Free chapter · Read without an account
Chapter 2: Heartless
Heartless
Saboda rashin isasshen bacci, da ƙyar ta iya tashi ta yi sallar asuba, ta wuce kitchen, tana tunanin yi masa breakfast, Idan ta yi masa ya ƙi ci, idan kuma ba ta yi ba, sai zata fita zuwa school ya ce ta koma ta masa
Kawai sai ta yanke shawarar yi musu oat da ƙosai, tunda ita tana iya ci, ko da bai ci ba za ta wuni tana cin abinta. Ta yi sauri ta wanke wake ta yi blending, sannan ta yi making yummy ƙosai with oat. Sai da ta ci sosai kafin ta wuce sama ta yi wanka
Tana sakkowa ta ganshi yana shigowa da bottle water a hannunsa, alamun daga jogging ya dawo. Sai da ta ƙarasa inda yake ta gaishe shi, amma bai amsa ba, ta kuma cewa, “Your breakfast is ready”
Kallonta ya tsaya yana yi, sannan ya ce, “And who asked you to make it?”
Ta yi shiru tana wasa da yatsunta, sai ya ce, “Na lura kwana biyu kin tsoma shishige min, do you really expect me to accept you or what? I would never, so stay within your limits” Ya ƙarasa maganar da tsawa, ya jefar da gorar ruwan sannan ya haura sama
Ganin haka ya sa ta koma dining area ta kwashe kayan ta kai mota, saboda maybe yau za ta kai yamma, tun kafin ta fita da motar, ta fara kiran Mufydarh, amma ba ta ɗauka ba har ta isa titin da take ɗaukar ta domin su wuce school tare
Tana zuwa ta gan ta, ta sauke gilashin motar sannan ta ce “Yau kuma sai na ce ki shigo kafin ki shigo ne?”
Mufydarh ta ja tsaki ta buɗe back door ta shiga. Amrah ta fara dariya tana ba ta haƙuri, domin ta san ranta ya ɓaci. Ganin kulolin ya sa Mufydarh buɗewa , ganin abun ciki ta ja tsaki
“Wani abu sai masu ciki wallahi, but let me taste the akara”
Amrah ta ce, “Kina cinye min abinci, Allah zaki sake min wani kuma exactly taste ɗin nake so”
Sai yanzu Mufydarh ta yi dariya, a haka suka ƙarasa school
Suna cikin lectures kawai sai maganar Mami na jiya ta faɗo mata a rai. Salati ta yi a hankali. Ita gaba ɗaya ta manta cewa yau za ta bi Mami asibiti. Da lecturer ya fita, ta tattara kayanta ta miƙe
Zainab ta ce, “Lafiya Amrah? Ina za ki? Kin san dai muna da wasu lectures ɗin”
Ta ce, “I’m going to see my project supervisor”
Ba ta ƙara ko second ɗaya ba ta fita, direct block ɗinsu ta nufa, Mufydarh ta kira a waya ta ce ta zo ta same ta. Su ma Mufydarh ba lectures suke yi ba, hakan ya sa ta ƙaraso
Ta ce, “kar dai haihuwa za ki yi?”
Amrah ta ce, “Dalla, ba ki da zance sai wannan, ni yanzu wajen supervisor dina zan je. Ina gama ganinsa zan wuce gida”
Mufydarh ta ce, “Amma lafiya?”
Ta ce, “Shap na manta cewa yau zan bi Mami asibiti, za ta sake yi min wasu gwaje-gwaje ne”
Ta c, “Oh, Allah sarki. Allah ya sa a ga abin da ya fi alkahiri”
A haka suka rabu
Direct wajen supervisor ɗinta ta fara zuwa, ta tsaya ta yi masa bayanin cewa za ta je asibiti, da yake yana da tausayi, lecturer ɗin ya ce “It’s okay, Hauwa, take your time”
Ta yi masa godiya sannan ta fita, direct ƙofar gidan Mami ta nufa. Ta yi parking, domin ba ta son ta shiga gidanta balle wani abu ya shiga tsakaninta da Sultan har jinin jikinta ya hau, ya hana sakamakon gwaje-gwajenta fitowa da kyau
Ta ja numfashi sannan ta ɗauki kula ƙosai ta ci kaɗan kafin ta fita ta shiga gidan. Ayrah ta zo da gudu ta rungume ta “Good morning, Aunty Amrah”
Amrah ta ce “Ba ki je school yau ba ko?”
Ta ce, “It’s Children’s Day, sai Grandma ta zo za ta kai ni park”
Amrah ta ce “Oh, ta fita ne?”
Ta ce “Sure, about an hour ago”
Tana shirin fita ta ga masu aikin Mami. Suka gaisa sannan ta fita daga gidan
Tana shiga mota sai ta ji kamar ta shiga gidanta, domin yanzu kusan sati ɗaya kenan bata yi updating wasiyar da take rubutawa ba kusan kullum, ta yi tunanin maybe Sultan yana nan, shi ya sa ta fasa komawa gidan ta wuce private hospital ɗin Mami
Tana zuwa ta kira ta a waya. Mami ta ce ta shiga ciki, domin tana nan. Da ta isa sai ta fara ba Mami haƙuri
Mami ta ce, “Ba komai. Ai da na fito mai gadinki ya ce kin wuce, sai na ce maybe akwai wani serious abu ne da ya hana ki zuwa, tunda ke final-year student ce”
Ta ce, “A’a, yanzu mun gama covering lectures ɗin, exams ma za mu fara”
Mami ta ce, “Tashi mu je mu fara, domin yau da kaina zan duba ki”
Tare suka fita, Mami na gaba ita kuma tana biye da ita a baya
Duk wani abu da Mami ta san ya kamata ayi mata, sai da tayi, sun kwashe some hours kafin a gama. Wasu daga cikin results ɗin da Mami ta gani sun sa ranta ya ɓaci matuƙa
Tana fitowa sai ta ce wa Amrah ta biyo ta, suna shiga office ɗin, Mami ta ce, “Amrah, in the next 15 days, we’ll perform your C, by then, you’ll be nine months pregnant, right?”
A hankali ta ce, “Eh Mami”
Mami ta ce, “Amrah!”
Hakan ya sa gabanta ya faɗi, ta kasa amsawa, sai kallon Mami da take yi
Mami ta fara faɗa, “Amrah, ba ki jin magana ko? Ba za ki ma kanki faɗa ba? Idan wani abu yana damunki, ba za ki je ki faɗa wa iyayenki ba? Idan kina ganin ba za ki iya ba, to ba gani ba. Kullum results ɗinki ba su da kyau. Ke yarinya ƙarama ce, amma kina fama da ciwon zuciya da hawan jini Idan kuwa saboda rashin jituwa tsakaninki da mijinki ne, idan ba ki yi wasa da waɗannan abubuwan ba, kina iya samun matsala wajen haihuwa. I’m sorry to say this, but you may be the one who will suffer during childbirth”
Ganin yadda jikin Amrah ya yi sanyi, idanunta kuma suka yi ja, ya sa Mami sassautawa. Sai ta jawo ta jikinta, cikin yanayi na tausayi ta ce, “Amrah, kina so ki rasa ɗanki ne?”
Ta girgiza kai
“To, ki daina saka damuwa a ranki, ko don lafiyarki kin ji?”
Hawayen da take riƙewa suka fara zuba, cikin muryar da take ƙoƙarin danne damuwarta, ta ce, “Mami, na san dole wata rana zan mutu, amma ina jin a jikina cewa na kusa”
Mami ta ce, “Ki daina faɗin haka, kin ji? You’re still young”
Ta ce, “Mami, parents dina suna fushi da ni, amma idan na riga su mutuwa, na san za su yafe min, tunda saboda Sultan suke fushi da ni”
Mami ta yi shiru. Ita tun ranar farko da ta fara ganin mijinta, ta san bai dace da Amrah ba, to ko dai shi ne ya had’ata da iyayenta?…
Ta shiga da motar cikin gida, tun kafin ta yi parking ta lura babu motar Sultan a ciki, ta sauke ajiyar zuciya cikin relief, tana addu’ar Allah ya sa tafiyarsa ta wannan karon ta zama irin wadda ya saba yi, domin aƙalla zai yi kusan months biyu kafin ya dawo
Ita kuma hakan zai fi mata, saboda babu wanda zai riƙa saka mata baƙin ciki har ta samu matsala wajen haihuwa
Ta kalli time, ta ga har lokacin sallar la’asar ya kusa, ta sauka ta wuce ciki, direct ta yi wanka, ta canza kaya masu sauƙi, ta yi sallah sannan ta sauka ƙasa
Tana ƙoƙarin shiga kitchen sai ta ji muryar Mufydarh, wani irin daɗi ta ji har cikin ranta. Ta ƙarasa ta buɗe mata ƙofa
Suka rungumi juna. Mufydarh ta ce, “So, bestie how were the results?”
Ta yi shiru na ɗan lokaci sannan ta ce, “Sister I’ll just tell you the truth, I don’t want you to panic”
Ta ce, “Okay, ina sauraronki”
Ta kama hannunta ta ja ta zuwa parlour suka zauna, sannan ta ce, “Bestie, the results are as usual, this time, they’re even worse than the previous ones, gashi kuma an ce zan shiga wata tara, za a yi min CS in the next 15 days”
Mufydarh ta yi shiru na wasu seconds kafin ta ce, “Wallahi Amrah, ba ki jin magana ta, dole ne sai kin yi biyayya ne? ki koma gidan Anty Badiyya mana Idan su Abbah ba za su karɓe ki ba, wallahi wannan shiru-shirunki shi zai kashe ki”
Ta ja numfashi sannan ta ce, “Ni kam, na fi so na mutu, Maybe su Ammi za su ga haƙurina”
Mufydarh ta ja tsaki “Wallahi, ki yi finding a way out. Ko na kai ƙara Human Rights, ko kuma na karɓo miki takardar saki da kaina a kotu”
Amrah ta ce, “Kin ga, wannan shi ne dalilin da ya sa ba na son faɗa miki gaskiya”
Tare suka shiga kitchen suka yi dinner, da ma bakinsu su biyu ne, sai abincin da za su zuba wa gateman
Suna cikin hira, Mufydarh ta ce, “Wallahi, halin da kike ciki yana damuna, anya ba zan je gidan su Sultan ba?”
Amrah ta ce, “So kike ki ƙara jefa ni cikin wata matsala? Kin san son ɗansu ne ya sa ba sa ganin laifinsa”
Ta ce, “Hakan ne ya sa zan je, saboda na tabbatar musu da abin da yake faruwa”
Ba ta ma gama rufe baki ba suka ji alamun an buɗe ƙofa, tare suka ɗaga kansu sama
Sultan ne tare da wata mace suke sakkowa
Mufydarh ta ce, “Chapdijam!”
Duk lokacin da Amrah ta gan shi tare da matansa, sai ta tsinci kanta cikin baƙin ciki, ta rasa dalilin hakan
Sai da suka ƙaraso parlour ɗin sannan Sultan ya fahimci akwai mutane, kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kansa, amma ganin irin kallon da Mufydarh take masa ya sa ya sake juyowa ya kalleta
Amrah kuma da ta ga haka ta ce, “Ina wuni, Ya Sultan”
Bai amsa ba, kamar yadda ta zata, ya tsaya yana kallon Mufydarh da take harararsa, Amrah ta taɓa ta “Ba ki gaida shi ba?”
Mufydarh ta ja tsaki “Allah ya tsawake da nayi asarar ranar da aka haife ni”
Ya nuna ta da yatsa “Ni kike yi wa wannan kallon?”
Ta murɗa baki ta fara magana a ƙasan murya “Da ka ɗauka kowa ne yake tsoronka”
Ya daka mata tsawa “Tashi ki wuce gidan ubanki. Kada na sake ganin kafarki a cikin gidan nan, domin idan kika kuskura muka sake haɗuwa, zan iya karya ki”
Ta ce “Thank God you know who my father is. And you think I’ll be scared of you the way Amrah is?”
Ya fara nufarta, hakan ya sa Amrah ta fara ba shi haƙuri
Mufydarh tayi gudu zuwa kofa ta tsaya ta ce, “Wallahi, ba ka isa ka hana ni shigowa gidan nan ba, tunda ka ajiye ’yar uwata a cikinta,mugun mutum mai baƙin hali kawai” Ta fita da gudu
Sultan ya tsaya a wurin, zuciyarsa tana tafarfasa, bai taɓa ganin yarinyar da za ta iya yi masa rashin kunya haka ba
Ya juya ya wanke Amrah da mari. Jikinta ya d’au vibration sbd yadda Marin ya shige ta, bai tsaya nan ba, ya sake kai mata wani marin sannan ya kama wuyanta ya manne ta da cushion ɗin da take zaune a kai
“Idan na sake ganin wannan kanwar taki, sai na kashe ta. Ki gaya mata! Tun yaushe na ba ki saƙo, amma kin gagara isar da shi, ki koma ki gaya musu su zo su warware abin da suka haɗa kafin na illata ki, jaka wawiya”
Matar da yake tare da ita, ganin halin da Amrah take ciki, sai ta zo da sauri ta cire hannunsa
“Haba, it’s okay mana at least, ka tausaya mata”
Ya nuna cikin jikin Amrah ya ce “So, this is your plan? Kina tunanin idan kin haihu, everything will change? You don’t have the guts to do anything, saboda ba ki kai matsayin da zan zauna da ke ba” Ya juya ya fita, matar ma ta bi shi
Suna zuwa motarsa, wadda ta fi kowace mota tsada a wurin, suka shiga ba tare da sun lura da tayoyin ba, ya kunna motar ya yi baya, sai ya ji kamar ya taka wani abu, amma bai san me ba, abin ya yi kamar ya fashe
Ya ci gaba da tafiya, amma da ya ƙara gaba ya sake taka wani abu, sai a lokacin ne ya fara tunanin abin da ya taka
Ya tsaya ya sauka ya duba, sai ya ga tayoyin motarsa huɗu sun fashe
Ya yi murmushi. Matar da ta kalle shi ta ce, “Lafiya?”
Ya ce, “Ga key ɗin ɗayan motar, mu shiga”
Ita kuwa a ranta Amrah ta ba ta tausayi, ta san Mufydarh ce kaɗai za ta iya aikata irin wannan abu, ya yi alƙawarin idan ya kama ta, sai ya tsorata ta yadda za ta san shi ba sa’anta ba ne
Suna fita, Mufydarh ta fito daga inda ta ɓuya ta shiga gidan. Ganin yadda ta tarar da Amrah ya sa ta ji wani iri , da gudu ta nufi inda take ta rungume ta
“I’m sorry Amrah, ni na jawo miki wannan matsalar, ki yi haƙuri please”
Ta ce, “Ba komai ki daina damuwa”
Mufydarh ta ce, “Me ya yi miki? Ya buge ki?”
Ta gyada mata kai kawai
Mufydarh ta ce, “Wallahi, yau kam ko su Abbah zasu kore ni, sai na gaya musu abin da Sultan ya yi”
Amrah ta ce, “Mufydarh please, ki tashi ki tafi kafin ya dawo, kin san halinsa”
Mufydarh ta tafi, amma duk jikinta yayi sanyi, ta yi alƙawarin sai ta fitar da Amrah daga wannan halin