Free chapter · Read without an account
LOKACI CHAPTER 20
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's
SADAUKARWA A GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI ❣️
***
PAGE 2️⃣0️⃣
Haka kawai ta kasa ɗagawa har kiran ya yanke, jin wani kiran ya shigo ne ya sa ta ɗagawa ta kai kunnenta.
"Hello Zahra"
"Barka da yamma sir"
"Yawwa barka fatan kina lafiya?"
"Alhamdullah" ta amsa.
"Daman gobe muna nemanki a restaurant, abu ne mai muhimmanci ya taso, please ki shigo da wuri"
"Allah ya kaimu" ta katse wayar tana mamakin abin da ya sa ya yi mata wannan kiran, yana kiranta akan aiki, amman bai taɓa mata irin wannan kiran ba.
Tun abin da ya faru gidan nasu ya dawo shiru, Salmah da take raya gidan da surutu gaba ɗaya ta yi sanyi, kukan da ta yi bata jin ko da Mahmah ko Baffan ne ɗaya daga cikinsu ya mutu zata yi irinsa, ta nemi yafiyarta bata san sau nawa ba, ita kuma irin son da take wa Salmah koda da gayya ta yi mata abu ba zata taɓa riƙe ta a ranta ba, domin tasan ba ta da wata me mata irin son da take mata.
Washe gari kamar lokacin da ta saba tafiya, ta shirya ta tafi, tana zuwa kai tsaye office ɗin manager ta nufa, knocking tayi, ta bata izinin shiga, da sallama ta tura ƙofar office ɗin.
"Good morning sir"
"Morning Zahra, zauna" ya nuna mata kujerar da take kallonsa.
Zama tayi tana kallonsa cikin girmamawa.
File ɗin da ke gabansa, ya buɗe takarda ya zaro, ɗan jim ya yi yana kallonta da takardar a hannunsa, sannan ya miƙa mata.
Karɓar takardar tayi ba tare data karanta kota meye ba, taji yayi mata gyaran murya.
"Zahra! Na kira ne saboda wannan takardar ta hannunki, munyi miki transfer zuwa Zay'd Signature restaurant"
Batasan san da ta zaro manyan idanuwanta ba, ta buɗe takardar ta fara dubawa cikin sauri.
"Zay'd Signature restaurant" ta maimaita sunan, a cikin zuciyarta sai dai abin da bata sani ba a fili ta furta.
"Ehh" ya ƙara mata tabbaci.
Ƙara karantawa take kamar wadda take ƙoƙarin tabbatar da wani abu a jiki.
"Amman sir me ya faru? Na yi wani laifi ne? Ko akwai abin da nayi da ba daidai ba?" Ta jera masa tambayar cikin sanyin murya tana mayar da idonta kansa.
Kallonta ya ke kawai, shi kansa ba'a san ransa hakan ta faru ba, sai dai umarni ne daga sama shima aka basa, baisan komai ba, kuma ba'a bashi damar faɗa mata komai ba, tabbas ta kawowa wajensu ci gaba, ba ɗan ƙarami ba har ya ce baya fargabar rasa ta a wajen yayi wa kansa ƙarya.
"A'a Zahra, babu wani laifi da kika yi, wannan canjin wajen aiki ne kawai"
Shiru ta yi cikin rashin jin daɗi ta ce.
"Amma me ya sa ni? Na saba da aiki anan, shekara ta nawa ina aiki anan, na san tsarinku, sannan na saba da mutanen da nake aiki da su, bansan dalilin da ya sa za'a mayar da ni wani waje ba, ba tare da an sanar da ni ba tun farko"
"Ki yi haƙuri na fahimci abin da ki ke ji, nima umarni kawai aka bani, sai dai ina da tabbacin an zaɓe ki ne saboda ƙwarewarki, ina fatan kuma za ki ci gaba da nuna ƙwarewar da kike da shi a ko ina ba'a iya nan ba, zaki fi jin daɗin aiki a can fiye da nan, dan babbanci gaba ne a gare ki, dan baki san wajen ba shiyasa har kike complain, ina miki fatan alkhairi"
Ajiyar zuciya ta sauke, miƙewa ta yi da takardar a hannunta.
"Zaki iya fara aiki daga gobe monday a can, good luck"
Godiya ta yi masa sannan ta saka kai ta fice, zuciyarta cike da tambayoyi, me yasa za'a mayar da ita can, tana ganin yanda suke yabonta da son aiki da ita, idan dai dan ƙwarewarta ne ai, su ma ba zasu bari su rasata ba, dole sai dai idan da akwai wani abun a ƙasa, juyawa tayi tana ƙarewa wajen kallo, har ranta take jin kewar gun tun bata bar sa ba, jin kanta ya toshe ne ya sa ta girgiza kanta ta fice gaba ɗaya ta tare napep, har ta je gida tunani take bama tasan ina ne Zay'd Signature restaurant ɗin ba, duk da taga kamar akwai address ɗin a jikin takardar.
Tun da ta koma ta saka takardar a gaba tana ta tunani, tarasa tunanin kamawa gaba ɗaya, hakan yasa tayi wani irin zurfi a cikin tunani, ba tare data ankara ba, Salmah da shigowarta ɗakin kenan, ta kula da yanda tayi nisa a cikin duniyar tunani, ga takarda a hannunta.
"Big sister" ta kira sunanta tana dafata.
Firgit ta ɗago tana kallonta. "Autah" ta kira sunanta a hankali.
"Lafiya? Me ya faru? Ko har yanzu abin da ya faru ne yake damunki?" A jere ta jera mata tambayar ranta a jagule.
Takardar hannunta ta miƙa mata, ba tare da ta ce mata komai ba. Hannu ta saka ta karɓa, fara karantawa tayi, kafin ta gama ta ɗago kanta da sauri tana kallonta. "Kai wai transfer aka miki, an mayar da ke Zay'd Signature restaurant? Ina ne haka?" Ta jera mata tambayar tana zama a kusa da ita.
Kanta kawai ta gyaɗa mata.
"Amman me ya sa? Me suka ce? Na ga fa yanda suke nuna son zamanki a tare da su"
"Nima shine abin da yake bani mamaki Autah, da na tambaye su ko nayi wani laifi ne, sai suka ce a'a wai saboda ƙwarewata ne" ta bata amsa kamar zatayi kuka.
Kamar ƙawarta Salmah ta dafata ganin yanda duk rauni ya bayyana a fuskar Auntynta ta. "Toh big sister idan sun ce saboda haka ne, wataƙila hakan ne, ko kuma suna ganin hakan wani matakin nasara ne a wajenki, tunda naga ko akan albashin da zasu baki ya ninka na inda kike aiki fa, ni banga abin damuwa ba"
"Ayya Autah ba za ki gane ba, sunan restaurant ɗin kawai wata iriyar faɗuwar gaba yake sani, duk fargaba ta dame ni, nidai kawai ina tunanin ajiye aikin ma"
Ƴar dariya Salmah tayi, ganin duk yanda tayi wani iri. "Kada ki bari fargaba ta tsorataki big sister, ta yuyu kawai saboda zaki koma sabon waje ne, kawai ki yi addu'a, ki dogara ga Allah, idan akwai alheri a ciki, Allah ya tabbatar miki da shi, ni wallahi a jikina ma nake jin wani abun alkhairi ne yake kiranki wajen, za ki ce kuma na faɗa miki"
Kallon Salmah ta yi kawai ta yi murmushi na ba za ki gane ba.
"Shikenan bari na je na kawai Mahmah" ta miƙe zata karɓi takardar a hannun Salmah.
"Wace Mahmahn za ki faɗa wa?" Salmah ta tambayeta tana zare ido tare da ɓoye takardar a bayanta. Kallon rashin fahimta ta yi mata, tana shirin magana ta riga ta. "Ai kawai ki tafi babu matsala, ki bari idan Baffa ya dawo mu faɗa masa shi kaɗai amma maganar a saka Mahmah ma bata ta so ba, idan ba so kike ta hanaki gaba ɗaya ba" sai a lokacin kuma itama tayi wannan tunanin dan haka, sai ta koma ta zauna.
Da daddare Baffa ya dawo Salmah tayi masa magana, suka fita waje ta yi masa bayani, sosai ya yi mata fatan alheri, sannan suka dawo cikin gidan ba tare da Mahmah yasan anyi ba.
Washe gari Salmah ce ta yi komai na gidan, sai azalzalarta take akan ta yi sauri kar ta makara, cikin shigarta ta ko yaushe ta shirya, har bakin titi Salmah ta rakata ta hau napep, address ɗin da yake jiki ta faɗa masa, wajen ba ɓoyayye bane hakan yasa bai sha wahala ba, wajen kaita.
Bayan ta fito daga cikin napep ɗin da ya kawo ta, shiga ciki tayi cikin tafiyarta ta nutsuwa, gyara mayafin kanta tayi, sannan ta ɗago kanta ta zubawa ginin wajen ido..
Wani irin sanyi ne ya ratsa jikinta, ba sanyi irin na sanyin iska ba, a'a wani irin sanyi ne da ya saka ta cikin wani irin yanayi da ita kanta ba ta san a yadda zata bayyana shi ba.. hannunta ta ɗora a kan zuciyarta da ta ji tana bugawa da sauri, idonta ta mayar kan ginin tana ci gaba da kallonsa tun daga sama har ƙasa, a hankali ta sauke ajiyar zuciya, sunan wajen ta ƙara kalla ta furta a saman laɓenta.
