Free chapter · Read without an account
LOKACI CHAPTER 9
***
⏳🕛 LOKACI 🕛⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI 🤍
***
⏳🕛 LOKACI 🕛⏳
PAGE 9️⃣
"Bakin alƙalami bai bushe ba big sister, kuma ba zai taɓa bushewa ba. Ina jin a jikina lokaci kaɗan ya rage miki ki gama fuskantar abin nan in sha Allah". Salmah tayi maganar a zuciyarta, tana kallon bayanta. Bayanta ta shige ta kwanta, "ki tabbatar kinyi azkar kafin kiyi bacci Autah" taji Muryar ta a sama. Toh kawai ta ce mata ta rufe idonta.
Sai da ta bari baccin Salmah yayi nisa sannan ta, tashi tayo alwala tazo ta fara sallah, sosai ta ƙanƙantar da kanta a gaban Ubangiji, tana mai kai mishi kukanta, da roƙonsa akan ya kawo mata mafita, dan ta tabbatar babu wanda zai fitar da ita a halin da take ciki idan ba shi ba, ta jima akan daddamu a haka har bacci ya ɗauketa. Ana kiran sallar asubah ta tashi, ta tashi Salmah sukayi Alwala tare da sallah, bata bar ta ta kwanta ba sai da sukayi azkar, tare suka koma suka kwanta, babu jimawa bacci ya ɗauke ta.
Leƙa fuskarta Salmah tayi taga bacci take, wayarta ta janyo ta kashe, sannan ta ajiye mata ta fice, duk wani aiki da Zahra take sai da ta tabbatar tayi shi, sannan ta haɗa musu breakfast, tana gamawa ta shige tayi wanka, shiryawa tayi cikin kayan gida a madadin unifoam, sauri take tayi ta fice daga gidan, kafin Mahmah ta fito dan akwai inda take son zuwa, akwai abinda take son aiwatarwa a yau ɗin.
Tana fitowa taga Baffa a ƙofar ɗakinsa a tsaye, bai amsa gaisuwar da take masa ba sai maganar da yayi mata. "yawwa Auta neman ki nake daman inata tunanin ko kin tashi" ɗan jim tayi cike da mamaki cewa ita yake nema. "Zonan" ya kira ta yana nufar hanyar ɗakinta, bin bayan shi tayi tana tunanin ko lafiya.
Tunda suka shiga ɗakin ya zauna a gefen gado, ita kuma ta zauna a ƙasa ɗan nesa da shi kaɗan. Shiru yayi ya zubawa ƙasa ido, maganganun Salmah na dawo mishi kashi_kashi. Sosai maganganun yarinyar suka shige shi, sun ratsa shi fiye da yanda zatayi tunani, dalilin hakan jiya ko bacci baiyi ba, ya kwana da tunanin meyake faruwa da rayuwar babbar ƴar ta sa, haka kawai yaji yana son sanin abinda Salmah take magana akai, tabbas zai dakatar da auren nan, ya zamar mishi dole ya tsaya mata a wannan lokacin, da wannan tunanin ya kwana, ya tashi yasan koda zai kira ta dan suyi magana bazata ce masa komai ba sai dai tayi murmushi.
A wani lokaci can baya daya shuɗe ne Zahra bata jin nauyin faɗa mishi komai da ya shafe ta, amman a yanzu daga gaisuwa bazai iya cewa ga wani abu da ya ke haɗa su magana ba, sai dai ko idan zai bata umarni ta amsa mishi kawai. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani irin nauyi a ƙasan zuciyarsa.
"Salmah ina son ki bani hankalinki, ki faɗa min komai akan abin da Zahra take fuskanta akan rashin auren ta, da kuma maganganun da kika yi jiya me kike nufi da su?" Cikin sanyin murya yayi mata magana.
Bata san ta koma kusa da Baffa ta zauna ba sai da taji hannunta cikin nasa.
"Baffa!"
Taja sunan nasa tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Ido ya zuba mata alamun yana sauraronta.
"Baffa Aunty Zahra tana cikin wani hali, da duk yanda zan yi maka bayani ba zaka gane ba. Babu wanda zai fahimci halin da take ciki sai wanda ya tsinci kansa a cikin irin yanayin da take ciki. Baffa Aunty Zahra na cikin wani irin yanayi, wallahi duk murmushin da zaka gani a kan fuskarta bai kai zuciyarta ba, bata cikin farin ciki. Baffa a waje a jefe ta da mugayen kalamai, ƙannanta su jefa ta da duk kalmar da ta zo bakinsu, babban abin tashin hankalin har da kai da Mahmah. Rana zafi inuwa ƙuna, faɗamin a ina zata jingina taji sanyi a ranta Baffa?".
Ta tambaye sa hawaye na zubo mata. Shiru yayi ya na jin yanda ƙirjinsa ya ƙara nauyi.
"Babu wanda yake fahimtarta, Baffa itama fa zata so ace yau tana gidan aurenta. Amman kowa gani yake lefinta ne, ita ce taƙi yin auren ko kuma ita ta ɗorawa kan ta jinkirin auren, bayan ba haka ba ne, komai yana da lokaci da iyaka. Nata lokacin bai zo ba taya zata janyo sa? Baffa ko so kuke ta fita waje tana tare maza tana roƙon su aureta? Baffa ko kuma.." shiru tayi jin yanda ya matse hannunta da ke cikin nasa. Wani irin kuka ne ya ƙwace mata.
"Babban tashin hankalina kar muje ta kamu da cutar damuwa, dan ni ina ganin alamarsa a tare da ita. Saboda yanda wasu lokutan zanta yi mata magana tayi shiru, alamun tayi zurfi a cikin tunani. Ko kuma ta zubawa waje ɗaya ido, bata ko ƙiftawa. Koda ace a yanzu ciwon bai kamata ba, ina da tabbacin idan har kuka yi ma ta wannan auren, wallahi komai zai iya faruwa da ita, ciki kuwa harda rasata gaba ɗaya!!!"
Tana kaiwa nan ta zame hannunta, ta tashi ta bar shi a wajen dan wani irin abu take ji akan iyayen nata.
Bata koma ɗakin nasu ba, ta wanke fuskarta, ta cire sakata ta fita daga gidan, rufo ƙofar tayi sannan ta fita daga layin gaba ɗaya, bakin titi taje ta samu napep ya kai ta bayan frosetry dake ba nisa daga gidan su, cikin lokaci ƙalilan ta ƙarasa.
Da ƙafa taje ƙofar gidan da zata je, ƙaramin gida ne me kyau, ba tayi mamakin ganin gidan a rufe ba, duk da garin Allah ya waye, murmushi tayi a fili ta ce "an daɗe ba'a haɗu ba ya zama dole na ja magana wallahi" iya ƙarfinta ta saka ta fara dukkan ƙofar gidan, gajiya tayi ta ɗauki ƙaramin dutse ta haɗa wajen bugun. Idan tayi da hannu sai tayi da dutsen, tana jin alamun za'a buɗe ƙofar ta ƙara ƙarfin bugun, tana dariya a fili.
"Wane sallamammen ne zai karya min ƙofar gida?"
Muryar tsohuwar ta ratsa kunnuwanta tun kafin ta buɗe gidan.
Tana buɗewa taci karo da Salmah a tsaye da dutse a hannun ta. Ƙanƙance idanuwanta tayi cike da takaici.
"Salamatu amman dai kamar ba da iya kuɗin Habibu aka gina min gidan nan ba ko?"
"Inna sau nawa zan ce miki sunana Salmah, me wani Salamatu" ta ce tana harararta cike da jin haushi.
Itama harararta tayi ta ce "lafiya ma zaki zo min gida da asubah, idan labari kika ji jiya Ummaru ya kawo min kaji, ba baki zanyi ba gwara ki koma"
"Haba Innata me babban suna, kin manta ni da ke bata ɓaci ne, muje muyi magana kin barni a waje a tsaye, kuma yanzu wajen ƙarfe 9 shine asubah?" Bata jira cewar ta ba, tabi ta gefenta ta wuce. Gidan fess ko alamar datti babu.
"Salamatu karfa ki shigar min ɗaki ki jirani nazo" itakam tuni har ta shige ta haye gadonta na ƙarfe. Shigowa tayi da danshin ruwa a jikinta alamun alwalah tayi. Tana jin yanda take mata mita na hawa gadon da tayi bata kulata ba, har saida taga tana shirin tayar da sallah.
"Inna wai sallah zaki yi?"
"A'a kinsan kafura ce ni" ta bata amsa tana shirin kabbara sallarta. Hantsilowa tayi daga kan gadon ta tsaya a gabanta. "Wallahi Salamatu kika karya min gado sai ubanki Habibu ya biyani" bata biye mata ba ta ce "Inna bazan iya zaman jiranki har ki idar da sallah ba, dan ke idan kina sallah sai ki fi awa biyar kina yi, ni kuma ina da abin yi gaskiya"
Hankaɗata tayi ta ɗaga hannu zata kabbara sallar, ta ƙara dawowa gabanta "wallahi Inna kina kabbara sallar nan tafiya zanyi dan bazan iya jiran ki ba na faɗa miki"
"Salamatu daman dai nasan ke salamammiya ce, amman bansan kin kafurce ba, zan kira Ummaru yayi min tsakani da ke, kamar yanda yayi min da gantalallun ƴaƴansa" cike da masifa tayi maganar tana neman wayarta a ɗakin.
Riƙeta tayi tana marairaicewa, ita wallahi dagaske bata son ta tsaya jiranta dan idan ta gama sallar walahar da zata yi, haka kuma zata zauna yin tazbiyi, duk maganar da zata mata kuma bazata kulata ba, ƙarshe ma sai dai ta zuba mata carbi, shi kuma Baba Umar Allah ya saka musu tsoronsa dan bashi da wasa, yayan Baffa ne, yanzu akan tsohuwar nan tasu, tsaf zai biyo ta har gida yaci mata mutunci, idan ma bata sha duka ba.
"Inna baki san me ya kawo ni ba, kina nan ana shirin kashe takwararki"
Dakatawa tayi da neman wayar, ta juyo tana kallonta. "Wani abu ne ya samu Fatsiman?" Ta tambayeta tana mayar da dukkan hankalinta kanta, dan bata wasa da abinda ya shafi Zahra ko kaɗan.
"A'a Inna auren sadaka za'ayi mata gobe, da wani tsoho tun jiya take suma, yanzu ma da na tawo ko numfashi bata yi, shine nace kafin baƙin ciki ya kasheta gwara nazo na faɗa miki"
"Shi habibun ya fara haukane bani da labari? Dan daman ita uwar ku nasan bata da cikakken hankali" da hijabin da take shirin ta yar da sallah ta fita tana faɗa, Salmah ta biyo bayanta, ɗakin kusa da ita ta shiga, ta taso autar Baba Ummaru da take sa'ar Salmah suka fita ta rufe gidan. Napep suka hau ya nufi can gidan su Salmahn da su....
★★★
Tun da Salmah ta fita ta bar Baffa da nauyin zuciya, wani irin tausayin Zahra ne ya dirar mishi a cikin zuciyarsa. Tunani yake, meyasa tun farko bai tsaya ya fuskanci yarinyar shi ba, tabbas ta bakin Salmah Zahra na fuskantar abubuwa da yawa, kuma muddin akayi mata wannan auren, an ƙarasa ruguza rayuwarta, ji yayi wani irin rauni ya rufe shi, tabbas ya gaza a matsayin na mahaifi.
Baisan meyasa tun farko ya tsaya ya biyewa Hafsa ba, gaba ɗaya ya manta su mata ƙaramin tunani garesu, a madadin ya tsaya har ya sa ta fuskanci jarabawar Zahra ce a haka, a'a sai ya biye mata suka dinga musgunawa ƴarsu da kansu, lokaci yayi da zai tsaya mata tabbas wannan auren baza'a yi shi ba, koda kuwa mai zai faru tsakaninsa da Mahmah.
Bai kai ƙarshen tunanin ba yaji wani irin bugun gida, da yasa gabansa ya faɗi.
Mahmah cikin bacci taji bugun gida, dan yadda ake bugun ƙofar kamar za'a karyata. A tsorace Zahra ta farka da addu'a a bakinta, hijabin da tayi sallah ta zura ta fito tsakar gida, kusan a tare suka fito ita da Mahmah da Baffa. Duk tsayawa sukayi suna kallon kallo. Can jin hayaniya ta fara tashi, daga wajen Baffa yayi ƙarfin hali tafiya dan ya buɗe yaga meke faruwa.
Yana buɗewa yaga mata a ƙalla su shida, gaba ɗayan su sa'annin Zahra ne, sai mutum biyu da zasu iya girme mata, ganin suna niyyar ban gazarsa su huce, sai yayi saurin basu hanya suka shige.
Bayan su ya biyo ya ce "bayin Allah lafiya?"
Basu kula shi ba sai kan Zhara da sukayi tana tsaye, tana kallon su.
Ganin haka ne yasa Mahmah ta sha gaban su, tana tambayar su lafiya.
"Malama ba wajenki muka zo ba, wajen wannan munafukar ƴar taki muka zo". Kusan a tare suka haɗa baki suka faɗa suna nuna Zahrah.
Bata kasance cikin mutane masu tsoro ba, tana da miskilanci idan ta so, bata ɗaukar wulaƙanci ko cin mutunci, dan haka a yanzu bata ga wani dalili da zai saka a zo har gidan su aci mata mutunci ba, har ana kiranta da munafuka. Fitowa tayi daga bayan Mahmah ta tsaya a gaban su, ba tare da tsoro ko shakka ba. "Lafiya zaku zo har cikin gidanmu kuna kirana da munafuka, su waye ku?" Ta tambaye su tana tsare su da manyan idanuwanta.
"Ah lallai babu shakka, har kina da bakin da zaki mayar wa da mutane magana". Ɗaya daga cikin su tayi magana. Bata tan kamata ba sai kallonsu data ci gaba dayi, dan tana buƙatar sanin meya kawo su kafin koma menene ya biyo baya.
"Kalleki dan Allah wata ƙatuwar guzuma dake, kin gama yawon ki da gantali a titi, shine har kike tunanin ki auri babanmu. Waya sani ma ko kin kwaso cuta ki shafa masa ki cuci iyayen mu" ɗaya ta amsarwa wadda tayi magana da farko.
Sai yanzu ta fahimci daga ina matsalar take, wani irin abu taji yazo ya tsaya ya tokare mata a ƙirji, a take miyan bakinta ya ƙafe, da ƙyar ta haɗiye wani abu mai zafi, tana shirin buɗe bakinta tayi magana taji Mahmah na ce wa.
"Akan haka shine zaku zo har gida, kune mi ciwa mutane mutunci, wallahi kome zakuyi aure babu fashi, idan har ba shi uban naku ne yace ya fasa ba, amman insha Allah gobe babu abinda zai hana auren Zahra da ubanku Bala..."
FULANI
***