Free chapter · Read without an account
A Calculated Quiet
by NorthernAngel · His Rose
Yau watan Baby Jasmine biyu a gida, wanda hakan ke nufin watanta uku da haihuwa—ma'ana chronological age ɗinta watanni uku ne, amma ainihin adjusted age ɗinta yana kan watanni biyu cif. Ba za ka taɓa kallonta ka ce preemie bace ba; sai dai ka ce tabarakallah, domin ta cika gwanin burgewa. Tuni kowa ya watse aka bar masu gidan. Aunt Oma ce ta fara komawa saboda aikinta, Aunty Hannah kuma two weeks after an yi suna ta koma. Yayin da Mommy ta koma bayan Jasmine ta yi wata ɗaya gida, Umma Deeza ma bayan tafiyar Mommy da sati ɗaya ta koma Abuja. Anne ce dai sai kwanaki shida da suka wuce ta koma saboda ita ce a cikin su babu aure kuma babu ɗan dake gabanta. Tun bayan tafiyar Anne, everything na Jasmine ya dawo hannun Zara gaba ɗaya. Domin zuwa lokacin, daga ita sai Doula team ɗinta da kuma house maids ɗinta a cikin gidan, sai kuma Sam—wanda ya gaba ɗaya ya kwaso kayansa ya dawo gidan da zama. Dalilinsa na dawo wa kuwa shi ne, a gidan Brother Obi surveillance ɗin ya yi yawa, kuma ya sa masa curfew ɗin dole. Sannan yasan duk ranakun da yake da lectures ba ya barin ya yi skipping school; gaba ɗaya dai Brother Obi ya takura masa sosai. Shi ya sa tun da ya yi kwana biyu a gidan Zara ya ga ba ruwanta da rayuwarsa, kuma ko ƙarfe nawa zai shigo estate ɗin ana buɗe masa gate ba mai questioning ɗinsa har gidan Zara ma haka zai shige ba mai tsayar dashi komai dare—ko Zafar ne ya gansa bai ce da shi komai, sai ma dai yamai sannu da zuwa. Gaba daya dai he’s been treated like an adult there, shiyasa yake jin dadin zama dasu. Ga shi kuma, motocin da yake so su yake hawa ba tare an hana shi ba, kullum yana cikin yawo da supercars din Zafar. Ranar kawai sai ya nufi gidan Brother Obi ya kwaso kayansa tass lokacin da shi Brother Obi ɗin ba ya nan, ya dawo gidan Zara ya ce mata shi ya dawo gidan da zama, har da sa ta kira Daddy ya shaida masa ya gaya wa Brother Obi ba zai koma gidansa ba. Tun daga lokacin suka yi zamansu peacefully a gidan. Amma fa, a cikin estate ba a rasa the usual gossip and drama ba. Tun da Aunty, maman Salma, ta kai wa su Ummi da Hajiya Mama gulma cewa ta lura da wani yaro mai shige da fice a cikin motocin Zafar—kamar ma a gidan Zafar ɗin yake zaune gaba ɗaya, kuma kamar ɗan uwan Zara ne saboda suna kama, ga shi kuma da idonta ta ga cross pendant a wuyansa randa yake tafiya da kafarsa a titin estate din. Nan suka hau bincike da tambayar securities, kuma tunda suka tabbatar hakan ne, shikenan Samuel ya tsone musu ido. Har gurin Baffa Hajiya Mama ta kai maganar cewa an kawo musu ƙaton arne cikin estate ga yaransu ƴan mata, kuma hakan bai kamata ba. Amma ko ta kan ta Baffa bai bi ba balle ya bata amsa; shi sai ranar ma yasan Sam na nan, kuma bai ga komai a cikin hakan ba tunda a gidan yayarsa yake zaune ba a gidan wani ba. Ummi kuwa ita ta je gurin Yemma ta kai gulma cikin dabara da hira, amma tana farawa Yemma ta katse ta akan cewa ba ta son zancen Amadis sam, domin bai shafeta ba. Kuma a tunanin Yemma, Sam ya dawo gidan ne don ya zamana akwai reliable support kusa da Zara a ranar girkin Rahama—domin duk a tunanin Yemma, Zafar ya raba musu kwana. Hakan ya sa zama ko rashin zaman Sam a gidan bai dameta ba ko kaɗan. Neonatal nurse ɗin ma tuni ta koma bayan an tabbatar the baby is medically stable. Don haka a gidan su kaɗai ne, sai Zwar wanda shima most of his days yana nan tare da su. ɓangaren zamantakewar Zara da Zafar kuwa, yana nan komai smooth. Yanzu da Zara ta warke tass kuma aka ɗora ta a kan contraceptive plan, tuni duniyar ta dawo masa back to normal. Yanzu sai ya bushi iska yake zuwa gidan Rahama—shima kuma da rana ne, ko kuma ya sa ta zo office ta same shi. Shi ma ganin dama ne kawai da kuma kashe mata baki karta kaiwa Yemma complaint. Sai dai abin da bai sani ba, duk wani move nasa Zara na sane da shi. Tun daga ranar da Zwar ya gaya mata ya gansa, ta fara tsantsar monitoring ɗinsa. Kullum tana cikin binciken phone ɗinsa, ta kuma san yana gama chat da Rahama yake gogewa. Har ma ya yi adding ɗinta a Snapchat kuma suna yin streak, sai dai yana gani yake goge ta gaba ɗaya. Duk wani caution da yake yi, Zara na sane da shi; domin wata rana kafin ya buɗe streaks ɗin Rahama ta gani, sai dai ba ta buɗewa ba don kar ya gane ta gano shi. Tuni ta riga ta sa a ranta cewa za ta gama da Rahama, amma ta gano cewa in ba wani babban scene ta haɗa ba wanda har authorities ko manya za su shiga ciki, hakan ba zai yiwu ba. To ta ji ƙishin-ƙishin ɗin tafiyar Baffa Umra a bakin Yusrah, don haka za ta jira sai ya tafi—domin shi kaɗai ne wanda take jin nauyin sa a kaf mutanen estate ɗinnan. Sai kuma Omar da take ɗan shakka, amma wannan ba wata damuwa ba ce, domin za ta tabbatar ya tafi aiki tukunna ta nuna nata kalar rashin arzikin. Da wannan kyakkyawan shirin Zara take kwana tana tashi a ranta, kuma kullum ƙara fito da sabbin dabarun abin da za ta aikata take yi a zuciyarta. Shi dai Zafar duk wadannan abubuwan bai san tana yi ba; ya ɗauka komai smooth yake tafiya, ba ta san komai ba. Musamman yadda bedroom life ɗinsu ke wani irin gingering su biyun—kullum suna cikin spicing things up, kai kace wasu sabbin lovers irin ana marmarin juna ɗinnan sosai, the chemistry is absolute. Don haka gani yake ba ta san komai ba, shi ya sa take kula da shi fiye da tunani. Yana kuma sane da banbancinta da Rahama; kawai dai shi kansa addu'a yake Allah ya shirye shi, ya kuma nuna masa lokacin da hankalin Yemma zai bar kan auren yadda zai saki Rahama salin-alin, ya yi rayuwarsa shi da matarsa—because she’s more than enough. Kawai dai idan yana kallon Rahama ne, sai ya ga ya gwara ya ci banza kar ya bar ta, yana kuma convincing kansa akan gwara hakan, da taje tana yi wa Yemma complain ta jawo masa sabuwar fitina. A ɓangaren Rahama kuwa, zuwa yanzu ta riga ta yi accepting reality ɗinta cewa tana tare da mutumin da a yanzu ta gane he is a coward—mutumin da ba kaɗan ba ne tsoron matarsa ke tafiya da rayuwarsa. Domin ko suna tare a office ɗinsa, idan Zara ta kira shi, nan da nan zai rikice! Kafin ya ɗaga, sai ya sa Rahama ta matsa nesa da shi, ya kuma yi mata mugun gargadi akan ko numfashi ta san yadda za ta yi ta yi kar matarsa ta ji ta. Idan kuwa video call ta kira shi—which she mostly does—to sai ya sa ta shiga cikin restroom ko dakin da ke cikin office ɗinsa gaba ɗaya har sai ya gama tattaunawarsu sannan za ta fito. A hakan dai ta yi accepting reality ɗinta, saboda Hajiya Saudah da aminiyarta Turai suka ce mata maza da yawa suna tsoron ɗaya daga cikin matansu, don haka ba wani abu bane kuma komai lokaci ne—kawai ta yi ƙoƙari ya zamana wata rana ita ce wadda ake shakka ba Zara ba. Kuma shirin da ta ƙulla da mahaifiyarta yana nan daram, suna ci gaba da tsarawa a hankali yadda komai zai zo ya tafi yadda suke so, kuma suna da cikakken confidence cewa zai yi aiki. Ita kuwa Hajiya Yemma, a yanzu tana ji a jikinta kamar komai ya fara dawo mata daidai, musamman da ta lura cewa ɗanta yana ƙoƙarin ba da full attention ɗinsa ga wadda ta aura masa, Don haka ko ba komai, ta san alkadarin Zara ya fara karyewa a kansa. Sau huɗu tana shiga gidan domin ganin Jasmine; idan ta zo, a ƙasa take ƙamewa ta zauna, shi kuma Zafar ta sa shi ya je sama ya ɗauko mata Jasmine ɗin. Ita da Imaan suke zuwa, kuma sai su shafe sama da awa biyu tare da Jasmine ɗin. Sai dai idan Zara ta yi pumping milk ta ba shi ya kawo wa Yemma ta ba ta, ko kuma ta haɗa mata formula. To Jasmine ɗince ma sam ta ƙi jinin formula, kuma tsaf take ganewa idan ba nono bane; haka za ta yi ta kuka! Da wata ‘Holle Organic’ suka fara amma sam ta ƙi ƙarba. Sai pediatrician ɗinta ya yi musu recommending wata HiPP Combiotic Stage 1, sai kuma Doula team ɗinnan na Zara suka yi mata recommending wata Kendamil saboda it has the closest taste to breast milk. Da ta gaya wa Zafar, sai kawai suka yanke shawarar su yi ordering duka a gani wacce za ta sha. Ko da aka kawo, Kendamil ɗin ta ƙarba kuwa, amma shi ma sai idan an ci sa'a take sha—most of the time ƙin sha take yi. To haka dai Yemma ke zama tare da Jasmine; ko ta yi bacci ba ta maida ita sama, sai dai ta sa Imaan ta hau har sama cikin nursery ɗinta ta ɗauko mata Portable Bassinet ɗinta. A nan parlour take kwantar da ita har ta yi bacci ta tashi. Har su tafi ba su sanya Zara a ido. Ita kuwa Zara bini-bini take leƙo su daga sama saboda a second parlour suke zama, don haka tana kallonsu ta bene. So sam bata damu ba, domin tana sane da cewa yarinyarta tana kusa da ita, kuma tana kallon duk wani motsinsu daga sama. Yau an wayi gari Asabar, agogo na nuni da ƙarfe 7:05 na safiya. Zara na zaune a kan sallaya a cikin praying corner ɗinta tana idar da adhkar ɗinta, a daidai lokacin da Zafar ya ɗaga drapes ɗin ya shigo ɗakin da Baby Jasmine maƙale a hannunsa—dawowarsa ke nan daga masallacin, yaji alert din tashinta. Zara da ke zaune a kan daddumar itama tana shirin tashi kenan taje gurinta, jin sun shigo yasa ta ɗago kanta a hanzarce, idanunta suka sauka a kan su yayin da ta ji ɗan soft sounds da muryar ɗiyarta ke fitarwa. Wani sassanyar murmushi mai cike da zallar soyayya da kulawa ya subuce a kan fuskarta. Ta rufe ƙaramin littafin da ke gabanta a hankali ta miƙe tsaye tana faɗin, “Good morning, sunshine! Look who’s ready for her milk.” Ta ƙarasa gaban Zafar a take, Ta ƙarasa gaban Zafar a take, tana shiga tana showering Jasmine da tarin kisses a fuskarta, yayin da yarinyar ke ta faman bin mahaifiyar ta da kallo duk inda tayi. Zuwa yanzu kam, idanun jaririyar sun fara fitowa sosai; are very grey with a little brownish tint, wanda hakan ya tabbatar musu da cewa tabbas idanun su Hajiya Yemma ta gado, Zafar yace mata sai ta kai irin 6 months dinnan Khaki green din zai fara bayyana. Zafar dai, shi ma kamar infant ɗin yake bin Zara da kallo cike da wani irin mayunwacin so dake ɗawainiya da rayuwarsa. A wurinsa, waɗannan watannin biyu da suka wuce su ne mafiya daɗi da farin ciki a tarihin rayuwarsa. Zara tana ta faman sauya masa rayuwa zuwa wata duniyar ta daban mai cike da wadata da natsuwa, ga kuma ɗiyarsa da yake ji a ransa ita ce cikakken ginshikin farin cikinsa. A yanzu, babu wani wuri a fadin duniya da yake samun nutsuwa da kwanciyar hankali irin kusa da su biyun. Zara ta cire mayafin sallar da ke jikinta, ta rataye shi sannan ta kalli Zafar ta ce,
“You two should head back to the bedroom. It’s way too chilly in here for her.” Ba musu Zafar ya juya da Jasmine a hannunsa ya koma ɗaki suka zauna zaman jiranta. Bayan ta gama cire kayan ta maida pjs ɗinta data kwana dasu wanda wani black silk cami and matching shorts ne. Bayan ta kashe fitilun ɗakin ta fito, kai tsaye ta nufi inda Zafar ke zaune a kan plush sofa. Tasa hannu ta karɓi Jasmine daga hannunsa, ta manna mata wani soft kiss a hancinta tana cewa,
“Hiiii, my little early bird. Why are you looking so adorable this morning, bubbles?” Daga haka ta ɗaura ta a kan kafadarta, ta juyo tana kallon Zafar tana faɗin,
“We need warm water, Obim. Can you get that started?” Kullum a duk safiya, ɗaya daga cikin Doula team ɗin ne ke taimaka mata wajen shiryata da miƙo mata abubuwan da take buƙata, amma idan Zafar na gida shi ne ke riƙe da wannan aikin da kansa. Da sauri ya amsa da, “Sure,” yana gyada mata kansa kafin ya miƙe a hankali ya nufi hanyar bathroom, yayin da Zara ta fice daga ɗakin ta nufi nursery ɗin Jasmine domin fara aiwatar da morning routine ɗinta. Suna shiga ta wuce da ita cikin closet ɗinta ta samu guri ta zauna kan plush one-piece sofa ɗin da ke cikin closet ɗin—wanda ke cike da kayan jarirai a tsare tsaf, kai ka ce wani babban shago aka buɗe a ciki. Komai na cikin closet ɗin abin kallo ne mai cike da ɗaukar hankali, tun daga kan shoe display ɗinta na alfarma har zuwa kan colorful kayan jariran da ke jere a kan automated valet racks masu motsi. Tana zaune tana ta yi wa ƴarta wasa cikin shirme irin nata da nishadi, sai ga Zafar ɗin ya shigo ta ƙofar closet ɗin da babban bowl ɗin ruwan ɗumi a hannunsa. Da ta ganshi, miƙewa tayi a hankali tana yin gaba. Tana isa gurin changing station ɗinta ta kwantar da Jasmine a hankali, Zafar ma ya iso da bowl ɗin a hannunsa. Zara ta fara cire mata sleep gown din jikinta, sannan ta cire smart socks din kafar ta, sai kuma ta hau cire pajama din jikinta a natse, bayan ta gama ta cire mata diaper ɗin. Zafar ta miƙa ma diaper ɗin bayan ta dunƙule sa; a cikin hanzari ya ajiye bowl ɗin ruwan ɗumin da yake riƙe da shi, ya karɓi diaper ɗin a hannunsa. Yana karɓa ya zura kafarsa cikin baseboard ɗin custom cabinetry ɗin da ke maƙale da changing station ɗin da Jasmine ke kwance. Zafar, wanda ya sa ƙafarsa a ƙasan gurin, yayi tapping ɗin wani flush, brushed-gold bounce-latch. Nan da nan, wani heavy drawer mai cike da akayi zallan na bleached oak yayi rolling open tare da fitar da wani soft, quiet click. A cikin ɗakin da ya buɗe ɗinnan, wani sleek, medical-grade Janibell Akord disposal system ne da aka yi integrating ɗin shi a tsakiyar woodwork ɗin. Bayan motorized trapdoor ɗin canister ɗin ya buɗe, kai tsaye Zafar yayi dropping ɗin rolled diaper ɗin da Zara ta ba shi ciki. Yana cire hannunsa, automated trapdoor ɗin yayi snapping shut a take, sannan ya sake tapping ƙafarsa a kan gurin; nan da nan drawer ɗin tayi gliding back into the wall, vanishing flush against the cabinetry. Zara kuwa, bayan ta miƙa masa diaper ɗin, ta shiga goge Jasmine da wani premium pure water wipe. Bayan ta gama ta sake miƙa masa ya yi disposing ɗin wipe ɗin ma a ciki. Daga nan ta ɗauki wani extra-large organic cotton cloth, ta yi dipping ɗin sa cikin wannan ruwan ɗumin mai tsabta da Zafar ya debo, ta hau goge wa Jasmine jikinta tass inda ita kuma ta fara yan kananun kuka na rashin son ruwa. Zara sai lallashinta take tana mata wasa cikin muryar kauna da ƴan waƙe-waƙe masu daɗin sauraro. Yayin da take hakan, Zafar na tsaye yana bin ta da kallo cike da tsantsar mamaki; a kullum yana shawar yadda take abubuwan nan, yadda take gudanar da komai ba wai don ana matsa mata ba ne ko don tana ganin nauyi ne, a'a, she’s so into this—cikin kulawa da kwarewa take komai ba tare da wata tangarda ba, kai ka ce ta taɓa haihuwa da ta taɓa riƙe yara kafin yanzu. Bai taɓa tunanin Zara za ta yi embracing motherhood cikin wannan sauƙin ba, ya zata za ta sha wahala. Sai dai bai san tun Umma Deeza na nan tasata ta kula da Jasmine ɗin a gabanta tana gani tana yi tana gyara mata har ta iya, ga kuma doula din da ke mata gyara kullum itama, gashi she has been reading and researching everything hatta yanda zata rike baby, shiyasa nan da nan ta koyi komai yanzu ko ba kowa tana iya komai ita kaɗai. Bayan ta gama goge mata jiki ta miƙawa Zafar tana cewa, “Throw that away, Obim, and grab us a onesie.” Daga haka ta dauketa tasa a kafada tana lallashi sai da ta yi shuru sannan ta sake kwantar da ita, Chantecaille bèbè lotion din ta ta janyo sannan ta hau shafa mata tana ta mata wasa. Zafar kuwa ya je ya dauko mata wani breathable cotton onesie dinta ya kawo wa Zara, bayan ta gama shafeta da lotion ta shafa mata chamomile diaper barrier cream a bottom ɗinta sannan tasaka mata wani diaper din. Daga haka ta karɓi onesie ɗin hannun Zafar ta saka mata, yayin da yarinyar ke ta kuka da kyau zuwa lokacin saboda yunwa da kuma bacci da take neman komawa. Cikin hanzari da ƙwarewa ta ƙarasa saka mata buttons ɗin sannan ta ɗauketa ta miƙawa Zafar ita. Karɓanta yayi a hankali ya hau lallashinta da wata gentle voice, yayin da Zara kuma ta hau maida komai da tayi amfani da dashi gurinsa, sannan bayan ta gama suka fice suna gaba tana biye da su har suka koma master bedroom ɗin Zara. Karɓanta tayi daga hannunsa sannan ta zauna kan babban gadon su, ta hau feeding ɗinta. Nan da nan Jasmine ɗin tayi shuru ta hau karɓan abincinta da sauri, idonta kyar akan fuskantar mahaifiyarta. Zafar dake kallonsu da wani murmushi ya ce, “Wow, she never locks eyes with me the way she does with you. I wonder why that is.” Zara tayi ƴar dariya mai sauti tana cewa, “It’s a mother-daughter thing, love. She strictly recognizes her mom for now.” Cikin sauri Zafar yace, “That reminds me—a few of Yemma’s friends are coming to see her today, so I’m gonna take her over to Yemma’s house later on.” Shuru Zara tayi tana ƙare masa kallo da idanunta masu cike da zallar izza, kafin a hankali ta maida kallonta kan Jasmine dake ta kallonta har lokacin. Calmly tace masa, “Me yasa baza su shigo nan su ganta ba? They should be the ones coming here if they want to see her.” Shrugging yayi, “I’m not entirely sure, but honestly, I think it’s way better if i just take her over there. It spares you from having to host them or deal with their energy. It's Hajiyar Sudan and that circle. You know exactly what kind of drama she likes to stir up.” Girgiza kai Zara tayi cikin katse sa da wani irin yanayi na bada umarni. “I don’t care what kind of drama she stirs up. This is my daughter, so I make the rules. Period.” Cikin sauri ya hau gadon yana zama kusa da ita, cikin lallashi ya fara magana. “I completely agree with you, princess. Your authority is absolute. But It's just a quick thirty-minute visit that Yemma practically begged for, so I reluctantly agreed. I genuinely thought it was a safer bet to keep them on that side of the estate so they wouldn't bring any unwanted comments or negative energy into your space. However, if you prefer to have them see her here under your roof, I will call Yemma immediately and shut her plan down. You call the shots, baby.” Shuru tayi cikin zurfin tunani, idonta na kan ƴarta. Allah ya sani ba wai dan za’a fita da ita bane kawai ainihin abin damuwarta, a'a—hannun kawayen Yemma ne sam bata so yarta ta je, ita kanta Yemman bata gama yadda da ita ba akan Jasmine, balle kuma kwayen Yemma. A hankali ta gyada masa kai tana cewa,
“Shikenan. Just thirty minutes.” Kissing ɗin cheek ɗinta ya yi yana cewa, “I appreciate you, maama.” Daga haka ya fara shafa fuskar Jasmine da ke shan abincinta tana lumshe idanunta cike da tsantsar jin bacci. Ganin Zaran ta ɗaure fuskarta tam yasa ya fara daɗin baki da lallashi cikin dabarunsa. “Look at it this way—it’ll give you a chance to finally get some rest. Because you’re not even resting enough lately. You hardly ever let anyone help with her except Amrah. So if I take her over there later, you can finally do your postnatal therapy or get your massage session in with the doulas. I’m sure Jasmine will be knocked out anyway, so kinga, you can actually squeeze in a solid nap after that.” Ita dai banza ta yi masa, fuskarta na nan a ɗaure ba tare da ta ce uffan ba har ya yi ya gama maganganunsa. Wajen ƙarfe 8:30am Jasmine ta koma bacci mai nauyi, Zara ta kwantar da ita cikin smart crib ɗinta a hankali, sannan ta miƙe ta shiga closet ta sauya kayanta zuwa gym wears ɗinta. Zafar dai na biye da ita a baya kamar jela, sai faman daɗin baki yake mata yayin da ta ci gaba da yi masa banza—amma kuma ba irin banzan da ke nuna fushi take yi ba, kawai dai mood ɗinta ne ya sauya gaba ɗaya. Gym ɗin ta nufa shi ma ya bi ta suka tafi tare, bayan ya ɗauki trifold ɗin Zara da ke kan gado don ya riƙa duba motsin Jasmine ta ciki. Ko da suka hau can saman suka shiga gym room ɗin, sai ya cire jallabiyar jikinsa ya rage daga shi sai shorts. Music Zara ta kunna, nan da nan ɗakin ya hau amsawa da sauti, yayin da shi kuma ya samu perfect spot ya ajiye trifold ɗinnan a gaba inda su duka biyun za su riƙa ganin Jasmine ras. Nan kowa ya kama harkar gabansa; shi ya fara workouts ɗinsa, ita kuma Zara ta nufi gurin smart 'The Mirror' ɗinta wanda shi ke guiding ɗinta gurin postpartum workout a kullum. Zuwa yanzu hankalinta ya ɗan fara kwanciya tun da ta fara ganin results a jikinta, amma duk da haka ba ta cika iya saka fitted kaya ba, saboda a nan ne tsantsar insecurity ɗinta ke tashi...
30 minutes tana yin workout ɗinta sannan ta gama ta fice ta bar Zafar a gurin, inda ta koma ɗakinta domin yin wanka. Tana cikin wankan ya shigo shi ma ya same ta a ciki, nan ya yi joining ɗinta shi ma ya fara gudanar da nasa wankan. Daga ƙarshe kuma suka shiga wasu lamuran inda they ended up having a hot, steamy sex. Bayan sun fito suka shirya tsaf, inda Zara ta saka soft cotton shorts and an oversized tee, shi ma Zafar ya sanya shorts da undershirt kawai. Suka sauko ƙasa suka yi breakfast, inda a nan suka haɗu da Sam da shi kuma tashinsa ke nan daga bacci, suka ƙarya gaba ɗayansu. Bayan sun gama breakfast ɗin, Sam ya fice daga gidan saboda weekends suna playing sports—mostly shi da Ahmad da Omar, wanda wani lokacin Muazzam na joining ɗinsu. Ta back gate ɗin manor yake bi ya shiga, shiyasa ba wanda ya taba ganinsa, saboda gaba ɗaya abin da ya shafi back-gate ɗin na mazan gidan ne kawai, don haka ba mai ratsawa ta can. Zafar da Zara kuwa komawa sama suka yi cikin lounge ɗinta, inda Zafar ya hau gudanar da aikinsa a laptop yana wayoyinsa, yayin da ita kuma ke kwance a jikinsa tana kallo a makeken flat screen ɗin da ke maƙale a wall ɗin.