Free chapter · Read without an account

THIRD TIER

by Maryam · THE THRONE OF THORNS


‎Yana gama faɗar haka ya fara tafiya da baya da baya yana wani killer smile har ya koma inda yake tun farko ya tsaya.
‎
‎
‎In banda kyarma ba abinda jikinta yake bowl ɗin sa rawa yake shima kamar zai faɗo.Ganin ya kuma sai ta ta da bindiga yasa ta rintse idon da ƙarfi,ba abinda take cewa sai la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu min zalimin(duk wata musiba ba inka shiga ka riƙi wannan addu'ar Allah zai yaye maka).
‎
‎
‎Kunamar bindigar ya saki ji ka tasssss,amma ko kallon inda suke ba wanda yayi.
‎
‎A hankali ta fara buɗe idonta saboda har yanzu bata tabbatar da tana raye ba.Idonta ne ya sauka a kan bowl ɗin ɗaya ragar gaje a ƙasan luxury marbles ɗin dake shimfiɗe a gurin .
‎
‎
‎
‎Tuna da tayi cewa da an sami mistake ko da na inch ɗaya ne da tuni yanzu kanta ne ya ragar gaje haka yasa ta kasa a miliyan ko juyowa ba tayi ta kalle su ballantane su hana ta tafiya.
‎
‎Kwashewa da wata dariyar basawa su kayi,inda wanda ya gama tafiyar girgiɗa kai yayi tare da murmushi mai ɗauke da ma'anoni masu yawa.
‎
‎
‎Gudu take har ta fita daga hayyacin ta kafin ta iya samo hanyar fita daga part ɗin da ƙyar.
‎
‎Gwaren su kayi har ya kusan sa Maleeka ɓarar da mocktails ɗin hannun ta.
‎
‎"Ke lafiyar ki..." 
‎
‎
‎Maganar ta katse ganin yanayin da ta ganta,jan hannun ta tayi suka shiga wani lungu mai ɗan duhuwa da rashin mutane.
‎
‎
‎Ganin yacce Ramlah ke shiɗewa numfashin ta na ɗaukewa ne ya ɗaga hankalin ta itama.Girgiza kafaɗun ta ta fara ta na cewa
‎
‎"Ramlah ki buɗe bakin ki ki gayan mai ya faru,wani abu ki ka gani,wani abu akayi miki,wane me ya same ki".
‎
‎Cikin tsawa take ta zuba mata wannan uban tambayoyin ko numfasawa ba tayi saboda rikicewa.
‎
‎Tsoron ta ɗaya Ramlah yace mata wani abu ne ya same ta,dan in wani abu ya samu Ramlah ba zata iya ya fewa kanta ba.
‎
‎
‎
‎Fashewa Ramlah kawai tayi da wani kuka mai taɓa zuciyar mai sauraro,wanda yake ɗauke da tsoro da firgici .
‎
‎Kukan da ta fara ne yasa jikin Atti ya gama ,ta gama saddaƙar wa abinda take tunani ne ya faru.
‎
‎
‎Rungume ta tayi a jikin ta tana buga shafa bayan ta tana cewa 
‎
‎"It's okay, sorry my dear everything will be alright ki dena kuka kanki zai yi ciwo"
‎
‎Sunfi minti 20 kafin Ramlah ta fara dawowa hayyacinta,sai sauke a jiyar zuciya take.
‎
‎Ganin ta dawo dadai ne yasa Attis ta ɗago ta daga jikinta ta na cewa 
‎
‎"Ya isa haka kinji, yanzu gaya min mai ya faru?"
‎
‎Ta faɗa duk da tana tsoron irin amsar da za ta bata.
‎
‎
‎Nan Ramlah ta fara bata labari tiryan-tiryan  na abinda ya faru har tazo ƙarshe tana cewa
‎
‎"Yanxu fah Anty da an samu kuskure kaɗan ne da tuni kaina ya tarwatsa" 
‎
‎
‎Ta ƙarasa faɗa tana sake fashewa da wani kukan.
‎
‎
‎Wani numfashi da tun da taga halin da Ramlah ke ciki ya maƙale ne ya samu hanyar fitowa yanzu,tana godewa Allah jin cewa ba abinda tayi tsammani bane.
‎
‎
‎"Wai bana ce ya isa haka ba ehmmm.Ban san dalilin ki na zuwa gurin nan ba , kuma bazan matsa miki ki gayan ba amma ki sa ka a zuciyar ki cewa KADDARAR MUCE TAZO A HAKA kuma Allah na tare da mu"
‎
‎ta numfasa saboda rashin sabo da magana da yawan magana tana ɗorawa da
‎
‎
‎"Ki ɓoye a nan kar ki fito zanje in cigaba da aikin ,zan zo in kawo miki ruwa da abinci kinji ".
‎
‎
‎Giɗa kai tayi tana cewa,
‎
‎"Tohmm Anty InshaAllah baxan fito ba Nagode sosai ".
‎
‎Ficewa Atti tayi daga gurin tana basarwa dan kar a gane ta.
‎
‎
‎Mocktails ɗin ta ɗauka tana nufar,gurin wasu tsofaffin najadu da suke ta ihu sakamakon chachar da suke yi.Ajjewa tayi ko kallon inda suke ba tayi ba duk da idon daya dawo kanta gaba ɗaya .
‎
‎
‎
‎
‎Dakatawa tayi sakamakon maganar da yaji wasu manya-manyan mutane dasu ke magana tayi inda ɗaya ke cewa
‎
‎"Kai daka bi ko ta hanyar THIRD TIER ne gwara kaje mutanen CRAZY LION su kama ka"
‎
‎Ɗayan ne yayi saurin katse shi da 
‎
‎"Amma dai kai ban taɓa tunanin baka da hankali baka da tunani ba sai yau wai kasan waye CRAZY LION kuwa. Kaf Nigeria kai kar Afrika ba wanda ya isa ya nuna mai yatsa ko shi waye.Ko ka manta cewa last year shi ya shiga har Bila ya kashe Minister of defense da tsakar rana kuma ko tari gwamnati bata yi ba".
‎
‎"Ko kuwa ka manta shi yashiga har barikin sojojin Morocco kuma yasaka wannan babban janar ɗin nasu da duniya ke ji dashi tsallen kwaɗo a idon duniya.
‎
‎Kai kasan in na cigaba da labarin crazy Lion sai mun shekara a nan.Bama wannan ba kasan hatsarin ADEYEMI family kuwa,toh kakan sa FATHER OF LAGOS kuma kasan dai wane shi. Sannan dukka uncle's dinsa sune masu riqe da madafun iko na ƙasar nan har ma da ƙetare."
‎
‎
‎Wancan ne yayi shiru saboda yasan duk abinda abokin nasa ya gaya gaskiya ne ko ma yace bai faɗi komai ba,kafin kuma yace
‎
‎"Amma kasan dai in mutum aka kama a third tier dai mutuwa ce mafi muni bayan azabtarwa da za'ayi mai"
‎
‎Murmushi yayi yana cewa 
‎
‎
‎"TOH bari kaji ah ƙididdgar da a kayi su kansu ADEYEMI family sun tabbatar da ba'a taɓa mara imani da basira irin sa ba a familyn kuma shine HEIR ɗin lenage ɗin.Kai a taƙaice in gayama duk tsantsar arziƙin da duniya ta sheda ADEYEMI family dashi yanzu ya takesu kuma naji ance da kansa ya nemi kayarsa"
‎
‎
‎"Hmmm" ɗayan  yace yana ɗorawa da kaga muyi shiru da maganar wannan hatsabibin mutumin 
‎
‎"Kai a tunanin ka mai akeyi a THIRD TIER haka ne da ba'a bari kowa ya kusanci ma inda take".
‎
‎
‎Atti dake tsaye tun ɗazu bata lura da daɗewar da tayi a gurin ba saboda son jin mai ake a third tier ɗin .
‎
‎Taɓatan da akayi ne yasa tayi firgigit tana juyawa,wata ƴar dattijuwa ce tace ke me kike a gurin nan cigaba da aikin ki.
‎
‎
‎Tafiya ta fara tana ƙara maimaita kalmar MAI AKE A GURIN a cikin zuciyar ta.
‎
‎
‎++++++++++++++++++++
‎
‎Manyan bouncers da body guards ne keta safa da Marwa a hanyar da zata  kaika ginin ƙasa (THIRD TIER) ,ko sauro bai isa ya wuce ta gurin nan batare da sun raba shi da da numfashin shi ba.
‎
‎Laɓe take a jikin bango tana hango yacce aka tsananta tsaro a gurin kamar gidan gwamnati.Hannun ta riƙe da matcha latte da beetroot juice.
‎
‎"Huh ta ina zan fara shiga gurin nan Allah ka taimake shirina ya yiwu" 
‎
‎tana rufe bakinta Jiniyar gobara ta fara ƙara wiiiiiiiiiii,cikin sakanni sai ga wani yazo ya raɗawa shugaban su magana a kunne cewa gobarar ce ta tashi a second tier. 
‎
‎Nan da nan ya bada order duka su tafi a bada taimakon gaggawa ,inda yabar mutum 3 su kula da gurin kafin su dawo.
‎
‎
‎
‎"Yesssss "
‎
‎Maleeka ta faɗa tana cewa plan A is done saura plan B .Sake mannewa tayi a jikin bangon saboda wucewa da suka zo yi ta gurin.
‎
‎Suna shigewa da minti 5 ta ƙara gyara rigar ta da sakin gashin ta mai sheƙi da adon maroon a jiki ta ƙara riƙe ƙaramin tray ɗin hannun ta.
‎
‎Wata tafiya ta fara ta na juya hips ɗin ta deliberately,su kuwa suna gano ta mayu suka  fa ra binta da ido kamar su cinye ta  har ta ƙaraso inda suke.
‎
‎Cikin Wata murya mai bala'in jan hankali da ta da tsigar jiki tace
‎
‎"Yallaɓai sannun ku da ƙoƙari"
‎
‎Har haɗa baki suke wajen faɗar
‎
‎
‎"Sannuki ƴan mata"
‎
‎
‎Wanin murmushin mugunta tayi a zuciyar tana cewa ƴan kwal uba mayun mata har sun faɗa tarko zaku yi bayani ne.
‎
‎Basarwa tayi tana murmushi tace 
‎
‎"Ai kune da sannu wannan ƙoƙari haka da yawa,ga wannan ku jiƙa maƙoshi"
‎
‎Taƙarasa faɗa tana miƙa musu mocktail ɗin ta na zuba musu grey eyes ɗin da suke ta ƙyali da ɗaukar ido.
‎
‎Zo kaga yacce rige-rigen karɓa,tuni su kafa kai suka fara sha.Haɗa ido suka yi da wani a cikin su sai kallon ta yake, ɗaga mai gira tayi tana kashe mai ido,shi kuwa nan da ya washe jajayen haƙoransa.
‎
‎
‎Tafiya ta fara yi ta tana komawa inda ta fito ta ƙara laɓewa.
‎
‎Ko minti goma ba'ayi bacci mai nauyi ya kwashe su.
‎
‎
‎Salallabowa tayi tazo ta fara jansu ɗaya bayan ɗaya tana jansu ta kaisu lungun da ta  fito.(Jama'a ko dai Maleeka ta taɓa aikin kaki ne ,wannan ƙarfi har ina jan samudawan ai ko namiji albarka)
‎
‎
‎Tray ɗin ta ɗauka  tana ɗora empty cups ɗin akai ta fara hawa ta nufi ciki.
‎
‎
‎Bene ne a gurin mai makon ya kaika sama wannan ƙasa zai kaika.Tana taka benan ya kawo wuta ashe transparent ne sai wani abu kamar vulcano da dutsen wuta ke haske a cikinsa .
‎
‎
‎Bayan ta sauka ciki,nan ma wata duniya ce mai zaman kanta da kanta daula iya daula .Wata ƙatuwar ƙofa ce ta zallar zinare sai walƙiya take tana ɗaukar ido.
‎
‎
‎Ganin ƙofar tayi a saye ba a rufe ba,duk da tayi mamakin haka amma haka tayi ƙarfin hali ta shiga zuruf.
‎
‎
‎"Wannan shi ake kira da DARK EMPIRE "
‎
‎
‎Maleeka ta faɗa a hankali,tana bin gurin da kallo,kama daga da furnitures,marbles,wall everything na gurin charcoal color inda duk wani haske dake gurin yake fitar da wani heavy dangerous burgundy lights,ga candles da chandeliers ta ko ina amma duk da haka gurin duhu yafi yawa aka haske.
‎
‎
‎Magana ta fara ji sama-sama daga wata ƙofa,nufar gurin tayi ganin ƙofar a kulle yasa ta nufi wani window da ke ta ɗan bayan ɗakin.
‎
‎Buɗewa tayi a hankali....wani irin bugawa zuciyar ta fara da sauri da sauri.
‎
‎
‎Mutane ne su su goma sha juna zaune a kujeru suna kallon juna,inda guda ɗaya yake a gaban su kujerar sa a tsakiya.
‎
‎
‎Gaba ɗaya fuskar su rufe da mask na namun daji wani tiger wani wolf wani cheetah gasunan dai kowa da irin nashi inda shi ta babban na sune wanda ke zaune a tsakiya ba'a gano nashi mask ɗin.
‎
‎
‎Magana suke da ɗan ƙarfi wanda ke nuna wata ƴar hatsaniya ke shugaban nasu yayi relax a jikin kujera kamar bai san me ake ba.
‎
‎
‎Buga hannun sa shugaban nasu yayi da karfi a jikin tebur ɗin da ƙarfi,yasa suka fara shiga taitayun su.
‎
‎Sai da suka zauna tukunna ta gano ashe bindiga ya ajje a gurin.
‎
‎Kamar daga sama taki wannan Muryar wacce bazata taɓa mantawa a rayuwar ba, wannan muryar da ta zama tamanin rugujewar rayuwar ta yace
‎
‎
‎"KILL HIM"
‎
‎Ɗaga idon da zatayi taga wane mamallakin muryar su kayi ido huɗu dashi .............end of chapter 17 ..... Written by Muraimaa Naabba.....    
‎
‎
‎
‎
‎
‎
‎
‎
‎
‎
‎
‎

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.