani apartment, Felicia ta koma can, Zayd kuma ya ɗauki nauyin biyan rent ɗin gidan, haka aka samu mafita, Felicia ta bar gidan Zayd, amma hakan bai sa ta bar rayuwarsa ba.

A school kuwa, duk da sabon arrangement ɗin, Felicia ba ta daina bibiyar Zayd ba, idan ta gan shi, sai ta je wajensa, idan ya zauna da friends, sai ta samu hanyar shiga cikin conversation, idan ya yi ƙoƙarin guje mata, sai ta sake bayyana a gabansa kamar babu wani abu da ya faru, Zayd kuwa ya yi ƙoƙarin ɗaukar komai da calmness, a wajensa, ya riga ya sa iyaka, amma Felicia? A wajenta, babu wani abu da ya canza, kuma a hankali, wannan ya zama farkon wani sabon yanayi tsakanin su inda Zayd yake ƙoƙarin sanya distance, yayin da Felicia take ƙara ƙoƙarin kusantowa.

Watarana, bayan sun gama lectures, Zayd yana fitowa daga cikin school building da wayarsa a hannu, Felicia ta same shi a parking lot, “Zayd!” Ya tsaya ya juya ya kalleta, Felicia ta iso gabansa tana murmushi, “My birthday is tomorrow,” Zayd ya daga gira kadan, “Okay,” Felicia ta yi dariya, “Just okay?” “Me kike so in ce?” “Come to my birthday party,” Zayd ya kalleta na wasu seconds ba tare da ya ce komai ba, daga nan ya ce cikin calm voice, “Kin san bana zuwa irin wuraren nan, ko?” “I know,” “Then why are you asking?” “Because I want you there,” Zayd ya sauke numfashi, “Felicia…” “Please, Zayd, just this once,” ya yi shiru, Felicia ta ci gaba da insisting, tana kokarin ganin ya amince, “It’s my birthday, I don’t want you to disappoint me,” Zayd ya sake kallonta, bai so ba, amma saboda Felicia ta dage, kuma ba ya son ya bata mata rai a ranar birthday ɗinta, daga karshe ya ce, “Fine, zan zo,” Felicia ta yi murmushi nan take, “Really?” “Yeah,” “Promise?” “Felicia,” ta yi dariya, “Okay, okay, I’ll see you tomorrow.”

Washegari da yamma, Zayd ya je wajen birthday ɗin kamar yadda ya yi alkawari, simple, babu wani shiri na musamman a kansa, ya zo ne a matsayin normal guest, ya gaishe da Felicia sannan ya zauna a gefe yana kallon yadda ake gudanar da komai, amma Felicia kuwa kamar ta samu wani abu da ta dade tana jira, “Everyone! Look who came!” Zayd ya juya ya kalleta, Felicia ta rike hannunsa, “This is Zayd,” ta fara gabatar da shi ga mutane daya bayan daya, “My best friend,” “My classmate,” “The guy I told you about,” Zayd ya fara jin rashin dadi, ya yi mata wani kallo na gargadi, amma Felicia tana cikin happiness, bata ma kula da shi ba, “Zayd, come here,” ya bi ta, “Say hi to them,” “Hi,” Felicia ta yi murmushi kamar ba komai, wani ya ce, “Ohhh, so this is Zayd?” Felicia ta yi dariya, “Yes!” Zayd ya dan sauke kansa, he was already regretting coming, amma bai so ya kunyata Felicia a bainannasi, saboda haka ya yi hakuri, ya tsaya, ya gaisa da mutane, ya amsa tambayoyi da wasu daga cikin mutanen ke masa, ya kuma bar Felicia ta yi farin cikinta.

Party din ya ci gaba har zuwa dare, music, laughter, food, drinks komai yana gudana, Zayd bai zaune da yawa ba dan ya fara tunanin barin wajen ma, amma dai ya zauna yana kallon mutane, lokaci zuwa lokaci yana duba wayarsa, wani friend din su a school ya zo gabansa da wani glass, “Here,” Zayd ya kalleshi, “What is it?” “Juice, naga kana ta zaune baka sha komai ba tunda kazo,” ya karba, bai yi tunanin komai ba, ya sha, sai ya sake ajiye glass din, amma bayan wasu mintuna, wani abu ya fara canzawa, da farko sai ya ji jikinsa ya yi nauyi, ya yi kokarin canza position ɗinsa, sai kansa ya fara nauyi, ya lumshe idanunsa na seconds sannan ya bude su, Felicia wadda take kusa da shi ta lura, “Babe, are you okay?” Zayd bai amsa nan take ba, ya dafe goshinsa, “Yeah…” Voice ɗinsa ya fara yin kasa, Felicia ta kalleshi sosai, “Are you sure?” Zayd ya yi kokarin tashi, amma kafafunsa suka kasa daukar jikinsa yadda ya saba, ya sake zama, Felicia ta matso, “Okay, lemme take you upstairs, you need to rest,” Zayd ya kalleta da idanun da suka fara yin nauyi, “I’m fine…” “No, you’re not,” ta kama hannunsa, a wannan lokacin Zayd bai da karfin yin musu, ta taimaka masa ya tashi, sannan ta kai shi wani daki da ke can gefe, ta kwantar da shi a kan bed, Zayd ya lumshe idanunsa, Felicia ta tsaya tana kallonsa, “Just sleep, okay?” Bai amsa ba, jikinsa ya yi sanyi, hankalinsa yana tafiya yana dawowa, Felicia ta juya kamar za ta fita, a take, Zayd ya kama hannunta, ta juyo, ya bude idanunsa kadan, amma kafin ya iya fahimtar abin da yake faruwa, consciousness dinsa ya kara dusashewa, daga nan… labarin ya sauya.