*"Zay'd Signature Restaurant"*
"Ya rabb!" Ta faɗa a fili tana ƙara dafe saitin zuciyarta, jin yanda sunan ya yi amsa kuwwa a cikin zuciyarta, idonta ta runtse ta fara addu'a.
"Ya Allah, ina roƙonka ka sa wannan wajen ya zama mafi alheri a gare ni, ka sanya min albarka a cikin aikin da zan fara, ka kuma kare ni da dukkan wani sharri da abinƙi" tana gama addu'ar ta fara takawa zuwa ƙofar shiga, tana saka ƙafarta wani irin sanyin Ac ya bugi fuskarta, tare da wani irin ƙamshi na freshner, idonta ta lumshe tana shaƙar ƙamshi da sanyin wajen jin yanda suka saukar mata wata iriyar nutsuwa.
A hankali ta dakata da tafiyar na ɗan lokaci tana ƙarewa wajen kallo, ma'aikata ne suke ta kai kawo cikin unifoam ɗinsu riga da wando Black sai kuma facing cap, sosai wajen ya yi mata kyau a idonta da kuma shigar ma'aikatan, ci gaba ta yi da yawo da idonta a wajen, can kuma ta ɗaga ƙafarta ta nufi reception, wata budurwa ce a zaune a bayan teburin, da akwai computer a gabanta, sai kuma wata da take duba takardu, mutum uku ne zaune a reception ɗin kowa da abin da ya ke yi, tsayawa ta yi a gaban su.
"Assalamu alaikum"
Kusan a tare suka ɗago suna kallonta.
"Wa'alaikumus salam, barka da zuwa, da me zan taimaka miki?" Ɗaya daga cikinsu ta amsa mata sallamarta.
Takardar transfer ɗin ta miƙa mata, "an turo ni ne daga Dara restaurant"
Gƴada mata kai budurwar ta yi, sannan ta buɗe wani fayil da ke gabanta.
"Zahra Habib?" Ta kira sunanta da sigar tambaya.
Da ɗan mamaki Zahra ta ce "eh ni ce"
"Ok ki ɗan jira bara na sanar da manager" ba ta jira amsar ta ba, ta ɗauki wayar reception ɗin, ta kira number manager, magana suka yi ta ɗan lokaci, sannan ta ajiye wayar ta sake kallon Zahra.
" Ki bi wannan hanyar akwai corridor, bayansa zaki ga office ɗin managern, idan kin bi zaki ga office ɗin"
"Ok nagode sosai"
Murmushi ta mata, sannan ta juya ta bi hanyar da aka nuna mata, tana tafiya zuciyarta na bugawa a hankali, tana bin hanyar taga office ɗin da sunansa a jiki, ƙwanƙwasa wa ta yi sau biyu.
Daga ciki aka ce mata.
"Yes come in"
Yana zaune a cikin office ɗin, akan teburin gabansa akwai computer da kuma tarin takardu a gabansa, yana ɗago kai ya ganta, sai ya ajiye takardun da ke hannunsa, ya ce.
"You must be Zahra?"
"Yes sir, good morning"
"Morning, Please have a seat" ya nuna mata kujerar gabansa.
Zama tayi a inda ya nuna mata ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Fayil ɗin da ke gabansa ya ɗauka ya fara duba bayanan ciki, kafin ya mayar da dubansa a kanta.
" A bayanan da muka samu a kanki, an tabbatar mana da kina da ƙwarewa sosai wajen yin Snacks da pastries, sannan an bamu tabbacin ƙwarewarki a harkar cake, da shirya kayan zaƙi kala-kala"
Yanda ya ƙarasa maganar sai da ya sakata murmushin da bata yi niyya ba, daga murmushin kuma ba tace masa komai ba.
Shima murmushin yayi, tare da yaba nutsuwarta a cikin zuciyarsa.
Wani file ɗin ya bata, a nutse ta karanta dokokin jiki, sannan ta saka hannu ta miƙa masa, karɓa yayi ya ƙara mata bayani.
"Muje na kai ki kitchen ɗin" tashi ya yi daga kan kujerar da yake zaune, sannan ya ɗauki takarda akan teburinsa, ya yi mata alama da ta biyo sa.
Tashi ta yi tabi bayansa, a ranta tana mamakin dokokin da aka shimfiɗa, wani corridor suka bi mai kyau da tsari, an yi wa bangonsa ado da hotuna na nau'ikan abinci da kayan zaƙi daban-daban, daga nan suka shiga wani ɓangare na restaurant ɗin, sai gasu a ƙaton kitchen, kitchen ɗin babba ne mai girma dan yayi huɗun na dara restaurant, suna shiga ƙamshin kayan abinci da na butter ya cika mata hanci, sai kuma hayaniyar ma'aikata, kitchen ɗin wani irin girma da faɗa garesa, an raba sa zuwa sassa daban-daban, saboda sauƙaƙa aikin ma'aikata, akwai manyan ovens, da kuma na'urorin haɗa kayan zaƙi da tebura masu sheƙi da aka yi da stainless steel, akwai shelves, da ake ajiye kayan aiki, sai kuma ma'aikata da suke aikinsu.
Tsayawa ta yi tana ƙarewa wajen kallo, wannan kitchen ɗin duk wanda yake da buri akan zama cikakken chief zaiyi fatan ace ya kasance a wajen, babu wani abu da babu a cikin kitchen ɗin, wani irin farin ciki ne ya ratsa zuciyarta, tare da fargabar fara aiki a sabon wajen.
"Nan shi ne sashin da za ki yi aiki a cikinsa, haƙƙin kula da cake da pastries yana a kanki, sai kuma sauran ma'aikatan da suke a ɓangaren"
Sannan ya nuna mata wani waje mai girma da aka ware domin shirya kayan aikin, sai kuma ya gabatar da ita a kitchen ɗin, daga haka ya juya zai fita, har ya yi nisa ya dakata.
"Zahrah"
"Na'am sir" ta amsa tana matsawa kusa da shi.
"Ina so ki duba kayan aikin da muke da su, sannan ki rubuta abubuwan da kike buƙata, saboda kifi jin daɗin aikinki yanda ya kamata, duk abin da kike so, ki rubuta kizo ki sameni yanzu"
Bayan ya tafi ta ɗauki biro da littafi a jakarta, zagaye ta farayi tana duba abubuwan da suke da su, kusan suna da komai saidai bada waɗanda take amfani suke amfani da su ba, ita kuma tafi son waɗancan, hakan yasa ta rubuta masa su, tunda shi ya bata dama, bayan ta gama office ɗinsa ta koma ta kai masa, karɓa yayi ya duba, ya ce mata babu matsala za'a kawo mata in sha Allah, sannan ya bata unifoam ya ce zuwa gobe ta dawo ta fara aiki, dan su dokar su dole ne saka unifoam, godiya tayi masa daganan ta fice ta tafi gida.
Tun da ta koma Salmah ta addabeta da maganar restaurant ɗin, dan tayi sarchine ɗinsa ta gani a media.
Ranar talata da ta koma an kawo duk wani abu data buƙata, an canza da wancan, kuma ta fara aikinta cikin nasara, dan sosai abin da ake buƙata ya fara samuwa a dalilin ta, ƙasan da restaurant ɗin yayi cikin ƙasa da wata ɗaya sai gashi yayi sama fiye da yanda ba'a yi tsammani ba.
Jin wayar restaurant ɗin tana ringing ne yasa ta ɗagawa.
"Zahra ki sameni a office yanzu"
Amsa masa, tayi sannan ta nufi office ɗin manager ɗin, da sallama ta shiga sannan ta gaishesa, wajen zama ya nuna mata ta zauna.
"Zahra mun samu wata babbar order, manyan mutane ne suka yi za suyi taro, order nan tana da muhimmanci, dan zata ɗaga mana restaurant ɗin nan fiye da yanda bakya tunani, zata kawo mana ci gaba, mun yarda da ke shiyasa zamu ɗora nauyin komai a kanki, karki manta ba'a wasa da irin wannan, ina tunanin Oga da kansa ma zai zo a ranar, dan haka ya kamata ki ƙara ƙoƙori akan wanda kike yi, akwai abin da ki ke buƙata?"
Ajiyar zuciya ta sauke
"Akwai komai, yaushe ne?"
"Ranar friday idan Allah ya kaimu, bayan an sakko da ga masallaci, kina da kwana uku kenan, kafin lokacin"
"Allah ya nuna mana" daga haka sukayi sallama ta fice.
Daren Alhamis da wani irin ciwon mara ta kwana, gashi washe gari ne, ranar da za tayi aikin da aka bata, dan ko a yau sai da aka ƙara maimaita da kuma nuna mata muhimmancin aikin, ga kuma wani gyara na musamman da ta ga anayi duk da C.E.O zai zo a goben, ranar batayi bacci ba saboda ciwo, da ƙyar ta samu tayi sallar ta asubah, a haka ta lallaɓa tayi wanka ta shirya, Salmah babu yanda bata yi da ita ba ta haƙura da zuwa aikin, amman ta ce ba zata iya ba.
A daddafe ta ƙarasa restaurant ɗin, tana shiga ta cire doguwar rigar jikinta, unifoam ɗin jikinta suka bayyana, facing cap ɗin ta ɗora a kanta, ƙafarta ta ɗaga da niyyar tafi wani irin jiri ya ɗibeta....
FULANI
***