Free chapter · Read without an account

Chapter 3: A breath of relief

by Hauwa Jibrin Sulaiman · AMRAH (Force Marriage)



Washe gari ta tashi da zazzabi. Maganganun Mami na kullum suna yawo mata a kai, sai ta ji haushin kanta da jiya ta kasa bacci tana ta tunani. Gaskiya ne, idan ta samu matsala, ita ce abin tausayi. Ta kawar da tunanin nan ta tashi ta yi sallah

Yau ba ta jin za ta iya cin komai, saboda haka kawai ta sha tea, domin da ƙyar ace ta wuni ba tare da ta sha tea ba, ta yi wanka ta shirya cikin gown ɗinta, ta jawo diary ɗinta ta yi updating ɗin wasiyarta, domin kusan kullum haka take yi. Ta rufe diary ɗin ta ajiye, ta ɗauki school bag ɗinta ta fita zuwa school

Yau Mufydarh ba ta da wani abu serious a school, shi ya sa ba ta zo ba sai wajen ƙarfe 12. Direct block ɗinsu Amrah ta nufa, tana zuwa ba ta gan ta ba, sai ta tambayi wata course mate ɗinta, Hafsa, wadda ta ce, “Kamar project supervisor ɗinsu ne ya nemi su”

Ta samu wuri ta zauna tana jiranta. Sai can daga baya suka dawo. Amrah ta ce, “Sorry, maybe kin daɗe kina jirana ko?”

Ta ce, “Don’t mind, kin ji? An sake exam timetable, kuma an saka ranar defense”

Allah ya taimaki Amrah, za ta gama exams ɗinta har da defense kafin lokacin CS ɗin ya yi. Hakan ya sa ta ji daɗi matuƙa

Sai da suka kama hanya a mota sannan Amrah ta ce, “Guess what?”

Mufydarh ta ce, “Guessing? Kin san dai I’m not good at that, kawai ki faɗa”

Ta ce, “Yau tare za mu tafi gida, sai da dare kafin in koma gidan da nake”

Mufydarh ta ce, “Wow! That’s so good, wallahi har na ji daɗi, dama Farhan ya yi missing ɗinki”

Tare suka tafi gidansu, tun daga bakin gate, da maigadi ya gan ta, ya wage baki ya fara mata kirari. Dariya kawai ta yi suka shige

Housemaids ɗinsu duk sun ji daɗin ganin Amrah, domin sun yi missing ɗinta. She was so kind to them, duk suna sonta, saboda lokacin da take gida ba ta ɗauke su a matsayin ma’aikata kawai ba, tana ba kowa respect ɗinsa

Suna shiga main parlour suka yi sallama. Farhan da ya ji muryarta ya fito da gudu ya zo ya rungume ta

“Oyoyo, Adda! What a surprise!”

Dariya kawai ta yi ta ce, “Toh kai ma ba ka sa Abbah ya ce wa driver ya kai ka ba”

Ya ce, “Toh Adda, ki dawo gidan nan mu ci gaba da zama kawai, dukkanmu uku kamar da”

“Toh kai wa ya gaya maka idan mutum ya yi aure yana dawowa gidan su?”Muryar Mummy suka ji tana ba Farhan amsa, duk suka juya suna kallonta tana tahowa cikin parlour

Amrah ta ji kuka ya taho mata, da sauri ta tashi ta ƙarasa inda Mummy take ta rungume ta, kawai sai ta fashe da kuka. Mummy ta fara bubbuga bayan Amrah, ita ma hawaye suka nemi zubo mata, shi ya sa ta kasa magana

Ta janye Amrah daga jikinta ta riƙe hannunta suka ƙaraso cikin parlour. Allah ya san tana matuƙar son Amrah, domin ita kaɗai ce ’yarta mace, kuma Amrah ce happiness ɗinta

Suna cikin gaisawa da Mummy, Abbah ɗinsu ya shigo. Amrah ta tashi daga jikin Mummy ta gaida Abbahn nata, ya amsa mata sannan ya ce, “Ya karatun naki? Hope ba matsala?”

Ta ce, “Eh babu, exams ma za mu fara”

Ya yi musu addu’a da fatan nasara kafin ya shige ciki domin ya yi freshen up

Mufydarh ta kalli Amrah ta yi mata alama da ido, sannan ta ce, “Bari in shiga kitchen in yi miki abinci, kin san na gida daban ne”

Amrah ta harare ta ta ce, “Sai kuma a ce idan ke kika dafa?”

Suna zaune sai ga masu aikin gidan sun kawo mata abinci, ta yi musu dariya tana gode musu. Mummy ta kira waya ta yi mata order ɗin dambun nama. Har cikin ranta Amrah ta ji daɗi, at least Mummy ba ta yi fushi da ita ba kenan

Amrah ta yi mamaki ganin yadda ta ci abinci sosai. Mummy ma da Mufydarh sun yi mamakin cin nata, domin sun san ba ta da yawan cin abinci

Sai can yamma ta fara shirin tafiya. Ta faɗa wa Mummy cewa an kusa yi mata CS. Mummy ta yi mata addu’a sosai, ta je ta yi wa Abbah sallama

Abbah ya ce, “Yawwa, kin ga, idan har za ki kwantar da hankalinki, ki bi zaɓinmu kuma ki yi mana biyayya, to ba za ki samu matsala ba”

Kanta a ƙasa ta kasa magana, sai dai ta gyada kai kawai. Ya yi mata addu’a sannan ya ba ta kuɗi masu yawa. Ta karɓa ta yi godiya. A gaskiya tana buƙatar kuɗin a yanzu, amma ta rasa wanda za ta tambaya, domin ta san ko da za ta mutu, Sultan ba zai ba ta kuɗi ba

Tana isa gida, wasu guraren sun riga sun idar da sallar Magrib. Tun kafin ta shiga, ta ga alamun akwai mutane a parlour. Gabanta ya fara faɗuwa, amma ta daure ta shiga

Sultan ne tare da wannan budurwar tasa, sai kuma wani abokinsa. Da alama suna tattauna wani serious issue. Ta gaishe su, amma abokin ne kaɗai ya amsa. Ta wuce dining area domin ta ajiye abincin da ta zo da shi, sai ta ji abokin nasa yana cewa, “So, Sultan, you might miss your flight. By now, you should be at the airport”

Wani irin daɗi ta ji har cikin ranta. Ta wuce sama tana addu’ar Allah ya sa idan ya tafi ya daɗe kamar yadda ya saba, domin ta yi exams ɗinta in peace, ta haihu in peace

A hankali ta ce, “Alhamdulillah”

Ta wuce bathroom ta yi alwala, sannan ta fara sallah. Tana idarwa sai ta ji ƙarar buɗe gate. Ta tashi da sauri ta buɗe labulen window, ashe Sultan ne da trolley. Aka saka kayansa a mota suka fita

Har cikin ranta ta ji wani irin daɗi da relief

Ta fito kitchen da tea a hannunta, sai ga kiran Mufydarh, ta ɗauka, Mufydarh ta fara faɗa

“Meyasa kika yi shiru? Ni fa duk tunanina kin zo ki faɗa musu gaskiya, amma sai kika yi shiru, kina cutar da kanki”

A hankali ta ce, “Mufydarh, ki riƙa bin abu a hankali. Yanzu da na faɗa musu abin da ya kawo ni ai zasu kore ni, amma yanzu fa duk suna farin ciki da ni. So, gradually zan faɗa musu, kada ki damu, kin ji?”

Ta ce, “Allah ya sa ki faɗa, ba wai ki yi shiru kamar wawiya ba”

Amrah ta yi dariya kawai, domin ta san Mufydarh ta ji haushi ne, ta yi hakan ne don ita ma ta ji haushi

Sai ta ce, “Toh yanzu yaushe za ki zo mu fara karatun exams? Though mun yi karatu before, yanzu zai zama like revision for us”

Mufydarh ta ce, “Kin san ba shiri da Sultan muke ba. Kar in dawo gidanki, wata rana a fitar da gawa ɗaya ko biyu”

Amrah ta ce, “Kai, Mufydarh! Wannan tunanin shaiɗan ne fa, ba ya gari yanzu, kawai ki zo, please”

Ta ce, “Better, but I’m going to think about it”

A haka suka yi sallama

Yau kawai ta ji kanta cikin wani irin shauƙi, kamar an sauke mata wani babban nauyi haka take ji, shi ya sa ta kwanta da wuri, tana feeling something different from her usual days

Ko saboda tafiyar Sultan ne, ko kuma yadda aka karɓe ta a gidansu, ba ta sani ba. Ta kwanta with so much relief, ta yi wani irin bacci mai daɗi wanda rabon da ta yi makamancinsa ya daɗe

Sai da ta kusa makara kafin ta farka. Ta yi sallah sannan ta koma bacci

Tana tashi, direct kitchen ta wuce. Tana cikin sarrafa abubuwan breakfast sai ta ji muryar Mufydarh tana sallama

Ta fito tana mamakin ko da gaske Mufydarh ce ta yarda ta zo. Suka rungumi juna

Amrah ta ce, “So, yanzu sai ki shiga kitchen ki ƙarasa suyar da nake yi”

Mufydarh ta ce, “Saboda abu ɗaya ne, wallahi zai sa na miki aiki, gwara ki sani”

Dariya ta yi ta ce, “Ai ba damuwa, hakan ma na gode”

Tare suka gama aikin gidan gaba ɗaya, sannan suka yi scheduling yadda za su riƙa karatunsu. Hakan bai ƙaramin daɗi ya yi wa Amrah ba, domin za ta yi karatu without any stress


baku following dina balle like ko comment? taya zan san kuna son littafin pls??

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.