Free chapter · Read without an account

LOKACI CHAPTER 6

by Rabi'atu kabiru Fulani · RANTSATTSEN RABO

***

⏳ 🕛 LOKACI🕛⏳


RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA 

Under Team Yota's Amazing Pen's.

SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER (An karime karime na)

     FULANI ❣️ 


***


    ⏳🕛 LOKACI🕛⏳

     
      PAGE 6️⃣

Banza ta yi masa, za su wuce ya yi sauri ya tare ƙofar gidan yana ƙara jefa mata tambayar ina za su kai mishi. "Malam ka matsa min a hanya mu wuce, inda ka aike mu can zamu kai ta. Kai idan har ka na da kunya za ka tambayi ina za a kai ta? A ce ka na cikin gidan har sai ta kira gida a kan ba ta da lafiya mtssss. Ba ni hanya na wuce, dan wallahi ka ce zaka min shirme irin naku na ƴan wiwi sai na sharara maka mari a wajen nan" Sosai take huci dan Allah ya sani ita daman can auren ba wani burge ta ya yi ba, bayan kuma cases ɗin da suka dinga yi ne auren ya fice mata a rai gabaɗaya. Yanzu kuma da ya tsaya a gabanta sai take jin muguwar tsanarsa a cikin ranta.

Zai yi magana cikin muryar rashin lafiya Khairiyya ta katse shi "dan Allah Auwal ka bari mu tafi, wajen mai magani za mu je, sannan.." Tassss ya ɗauke ta da mari ba tare da ya bari ta ƙarasa ba. Tassssss! Tassssss! Wasu ƙaran marin suka ƙara tashi wanda yafi wancan na farkon ƙara. Wani irin shiru ne ya ratsa soron da suke ciki sai wani irin ɗumi da wajen ya ɗauka.

"Auwal dake dafe da kunci, tamkar mutum mutumi haka yake kallon Aunty Maryama da ta jera masa lafiyayyun maruka har guda biyu. Abin da zai iya cewa babu wata halitta da ta taɓa kai hannunta jikinsa. Sai gashi yau wata ta mare shi, ba ma ɗaya ba har biyu. Sosai ita ma Aunty Maryama take wani irin huci da zai nuna maka irin tsananin ɓacin ran da take ciki. Ita kuma Khairiyya jikinta ne ya ɗauki rawa dan tafi kowa sanin wane ne Auwal, tunanin wani lokaci da ya mare ta, ta rama ne ya gilma mata a cikin idanuwanta. A take ta ji wani irin jiri yana ɗibar ta.

A haukace ya yi kansu, gabadaya ya ɗaga hannunsa ya kaiwa Aunty Maryama naushi a fuska, sai dai kafin hannun nasa ya sauka a fuskarta aka kai masa duka ta baya. A zabure ya ƙara juyowa dan ganin wane me ƙarar kwanan ne ya yi mai wannan aika aikar. Ganin ƙanin Aunty Maryama ne, ya kuma a wajen Khairiyya, sai ya yi kansa a haukace cike da son huce haushinsa a kansa. Sai dai jikin da shaye-shaye ya huda da wanda ba ya shan komai akwai banbanci kafin ka ce me ya kai shi ƙasa, ganin yanda Ahmad yake dukan Auwal yasa Aunty Maryama janye shi suka fice a fusace.

Motar da suka zo da ita suka shiga ya ja suka bar ƙofar gidan. "Mene ne ya shigo da kai Ahmad ba a mota na bar ka ba?" Cewar Aunty Maryama tana kallonsa ta mudubi. "Ji na yi shirun ya yi yawa shine na fito, amman meya haɗa ku yake neman dukan ki?" Murmushi ta yi ta ce

 "Toh ai bai dake ni ba, ni dukan da ka yi mai ma ka wanke min zuciya wallahi. Yanzu kwanar ungwaggo za ka kai mu, gidan Malam Almajiri dan na fi tunanin buguwa ta yi, ta duba ta, idan kuma sai mun je asibiti sai mu wuce can" 

Toh ya ce mata ya ci gaba da jan motar dan ya san gidan. Lokacin da suka je ba su ta shi ba mutanen gidan, sai da suka jira shi sannan yazo ya duba ta. Kamar yanda ta yi hasashe buguwa ce ta yi a ƙugun sosai, shi ya saka mata zazzaɓin da take ji. Magani ya ba ta, suka mai sallama suka wuce gidansu dake a Kuntau Zainab vision. Kafin su ƙarasa sai da suka tsaya a pharmacy suka sayi magani sannan suka wuce. Gidan su babban gida ne me ɗauke da part guda biyu, ginin duka iri ɗaya ne babu wani banbanci alamun dai gidan mata biyu ne. Sai ƙaramin part wanda bai kai waɗan can girman ba. Part ɗin mazan gidan.

Part ɗin da ke farko suka shiga babban parlow mai ɗauke da set ɗin kujeru guda biyu saboda girman shi. Part ɗin a cike yake ko da suka shiga, suna sallama Ummu dake kitchen ta fito ta tare su. "Sannu Ummul khairi mene ne abin da ya same ki haka? Zaman me ku ka yi kuma?" A tare duk ta jera musu tambayar. "Ummu sai da muka je aka gyarawa Aunty Khairiyya ciwo kafin nan, kuma yaya Ahmad sai da ya zane mijinta" 

 Cewar Auta da ba ita aka tambaya ba.

"Innallilahi wa'inna ilaihir'raji'un! Ahmad ba ka da hankali ?/Mijin nata ka je ka daka? kashe mata aure za ka yi kome?" gabadaya tashin hankali ne kwance a kan fuskarta.

 "Amman Ummu kin san me ya aikata ne da har hakan ya faru..." Saurin katse shi ta yi "Dallah rufe min baki koma mene ne ya faru ina ruwanka da dukan mijinta idan ba so ka ke ka kashe mata aure ba?" Shiru ya yi dan bai san mai kuma zai ce mata ba.

"Ummu ba zan koma gidan Auwal ba wallahi, na gama zaman aure da sbi!!" Maganar Khairiyya ta katse Aunty Maryam dake shirin yin magana. "Ba za a yi haka ba kin ji Ummul khair, koma mene ne ya faru haƙuri za ki yi a sulhunta hakan zai fi. Amman mene ne a cikin zaman gidan? Gwara miki gidan mijinki kin ji ƴar albarka" 

"Haba Ummu, ba ki tsaya kin ji mene ne hujjarta ba har ki ke wannan maganar? Gaskiya ba za ta koma ba. Ni kaina ina bayanta wallahi, me ake da aure irin na Khairiyya da shi ai gwara babu" A takaice Aunty Maryamah ta yi mata bayanin abin da ya faru bayan zuwan ta gidan, da kuma gyaran da suka je a ka yi mata. "Duk da haka dai wannan bai kai dalilin da zai saka a kashe aure ba, zama za a yi a tattauna a kawo ƙarshen abun, zai fi ai kamar nake gani" cewar Ummu cikin sanyin murya.

"Wallahi Ummu ba zan koma ba, Auwal shi ne shaye shaye, Auwal shi ne dukana da cin mutuncina. Jiya daga kangado ya wullo ni har na ji wannan ciwon. Na gaji ! Na gaji ! Na gaji da wannan auren, wallahi ni da gidansa har abada, ko ya sake ni ta lallama ko kuma kotu ta raba mu, amman na gama zaman aure da shi....."


★★★

Addu'ar shiga gida ta karanta tare da bismillah ta shiga gidan da ƙafar dama, dan a jikinta take jin wani abu mai girma yana shirin faruwa da ita a yau ɗin nan. Babu kowa a tsakar gidan hakan ya saka ta sauke ajiyar zuciya ta wuce ɗakinta. Duk yanda ta so zuwa ta ce wa Mahmah ta dawo tsoron abin da za ta je ta tarar ya hana ta, dan haka kawai ta zaɓi wucewa. Da sallama ta shiga kamar yanda yake a al'adarta duk inda za ta shiga sai ta yi sallama. Toilet ta shige ta yi wanka da brush ta fito. Ta samu riga mara nauyi ta saka a jikinta sannan ta ƙara fitowa.

Ƙofar ɗakin Mahmah ta nufa, a ƙalla ta kai minti 5 a tsaye, sannan ta yi bismillah ta yi sallama ta shiga. A zaune ta same ta a kan kujera me zaman mutum ɗaya. 


 "Barka da dare Mahmah na dawo" 

Ko kallon inda take ba ta yi ba bare ta saka ran zata mata magana. Wani irin sanyi jikinta ya yi, dan a duniya ba ta ƙaunar fushinta ko kaɗan. Cikin rawar murya ta ce, "Mahmah da na je gidan Sadiya na ga abin da ban ji daɗi ba, gabaɗaya ta daina tsafta gidan kaca-kaca. Shine na saka ta gyara, duk da bai yi ba, sai na sake gyarawa sannan na yi mata abincin" 

Ƙasa ta yi da kanta ganin taƙi kallon, ta bare ta yi mata magana. "Mahmah! Na yi miki laifi ne ban sani ba? Dan Allah ki yi haƙuri ki gi min magana" 'Kofa ta nuna mata da hannu ba tare da ta ce mata uffan ba. Ji ta yi kamar an riƙe mata ƙafafu ta kasa tashi. Kelle-kalle ta ga Mahmahn na yi wanda tana da tabbacin abin duka take nema, amman duk da haka ta kasa ta shi. Ba ta son shirun, ta fi son ko zagi ne ta yi mata, haka idan dukan ne, da dai shirun nan nata a kanta babban tashin hankali ne a wajen ta. Gajiya ta yi da zaman ta fita zuwa ɗakinta.

