Free chapter · Read without an account

BEYOND HIS COMPOSURE

by Jiddaah Barkum · ZAYD ARMAAN


*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER NINETY NINE:99*

*BEYOND HIS COMPOSURE*

*JIDDAAH BARKUM*

—————

Ta kasa ɗaga kanta ta kalle shi, saboda yadda kalaman nasa suka ƙara sa ta jin kunya, ba wai maganar ce kaɗai ta ba ta mamaki ba, sai yadda ya faɗe ta cikin irin wannan natsuwar tasa, kamar yana jin daɗin ganin yadda take ƙoƙarin ɓoye fuskarta, ta ciji leɓenta na ƙasa, tana ƙoƙarin danne kunyar da ta mamaye ta, ta so ta mayar masa da martani, ta nuna masa cewa ba wani noke-noke da take yi, amma muryarta ta maƙale a maƙogwaronta, kawai sai ta sunkuyar da kanta, tana mai yi wa kanta faɗa a zuciya saboda yadda ta bari ya rikita mata tunani, Zayd ya miƙe tsaye a hankali, yana daidaita tsayuwarsa da irin poise ɗin nn nasa wanda ko a wane hali yake, ba ya sauyawa, ya zuba mata idanunsa na ƙarshe kafin ya ɗauki wayarsa da ke gefensa, sannan ya fara takawa zuwa hanyar fita daga falon, “Kar ki kuskura ki bar wani abu a cikin plate ɗin nan,” ya faɗa a hankali, yana juyowa ya kalleta kafin ya kai ga fita, “Otherwise… kin san sauran,” ya ƙarasa maganar da wata murya mai zurfi, wadda ta sauka ƙasa sosai, kafin ya ɗan ɗaga gira yana jiran ya ga ko za ta yi ƙarfin halin mayar masa da martani, amma Raihana ta tsaya cak, tana kallonsa kawai, ganin kawai kallonsa take amma bata ce komai ba, kawai sai ya juya ya fice daga falon da irin takun nasa mai cike da izza da ƙwarjini, ya bar ta a nan zaune, tana binsa da kallo har sai da ya ɓace daga ganinta.

Raihana ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya, sannan ta ɗan tabe baki, ta girgiza kanta a hankali kafin ta fara magana da kanta, “Kalle shi! Sai ya dinga zaro magana kamar ba daga bakinsa take fita ba…” Ta faɗa cikin ɗan shagwaɓa, tana ɗan hararar ƙofar kamar har yanzu yana tsaye a gabanta, amma duk da irin taurin kan da take nunawa a gabansa, ta san a ranta cewa yana da wani irin iko a kanta wanda, duk yadda ta so ta guje masa, hakan ba ya yiwuwa, kuma abin da ya fi ba ta mamaki shi ne yadda yake yin hakan ba tare da ya yi wani ƙoƙari na musamman ba, a hankali ta ɗauki spoon ɗin, ta fara cin abincin kamar yadda ya umarce ta, tana ƙoƙarin mayar da hankalinta kan abincin maimakon mutumin da ya bar ta da tunani iri-iri, sai dai duk yadda ta yi ƙoƙarin nutsuwa, zuciyarta ta ci gaba da bugawa da wani irin mix of feelings da ita kanta ta kasa ba wa suna.

Har bayan Maghrib, Zayd bai shigo gidan ba, Raihana kuwa tana nan zaune ita kaɗai, da farko tana falo, amma da ta gaji, bayan sallar Asr ta wuce ɗakinta ta yi wanka, sannan ta sake dawowa falon, ta riƙe ƙugu, kawai tana kallon wajen, ita dai ba ta san ma abin da za ta yi ba, “Ko na dafa abinci ne?” Ta tambayi kanta a hankali, tana kallon hanyar kitchen ɗin, sai kuma ta turo baki, “Yanzu sai ya ce na cinye duka abincin da aka kawo shiyasa na daga wani kuma…” Ta faɗa a hankali, tana tuna yadda Zayd ya umarce ta da kada ta bar ko da ragowar abinci a plate ɗinta, ta ɗan girgiza kai, kamar tana korar tunanin nasa daga kanta, daga ƙarshe dai ta koma ta saka hijab ɗinta, ta shiga kitchen ɗin ta ɗauko food warmers ɗin, sannan ta wuce compound, can ta samu gateman a zaune, ta ƙarasa wajensa ta miƙa masa food warmers ɗin, ai kuwa, nan ya shiga godiya kamar wadda ta ba wa duniya da abin da ke cikinta! Raihana ta ɗan yi murmushi, “Ba komai fa, ba sai ka yi ta godiya haka ba,” ta faɗa cikin ladabi, tana jin kunya saboda yadda mutumin yake ta yi mata godiya, bayan ta gama miƙa masa abincin, sai ta juya ta dawo cikin part ɗinta, ta shiga ta kulle ƙofar da key, sannan ta ajiye hijab ɗin a kan sofa, sai ta wuce kitchen, ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon kitchen ɗin, gaskiyar magana, idan dan ita ne, da ba za ta dafa komai ba, amma duk lokacin da ta tuna hudubar maman Ihsan, sai ta ji kamar an saka mata wani abu a zuciya, ta tuna yadda maman Ihsan ta ce ko da mijinki ba zai ci abincin ba, ki dafa masa, haka ake yi, kada ki saba da rashin yi masa abinci, domin ranar da ya samu wacce za ta riƙa yi masa komai a shirye, zai fara ganinki kamar wata fanko, Raihana ta ɗan turo baki, tana tuna kalaman nata.

Ta ƙarasa store ɗin, ta buɗe ƙofar tana kallon kayan da ke ciki, “Me ma zan dafa to?” Ta tambayi kanta, tana bin kayan da idanunta, bayan ɗan tunani, sai ta yanke shawaran yin tuwon shinkafa da miyar yaushe, ta duba kayan amfani, Sameer ya siyo kayan miya, fruits da sauran vegetables, daga nan ta fara aikin girki, ta wanke nama, ta shirya kayan miya, sannan ta fara dafa miyar wacce ta sha nama sosai, ta yi ta motsa miyar tana duba yadda take tafasa, a gefe kuma tuwon ya fara, shima lokaci-lokaci tana ɗan duba miyar domin tabbatar da komai ya yi daidai, kitchen ɗin ya cika da ƙamshin girkinta sosai ta ko ta ina, bayan komai ya hadu, ta shirya komai da kyau, cikin warmers, sannan ta haɗa fresh coconut juice ta saka a fridge domin ya yi sanyi, da ta gama, ta gyara wajen kamar ba a taɓa yin komai ba, ta wanke duk abin da ta yi amfani da shi, ta goge kitchen ɗin, sannan ta ajiye komai a inda ya dace, a lokacin ana shirin kiran sallar Maghrib, Raihana ta fito daga kitchen ɗin ta koma falon, ta sake gyara wajen duk da cewa bai yi wani datti ba, ta duba komai da kyau, sannan ta kunna burner, ta zuba turare, wuta, ƙamshi ya fara cika part ɗin, bayan ta gama, sai ta saki curtains ɗin windows ɗin domin ɗakin ya ɗan kama, ta kuma gyara su yadda ya dace, ta tsaya tana kallon wajen tana jin ɗan gamsuwa da yadda komai ya kasance, daga nan ta juya ta nufi ɗakinta domin yin alwala.

Tana shiga ɗakin, sai ta nufi toilet ɗin ta buɗe ƙofar, ta karasa wajen toilet zata kama ruwa, amma da ta bude murfin toilet din, nan idanunta suka sauka kan wani abu a cikin toilet ɗin, sai ta tsaya cak! Maciji! Wani babban maciji ne a ciki, na ɗan lokaci, Raihana ta kasa fahimtar abin da idanunta suke gani, kamar hankalinta ya ƙi karɓar abin da ke gabanta, sai kuma ta ƙwala wani irin ihu mai firgitarwa, ta juya da gudu kamar wadda aka harba da bindiga, “WAYYO ALLAH NA!!!” Ba ta san ta yaya ta yi hakan ba, amma kafin ta ankara, ta riga ta kai kanta bakin entrance ɗin part ɗinta, babu hijab, babu takalmi, babu komai! Tana nan tsaye a bakin ƙofar, tana haki, kirjinta yana tashi yana sauka da wani irin sauri, idanunta a zare kamar za su faɗo, “Wayyo Allah na! Maciji! Maciji!!!” Ta yi ta faɗa cikin firgici, tana kallon kofar part dinta kamar macijin zai fito ya biyo ta, jikinta gabaɗaya rawa yake, numfashinta ya rikice, har ta kasa tantance ko ta kamata ta tsaya a nan ne ko kuma ta gudu ta fita daga part ɗin gaba ɗaya, “Ya Allah! Ya Allah! Me ya kawo maciji cikin toilet ɗina?!” Ta ƙara faɗa, tana haɗe hannayenta a kirjinta, ta rakube a nan wajen tana kuka a hankali, tana kiran Ummanta, gashi ko waya ba ta ɗauko ba, bare ta kira Zayd ta ji yana ina, dan wallahi, ko me zai faru, ba za ta yi kuskuren sake shiga part ɗin ba, ta kusan minti talatin a zaune a wajen, har duhu ya fara yi sosai, daga inda take zaune, sai ta hangi gate ɗin ya fara buɗewa, ta sauke ajiyar zuciya, tana fatan wanda zai shigo gidan ya kasance Zayd ne, har motar ta ƙarasa parking lot, Raihana tana wajen tana bin ta da kallo, bayan wasu seconds, sai murfin motar ya buɗe a hankali, nan Zayd ya fito cikin nutsuwa, bayan sun yi ƴan magana da gateman, sai ya fara takowa zuwa hanyar part ɗin nata, saboda hasken compound ɗin, idanunsa suka sauka a kanta fes! Yana ganinta a durƙushe a gefe, ta rungume jikinta da hannayenta, fuskarta kaca-kaca da hawaye, dan ganinsa ma ya sake sa wasu hawayen suka balle daga idanunta, Zayd ya tsaya cak, yana kallonta da mamaki, ita ma kallonsa take, amma har yanzu tana nan a wajen a durƙushe, ba ta tashi ba, for a few seconds, Zayd ya kasa fahimtar abin da yake faruwa, ya kalli ƙofar part ɗin, sannan ya mayar da idanunsa kanta, “Me kikeyi a nan?” Ya tambaya a hankali, muryarshi dauke da mamaki, amma maimakon ta amsa, sai ta ƙara rungume jikinta, tana kallonsa cikin kuka.

A hankali ya ƙarasa gabanta yana kallonta, “What happened?” ya sake tambaya a hankali, domin shi duk tunaninsa Seeyama ce ta yi mata wani abu, amma Raihana wata sabuwar tabara ce ta ziyarce ta bayan ganin Zayd, sai ta ci gaba da kuka kawai, ba tare da ta iya cewa komai ba, Zayd ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya sake buɗe su a hankali, bai fahimci abin da yake faruwa ba, ya sake kallonta, yana ƙoƙarin ganin ko za ta yi magana, amma ita sai kuka take yi, daga ƙarshe, ya ƙarasa gabanta gaba ɗaya, ya sa hannuwansa ya ɗago ta a hankali ta tsaya a gabansa, ya zuba mata ido, yana kallon yadda take kuka sosai, fuskarta cike da hawaye, numfashinta ma ya rikice, “What is wrong with you?” Ya sake tambaya, wannan karon muryarsa ta ɗan yi nauyi, amma har yanzu ba ta ce komai ba, Zayd ya sauke ajiyar zuciya a hankali, sannan ya kama hannunta, ya yi hanyar shiga part ɗin, saboda compound ɗin akwai haske sosai, ana ganinsu fes, ga shi kuma ko hijabi babu a jikinta, amma da Raihana ta fahimci zai shigar da ita part ɗin, sai ta fisge hannunta da sauri, tana kuka sosai, Zayd ya tsaya cak! Ya zuba mata ido da uban mamaki a fuskarsa, yana ƙoƙarin fahimtar abin da ta yi yanzu, “Wai menene? Open ur mouth and talk to me,” amma maimakon ta amsa, sai ta koma gefe ta rabe, tana ci gaba da kuka kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwar uwa da uba, Zayd ya bi ta da kallo, har yanzu mamakin abin da yake gani bai bar fuskarsa ba, a hankali ya ɗan karkatar da kansa, “Are you serious right now?” Ya tambaya, yana kallonta kamar yana jiran ta yi masa bayanin abin da ke faruwa, amma Raihana dai sai kuka take yi, Zayd ya shafa fuskarsa da tafin hannunsa, ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya sake kallonta, “Can you at least tell me what happened?” Ya tambaya cikin natsuwa, duk da cewa a fili yake cewa haƙurinsa ya fara ƙarewa, Raihana ta ɗago idanunta da suka cika da hawaye ta kalle shi, amma da ta tuna abin da ta gani a cikin toilet ɗinta, sai ta sake fashewa da kuka.

Zayd ya tsaya yana kallonta, a wannan lokacin, ya tabbatar da abu ɗaya, whatever had happened inside that house, Raihana was clearly terrified, amma abin da ya kasa fahimta shi ne… me ya faru da ita har ta kasa ma gaya masa ko kalma ɗaya? “Macijiii!” Ta faɗa cikin rabewar murya, tana sake komawa gefe, “Ni ba zan shiga ba, maciji ne a ciki!” Ta faɗa, muryarta na rawa sosai, Zayd ya tsaya yana kallonta, har yanzu bai fahimci yadda lamarin ya kai haka ba, a hankali ya furta, “Maciji kuma?” Raihana ta jinjina kai kawai, ba tare da ta ce komai ba, ya yi shiru yana tunani, sai kuma ya sake tambayarta, “A ina kika gan shi?” Raihana ta share hawayenta da bayan hannunta, sannan a hankali ta ce, “Toilet ɗin ɗakina,” Zayd ya yi shiru na wasu seconds, yana ƙoƙarin fahimtar abin da ta faɗa, sai kuma daga ƙarshe ya sake matsowa kusa da ita, “Mu je da safe sai a duba a cire shi, na san by now ma ya gudu ai,” da jin haka, Raihana ta yi kamar wadda ya zuba wa garwashin wuta! Ta sake daka tsalle, ta koma baya, tana ƙananan kuka, “Ni wallahi ba zan shiga ba! Ba zan zauna gida ɗaya da maciji ba! Wayyo Umma na! Wayyo Baffa!” Ta faɗa, tana girgiza kai cikin firgici, Zayd ya tsaya cak, yana kallonta da wani irin kallo, “It’s just a snake,” ya faɗa cikin nutsuwa, “JUST A SNAKE?!” Ta maimaita cikin rashin yarda, tana zare idanunta, “Kana jin abin da kake faɗa kuwa? Maciji fa! Maciji! Ba mage ba ne!” Zayd ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya buɗe su yana kallonta, “Na ji,” “To, idan ka ji, me ya sa kake cewa just a snake? Ka shiga ka zauna da shi mana, ni wallahi ba zan shiga ba!” Ta faɗa, tana sake share hawayenta, Zayd ya sauke ajiyar zuciya a hankali, ya ɗan kalli ƙofar part ɗin, sannan ya mayar da idanunsa kanta, “Okay, stay here,” ya faɗa a taƙaice, kafin ya juya ya fara takawa zuwa ƙofar, amma kafin ya yi nisa, sai ya ji muryarta a bayansa, “Wayyo Umma na, wayyo Allah naaa!” Ya tsaya, amma bai juya ba, “Kar ka bar ni ni kaɗai a nan!” Ta faɗa cikin kuka, muryarta cike da tsoro, a hankali Zayd ya juya ya kalleta, “Yanzu kuma ba za ki bar ni in shiga ba, ba kuma za ki tsaya ke kaɗai ba, what exactly do you want me to do, rn?” Ya tambaya cikin natsuwa, Raihana ta ɗan buɗe baki, amma ba ta samu amsar da za ta ba shi ba, ta dai tsaya tana kallonsa, hawaye na zubo mata, Zayd ya sake kallonta na ɗan lokaci, sannan ya girgiza kai a hankali, “Ya Allah…” Ya furta ƙasa-ƙasa, kafin ya dawo kusa da ita, “Mu je toh, sai ki zauna a wani ɗakin daban, ai ba ɗaki ɗaya ba ne a gidan,” ya faɗa yana kallon fuskarta, as if he was trying to make her understand that there was nothing to be afraid of, sai ta fara kuka again, “Ni wallahi ba zan zauna ba! Wayyo Allah naaa!” Ta sake fashewa da kuka, tana girgiza kai da ƙarfi, Zayd ya zuba mata ido, wallahi, ya rasa abin da zai yi yanzu kuma, he had dealt with difficult people, stubborn business partners and all kinds of situations, but right now, this woman was giving him a headache he couldn’t explain, kafin ta ankara, ya ɗaga ta, ya sa ta a kafaɗarsa, ya yi hanyar shiga cikin part ɗin da ita, ya bude kofar ya shiga, sannan ya tura ya rufe ƙofar da ƙafarsa.

Raihana kuwa ta fara dukan shi, tana wutsil-wutsil da ƙafafunta, “Ka ajiyeni! Na shiga uku! Maciji ne fa na ce maka! Don Allah, kar ka shigar da ni ɗakin! Wayyo Allah naaa!” Amma ina! Zayd ya ci gaba da tafiya kamar bai jin ta, ko kuma ya zaɓi ya yi ignoring ɗin duk ƙorafinta, ba zato ba tsammani, wani murmushi ya bayyana a fuskar Zayd, not just an ordinary smile, murmushi sosai har haƙoransa suka bayyana, yayin da ya ɗan girgiza kansa a hankali, yana jin daɗin yadda take ta faman yi, a hankali ya ce, “Ba dai ke kin iya tsiwa ba? Ai macijin ne daidai ke, ɗakin zan kai ki, in na rufe ki a ciki,” da jin abin da ya faɗa, Raihana ta sake rikicewa, ta fara dukansa sosai, harda ƙoƙarin cizon shi, “Ka ajiyeni! Raihana ta fara tirjewa a jikinsa, hawaye na cigaba da zuba, “Karka kaini, zan mutu, wayyo!” Amma maimakon ya tsaya, sai ya ƙara sauri da ita zuwa cikin part ɗin nata, Zayd ya kasa riƙe murmushinsa, he had never seen her this dramatic before, and the sight was almost unbelievable, amma kafin ka ce me, sai ya lura da wani abu, Raihana ta yi shiru, ta daina ƙoƙarin dukan shi, ta daina wutsil-wutsil da ƙafafunta, har ma ta daina cizon shi, Zayd ya ɗan dakata, yana tunanin ko ta hakura ne a ƙarshe, sai ya ji nauyinta ya ƙaru a jikinsa, “Kee?” Babu amsa, ya ɗan sauya yadda yake riƙe ta, sannan ya ƙara kallon fuskarta, sai ya ga idanunta a rufe gaba ɗaya, murmushin da ke fuskarsa ya ɓace nan take, ya girgiza ta a hankali, amma jikinta ya yi laushi a hannunsa, she had completely passed out, “Raihana!” A wannan karon, muryar Zayd ta sauya gaba ɗaya, Zayd ya rikice sosai a lokacin da ya tabbatar da cewa Raihana ta suma, without wasting another second, ya juya da ita da sauri zuwa ɗakinsa, yana riƙe da ita a hankali duk da irin firgicin da ya kama shi, ya isa gadonsa, ya ajiye ta a hankali a kan lafiyayyen gadonshi, sannan ya tsaya yana kallon fuskarta, ya sake sunkuyawa kusa da ita, yana ta aikin shafa fuskarta, amma har yanzu idanunta a rufe suke, for the first time, Zayd Armaan was completely lost, “Damn it!” ya furta, yana ɗan ja da baya tare da shafa fuskarsa da hannuwansa, ya kalli Raihana, ya sake kallon ƙofar ɗakin, his eyes kept returning to her face, as if he was expecting her to open her eyes any second, ya fara yawo da idanunshi a dakin, as if he was desperately searching for something to do, he had no idea what to do, tuno yadda jikinta ya yi laushi a hannunsa ya sa zuciyarsa bugawa da sauri, while his mind struggled to process what was happening, sai kwatsam, ya tuna da wani abu, da sauri ya juya zuwa fridge ɗin da ke cikin ɗakin, ya buɗe shi ya ɗauko ruwa, ya dawo kusa da gadon, yana kallonta da fuskarsa cike da damuwa, da sauri ya buɗe murfin ruwan, ya ɗebo kaɗan a tafin hannunsa sannan ya yayyafa mata a fuska, Raihana ta ja wani uban numfashi da ƙarfi, idanunta suka buɗe a hankali, sai kuma suka sake lumshewa, ta yi wani irin murginawa, jikinta ya motsa kamar za ta tashi, amma sai ga shi ta karkata gefe, saura kaɗan ta faɗi daga kan gadon, Zayd, wanda ya durƙusa a gabanta, ya yi saurin cafko ta, ya riƙe ta da sauri, sannan ya ɗan gyara yadda yake riƙe ta, ganin cewa har yanzu ba ta gama dawowa hayyacinta ba, a hankali ya manna kanta a kirjinsa, hannayensa suka zagaye ta don kada ta sake zamewa, ya lumshe idanunsa, yana sauke ajiyar zuciya mai nauyi, a hankali ya sake kallon fuskarta, yana jiran ta dawo hayyacinta sosai, duk da cewa yana ƙoƙarin kasancewa calm, the worry on his face was impossible to hide.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.