Free chapter · Read without an account
LOKACI CHAPTER 16
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI ❣️
***
PAGE 1️⃣ 6️⃣
Bata tsaya sauraronsa ba, ta shige cikin kitchen, jin abin take wani irin banbarakwai, wai ita ake bi, wasa ma kenan, ranta a jagule ta ƙarasa aikin da take, yamma nayi tayi shirin tafiya, babban abin da ya bata mamaki, koda ta fito yana zaune, yana facing Salmah, gabansa da ruwa da lemo.
Bata ƙara kallon in da yake ba tayi musu sallama suka fita da Salmah.
"Big sister gaskiya wannan mutumin yana tsananin sonki, kinga yanda yake ta zirga-zirga shigowa da fita, shiyasa naƙi dawowa fa na zauna ina kallonsa"
Banza tayi mata bata amsa.
Wata mota ce ta ɗauki idonsu su duka biyun, Zahra a zuciyarta ta jinjina kyaun motar, baƙa ce sai ɗaukar ido take.
"Wayyo Allah kayi mana arziƙi" cewar Salmah tana nufar wajen motar.
Tunda ta tunkaro motar ya zuba mata ido ko ƙiftawa ba yayi, dake motar tint ce, na ciki yana ganin na waje, amman na waje baya ganin na ciki, kujerar daya kwantar ya ɗago, wani irin kallo yake wa Salmah, wanda shi kansa bai san kallon menene ba.
Wajen mudubi ta tsaya har lokacin da murmushi a fuskarta, gyara fuskarta tayi, duk da babu abin da tayi, sai kuma ta ɗakko wayarta, zatayi hoto.
"Salmah ranki zaiyi bala'in ɓaci, wane irin iskanci ne wannan"
Sosai muryar ta ratsa kunnuwan su, da shi da ke a cikin motar da ita kanta, da ke waje.
"Yah haƙuri Aunty Zahra muje na fasa"
"Zahrahh"
Ya maimaita sunan a saman leɓensa, sai kuma ya taɓe baki, yana ganin yanda tabi bayan wadda tayi maganar dan baiga fuskarta ba, sai dai ya zubawa tafiyar tasu ido, dake shige da ta juna.
Mutumin ɗazu ne ya ƙara shan gabansu, yana wa Aunty Zahra magiya, wadda dole ta saka su tsayawa.
"Nasan bai kamata na tsayar daku a kan hanya ba, sai dai bani da wani zaɓin, dan Allah koda phone number ce ki bani, sai na zo gida na sameki muyi magana"
Ta buɗe baki zatayi magana, Salmah tayi saurin tarar numfashinta.
"Kawo wayar"
Bata yayi ta saka mishi number Aunty Zahra, sannan ta mayar masa da wayar, wuce wa sukayi suka tafi, shi kuma ya tsaya yana murmushi.
Yana da ga cikin mota yana kallonsu duk da bayajin abin da suke cewa, har suka shiga napep idonsa na kansu, shi kansa baisan ko kallon me yake musu ba..
★★★
*Khairiyya*
Bayan tabbatar sakin da Auwal, yayiwa Khairiyya, gidan nasu ya kasance cikin wani irin yanayi, babu hayaniya, babu wani abu na farin ciki ko nishaɗi dake faruwa a cikin gidan.
A wannan lokacin ne kowa ya fahimci cewa tana buƙatar rarrashi da tausayawa, a halin yanzu tana buƙatar lokaci, dan shi ne kaɗai zai bata damar ta fara watsi, da waɗan can ɓangaren da Auwal ya tarwatsa a cikin zuciyarta, dama rayuwarta.
Da sassafe, Ummu ta tura ƙofar ɗakin da take a hankali.
Tana zaune, a bakin gado, ta jingina da bango, hannayenta rungume da gwiwowinta, kanta akansu, tun bayan tayi sallar asuba, take zaune a wajen, saboda ta kwanta ta kasa bacci, jikin wardrobe ta zubawa ido, wanda ita kanta batasan me take kallo a wajen ba, dan babu wani abu na kallo, ko na jan hankali a jiki, sosai tayi zurfi a cikin tunanin da ta tafi.
"Khairiyya!!"
Ummu ta kira sunanta da ƙarfi, ganin yanda tayi zurfi a cikin tunani, har bata ji sallamarta ba.
Firgit ta ɗago kanta tana kallon Ummu.
"Na'am Ummu"
Zama Ummu tayi a kusa da ita cike da tausayi. Gaisuwar da tayi mata ta amsa, sannan ta ce.
"Kin tashi lafiya Khairiyya?"
Ɗan murmushi tayi wanda iya kacinsa, saman leɓenta, sannan ta amsa a hankali. "Alhamdullah"
Kallon fuskarta Ummu tayi na wasu daƙiƙu, wannan murmushin nata duk wanda ya gansa yasan na yaƙe ne, murmushi ne na mutumin da yake ƙoƙarin danne damuwarsa a bayan murmushinsa, sai dai duk mai hankali kallo ɗaya zai mata ya fahimci tana cikin damuwa, kodan yanda duk ta bi ta rame, babu komai a fuskarta sai dogon hanci, da ido.
"Yanzu ina jin Khairiyya ai babu sauran damuwa, tunda dai auren ya mutu, kuma kin dawo gida, ko bakya farin ciki da sakin ne?"
Shiru tayi mata, sai faman matsa hannunta da take, ta jima kafin tayi magana ganin yanda Ummu ta zuba mata ido.
"Nayi farin ciki sosai Ummu kawai dai.."
"Kawai dai me ina jinki"
Ƙasa tayi da idonta hawaye ya zubo mata.
"Ummu ina ta tunanin ko ina da rabon ganin gudan jinina a duniya, aurana uku, ban taɓa ko ɓari ba, duk sanda nayi sujjada Ummu sai na roƙi Allah akan ya bani yara, Ummu Allah yaji roƙona ya bani, ya bani a lokacin da banyi tunani ba, amman gangancin Auwal yayi min sanadinsa, yanzu haka Ummu daga kansa, bani da rabon ƙara samu ciki, wataƙila shi kaɗai ne ƙwai na a duniya, Ummu wallahi zafi nake ji, a cikin zuciyata, idan na tuna raɗaɗi nake ji!!!"
Cikin wani irin gunjin kuka ta ƙarasa maganar, tabbacin abun yana matuƙar ƙona mata zuciya.
Hawaye ne ya cika idon Ummu na tausayinta, ba zata ce tasan raɗaɗin rashin haihuwa ba, tunda ita dai gasu nan Allah ya bata, sannan duk cikinsu babu wanda ya rasu, dukansu suna nan a raye, farin cikin samun ɗa ta sani, ba raɗaɗin rashinsa ba, dan haka kome zata faɗa mata a yanzu, sai dai dan ta kwantar mata da hankali ba wai dan tasan abin da take ji ba.
"Baki san zaki samu wancan cikin ba, kuma kika samu, dan haka ki ci gaba da roƙon Allah, ina mai baki tabbacin lokaci zaizo da zaki farin ciki, lokaci zai zo da zaki manta da duk wannan ƙuncin, wallahi Khairiyya a jikina nake jin zaki farin ciki irin wanda baki taɓa tunani ba, bansan me kike jiba, amman zance miki kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, kiyi haƙuri Khairiyya"
"Lokaci!!!"
Ta maimaita kalmar a hankali.
"Da ace lokaci yana da ikon goge abubuwan da suka faru dani Ummu da yafi min sauƙi wallahi"
Share mata hawayen tayi, sannan ta ce.
"Ba zan ce zan iya goge miki abin da ya faru ba, amman zan yi iya abin da zan iya, dan ki kasance cikin farin ciki, zan iya ƙoƙari na dan ganin kin manta baya Khairiyya"
Kallonta tayi, a karon farko tun lokacin da ta dawo gida tayi murmushin da ya fito daga ƙasan zuciyarta.
"Nagode Ummu"
Rungumeta Ummu tayi tana bubbuga bayanta.
Bayan wasu kwanaki, Khairiyya ta fara samun nutsuwa, tana yaƙi da abun da yake sukar zuciyarta a koyaushe, ba zata tace ta manta ba, a'a sai dai ta fara koyon yanda zata rayu ba tare da barin abun da ya faru ya ci gaba da shafar rayuwarta ba.
Yanzu tana fitowa waje, tana zama da ƴan uwanta, saboda yanda ko wannensu yake ƙoƙarin saka ta farin ciki, yanzu har ayyuka tana taimakawa Ummu da shi.
Tana zama ayi hira da ita, amman da zarar an ambaci aure take duk farin cikin da take ciki zai gushe, ta riga ta jinge ne kalmar aure a babin rayuwarta.
Tana zaune a ɗaki tana dannawa waya taji sallamar Aunty Maryam, da murmushi ta amsa mata, tana tambayar ta yaushe ta zo, tun ɗazu ta bata amsa.
"Khairiyya" ta kira sunanta cikin nutsuwa.
Ɗagowa tayi ta kalleta.
"Na'am Aunty"
Zama Aunty Maryam tayi a kusa da ita.
"Ya kamata ki bar abin da ya wuce_ ya wuce ina ganin lokaci yayi da ya kamata ace kin fara sabuwar rayuwa, zama haka ba zaiyi ba, kin riga kin gama idda, toh me yayi saura, yanzu me kike shiryawa kanki?"
"Me zan shirya Aunty?" Ta mayar mata da tambayar kamar zata yi kuka.
Murmushi Aunty Maryam tayi.
"Ba wai ina nufin kiyi aure ba, a'a nima zan so ki samu lokaci sosai ki huta, kawai dai wani abu haka da kika taɓa sha'awar yiwa kanki, baki ba, ko kuma wani buri da kike da shi a ranki"
"Babu wani buri da nake da shi, kuma ni bansan abin da zan yi ba"
"Ki binciki kanki, abin da kike so, idan kuma gidan Auwal ne, ai da sauran igiya ɗaya"
Shiru tayi mata sai idonta da ta fito da su waje, kamar zasu faɗo.
"Me kike so toh" ta ƙara tambayarta da murmushi a fuskarta, dan tsokanarta kawai tayi da ta sako zancen Auwal.
Tunani ta tafi, cikin sanyin murya kuma ta ce.
"Ina son ina zama mace mai dogaro da kanta"
"Wannan ma abu ne mai kyau, sai kiyi tunanin me ya kamata ki fara"
Hannayenta ta zubawa ido, wannan ne lokaci na farko, da tun bayan aurenta na farko, aka tambayeta abin da take so, ba abin da Ummu take so ba, ko mijinta, ba kuma abin da wani ne ya zaɓa mata ba, a'a nata zaɓin ake so ma a ji.......
★★★★
Zay'd har ya ja motarsa zai tafi, sai kuma wani tunani ya gifta a cikin kansa, dawowa yayi ya matsa gaban restaurant ɗin, sannan ya shiga ciki, waje ya samu ya zauna, inda ya zauna yana facing glass na kitchen ɗin restaurant ɗin, sai dai bai ga kowa a ciki ba.
Waiter's ce tazo tana tambayar sa me yake so, magana yayi mata babu jimawa ta bar wajen ta nufi office ɗin manager, bayani tayi masa shima bai tsaya ɓata lokaci ba, ya zaro wayarsa ya danna kira.
Zahra shigar su gida kenan, taji wayarta na ringing, ɗakkowa tayi a cikin jaka dan ganin mai kiran nata, sunan manager ta gani na yawo akan screen ɗin, ƙin ɗagawa tayi, dan wallahi ta gaji, ta san kuma aiki zai bata tun da ta ga kiransa.
Mahmah sukayi sallah, sannan suka faɗa mata sun dawo, Salmah kawai ta iya amsawa, ita kuma Zahra ta shige ciki dan yin wanka, gaba ɗaya zafi take ji.
Ɗaure da towel ta fito, tana goge kanta da ƙaramin towel, dakatawa tayi tana kallon Salmah dake waya da wayarta, har suka gama ta kashe wayar bata fasa kallonta ba.
"Kin kasheni Salmah meyasa kika ɗaga?"
Ta tambayeta kamar zatayi kuka.
"Manager kune naga yana ta kiranki shiyasa big sister, yace lallai ana buƙatarki a restaurant yanzu"
Muguwar harara ta watsa mata. "A gajiye na dawo gida, kuma kina ganin an kusa kiran magriba, taya Mahmah zata barni naje restaurant dan Allah"
"Kar ki damu ba ina nan ba, dole zamu je, na ƙara kashe kwarkwatar idona"
Banza tayi mata ta fara shiryawa, dan wani lokacin magana da Salmah ma, ɓata lokaci ne, doguwar riga ta saka coffe, wadda ta matuƙar haska fatar jikinta, gashinta ta gyara, haka kawai taji shauƙin kwalliya, na ɗibarta abin da bai kasance ɗabi'ar ta ba, ba ta shafa powder ba, sai lipstick da ta saka pich colour, sannan ta saka kwalli ta taje gashin idonta da mascara, aikam sosai gashin idon nata yayi kamar ta saka eyelashes, gel ta saka ta gyara gashin dake gaban kanta, sannan ta gyara girarta, rolling ɗin mayafin rigar tayi, haka kawai ta tsaya ta zubawa kanta ido.
"Wayyo Allah na!" Salmah ta furta da ƙarfi tana tsayuwa a gabanta. A tsorace Zahra ta juyo tana kallonta. "Bazan gaji da faɗa ba ko zaki dakeni, wallahi big sister kina da wani irin mugun kyau, ba iya kyau ba kar ki manta mugu gareki a kyaun ma" batasan sanda ta kwashe da dariya ba, cikin dariya ta ce.
"Autah kyaun ma, akwai mugu kenan?"
"Ehmana big sister kamar dai naki wallahi, zo mu tafi kafin Mahmah ta canza shawara, nace mata Inna ce take kiran mu, amman tsaya nima nayi kwalliyar"
Gaban mudubinta, taje ta hau shafe_shafe, bayan ta gama ta buɗe wardrobe ɗinta, ta ɗauki sabuwar abaya ta saka, Zahra bata gajiya ko kaɗan da siyan dogayen riguna, da zarar ta samu kuɗi zata siya, mafi akasarin kayanta, babu sket, sai dai ɗaiɗai kun zani, koyaushe cikin ɓoye baiwar da Allah yayi mata take, dan sai sanda wani ya ganta babu doguwar riga, ko da kayan shan iska zai fahimci dalilin ta na sitirta jikinta.
Sallama suka wa Mahmah sannan suka fice daga gidan, drop ɗin napep suka hau, ya mayar da su Dara, lokacin da suka je ana kiran sallar magriba, hakan yasa da suka shiga babu mutane da yawa, kai tsaye office ɗin manager, ta nufa sai dai bata same sa ba, amman ya bar mata saƙo, tare da Salmah suka shiga, basuyi mamakin ganinta ba, dan su kansu mamakin order da aka saka suke, ya saki kuɗi me kayan kuma ya faɗi abin da yake so, kamar dai ya ninka musu abin da ya saka a masa.
"Auta ba shiririta zaki ba, kinsan yan da nake haɗa doughnut, dan haka ina buƙatarsa yanzu, kar ki canza komai, kuma kar ki ƙara, kiyi maza ki haɗa, sai ki basu su gasa, ni kuma zan haɗa cake, bana son muyi dare yanzu dan Allah"
Juyawa tayi ta bawa sauran ma aikin da zasuyi mata. Ita kuma ta fara haɗa cake ɗin, cike da ƙwarewa.
★
Tunda aka tabbatar masa da wadda zatayi masa kayan da yasaka order tana hanya ya yanke shawarar yaje gida yayi wanka sai ya dawo, yana hanya akayi sallah hakan ya tilasta masa, tsayawa yayi sallah a hanya, sannan ya nufi gida, a gyare ya samu part ɗinsa wanda ya tabbatar aikin Princess ne, wanka yayi ya fito.
Cikin kaya masu sauƙin nauyi ya shirya, ya fito, yana shirin kunna motar sa yaji an kira sunansa daga bayansa.
"Yah Zay'd"
Juyawa yayi yana kallonta, fuskarta kawai ya kalla yasan tayi kuka.
"Me ya faru" ya tambayeta yana shafa kumatunta. Wani kukan ta ƙara sakar masa, sai kuma ta faɗa jikinsa, rumgumeta yayi back yana jin kukan nata har cikin zuciyarsa.
"Ba ya khaleel ba ne"
Bai bata amsa ba sai hannunta da ya ja ya sa ta, a mota, indai faɗansu ne sun saba, amman tun da tayi kuka, ya tabbatar ba irin faɗan da suka saba bane, cool music ya saka a motar saboda yasan tana so, ai kuwa sai gashi ta fara warewa a hankali.
Ganin a inda suka yi parking sosai abin ya bata mamaki.
"Yah me za muyi anan bayan kana da restaurant?" Bai bata amsa ba sai hannunta da ya ja suka shiga ciki....
FULANI
***