"Me na miki haka da zafi Sadiya bayan maganar da ki ka faɗamin har sai kin haɗani da mahaifiya ta?!" Cikin karyewar murya ta yi maganar tamkar Sadiyar na gabanta. Kwanciya ta yi tana jin yanda cikinta yake ƙuƙin yunwa, amma ta kasa tashi ta sakawa mai komai. Idan ba ta manta ba tun jiya a wajen aiki ba ta ƙara cin komai ba. Dole ma ta ji yunwa. "Assalamu alaikum big sisterta" Salmah ta yi sallama ta shigo cikin unifoam ɗin islamiyya. Amsawa ta yi . Ta karasa shigowa, sannan ta gaishe ta. Ta amsa, ita kuma ta zauna tana cewa " Na gaji Aunty, ga baƙar yunwar da nake ji, gashi yau an yi min dukan hadda. Klli hannuna" Ta yi maganar kamar za ta yi kuka tana nuna mata hannun nata.

"Salmah yanzu wasa ki ke da karatu kusan kullum sai kin ce an yi miki dukan islamiyya. Ina ganin za ki baro ɗakinki ki dawo nan da zama idan ma wani abu ne yake ɗauke miki hankali a kan karatun zan gani" Ba ta bata amsa ba sai tambayar da ta jefa mata "baki da lafiya ne Aunty Zahra?" Kanta ta girgiza mata alamun lafiya take, babu abin da yake damunta.

 "Amman na ga kin yi wani iri" 

"Idon ki bai nuna miki daidai ba, zubo abinci ki ci mu shiga kitchen" Fahimtar ba ta son zancen ne ya sa ta yi abin da ta ce ɗin, badan ta yarda da babu abin da ke damunta ba.

"Gashi na zubo mana sakko muci"  

"Oh Salmah na ce miki zan ci abinci ne?"

 Turo mata baki ta yi gaba cike da shagwaɓa ta ce ,"Allah yunwa ki ke ji, baki ga yanda idanuwanki suka ƙara girma ba, abin tsoro" Murmushi ta yi ta sakko dan ba ta fiya son Salmah ta nemi abu a wajenta ba ta yi mata ba, saboda yanda take nuna mata so da kulawa. Shiyasa ko cikin zuciyarta soyayyar ta daban take kowa ma ya sani. Tare suka ci abincin, amman ita ba wani ci ta yi sosai ba, sunan dai kar a ce ba ta ci bane kawai. Suna gamawa Salmah ta kai flet ɗin kitchen.

"Hajiya Mahmah" 

Ta kira sunanta ganin ta fito daga ɗakinta, harararta ta yi ta wuce yin abin da ya fito da ita. Dariya Salmah ta yi ta ce "Allah ya dai ya bar min ke uwata" Ita kanta sai da ta yi murmushi ba tare da Salman ta gani ba. 

Fitowa ta yi daga ɗakin jin maganar Mahmah da Salmah "Mahmah" Ta kira ta a ɗarare. Ko alamun ta nuna ta san da mutum a wajen ba ta yi ba. Kitchen ta shiga tana maida hawayen da ya cika mata kwarmin ido. "Meyafaru Aunty Zahra?" Salmah dake biye da ita ta tambaye ta.

"Babu komai mai ki ka gani?" 
Ta mayar mata da tambayar. Da hannun ta ta nuna mata idonta. Ɗan murmushi ta yi kawai ta fara haɗa abin da za ta dafa. "Nama san abin da ya faru koma mene ne matsalar daga gidan ya Sadiya ta fara wallahi." Juyowa ta yi za ta dakatar da ita amman ina, har ta fice daga kitchen ɗin a guje.

Biyo bayanta ta yi, dan ta san babu wata jituwa a tsakaninsu. Kuma kiran ta a waya yanzu ba mafita bace, tana shiga ɗakin ta ji tana cewa "banza sheɗaniya me haɗa uwa da ƴarta, ki ji tsoron Allah wallahi ya Sadiya, bautar da ta zo ta yi miki ba ta miki ba shine har sai kin biyo ta da bita da kulli?."

Karɓe wayar ta yi da sauri ta kashe gabanta na faɗuwa. "Aunty Zahra ai da kin barni na.." Ganin tana harararta ne ya sa ta yin shiru tana gunguni.

"Kin san me ki ka aikata Salmah?." Ta buɗe bakinta kenan suka ji kiran sunansu a jere a tsawa ce kuma..

"Zahrah!! Salmah!!!....

FULANI
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol