Free chapter · Read without an account

LOKACI CHAPTER 1

by Rabi'atu kabiru Fulani · RANTSATTSEN RABO

***

⌛🕛 LOKACI 🕛⌛


BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA)

*Under Team Yota's Amazing Pen's*

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN KACOKAN ƊIN SHI GARE KI KARYMAT BASHEER (AN KARIME KARIME NA) ALKHAIRAN ALLAH YA KAI MIKI HAR GADON BACCIN KI.


Wannan littafin ƙirƙirarren labari ne. Duk wasu abubuwa da za ku ci karo da su a cikin labarin, ƙirƙirarre ne kawai domin isar da saƙo. Ban rubuta shi da niyyar cin mutuncin kowa ko tozarta wani ba. Ina fatan zaku bani haɗin kai, tare da biyo ni sannu a hankali domin ku ji irin salon da nazo muku da shi a wannan karon.

Gaisuwar ban girma da jinjina a gare ki amintacciya ta *AMINA MUHAMMAD HARUNA* tare da ke ta hannun damana *FATY SABO* Da kuma abokiyar shawara ta *AYEESHAT KISSAR* ubangiji Allah ya yi mu ku abinda zato bai taɓa bai taɓa zato ba. Allah ya ba ku Aljannah. Ina godiya da irin gudunmawar da kuke bani. FULANI proud of you my people.

Ina miƙo gaisuwa ta musamman ga jama'ar Yota da shuwagabannin mu masu capacity, Alkhairin Allah ya ci gaba da riskar ku.

Ina alfahari da ku Team Yota's Amazing Pen's, ƴan team ɗina, Allah ya ci gaba da dafa mana ya yi mana jagora baki ɗaya.

Bissmillahirrahmairrahim

    FULANI
***

 
⌛🕛 LOKACI🕛⌛

      PAGE 1️⃣ 

A zahiran ce tafiya take cikin nutsuwa, amma a cikin zuciyar ta sauri take harda sassarfa, tunda taga yamma tayi hankalin ta yayi mugun tashi, kuma tunanin ta yayi hijira ya koma gidan su, a halin yanzu bata da wani buri daya wuce ta buɗe ido ta ganta a cikin gidan su, saidai me titin kamar anyi shara babu ababen hawa, hakan ne yasa ta yanke hukuncin ta taka a ƙafar ta ko Allah zaisa ta dace.

Saida tasha wahala kafin ta samu napep ɗin daya ɗauke ta ya shigar da ita cikin unguwar su, dake nan kuntau old airport, tana zuwa ƙofar gidan su ta sauke ajiyar zuciya, dan sosai ta samu relief ganin ba'ayi sallar magriba ba ta dawo gidan, kuɗin shi ta ciro ta bashi a cikin jaka, sannan ta nufi gidan da zan iya cewa yafi kowanne gida girma a layin, tana da key a hannun ta hakan yasa bata tsaya knocking ba, kawai ta saka ta buɗe ta shiga da sallama.

   "Barka da yamma mahmah" ganin ko kallon ta batayi bane yasa cikin sanyin jiki ta matsa kusa da ita "sannu da gida mahmah"

Wani shegen kallo ta ɗago ta watsa mata wanda yasa jikin ta ya fara rawa a hankali, ƙasa tayi da kanta batare data bar wajen ba, duk kuwa da yanda zuciyar ta take bugawa da tsananin ƙarfi.

   "Sau nawa zan faɗa miki babu ruwan ki dani a cikin gidan nan idan har bani ce na neme ki ba? Kinje gantalin ki kin dawo shine zaki zo kina wani sunne min da kai kamar ta Allah? Tunda har kika fara kai gab da magriba a waje nan gaba kaɗan nasan kwana zaki farayi a can wajen yawon ki" yanda take mata faɗan sosai abin zai matuƙar baka mamaki bazaka taɓa cewa ƙatuwar budurwa ta saka a gaba take wa wannan faɗan ba.

 Da ƙarfi ta runtse idonta ba tare data bawa hawayen ta damar fitowa ba, ta rasa sai yaushe ne mahaifiyar tata zata dena jifan ta da mugayen kalamai, batasan sai yaushe ba, tana jin daman tana da damar yiwa mahaifiyarta ta abinda take so, ko hakan zai kawo musu zaman lafiya kaman ko wace uwa da ɗiyar ta, cikin sanyin jiki ta nufi ɗakin ta, tamkar mara laka, key ta saka ta buɗe ta shiga da sallama duk da tasan babu kowa a ɗakin.

Kayan jikin ta ta cire ta shiga toilet ɗin dake ɗakin nata, ta jima sosai a ciki sannan ta fito ɗaure da towel a jikin ta, gaban mudubi taje ta tsaya ta zubawa kanta ido, duk inda kake neman kyakykyawar mace zaka saka ta a ciki, idan har maganar kyau ake faɗar ma tana da shi ɓata baki ne, idan dirarriyar mace ake magana shima babu abinda zata ce, ta ko ina ta kai a kira ta da mace, toh menene matsalar ? Daga ina matsalar take? Meyasa abubuwan suke tafiya a haka ne? Bata da amsar da zata bawa kanta hakan yasa ta fara shirya kanta a hankali, bata jima ba ta gama shirin ta baka jin komai a ɗakin sai ƙamshin humrah da ke tashi a jikin ta, jin an kira sallar magriba ne yasa ta zura kayan ta ta tayar da sallah dan daman tayi alwala.

Tana cikin sallahr matashiyar budurwa ta shigo ɗakin mai kama da ita, wadda kallo ɗaya zaka mata kasan itaɗin jinin tace, toilet ɗin ɗakin nata ta shiga tayo alwala tazo ta tayar da sallah a kusa da ita, tana sallame wa ta kalle ta cike da farin ciki tace "aunty zahra yaushe kika dawo? ina ta jiran ki tun ɗazun" murmushi tayi cikin Muryar ta mai daɗi tace "babu jimawa Salmah mai zaki bani?" Dariya wadda ta kira da salma tayi ta bata da amsa da "babu komai kawai nayi kewar ki ne, gidan babu daɗi idan babu ke" murmushi tayi ba tare da tace mata komai ba.

Su bakwai ne a wajen iyayen su duka mata itace babba mai kimanin shekara 35years, sai ƙanwar ta A'isha, sai mai bi mata Amina, sannan Zainab, sai Raihana, Sadiya, sai auta Salmah, rayuwar gidan su rayuwa ce ta rufin asiri, kai tsaye baza'a kira gidan su na masu kuɗi ba kuma baza'a kira shi da na talakawa ba, saidai a kira su da masu rufin asiri, unguwar su bata masu kuɗi bace, dan kaf layin su ma babu gidan da ya kai nasu girma.

Sun taso cikin rayuwar farin ciki, dan babu abinda suka nema suka rasa, dukan su a iya kacin secondry suka tsaya da karatu zahra ce kawai wani dalili yasa ta ci gaba da karatu har ta fara aiki, kaf ƙannan ta sunyi aure itace kawai da auta Salma sukayi saura a gaban iyayen su, sosai tayi zurfi a cikin tunanin har bataji kiran da mahaifiyar ta take mata ba, Salma na shirin taɓa ta Mahmahn tasu ta shigo ɗakin, ganin yanayin fuskar ta sosai gaban ta ya faɗi dan tasan a zuwan nata dole wani abu sai ya faru. Bata kai ƙarshen tunanin nata ba taji ƙarar saukar mari tassss, idon ta ta lumshe hawayen tausayin yayar tata ya zubo mata.

A gigice Zahra ta dafe kuncin nata dan marin yazo mata unexpected, koda bata kalli mai marin ba tasan mutum ɗaya ce kaf duniya zata mata haka, hakan yasa bata iya ɗagowa ta kalli Mahmahn tata ba, sai yatsun ƙafar ta data zubawa ido da suke nan sak irin nata, "ke wace iriyar daƙiƙiya ce kina ji ina kiran ki zaki min shiru? Raini ne yasa bazaki amsa ba ko kuma dai kina tunanin kan mu ɗaya?" Idon ta ta runtse ba tare da tace mata komai ba, inda sabo yaci ace ta saba amman ina zuciyar ta ta kasa sabawa. "Zaki tashi kije kiran da ake miki a waje ko saina rufe ki da duka banza shashasha" 

Cikin sanyin jiki ta miƙe da hijabin sallar jikin ta, ta nufi hanyar waje ba tare data ganin inda take jefa ƙafar taba, duk da ba ganewa take wa ba amman ganin wanda yake a gaban ta batasan sanda ta ware manyan idanuwan ta akan shi ba, zuciyar ta na bugawa da matsanancin ƙarfi. Shi kuwa tunda yaga fitowar ta ya gyara babbar rigar jikin shi, take dattijuwar fuskar shi ta washe da fara'a haƙoran shi da goro ya dafar dasu suka bayyana jajaye da su babu kyan gani.

Baya tayi jikin ta na rawa a hankali a cikin hijabi "Faɗimatuz_zahra" ya kira sunan nata har lokacin haƙoran shi a waje tabbacin yana cike da farin ciki ganin ta a gaban shi, shiru tayi kawai tayi ƙasa da kanta har lokacin zuciyar ta bugawa take cike da fargaba, dogon tunani take shirin tafiya saidai yayi hanzarin katse ta kamar yasan tunanin da yake shirin kutsowa zuciyar ta. "Fati jiya mahaifin ki ya same ni a masallaci akan idan zan iya taimaka wa na aure ki, da dai bazan amince ba sai kuma naga waye zai ƙi wannan zuƙeƙiyar halittar" ya faɗa yana ƙara washe mata jajayen haƙoran sa.

A hankali ta haɗe da jikin bango dan wallahi jiri ne yake niyyar zubar da ita, mai baffa yake nufi daman maganar da yayi dagaske yake innallilahi wa'inna ilaihir'raji'un, yanzu ita ya zatayi da baba Bala, kai tsaye bazata kira shi da abokin baffa ba saboda ya girmi mahaifinta nesa ba kusa, maganar shi ce ta katse mata tunanin da ta tafi, "Yanzu yaushe kike ganin za'ayi kinsan auren sadaka babu jan lokacin, dake malam Ahmad sadaka ya bani auren kuma dai akwai ɗaki ɗaya a gida na nasan ya ishe ki, kar ki damu bazan bari waɗan can tsofaffin matan nawa da ƴaƴan su su takura miki ba, ki kwantar da hankalin ki kinji fatiti" yayi maganar kamar mai rarrashin ta, amman ita a wajen ta daidai yake daya ɗebo tafasasshen ruwan zafi ya watsa mata, rasa abinda zata ce mishi tayi hakan yasa ta juya ta nufi cikin gidan kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki, kasa buɗe bakin ta tayi tayi sallama hakan yasa kawai ta nufi ɗakin ta jiri na neman kayar da ita.

"Toh salamammiya huce wa zaki yi ba tare da kin faɗa min ya kuka yi da malam Bala ba?" 


    ★★★

KURNA BABBAN LAYI

A durƙushe take tana wanki duk ta haɗa zufa saboda yanda rana ta ƙwalle a tsakiyar ƙaramin gidan nasu, wankin kayan maza take wanda zan iya cewa kayan sunfi ƙarfin hannun ta da take wankin da su, tana yi tana kallon ɗaki ɗaya da yake cikin ɗaku na guda biyu da yake cikin gidan, ganin bata ga abinda take nema da yake ɗaga mata hankali ba sai taci gaba da wankin tana sauke ajiyar zuciya, ƙara ɗagowa tayi da niyyar dubawa aikam karaf idon ta ya faɗa cikin idanuwan shi, daga yanayin da ya fito saida gaban ta ya yanke ya faɗi dan tasan da tijira ya tashi daga yanayin kallon da yake mata, cikin sanyin jiki ta janye idon ta ta mayar da shi kan kayan wankin da take wanke wa.

Allah ne kaɗai yasan irin bugun da zuciyar ta take yi da ganin shi, kasa yin wankin tayi sai hannun ta dake rawa a cikin ruwan, tafiya yake amman duk takun shi da bugun zuciyar ta yake tafiya, bata gama fita daga cikin tsoron da take ba taji anyi ball da ita, daɓas haka ta zauna dan Allah yasa ni ƙafar da yayi mata ta shige ta "dan uban ki na baki wanki tun safe shine har yanzu baki gama ba? Raini ne ko kuma kina ganin ni sa'an kine?" Kanta take girgiza mishi ta kasa furta komai saboda kukan da yake neman ƙwace mata, tuna cewa baya son yayi magana a yi mishi shiru yasa da sauri tace "A'a kayi haƙuri dan Allah zazzaɓi ne a jiki na"

Harara ya watsa mata ya zagaye ta ya wuce ɗan madaidaicin toilet ɗin dake tsakar gidan, wankin ta ci gaba dayi cikin sanyin jiki dan tasan idan har ya fito ya ganta a zaune tsaff jikin ta zai faɗa mata "ya Allah ka kawo min ɗauki ya rahman ka kawo min ƙarshen auren nan" tayi addu'ar wasu irin hawaye na kwaranyo mata. 

Saukar belt kawai taji a jikin ta "kika ce mene? Auren nan idan kinga ya mutu kema kin mutu dan uban ki shegiya me baƙin hali a banza kikayi aure a gida biyu kika fito ehh faɗa min...........

FULANI
***

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol