Free chapter · Read without an account
LOKACI CHAPTER 17
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI ❣️
***
PAGE 1️⃣ 7️⃣
Hannunsa riƙe da Teemah suka shiga cikin restaurant ɗin, kallon wajen ya yi kafin ya zaɓi inda za su zauna, abin da ya ja hankalinsa a yanzu mutane sun fi cika a cikin wajen fiye da lokacin da ya zo, girarsa ya ɗaga ɗaya yana zama.
Hankalinsa ne ya koma, kan glass ɗin, da ke tsakanin wajen cin abinci da kitchen, glass ɗin ya zubawa ido domin tanan customer's suna ganin yanda ake shirya abubuwa. Wajen ya zubawa ido yana son tantance wace a cikin matan da ke aiki.
Kusan su 6 ne a wajen, huɗu suna sanye da unifoam me ɗauke da tambarin restaurant ɗin, biyu kuma sauna sanye da dogayen riguna, ɗaya ta ɗaura apron akan rigar jikinta, ɗayar kuma babu wani abu da ya alaƙantata da wajen.
Bayanta Zay'd ya zubawa ido, ba tare da yasan abin da yake kallo ba, yana son dai ya tuna kamar yaga me irin bayan a ɗazu da yamma, daga inda yake yana ganin yan da suke aiki, yana jin yanda wasu abokai suke hira har baisan ya kallesu ta gefen idonsa ba.
"Wallahi ni yanzu babu wani snacks da nake jin daɗi idan bana wajen nan ba" ɗayan ma ya basa amsa.
"Yah ina zuwa dan Allah" Teemah tayi maganar tana tashi daga wajen, ba tare da ta jira cewarsa ba. Hankalinsa ba akanta yake ba, hakan yasa bai masan ta bar wajen ba.
"Big sister, tun da mun gama bara na fita na sha iska, nagaji"
Kanta kawai ta girgiza tana murmushi. "Raguwa sauran kuma kiyi nisa" itama murmushi tayi ta fice.
Tana fita idonta bai sauka a ko ina ba sai akan Zay'd da yake zaune ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, wata iriyar faɗuwar gaba ce ta ziyarci Salmah dan zata iya ce wa, tun da Allah ya halicceta bata taɓa ganin namiji me kyaunsa ba, ɗauke kanta tayi tayi waje da sauri zuciyarta na bugawa.
Tana fita daga wajen, taga wata yarinya tana ta ɗaukar hoto tana murmushi, bata damu ba duk da wayar yarinyar iphone ce, ta ta kuma redmi, haka ta ciro abarta itama tana ɗauka.
"Please sister ko zaki taimaka kiyi min hoto" siririyar muryarta ta ratsa kunnuwan Salmah.
"Me zai hana" ta bata amsa tana karɓar wayar tata, sosai suka shagala suna ta yin hotunan cikin kwanciyar hankali, kamar a cikin gida, har basu san sanda suka fara yi a tare ba.
Zahra na tsaye a gaban table, hankalinta gaba ɗaya, yana kan cake ɗin dake gabanta, a hankali take shafa cream ɗin cake ɗin, cikin nutsuwa take dan tana son komai yayi mata daidai kamar yanda take so, bayan ta gama shafawa, ta ɗauki piping bag ta fara yi masa yi masa kwalliya, wata iriyar kwalliya tayi wa cake ɗin ta fulawa, kallon cake ɗin tayi da murmushi a fuskarta dan ita kanta decoration ɗin da tayi masa ya matuƙar burge ta.
"Alhamdullah" ta furta a hankali, dan sosai cake ɗin yayi kyau kamar bada hannun mutum aka yi sa ba.
Matsawa tayi inda Salmah tayi mata doughnut, dan sun riga sun soya sa, shirya su ta fara yi cike da ƙwarewa, wasu ta saka su a cikin chocolate, wasu kuma tayi musu kwalliya da icing da sprinkles.
Wata ce da suke ɗan wasa wasu lokutan, ta matso wajen da murmushi ta ce.
"Zahra wallahi da yawan lokuta, idan kika haɗa abu sai naji daman ni ce, kedai Allah ya baki kin iya komai"
Murmushi tayi kaɗan "ba dai komai ba, kema ai kin iya, tun da anan nazo na same ki"
"Chaɓ ke kike ganin haka wallahi, kina ganin yanda yanzu restaurant ɗin nan yake mugun cika da mutane wanda kuma duk saboda ke ne, ai wallahi duk ranar da akace babu ke restaurant ɗin, ya tashi daga aiki"
Rausayar da idonta tayi ba tare da ta basa amsar maganar ta ba, ta canza da wata.
"Ni dai tai maka min ki kai waɗannan wajen counter"
Ɗauka tayi ta fice, ita kuma ta ci gaba da haɗa abubuwan, ganin komai ya kammala ne yasa ta sauke ajiyar zuciya, dan hankalinta yayi gida kuma.
Juyawar da tayi ne ya bawa Zay'd damar ganin gefen fuskarta, duk da bai san taba, amman ganin yanda take komai ya tabbatar masa da cewa itaɗin ce, bai taɓa jin tsanar mutum a lokaci ɗaya ba, sai a kanta, wata iriyar ƙiyayyarta yake ji har ƙasan zuciyarsa, tun kafin ya ganta, yana kallonta tayo hanyar waje zata fito daga cikin kitchen ɗin.
"Toh Autah sai an jima kice wa takwarata ina gaisheta, sai munyi waya"
Muryar Teemah ta katse masa tunaninsa, har baisan ya ɗago yana kallonta ba. "Autah zo ki gaisa da yayana" tayi maganar tana nufar inda Salmah tayi. Tana ƙoƙarin turjewa taja hannunta suka nufi inda yake.
"Barka da dare" Salmah ta furta muryarta na rawa, dan wani irin kwarjini yayi mata, mussamman daya watsa mata idonsa. A dake ya amsa mata, yana maida kallonsa kan masu ajiye masa order da ya saka.
"Salmah ina kika je, kina ganin yanda dare yayi ko, wuce mu tafi"
"Lah ga Aunty Zahra ta ku gaisa, ta kwararki" Salmah tayi wa Teemah magana tana nuna mata ita da hannunta.
Ta ƙasan ido ya kalli wadda aka kira suna da Zahra, dan sosai sunan Ya daki zuciyarsa, yana girmama duk wata mai wannan sunan, saboda muhimmancinsa a gare sa.
Baisan ya ɗago duka idonsa yana kallonta ba, har sai da tabar wajen, inda ta bari ɗin ya ci gaba da kallo baya ko ƙiftawa, zama Princess tayi, dan batasan koya gama abin da yake ba.
Kayan gabansa ya ɗauka, itama ta ɗauki wasu, suka fice daga restaurant ɗin, da sassarfa ya ƙarasa motarsa ya buɗe, ganin yanda yake sauri ne yasa itama ta ɗaga ƙafarta ta bisa.
Wani irin gudu yake kamar zai tashi sama, gaba ɗaya Teemah ta gama tsorata, gashi bata ga fuskar da zata dakatar da shi ba, dan wani irin ja idonsa yayi mai ban tsoro, ƙanƙame jikinta tayi hawaye na bin kumatunta na tsoro, Allah ya taimaka dare ne, babu cunkoson ababen hawa, wani irin horn ya danna, da yasa ka mai gadi buɗe masa get ɗin cikin sauri, yana ja da baya.
Bai gama parking ba, ya fita daga motar, cikin wani irin taku ya nufi part ɗinsa, yana jin yanda ya jiƙe da gumi, yana shiga ya ware ac ɗin da ke cikin ɗakinsa, amman duk da haka wani irin gumi yake haɗawa, toilet ya shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyi, ko zai samu ya dena jin abin da yake ji, amman a banza, ya kusa 30minutes a ciki kafin ya fito.
A gefen gadonsa ya zauna ya dafe kansa, ƙasan carpet ya ƙurawa ido, shi kansa baisan tunanin me yake ba, kamar yan da baisan abin da ya tunzura masa zuciya ba, sai dai ya alaƙanta hakan da tsanar yarinyar da yaji. Wayar sa ya ɗakko yana jujjuyawa.
Number Sameer ya nemo, shiru yayi na ɗan lokaci kafin ya danna masa kira.
"Dude kira nawa nayi maka amman baka ɗaga ba, an ce min kaje restaurant ɗin fatan komai dai-dai babu wata matsala?"
Shiru ya yi na wani ɗan lokaci.
"Ina buƙatar yarinyar" yayi maganar kamar an fizgota daga bakinsa.
Shiru Sameer ya yi, dan baisan akan wa yake magana ba.
"Wace yarinya kake magana Zay'd"
Shiru yayi masa yaƙi magana.
Cikin rarrashi ya ce "Zay'd please talk mana"
Ajiyar zuciya ya sauke.
"Sameer" sai ya yi shiru kamar mai shawarar abin da zai faɗa.
"Ina jinka Zay'd"
"Yarinyar da nazo Kano saboda ita, ina buƙatarta a restaurant ɗina, kota halin yaya, dole ne ta koma wajena da aiki" duk da Muryar sa ta kasance da sanyi, amman zaka ji zafi a cikin furucinsa.
"Zay'd"
Daga haka Sameer yayi shiru dan ya ma rasa abin da zai ce masa, yasan Zay'd baya taɓa abu sai da dalili, ya kuma san sa da taurin kai, tun da kuma yace yana buƙatarta, koda bala'i sai ta koma wajensa da aiki, yanda yayi magana akan ta, abin ya basa mamaki dan Zay'd duk yanda zaiwa wani bayanin wanene shi, ba zai taɓa fahimta ba idan har ba farin sani kayi masa ba, ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
"Sunanta?"
"Bansaniba"
"Toh ni yanzu taya kake son naje nema maka ita baka san sunanta ba?"
Tsaki kawai Zay'd yayi ya kashe wayar sa, wata wayar ya ƙara kira tana fara ringing aka ɗaga, gaishesa akayi ya amsa sannan yayi bayanin abin da yake so daga haka ya kashe wayar sa....
★★★
"Autah dare yayi anya zamu je gidan Inna?"
Shiru tayi alamar tunani sai kuma ta numfasa "gwara dai muje ko bamu daɗe ba" napep suka tare ya kai su har ƙofar gidanta, Zahra na basa kuɗi, Salmah ta wuce ta fara bugun ƙofar, jin an buɗe ƙofar ba tare da wata hayaniya ba, sai abin ya bata mamaki, amman tana ganin Maryam ta saki murmushi.
"Haba nayi mamaki wallahi ashe kece"
Itama murmushin ta mayar mata, suka gaisa sannan Zahra ta ƙaraso suka gaisheta, suka nufi cikin gidan, da sallama suka shiga, ɗakin Inna dake ɓoye abu a ƙarƙashin gadonta.
"Jimin jaraba tunda garin Allah ya waye baku zo ba sai cikin dare, halan Habibu ne ya baku labari ya kawo min abin arziƙi, shine kuka kwaso ƴammatan ƙafafuwanku kuka zo dan ku ci"
"Toh ke ma dai Inna tun da har kinsan babanmu ne ya kawo ai dole muzo aci tare da mu" Salmah ta bata amsa tana ƙoƙarin janyo abin da ta saka a ƙasan gadon.
"Fatsima ki rabani da Salamatu" tayi wa Zahra magana tana ture Salmah.
Waje ta samu ta zauna sannan ta gaisheta, ba tare data biye mata ba, faɗa suke sosai da Salmah dan ta ce lallai sai taci ko menene ai babanta ne ya kawo, ita kuma Inna ta ce bata isa ba, idan ubanta ne ita kuma ɗanta ne, ƙarar wayar Zahra da ake ta kira ne ta ishi Inna ta ce. "Amman dai Fatsima kamar wayarki ake kira ko?"
"Wai sau nawa zance miki idan ba zaki ce min Fatima ko Zahra ba, kiyi shiru ba sai kin ambaci sunana ba, ke tsohuwar nan kin fiya fitina wallahi" tana mita tana duba mai kiran nata, baƙuwar number ce, hakan yasa ta mayar da wayar silent, ta saka a cikin jaka.
"Ga fitinanniya can kin barota a gidan habibu"
Gajeran tsaki taja ta cewa Salmah ta tashi su tafi. "Ke matsalata da ke kin fiya zuciya takwara, zauna na baki toh kar ki tafi, amman kar ki bawa Salamatu kinji" Inna tayi maganar da sigar rarrashi tana janyo samira daga ƙasan gadonta. Gasashiyar kaza ce, da tsire yaji ƙuli_ƙuli ta zuba mata a faranti ta miƙa mata, sannan ta ƙara janyo kofin sha, ta zuba mata fura damammiya, bata yi musu ba ta zauna ta fara ci, tana haɗawa da furar.
Ƙasa_ƙasa Salmah ta ce "kuma wallahi labari me daɗi nazo baki, amman tun da kika hanani kinwa kanki" ita ma murya a ƙasa ta ce "ki fara faɗa min sai na baki"
"Ba zan faɗa ba" ta ce tana hararar Inna dan miyanta sai tsinkewa yake. Ita kuwa ta ƙara mayarda kayanta ƙasan gado. Ganin dagaske bazata bata sai ta ƙara matsawa kusa da ita "ba dai kinga anata kiran wayar Big Sister ba?"
"Eh toh sai akayi yaya"
"Saurayi tayi fa, shine ya ke ta kiranta, baki gansa ba, kyakykyawa wallahi, kuma data tashi kwatantata masa gidansu, nan ta nuna masa shiyasa kika ganmu yanzu ai"
Take kuwa farin ciki ya bayyana akan fuskarta, har ta juya tana kallon Zahra, da haka kawai ta tsargu akan maganarta suke, ganin yanda suke ƙus_ƙus, gashi kuma duk sun zuba mata ido, bata ƙara shan mamaki ba, sai da ta ga Inna ta bawa Salmah abubuwan da ta bata, bakinta ta taɓe a ranta ta ce "kwa ji da shi"
Wajen ƙarfe 9 suka bar gidan Inna suka tafi gida, bayan ta gama tofe Zahra da addu'a, lokacin da suka je, Baffa da Mahmah suna tsakar gida a zaune, gaishe su suka yi, Zahra ta wuce ɗaki, yayin da Salmah ta zauna a kusa da Mahmah, ita da kanta tasan Mahmah tana sonta, dan duk abin da zata mata bata iya fushi da ita, kamar yanda itama Salman take matuƙar ƙaunar iyayen nata, hira suke ta zauna anayi da ita.
Toilet ta shiga tayi wanka ta fito, bata Sallah hakan yasa, tana fitowa tayi shirin kwanciya, ba yunwa take ji ba, shiyasa tana saka kayan bacci tabi lafiyar gado, dan jikinta ciwo yake mata sosai. Wayarta ta ɗakko sosai tayi mamakin ganin tarin misscalled har da message guda 2, bata ma tsaya karantawa ba, tabi misscalled ɗin, katse kiran akayi, taɓe bakinta tayi ta ajiye wayar ta fara addu'a kenan, taji wayar na ringing, ɗagawa tayi ta kara a kunnenta.
"Assalamu alaiki"
Muryar mutumin ta ratsa kunnuwanta, amsawa tayi, daga haka ta tsuke bakinta.
Cikin nutsuwa ya fara gabatar mata da kansa "Nine wanda ɗazu ya karɓi number ki, sunana Fahaad, daman naga sister ɗinki ce, kuma tayi min, naga bai kamata na tunkareta kai tsaye ba, tunda tana tare da ke, shiyasa nayi miki magana, dan Allah idan babu damuwa a bani dama a wajenta"
Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, ba tare da ta bari ta fito fili ba. "Ma sha Allah zan tura maka number ta sai kayi mata magana"
"Nagode sosai Auntyn mu, amman baki faɗa min sunan ki da nata ba"
"Sunanta Ummu Salmah, amman an fi kiranta da Salmah" daga haka tayi masa Salmah ta katse, tana kashewa tayi masa sending number Salmah.
Harta fara bacci Salmah ta shigo ta tashe ta "Big Sister saurayinki ya kirani, munyi magana, yana da kirki sosai wallahi" ita dai da ido ta bita, ta fahimci har yanzu Salmah sai a hankali.
"Baffa ne ya ce yana sha'awar wainar shinkafa da sinasir, wai ya daɗe bai ci ba" ta faɗa mata tana kwanciya a bayanta, nan ma bata tankamata ba, sai da taga zata yi bacci sannan ta ce tayo alwala tazo tayi azkar sannan tayi baccin. Tana tura mata baki ta shiga toilet ɗin ɗakinta, ita kuma ta fita ta nufi kitchen.
Shinkafar tuwo ta ɗiba, daga tsaye ta gyara ta, sannan ta jiƙa, duk wani abu da zata buƙata na wainar saida ta tanadesa tun a daren, sannan ta sabunta alwalah ta kwanta, babu jimawa bacci yayi gaba da ita, ba ita ta farka ba har sai da akayi kiran sallar asubah, Salmah ta tasa, sannan ta shige toilet tayi alwala, tana fitowa Salmah ta shiga, karatu ta fara a hankali, Salmah kuma tayi sallah, bayan ta idar sukayi azkar, sannan suka koma suka kwanta.
Wajen ƙarfe 9 ta farka, ruwa ta watsa, ta saka kayan zaman tsakar gida, sannan ta nufi kitchen, wanke shinkafar tayi, ta gyara kayan miya, cikin few minutes ta dafa farar shinkafa, ɗaki ta koma, Salmah dake bacci ta tasa dan dole ta kai maita markaɗe.
"Autah" ta kira sunanta tana jan ƙafarta.
"Uhmmmnm" ta ce tana gyara kwanciyarta. Da ƙyar ta samu ta tashi, hannunta cikin nata, suka shiga toilet ta wanke fuskarta, sannan ta fito tana mitar bacci bai ishe ta ba.
"Idan kin dawo sai ki koma ai" ta bata amsa bayan sun fito daga toilet ɗin. Hijabi ta zura itama, suka tafi kai markaɗen tare, da suka je da ɗan layi, dan ma inji biyu ne a wajen, na markaɗen kayan miya daban, na markaɗen wake, shinkafa, gero daban, shiyasa abin yazo musu da sauƙi, sun kai wajen 25minutes a wajen, sannan akayi musu, gida suka koma har lokacin babu wanda ya tashi.
Kitchen ta shiga ta fara aikinta, ita kuma Salmah ta fara gyara gidan, kafin kace me sun kammala gyara da abinci, wanka Salmah ta shiga a ɗakinta, zaman jiranta tayi dan itama dole tayi wanka, ita ya zamar mata jiki ma, muddin tayi aiki sai tayi wanka, Salmah na fitowa ta shige, bata jima ba ta fito, shirin bacci tayi dan yau ba zata wajen aiki ba, tama kashe wayar ta.
"Big sister, ba zaki aiki bane naga kin kwanta, har da kashe waya?"
"Eh Autah hutawa zanyi nagaji"
Fita tayi ta bata waje, dan ita dai nata baccin ya fece, ɗakinta ta tafi ta kunna data, sabuwar ƙawarta taga tayi mata magana, a watsapp, sai kuma Fahaad da tayi saving da yayana, chartting ta zauna tana yi, hankali kwance.
"Yaushe zan same ki a gida?" Fahaad ya tambayeta.
"Yau ma big sister tana gida bazata aiki ba, zaka iya zuwa" ta basa amsa.
"Ok ki bani address toh, zan zo bayan magriba in sha Allah" a take ta tura masa, daga nan ta kashe data, ta kwanta itama, sai dai farin ciki ya hanata bacci, dole ta watssake, wani irin farin ciki mara misaltuwa take ji a cikin zuciyarta, big sister ɗinta tayi saurayi, kuma ɗan gayu, yau itama zata yi zance taji ya ake ji, bata taɓa zance ba, dan da wayonta bata taɓa jin ance ana sallama da itaba, amman bata saniba koda bata da wayo.
Kasa haƙuri tayi ta tafi ɗakin Mahmah, suna zaune da Baffa suna hira sama_sama, tayi musu sallama ta shigo, zama tayi idan ta kalli Mahmah sai ta kalli Baffa, fuskarta ɗauke da dariya.
"Salmah kefa sai a hankali, lafiya zaki zo ki saka mu a gaba, kina dariya?" Mahmah ta katse ta.
"Autah me muka samu?" Baffa ya tambayeta yana jin daɗi ganin yarinyar tasa a farin ciki.
"Albishir ne me tsada, dole ku kawo tukwuici"
Ba musu Baffa ya zura hannunsa a aljihu ya ciro kuɗi ya bata, hannu ta miƙawa Mahmah, murmushi tayi ta tashi ta ɗakko humrah ta bata.
"Jiya big sister tayi saurayi, Anjima zai zo wajenta, na basa address na gidanmu, ji nake kamar daɗi zai kasheni" ta ƙarasa fuskarta ɗauke da wani irin farin ciki.
"Dagaske Salmah?" Mahmah ta tambayeta cikin sanyin murya.
"Dagaske Mahmah ai bazanyi wasa da irin wannan ba kin sani"
Shidai Baffa baice komai ba sai fatan alkhairi da yayi a cikin zuciyarsa. Tashi tayi ta koma ta sameta har lokacin bacci take yi.
Kwanciya tayi, a kusa da ita tana ta kallonta, addu'a take ta mata na fatan Alkhairi, da fatan Allah yasa ayi komai cikin ƙanƙanin lokaci a gama.
A hankali ta buɗe idonta tana addu'a, da sauri ta tashi tana kallon Salmah da ta zuba tagumi tana kallonta kamar ta samu tv. "Salmah lafiya?" Ta tambayeta tana taɓa kanta.
"Ras nake" tsaki tayi ta shiga toilet ta wanke fuskarta da bakinta ta fito, har lokacin Salmah na a yanda take, kasa haƙuri tayi sai da ta ƙara tambayarta kodai bata da lafiya ne, ta ƙara bata tabbacin lau take, haka kawai taji a ranta bazata faɗa mata abin da ya faru ba, har sai yazo sannan zata ce mata ta fito, suprise nata zatayi.
"Muje ni yunwa nake ji"
Batayi musu ba tabi bayanta, ɗakinsu Mahmah suka shiga, suna a yanda Salmah ta bar su, gaishesu tayi, suka amsa har da Mahmah, da mamaki ta ɗaga ido ta kalli Mahmah jin yanda ta amsa mata gaisuwar, ɗauke kanta tayi, shiru ɗakin ya ɗauka. Baffa ne ya katse shirun ɗakin.
"Uwata a bamu abinci mana yunwa nake ji"
Fita tayi ta haɗa musu abincin, ta kawo sannan ta fita ta zuba musu suka tafi ɗaki, sosai take mamaki a ranta, na kulata da Mahmah tayi, amman ta bar hakan a ranta ko Salmah bata bari ta fahimci halin da take ciki ba, sai dai ta makara dan tana ankare da komai.
Ranar hini sukayi a gida ba tare da sunje ko ina ba, da yamma Salmah taje ɗakin baƙin da suke ajiye baƙi maza, ta gyara dan an daɗe ba'ayi zance a cikinsa ba, sannan tayi masa turaren wuta, bayan ta dawo ta zaɓar wa Zahra kaya tayi musu turaren kabbasa, har da simple abinci ta haɗa, da lemo tana gama wa ta kai ɗakin ta ajiye, sannan ta yi wanka dan ta gaji.
"Autah yau tsafta kike ji naga alama" Aunty Zahra tayi maganar tana kallonta.
"Bazaki gane ba ne, yau ina cikin Alkhairi dumu_dumu wallahi"
Murmushi tayi, a haka suka ci gaba da hira, bayan sallar magriba ya kirata yana kan hanya, farin cikinta ne ya ƙara daɗuwa akan wanda take yi, idan ta kalli Zahra da tasaka abayar data ajiye mata tana ta tashin ƙamshi sai taji kamar ta taka rawa dan murna.
Yana mata waya yazo ta daka tsalle tana ihu, Mahmah ce ta shigo ɗakin dan ganin ko lafiya, amman sai ta sameta tana ta juyi tana dariya, Zahra na mata magana ko bi takanta ba tayi ba.
"Ke lafiyar ki?" Mahmah ta tambayeta.
"Mahmah saurayin Aunty Zahra ne ya zo, yayi min waya yanzu"
Wata iriyar faɗuwar gaba ce ta ruski Zahra, a ranta tana jin shikenan Salmah ta ƙara ɓallo mata ruwa, kar dai bai faɗa mata ita yake so ba, ya bar ta da tunanin ita yake so, kun kashe ni ta ayyana hakan tana kallon Mahmah ta gefen idonta.
"Kin tsaya shirme kije ki shigo da shi"
Da gudu ta ɗauki hanya zata fita, duk da Zahra bata cikin nutsuwa sai da ta dakatar da ita.
"Ki canza kaya malama, sannan ki tafi a hankali"
Babu musu ta canza ta saka turare sannan ta fice. Yana tsaye cikin manyan kaya a jikin motarsa, sallama tayi masa sannan tayi masa jagora zuwa ciki, bayan ya zauna ta gaishesa, amsawa yayi, sai ta miƙe.
"Ina ƙara maka barka da zuwa yayana, bara naje na turo maka ita"
"Dakata" ya ce ganin tana niyyar fita.
"Wa za ki kira min?"
"Big sister mana" ta basa amsa.
"Ki bari mu gama toh sai ki kirata mu gaisa" bata wani fahimcesa ba, hakan yasa ta dawo ta zauna.
Kallonta yake tayi, har sai da taji ta takura da kallon, ƙoƙarin tashi take ya ƙara dakatar da ita.
"Kamar yanda nayi wa Auntyn mu bayani, ni sunana Fahaad, na ganki kuma na yaba, ina fatan zaki karɓe ni hannu bibbiyu"
A take kuwa duk wani farin ciki dake kan fuskarta ya ɓace, cikin wani irin yanayi ta ce.
"Daman ba Aunty Zahra kake so ba?"
"Ba yayarmu nake so ba, Ummu Salmah nake so..
Na biya bashin har