Bayan wani lokaci mai tsawo, Zayd ya fara dawowa hayyacinsa, numfashinsa ya yi nauyi, ya bude idanunsa a hankali, na farko bai fahimci inda yake ba, ya kalli ceiling, ya lumshe idanunsa sannan ya sake budewa, kansa yana masa wani mugun ciwo, jikinsa yana da wani irin weakness da bai taba ji ba kamar an sa itace an buge shi, ya yi kokarin tashi, sai ya tsaya, something was wrong, ya kalli gefensa, Felicia tana zaune kusa da bed, tana kuka sosai kamar ranta zai fita, hawayenta suna zuba ba kakkautawa, Zayd ya kalleta na wasu seconds, fuskarsa cike da confusion, “Felicia…” Ta daga kanta, Zayd ya yi shiru, yana kallonta kamar mutum da yake kokarin hada pieces na wani abu da bai fahimta ba, “What happened?” Felicia ta qara fashewa da uban kuka sosai, Zayd ya daure fuska, “Felicia… what happened?” Ta rufe fuskarta da hannuwanta, shi kuwa ya zauna a hankali, yana kallonta, still confused, bai san abin da ya faru ba, amma wani abu a cikin zuciyarsa ya gaya masa cewa this was not normal.

Bayan da Zayd ya fahimci abin da ya faru, ya dade zaune a gefen gadon yana kallon kasa, bai sake yin magana ba, kawai ya rike kansa da hannuwansa yana ta salati a hankali, zuciyarsa cike da wani irin tashin hankali da shi kansa bai san yadda zai bayyana shi ba, ya dade haka kafin daga karshe ya mike da kyar, ko motar da ya zo da ita bai bi ta kanta ba, ya fita daga wajen kawai ya tsaya a gefen titi ya dauki taxi, a cikin motar kuwa, ya yi shiru gaba daya, idanunsa a kan window, amma hankalinsa yana can, what happened? Daga yanayin da ya ganshi kuma ya ganta, ya san ya kusanci Felicia, ya san ya kasance a dakin, amma daga lokacin da jikinsa ya fara nauyi, abubuwan da suka biyo baya sun kasance kamar wani blank space ne a cikin memory dinsa, ya rufe idanunsa, ya bude su, ya sake tuna abin da ya iya tunawa, amma duk lokacin da ya kai wannan bangaren, sai hankalinsa ya tsaya, ya kasa, bai iya hada komai ba.

Da ya koma apartment dinsa, bai samu sukuni ba, ya yi ta yawo daga daki zuwa daki, ya zauna, ya mike, ya sake zama, ya shiga bathroom ya wanke fuska, ya fito, ya tsaya gaban mirror na dogon lokaci, he didn’t recognize the look on his own face, daga wannan ranar kuwa, Zayd ya sauya completely, Felicia za ta kira shi sau daya, bai daga ba, sau goma, bai daga ba, sau dari, still nothing, messages suka fara shigowa daya bayan daya, Zayd, please answer me, can we talk? Ya gani, amma bai amsa ko daya ba, ta yi ta kira, ta yi ta aika masa da messages, ya yi banza da komai, ba don bai san Felicia ba, amma saboda a wannan karon, akwai wani abu da ya mutu a tsakaninsu, trust, Zayd ya mayar da hankalinsa gaba daya kan karatunsa, lectures, assignments, exams, komai ya koma kamar yadda yake a da, sai dai shi kansa ya san cewa he was no longer the same.

Wata rana, bayan classes, Zayd yana tafiya zuwa motarsa sai ya ji muryar Felicia a bayansa, “Zayd…” Ya tsaya, ya juya, Felicia tana takowa zuwa wajensa, fuskarta ta baci, idanuwanta sun kumbura kamar wadda ta dade tana kuka, Zayd ya kalleta kawai, ba tare da ya ce komai ba, ta iso gabansa, “Zayd…” Voice dinta ya karye, “You take away my pride…” Ta ci gaba da kuka, “Shi ya sa ka yi dumping dina?” Ya yi shiru, “Ni ba komai ba ce yanzu a wajenka koh??…” Hawayenta suka kara zuba, “Because I didn’t give myself to you willingly, na san ka sani?” Zayd ya sauke idanunsa, “Felicia…” “Ba haka bane?” Ta tambaye shi, tana share fuskarta da hannunta, “Ka san ni, ka san abin da ya faru, ka san ba da yardata bane, ba da amincewata bane,” Zayd ya daga idanunsa ya kalleta, ta jingina da motarsa, jikinta yana rawa saboda kuka, “Kaine ka dage…” Ta kasa karasa maganar, sai ta rufe fuskarta da hannayenta, “Ni da zan yi fushi da kai, ban yi ba…” Ta sauke hannuwanta a hankali, “Amma yanzu kai ne kake fushi da ni,” Zayd bai motsa ba, ya tsaya kawai yana kallonta, “Waye zai aure ni haka?” “Bayan kai ne ka sanni… kai ne ka san komai game da ni,” Zayd ya lumshe idanunsa na dan lokaci, “Felicia…” Amma ta girgiza kai, “Don Allah…” Ta sake jingina da motar, “Idan har ina da wani pride din da ya rage bayan wannan…” “Zan iya sake ba ka komai, zan iya…” Muryarta ta sake karyewa, “But what is baffling me is… why did you ignore me?”

Zayd ya yi shiru, kallon da yake mata ya kasance mai nauyi, ba fushi kawai ba ne, ba tausayi kawai ba ne, there was disappointment, there was confusion, and there was something else Felicia could no longer reach, Zayd ya dauki numfashi a hankali, har yanzu bai ce komai ba, kawai yana kallonta, kuma a karon farko, Felicia ta gane cewa ba wai Zayd yana son ya yi mata punishment bane, ya kawai daina iya kallonta da irin kallon da yake yi mata a da, daga nan Felicia ta samu abin da za ta juya komai da shi, ko Zayd ya share ta, ko ya yi kamar bai san ta ba, sai ta fashe da kuka, “He took away my pride…” Ta ce cikin kuka, “Yanzu ya zan yi?” Zayd ya kalleta kawai, bai ce komai ba, amma kalamanta suka fara samun wuri a cikin kansa, a hankali hankalinsa ya fara tashi duk idan ta fada, domin har zuwa wannan lokacin, Zayd bai taba tunanin cewa Felicia ta ba shi wani abu ba, a’a, abin da yake tunani shi ne yadda kansa ya kasa tuna komai daga wannan daren, ya san kansa, ya san irin karfin sha’awar da yake da shi, ya san yadda a wajen mata suke ta kai kawo a wajensa, wasu har suna zuwa cikin yanayin da zai sa namiji ya lura da su sosai, wasu ga su nan half naked, amma Zayd ya taba ganin hakan a matsayin wani bangare na rayuwar da yake kokarin kaucewa, saboda haka, lokacin da ya fara tunanin abin da ya faru da Felicia, wani bangare na kansa ya yi kokarin alakanta shi da yanayin jikinsa da kansa da kuma yanayin matan wajen da yanda wajen ya sauya a lokacin birthday din, duk tunaninsa shine abinda ya motsa shi, maybe it was just the situation, maybe it was his own body, maybe…

Amma duk lokacin da ya yi wannan tunanin, sai kuka ya dawo masa, kukan Felicia, da kuma yadda ta ce, “You took away my pride,” sai ya yi shiru, domin abin da ya faru ya fi yadda yake zato, karfin sha’awarshi kadai bai kai ya sauya ya fita a hayyacinsa ba har ya aikata haka, fiye da wani moment na weakness, there was something he couldn’t understand, amma duk da haka… har yanzu bai iya tuna komai ba.

Kusan watanni biyu suka wuce, Zayd ya ci gaba da rayuwarsa, komai kamar ya koma normal, sai dai wani bangare na zuciyarsa bai taba samun cikakken sukuni ba, wata rana yana zaune a falo, laptop ɗinsa a gabansa, yana karanta wani abu, sai aka buɗe ƙofar apartment ɗin, ya daga kansa, Felicia ce ta shigo, ba irin Felicia da ya sani ba ce, ta shigo kamar wadda aka koro, gashinta ya watse, idanunta sun kumbura sosai, fuskarta cike take da alamun dogon kuka, Zayd ya zuba mata idanu, bai ce komai ba, ita ma ba ta ce komai ba da farko, kawai ta tsaya tana kallonsa, sai hawaye suka sake gangarowa daga idanunta, a hannunta kuwa akwai wata takarda, ta matso a hankali, mataki daya, sai wani, har ta karasa gabansa, Zayd ya kalli fuskarta, sai ya kalli takardar da ke hannunta, ya sake kallonta, kamar yana neman karin bayani, Felicia ta kasa magana, kawai ta gyada masa kai, hawaye na zuba mata kamar an bude famfo, “Take please…” Muryarta ta fito a karye, Zayd ya dade yana kallonta, sai ya mika hannu a hankali ya karbi takardar, ya bude ta, idanunsa suka fara bin rubutun, fuskarsa ta sauya, ya sake karantawa, sau daya, sai karo na biyu, kamar bai yarda da abin da idanunsa suka gani ba, a saman takardar akwai sakamakon gwaji, PREGNANCY — POSITIVE, sai bayanin shekarun ciki, approximately 6 weeks.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.