Free chapter · Read without an account

LOKACI CHAPTER 15

by Rabi'atu kabiru Fulani · RANTSATTSEN RABO

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

🕛⏳ LOKACI 🕛 ⏳ 

RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA 

Under Team Yota's Amazing Pen's.

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN A GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️ 

    FULANI 🤍
***

        ⏳🕛 LOKACI🕛⏳
          
          PAGE 1️⃣ 5️⃣

Cikin wani irin zafi ya ƙarasa maganar tasa, har yana dukan table ɗin gabansa.

"Calm down Zay'd please, ka bari mubi komai a hankali" cike da rarrashi Sameer yayi masa maganar.

"Na kwantar da hankalina Sameer, akan restaurant ɗina ake magana fa? Kasan matsayinsa a wajena kuma kake cewa na kwantar da hankalina? Idan akan Company ne, babu abin da ya dame ni, amman ana magana ne akan wajen da ya fimin duk wani abu da na mallaka muhimmanci a rayuwata, dole zanje a yau ɗinnan, na gama magana..."

Sosai wata jijiya ta miƙe akan goshinsa, alamun ya kai ƙarshe a ɓacin rai...

★★★

Ranar friday ta makara wajen tafiya aiki, saboda bata jin daɗi, da har ta haƙura da zuwa, amman wayar da manager ya yi mata dole ta shirya, Salmah ta saka ta shirya ta raka ta, haka kawai taji yau, tana son tafiya da Salmahn, dan daman tana son zuwa, ita take hanata gudun abin da zai je ya dawo.

Cikin dogayen riguna suka shirya, sosai sukayi kyau, kamar su ta fito a fili, bazaka taɓa cewa akwai ratan shekaru tsakanin Salmah da Zahra ba.

Da sauri Salmah ta fita, ta tafi ɗakinta, sai gata ta dawo da jaka da wayarta a hannunta.

"Big sister kin gama mu tafi?" Ta tambayeta haƙoranta gaba ɗaya a waje, wani irin ɗokin zuwa take ji, farin cikinta a bayyane yake ya gaza ɓoyuwa.

"Eh nagama, amman na canza shawara ki bari basai kinje ba, kiyi zaman ki kawai" ta bata amsa fuskarta a haɗe.

Shar sai ga hawaye ya zubo a kumatunta, kamar ƙaramar yarinya ta fara bubbuga ƙafarta a ƙasa "amman dai alƙawari kika min ai, kuma sai bayan kin gama samun rai" 

Ganin dagaske kuka take sai tayi dariya "Autah wasa nake miki share hawayenki, na gama gyara fuskarki mu tafi" 

Babu musu kuwa ta gyara fuskar, tana murmushi, tare suka fito suka nufi ɗakin Mahmah.

Da wani irin yanayi take kallon su, yanayin da idan har ba ita ce ta faɗa ba bazaka taɓa ganewa ba, a ƙasan ranta, wani irin alfahari take ji, ita da kanta tasan kaf yaranta masu kyau ne, amman idan ana maganar Zahra ƙarshe ce a wajen kyau, sai kuma Salmah da take kama da ita sosai, ɗauke kanta tayi tana tamke fuska.

"Mahmah zamu tafi" Salmah ta faɗi haka cike da ɗoki a muryarta.

"Zuwa ina?" Ta tambayeta ba tare da ta kalleta ba.

"Dara restaurant wajen aikin big sister"

Da sauri ta juyo tana kallon Zahra. 

"Ban amince ba, bada yawuna ba, yawon da kika saba zaki koya mata? Wallahi ahir ɗinki Zahra, watakam kinga zatayi candy ta samu miji tayi aurenta, shine zaki jata, dan itama mazan suƙi aurenta ko?" Cikin wata iriyar hargowa take maganar kamar zata kai mata duka.

Buɗe baki tayi zata bata amsa, sai kuma Salmah ta riga ta.

"Mahmah bazan gaji da faɗa miki ba, Aunty Zahra kamar mahaifiya take a wajena, ko a mafarki bana tunanin zata aikata abin da kike jifanta da shi, bare har tayi tunanin sakani na aikata, kuma ni na taɓa ce miki ina son nayi aure idan nayi candy Mahmah? Bazan taɓa aure ba idan har batayi ba, na gwammace na mutu babu aure wallahi da dai, nayi ita kuma tana gida a zaune, sannan Mahmah...."

"Salmah baki da hankali Mahmah kike wa magana a haka" Zahra ta katseta cikin fushi.

Shiru tayi badan ta so ba.

"Kiyi haƙuri Mahmah daman saboda tana son zuwa ne, shi ya sa nace yau ta shirya muje, amman tun da bakya so, basai taje ba, tayi zamanta, kiyi haƙuri Autah idan da rabo wata rana zaki je" 

Tana faɗar haka ta juya ta fita tana danne hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata, ta kai 5minutes a soron gidansu, taji alamun tafiya, ta fice da sauri, dan bata fatan ko waye ya ganta tana kuka.

  "Big sister"

Sunan ya ratsa kunnuwanta, cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba.

"Mu tafi duk mun makara Allah yasa ba'a dukan latti" 

Batasan ya akai ba, kawai sai ji tayi Aunty Zahra tayi mata wata iriyar runguma, ajiyar zuciya ta sauke, itama ta rungumeta back, basu ɗauki wani lokaci a haka ba, ta sake ta, ta riƙe hannunta suka nufi titi.

Saboda ta makara, tana samun napep suka, bai ƙarasa da su wajen da zasu ba suka sauka, dake babu nisa, sai suka ɗauki hanya a ƙafa, suna tafiya suna hira, cikin nishaɗi, duk da Salmah ce ƙarfin hirar, amman ta inda zaka gane hirar tana mata daɗi, fuskarta a sake take da murmushi.

Kamar ance Salmah ta juya, sai taga wata mota har ta wuce, kuma sai ta rage gudu, har suka zo suka gifta motar.

Shi kuma mutumin cikin motar, idan ya kalli Zahra sai ya maida kallonsa kan Salmah, kamar mai son tantance wani abu. ganin kallon yayi yawa Salmah sai ta dena labarin ta haɗe ranta sosai, jin kamar motar na daf da su, saita waiwaya, motar ce dai ke biye da su.

"Big sister"

"Me ya faru" Zahra ta tambayeta ganin yanda tayi kicin_kicin da fuska.

"Wani mutumi ne yake bin mu a mota"

A hankali ta waiwaya, sai suka haɗa ido, shi kuma sai ya sakar mata murmushi.

Taɓe bakinta tayi, ta ce "meybe hanya ce ta haɗa mu"

Salmah gyaɗa mata kanta tayi kawai badan ta yarda ba.

Bayan sun ƙarasa restaurant ɗin, wani decoration sai ya ɗauki hankalin Salmah, wajen ta nufa, ta tsaya ta kalli kanta a jikin mudubin, sai ta ciro wayarta, tayi hoto, ƙara gyara fuskarta tayi, tana ta sakin murmushi, a ranta take jin daman ace itace take aiki a wajen, ai wallahi da kullum sai tayi hoto kamar 100 haka.

Bayan Zahra sun gaisa da mutanen reception, ta fara gabatar musu da Salmah da take tunanin tana kusa da ita, sai da ta gama juyawar da zata yi taga babu Salmah sai ita kaɗai a wajen, baya ta koma sai ta ganta a wajen tana ta hoto tana sakin murmushi.

"Me kike haka Salmah?"

Cikin dariya ta ce "da farko dai na fara duba ko nayi kyau, da na duba kuma sai naga nafi kyau yin kyau, dan haka nace kyaun ba zai tafi a banza ba, dole ne na kashewa kaina zuciya da zafafan hotuna"

Zahra batasan sanda ta saki ƴar siririyar dariya ba, Salmah dai sai fatan Allah ya shirya mata ita.

"Allah ya shirya ki Autah wuce mu tafi, ina da aiki ni"

Juyowa tayi zata bata amsa, sai idonta ya sauka akan mutumin cikin motar ɗazu.

Yana tsaye kamar me neman wani abu, a hankali Salmah ta buɗe bakinta, sosai tayi ƙasa da muryarta tana matsawa kusa da Aunty Zahra.

"Big sister"

Zahra da har ta juya, ta juyo tana kallonta.

"Hmm?"

Salmah ta nuna mata wajen da mutumin yake da hannunta. "Kalli wannan mutumin na ɗazu" Zahra sai tabi hannun nata da kallo, aka ƙara rashin sa'a suka haɗa ido, again ya ƙara sakar mata murmushi, ɗauke kanta tayi, tana haɗe fuska sosai. 

Fuskar Salmah cike da farin ciki, "wayyo Allah na big sister, daɗi kasheni"

Da mamaki Zahra ta kalleta "ke lafiyar kuwa?"

Cikin farin cikin da ya gaza ɓoyuwa har a muryarta ta ce.

"Bazaki gane ba, na rantse kinyi masoyi yau a hanya, wayyo Allah na, yau dai Allah ya amsa addu'ata, ke baki ga tun daga inda yake binmu ba, kuma yanzu har cikin nan"

"Salmah!!" 

Bata ma jita ba, dan ta waiwaya tana kallonsa.

"Kai big sister kallesa kuma, wallahi kyakykyawa ne, kunyi bala'in dacewa"

Tsaki tayi, ta ja hannunta suka nufi cikin restaurant ɗin.

"Bana son ki ƙara wannan maganar Salmah ta tsaya iya haka, bana so kin jini ko?"

"Dagaske nake big sister saboda ke yazo nan"

"Salmah!" Ta kira sunanta a kausashe.

"Shi kenan, na yi shiru, kiyi haƙuri"

Cikin kitchen suka shiga, aikin da tazo dominsa, ta fara Salmah na taya ta da wani abin, suma ma'aikatan cikin kitchen ɗin suna nasu, hannu da yawa, dandan suka kusa kammalawa.

"Big sister na gaji bara naje daga wajen reception na zauna"

Kanta kawai ta gyaɗa mata. Ita kuma ta juya ta tafi, a ranta tana fatan ta samu wannan saurayin. zama tayi, a kujerun wajen, ta ɗauki wayar Aunty Zahra tana dannawa, amman lokaci bayan lokaci, tana kallon waje.

Babu tsammani ta ga mutumin ya buɗe ƙofa ya shigo.

"Big sister!" Ta ɗan ɗaga muryarta wajen kiran sunanta.

Ƙasa tayi da kanta, tana sakin murmushi, wayar Zahran tayi amfani da ita, wajen kiran tata wayar dake cikin kitchen. Zahra najin ringtone ɗin wayar ta fito, dan daban ta saka akan number ta.

"Ya akai? Kina buƙatar wani abu ne Autah"

"A'a kalli can"

Juyawa tayi ta kalla, dan tayi tunanin wani abu ne, sai taga mutumin ne dai a wajen, yana tsaye yana kallon cikin restaurant ɗin. Wata muguwar harara ta wurga mata.

"Bazaki kyaleni ba ko Salmah?"

Ta buɗe baki zata bata amsa, sai taga mutumin ya nufo inda suke, shiru tayi dan ma kar tayi magana ta koma cikin kitchen ɗin, dan burinta, yazo ya gabatar da kansa, a wajen Yayarta.

"Assalamu alaikum"

"Wa alaikumus salam" 
Salmah ta amsa a fili, Zahra kuma ciki_ciki.

Kallon Zahra ya yi ya ce.

"Dan Allah.."

Shiru yayi ganin yanda ta zuba masa manyan idanuwanta, fuskarta a kame.

"Ko zan iya samun..?"

Salmah ce data matsu yaje ga batunsa kai tsaye, ta kalli Aunty Zahra cikin farin ciki, tana jiran jin ƙarshen zancen.

"Please ina son magana da ke ne idan babu damuwa"

Ƙara ɗaure fuskarta tayi ta juya zata koma kitchen.

Salmah da sauri ta kalli Aunty Zahra ganin, zata bar wajen, ga fuskarta, babu alamun wasa, bare tayi tunanin dakatar da ita.

"Dan Allah ki tsaya ki saurare ni" 

Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba...

★★★

Duk yanda Sameer yaso ya bari ko a washegari ne, ya bar Abuja ya tafi Kano, yaƙi yarda, gashi bai samu flight ba, tafiyar mota zaiyi, kuma yamma tayi sosai.

Kamar ko yaushe a hannunsa ya bar duk wani abu da ya shafi Zay'd Holding's, shi kuma ya nufi Kano, dan sanin matakin da ya kamata ya ɗauka.

Daga shi sai driver suka tawo Kano, duk yanda yake gudu gani yake kamar ba gudu yake ba, ya kasa yarda ace, mutum ɗaya ne yake ƙoƙarin rusa masa abu mai matuƙar muhimmanci a wajensa, ganin kamar driver baya gudu ne, ya sa shi karɓar driving, wani irin gudu yake Shararawa a hanyar kamar zai tashi sama, sai kuma Allah ya taimaka, dare ne babu cikowar ababan hawa, wajen shaɗaya suka shigo cikin Kano, hakan yasa shi ɗaukaf hanyar gida kai tsaye.

Da ƙarfi ya danna horn, mai gadi har ya fara bacci, horn ɗin ya tashesa, kusan ma gaba ɗaya mutanen gidan saida suka tashi.

 Ta saman belcony Abhie ya leƙo da kayan bacci a jikinsa, yana ganin motar waye, ya kasa barin wajen, yana kallo aka buɗe masa get ya shigo, daga yanda ya buɗe motar da rufeta, ya fahimci yanda ransa yake a ɓace, kasa barin wajen yayi har ya shiga part ɗinsa, ya kai a ƙalla 5minutes a tsaye, sai kuma ya koma ciki, ammie dake zaune cikin shirin bacci ya kalla, kamar zaiyi magana, sai yayi shiru, ci gaba yayi da kallonta.

"Akwai magana a bakinka Babban mutum" ta ce tana murmushi.

"Ba bu komai, kawai dai kamar yaronki yana buƙatarki"

"Zay'd ne ya dawo?"

Kafaɗar sa ya ɗaga mata, hakan yasa ta fahimci ya gama magana, doguwar riga ta saka, akan kayan jikinta, ta fice daga ɗakin, sai da ta fara shiga kitchen, ta sama masa abu mai sauƙi, sannan ta wuce part ɗin nasa.

Fitowarsa kenan daga wanka ya ji ana masa, knocking, ƙananun kaya ya saka marasa nauyi, ya zo ya buɗe.

"Ammieeee" ya kira sunanta bayan ya karɓi kayan hannunta.

A parlown suka zauna, ammie na kan kujera, shi kuma ya zauna a wajen ƙafarta. Tea ta haɗa masa baiyi musu ba ya karɓa yana sha, a hankali, karantarsa take, hakan ya hanata ce masa komai, har sai da ya gama.

"Me ya faru?" Ta tambayesa har lokacin idonta a kansa.

"Babu komai ammie"

"Akwai oyaa bana son musu faɗa min"

Matsowa yayi ya ɗora kansa akan cinyarta. hannunta ta saka a cikin sumarsa tana shafawa, ajiyar zuciya ya sauke, yana jin wata iriyar nutsuwa na saukar masa.

"Ammieey restaurant ɗina.."

Sai kuma yayi shiru dan baisan me zaice mata ba, bayan hakan.

"Uhm Ina jinka meyasa mesa?"

"Kawai yanzu ba'a ciniki sosai a cikinsa, shiyasa na dawo naga abin da ke faruwa."

Ci gaba da shafa kansa tayi. "Hakan ai ba abin damuwa bane daman, kasuwa ta gaji haka, amman ka kwantar da hankalinka, in sha Allah cinikin zai dawo fiye da can baya ma, kaji yaron kirki"

Shiru yayi mata, dan yana ganin batasan abin da ya ke faruwa ba ne, shiyasa ta ke ce masa haka. Jin yanda yake ta sauke ajiyar zuciya ne, ya sa ta ci gaba da kwantar masa da hankali da kalamai, masu daɗi, har abinci sai da ta saka sa, ya ci, sannan ta tashi zata tafi, tashi yayi suka fito tare, har bakin bene ya rakata, sannan ya juya ya koma nasa part ɗin.

A bakin ƙofa ta samu Abhie a tsaye yana jiranta.

"Zaman me kika yi, sannan me aka masa?"

Shiru tayi ta na tunani, dan idan ta faɗa masa akan meye, zai iya botsare mata.

"Babban mutum, bai faɗa min komai ba, amman ina ganin kaje da kanka ka, wataƙila yayi maka bayani" 

Zaga ye ta, yayi ya tafi ya kwanta. Kanta kawai ta girgiza, yana son ɗansa, amman yaƙi bari su dawo kamar baya.

"Yaushe zaka dena fushi da shi ne?" Ta jefa masa tambayar cikin sanyin murya, tana kwanciya a bayansa.

"Ranar da yayi min bayanin dalilinsa na fara ƙin bin abin da nake so"

★

Baiyi wani cikakken bacci ba, bayan ya dawo daga masallaci shi da Khaleel part ɗin ammieey suka nufa, tana kitchen ita da Teemah, duk yanda suke da arziƙi, da masu aiki, ammie bata yarda suyi mata girki ba, ita ce take yin abinta, bayan Teemah ta girma kuma suke yi tare, gaisheta sukayi, Teemah da sai lokacin ta gansa, a guje ta tawo ta rungumesa, cike da farin cikin ganinsa.

"Yah Zay'd ka dawo lafiya? Nayi kewarka"

Khaleel ne ya ture ta "Matsa Malama"

Murmushi ya yi.

"Nima nayi kewarki princess, fatan babu matsala dai ko?"

A take kuwa ta marairaice fuska, zata yi magana, Khaleel ya tare ta.

"Daman bro ba kai take kewa ba, yanzu zata ce maka wani abu take so, bara kuma ka gani"

Hararsa tayi, tayi shiru badan ta so ba, shidai har lokacin murmushi ya ke, suna nan a kitchen ɗin har Ammie ta gama abin da take, suka ta yata kaiwa kan dianing, daga nan ya wuce dan wanka, suma duk wuce wa sukayi, ba su koma ba.

Wanka yayi ya shirya cikin, ya koma part ɗin Ammie, bayan sun gama breakfast, ya ce Teemah ta tashi ya kaita school, cikin farin ciki ta tashi ta je ta ƙarasa shirinta, sallama yayiwa Ammie suka fice.

Har bakin get ya kaita, sannan ya bata kuɗi mai yawa, driver ya ja suka wuce.

Wajen ƙarfe tara na safe, motarsa ta tsaya a bakin Zay'd Signature restaurant, bayan zuwan sa ya ɗauki ƴan daƙiƙu kafin ya fito, cikin army green suit, gyara cuff ɗin hannunsa yayi, agogon hannunsa ya kalla, sannan ya kalli restaurant ɗin.

Fuskarsa cike take da nutsuwa da kamala, babu gaggawa a tare da shi, ba zaka taɓa gane a yanayin da fuskarsa take ciki ba, da ganinsa, wasu daga cikin ma'aikatan suka fara gaishesa, amsawa ya ke cikin yanayin maganarsa.

"Good morning sir"

Manager ya gaishesa yana bin bayansa.

"Morning"

"Welcome sir, we weren't expecting you today"

Ba tare da ya kallesa ba, ya ce.

"Ni ma ban shirya zuwan ba"

Murmushi yayi jin yanda ya amsa masa kai tsaye. "Is everything okay sir?"

Kansa ya gyaɗa masa ya wuce ciki.

Babu inda bai shiga ba, duk sai da ya gama duba duk abin da ya dace sannan ya wuce office ɗinsa.

Yana zama wayar sa ta fara ringing, cirowa yayi daga aljihu, ganin Sameer ne sai ya share sa, ba tare da ya ɗaga ba, aiki ya fara a computer, wajen 2:pm ya fito daga office ɗinsa. Wajen manager ya nufa.

"Bani address na Dara restaurant"

Da tsananin mamakin abin da zai kai sa ya ɗago ya kallesa, amman baiga fuskar tambaya ba hakan ya sa ya bashi, shi kuma ya fice.

Ya kusa ƙarasawa yaji an kira sunansa.

"Sir"

Juyawa yayi ya na kallon manager dake bin bayansa, girarsa ya ɗage masa alamun me ya faru.

"Idan babu damuwa zan raka ka muje tare"

"Zan je ni kaɗai"

"Amma sir"

Kallon da yayi masa ne ya hana sa cewa komai, yana kallo har ya shige motar sa, shi kaɗai ba tare da driver yaja motar ya fice, jin wayarsa na ringing ne, yasa shi duba.

"Oga Sameer" sunan ta fito raɗau akan wayar.

"Hello oga"

"Ya akai ya yarda kuje tare?"

"A'a Oga yama tafi"

Sallama yayi masa ya katse wayar shi kuma ya mayar da akalar kiran wayar gun Zay'd.

Wajen 2:30 ya ƙarasa Dara restaurant, ba tare da ya fito daga motar sa ba, ya tsaya ya na ƙarewa wajen kallo, bayan wani lokaci kuma ya zuro ƙafarsa, ya fito........


FULANI
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol