Free chapter · Read without an account
LOKACI CHAPTER 18
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
SADAUKARWA A GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI ❣️
***
PAGE1️⃣8️⃣
Ya bata amsa fuskarsa ɗauke da murmushi.
Wani abu ne yazo ƙirjinta ya tsaya, da ta tuna abin da hakan zai iya haifarwa Aunty Zahra, take taji wani irin gumi yana tsatstsafo mata, fuskar Mahmah kaɗai data gifta a idanunta, sai da ta kusa fasa ihu saboda tashin hankali, wani irin tunani ta tafi na neman mafita.
Ganin yanda tayi zurfi a cikin duniyar tunani ne ya sa shi katseta.
"Ina fatan Salmah zaki taimaka ki amshi ƙoƙon barata"
Kallonsa take, ko ƙiftawa batayi, shawara ɗaya ta yanke a cikin ranta, ba tare da wani dogon tunani ba, kuma ta bayyana masa.
"Ina son ka janye son da ka ce ka na min, ka mayar da shi kan yayata, har ka aureta"
Cikin rashin fahimta ya ke kallonta, ya jima yana kallonta kafin ya ce.
"Bangane me kike nufi ba"
"Ni duk a tunani ita kake so ba ni ba, ni a yanzu babu lissafin soyayya ko aure a cikin rayuwata, shiyasa na ce maka ka auri yayata, tafini komai, ilimi, kyau, nagarta, kyakkyawan hali, babu a inda zan ce maka ta na da makusa, dan haka ka koma wajenta"
Tun da ta fara maganar ya zuba mata ido, yana so ya tabbatar da ko lafiyarta ƙalau.
"Ta ya ya ke na gani ina so, zaki ce na koma wajen yayarki? Ita yayar taki ta rasa manema ne, da zaki turani wajenta?" Ya jera mata tambayoyin yana ƙara kallonta.
Shiru tayi ta rasa amsar basa, sai kuma ta miƙe tsaye.
"Ba zaka samu soyayya a wajena ba, dan haka ka manta ka taɓa ganina, amman idan har zaka so yayata hanya a buɗe take zan ta yaka neman soyayyarta"
Shima miƙewa yayi "bana jin da mutuniyar kirki ce, zaki dinga neman kai da ita, ke na so har zuciyata, amman naga alamar kema bata kirkin ba ce, dan haka da ga ke har yayar taki, kusha zamanku bana buƙatarku"
Bata son hayaniya, dan kanta wani irin sarawa yake, hakan yasa kawai ta nuna masa ƙofar ɗakin da hannunta, giftata yayi yana jan dogon tsaki, yana fita ta zube a wajen ta fashe da kukan da take ta riƙewa, babban tashin hankalinta, yanda surutunta ya kaita ta kai zancen gaban Mahmah, amman ya zatayi, gashi tana ji ya yaɓa musu magana amman gudun janyo hankalin Mahmah ko maƙota yasa ta dole ta shanye, sai dai ta sha alwashin ko a waya ne sai ta basa amsa wallahi.
"Karɓi turaren ki fesa, nama rasa zaman me Salmah tayi daga zuwa shigo da shi" Mahmah ta miƙawa Zahra turare tana mita.
Kasa karɓa ta yi, dan a take jikinta yayi wani irin mugun sanyi, Allah kaɗai yasan yanda zuciyarta take bugawa, tana shirin magana Salmah ta shigo.
"Ke lafiyar ki?" Mahmah ta tambayeta ganin yanda ta shigo tana kuka.
"Mahmah ya tafi?" Ta ce tana ƙara fashewa da kuka.
"Ban gane ya tafi ba?" Mahmah ta ce tana mayarda hankalinta kanta.
Shiru tayi ta rasa me zata ce mata, wata iriyar tsawa ta daka mata, wadda ta saka Zahra runtse idonta, duk da ba da ita take ba.
"Mahmah wai ba Aunty Zahra ya ke so ba, ni ya k..ee.. so..." Ta faɗa tana ƙara rushewa da kuka, dan sosai abin yake cin ranta.
Shiru Mahmah tayi na wani ɗan lokaci.
"Toh meye a ciki dan ya ce ke ya ke so ba ita ba?" Tayi maganar tana tsare ta da ido.
Kanta ta fara girgizawa tana haɗiye kukan da take.
"Mahmah bana sonsa, duk tunanina ita ya ke so, saboda haka alamun sa ya nuna tun farko,amman daga baya ya canza ya ce ni, na faɗa masa ya nemi soyayyarta, sannan ya aureta, amman daga ƙarshe ya ƙiya, ya ce dukan mu yama fasa, dan haka ya je tafi nono fari, kuma na faɗa muku gaskiya wallahi bazan taɓa aure ba muddin Aunty Zahra batayi ba..."
"Innallilahi wa inna ilaihir'raji'un!!"
Mahmah ta furta kalmar da ƙarfi, cikin wani irin fushi, ta juyo tana kallon Zahra dake zaune kanta a ƙasa.
"Ko menene ya faru kece sanadi Zahra!"
A hankali ta ɗago kanta, cikin mamakin daya gaza ɓoyuwa har akan fuskarta, ta ce.
"Ni kuma Mahmah?"
"Eh, ke! Ke ɗin nan dai! Saboda ke ba ki yi aure ba, Salmah ta ce ba zata yi ba, ke kin ƙi auren, ita ma kin fara hure mata kunne akan kar tayi, ta ya zata ce ba zatayi aure ba, idan har ke ba kiyi ba, wanene ya ga ranar da ke zaki auren Zahra? Wallahi toh baki isa ba!!" Cikin wata iriyar murya ta ƙarasa maganar, kamar ba tata ba.
Zahra ji ta yi kamar ana watsa mata ruwan zafi, buɗe baki ta yi za ta yi magana, amman ta kasa furta ko wace iriyar kalma, dole ta haɗiye abin da take niyyar furtawa.
Ganin ta yi shiru ne ran Mahmah ya ƙara ɓaci, ta ci gaba da jifanta da maganganu masu zafi.
"Kin ga abin da ya faru yanzu ko? Ga saurayi ya zo, wataƙila ya zo da niyyar aurenta, amman saboda rashin hankalinta da kuma hure mata kunne da kike ta koresa, wanene ya san adadin mazan da ta ke kora akanki, ni nasan ba wannan ne na farko ba, yau ma Allah ne ya tona miki asiri har nasani, abu ɗaya da zan faɗa miki, ko kuma na ce umarnin da zan baki, dole ne ki rabu da Salmah, wallahi sai na rabaku, dan idan ba haka ba, yanda kika shekare a gida itama haka zatayi.."
"Haba Mahmah, dan Allah.." salmah ta katse ta cikin tashin hankali, jin abin da ta ce.
"Ke kuma ki yi min shiru" Mahmah ta daka mata tsawar da bata taɓa mata irin ta ba. "Ai ke ce kika jawo koma menene, da kin yi masa shiru kin karɓesa da zai tafi ne? Ina ruwanki da ita da har zaki ce masa ya aureta, ba ya ganta ba amman ya ce ke ya ke so, nifa daman nayi mamaki da kika ce ta yi saurayi, basai tana da lissafin auren ba, sannan zata fara lissafin ta yi saurayi, yanzu gashinan ku duka kun rasa ai"
Tun da ta fara magana take girgiza kanta, tanajin duk wani abu da Mahmah tayi wa big sister a yau ita ce sila, lefinta ne ƙaiƙaiyin bakinta ne ya janyo mata da surutunta, wanda ita tasani, Allah shine shaidar ta, wallahi batayi da wata manufa ba, tayi ne kawai dan farin cikin ganin wani ya tsayar da Aunty Zahran, cikin kuka ta ce.
"Mahmah wannan duk tunanin ki ne, abu ɗaya nasani zan kuma ƙara maimaita miki, ba zan iya yin aure ba, alhali ga Aunty Zahra ba ta yi ba, na riga na yi alƙawarin ba zan yi ba, sai bayan tayi"
Maganar da Salmah ta yi ne ya sa ta ɗago kanta da sauri ta na kallonta, dan duk wanda ya ji a yanda take maganar yasan daga ƙasan zuciyarta, take furtawa.
"Salmah!"
Ta kira sunanta cikin rawar murya.
Kallonta, ta yi, sannan ta mayar da kallonta kai tsaye kan Mahmah.
"Mahmah ko da kuwa hakan ya na nufin zan jira tsawon shekaru, ba zan gaji ba, ba zan iya barin gidan nan na bar ta ba, da ace tana samun farin ciki a wajenki ne ma, amman bata samu, da ni kaɗai take farin ciki a gidan nan, sai Baffa taya kike tunanin zan iya tafiya na barta daga ke sai ita Mahmah?"
Wata iriyar dariyar takaici Mahmah ta yi.
"Lallai kuwa Salmah, ni ki ke faɗawa haka?" Ta tambayeta tana nuna kanta.
"Shikenan sai ki zauna ku jira juna har Mahadi ya bayyana, idan ɗaya ba tayi ba, ɗayar ma kar tayi, amman mu zuba dani da ku baki ɗaya"
Kasa jurewa Zahra tayi, dan ta daɗe ba taga ɓacin rai a fuskar Mahmah irin wannan ba, Muryar ta na rawa ta ce.
"Mahmah dan Allah ki daina faɗar haka, kinsan fushinki musiba ne a garemu baki ɗaya, ni ban taɓa roƙon Salmah ta hana kanta aure saboda ni ba, ban taɓa ce mata ta jira ni ba, kiyi haƙuri Mahmah Autarki zatayi aure ko da banyi ba, dan ni nasan bani da rabon auren ne gaba ɗaya.."
Juyawa tayi ta kalli Salmah, muryarta na rawa ta ce.
"Autah me ya sa za ki ɗorawa kanki wannan nauyin saboda ni? Me ya sa za ki hana kanki abin da, ko wace mace ta ke buri da fata, saboda halin da nake ciki?"
"Saboda ke ƴar uwata ce Aunty Zahra, kuma farin cikina ba zai taɓa cika ba idan na san ke kina cikin damuwa, zamu zauna tare har zuwa lokacin da Allah zai yanke mana zaman gidan nan, kar ki damu da duk abin da Mahmah zatayi"
Da sauri ta rungume Salmah, hawaye masu zafi suka ƙara zubo mata, ta rasa wane irin ciwo ne ya fi damunta a yanzu, abin da wanda ya zo ya haddasa mata, ko kuma maganganun Mahmah, ko alƙawarin da Autah ta yi, wanda ya sa ta ji kamar ita ce sanadin duk wata damuwa da ƙanwartata za ta iya fuskanta a wajen Mahmah.....
FULANI
***