Free chapter · Read without an account

Chapter 6: The truth behind her death

by Hauwa Jibrin Sulaiman · AMRAH (Force Marriage)

Dukkansu sun kasa yin wani kwakkwaran motsi. Kallon gawar Amrah kawai suke yi, kamar kowannensu yana jiran wani ya faɗi abin da ke zuciyarsa


Abbah ne ya iya daurewa, ya gyara maƙogwaronsa kafin ya ce, “Ya kamata mu mayar da ita gidan mijinta, a shirya ta a can”


Umar ya yi wa Anty Badiyya wani irin kallo, wanda kana gani kasan magana ya mata da ido 


“Gidan wannan azzalumin da ya kashe ta kuke fatan mayar da ita?” Anty Badiyya ta tambaya cikin fushi


Ammi ta ɗan gyara zama “Toh, ba gidan mijinta ba ne? Kuma ai shi ne gatanta”


“Ke! ki yi min shiru, domin ba ke nake yi wa magana ba, ke kuma Hajara, ki sani cewa ke da mijinki kun shiga haƙƙin ’yarku ga shi ta bar muku duniya, sai ku san yadda za ku yi da haƙƙinta”


Mami ce ta ƙaraso cikin ɗakin. Ta kalli kowa daga cikinsu, sannan ta yi magana cikin sanyin murya


“Ga shi ’yar da ta haifa, an samu baby girl”


Ta miƙa jaririyar ga Mummy, wadda ta karɓa tana kallonta, sosai jaririyar kama take yi da Amrah, kamar dai lokacin data haifi Amrah din, carbon copy ɗinta sak


Mami ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ci gaba “Amrah ta sha wahala tun kafin ta haihu, tun daga laulayi har zuwa lokacin haihuwar. Abin da ya rage mana shi ne mu mata fatan dacewa, ba kuka kawai ba”


Mufidarh ce ta buɗe ƙofar ɗakin, ta tsaya tana bin kowa da kallo kafin idanunta suka sauka kan inda Amrah take kwance


A hankali ta ƙarasa ciki, ta nufi Amrah, sannan ta zauna kusa da ita. Hannunta ta kai fuskar Amrah, ta shafa ta a hankali, kamar tana fatan za ta buɗe idanunta ta kalle ta


“Amrah kin wuce ’yar uwa a wajena. Ba ni da tamkar ki a duk duniya. Kin ɗauke ni a matsayin ƙanwarki ta jini, uwa ɗaya, uba ɗaya, In shaa Allah, zan bi miki haƙƙinki, wallahi Sultan sai ya yi nadamar kashe ki, sannan zan cika miki burinki, zan fito da wasiyyar da kika bari kamar yadda kika buƙata”


Abbah ya kalle ta “Me ya sa kuke ta cewa Sultan ne ya kashe ta? Bayan kowa ya san a wajen haihuwa ta rasu, please, ku daina waɗannan abubuwan, ya kamata mu koma gida”


Mufidarh ta yi murmushi mai ɗauke da baƙin ciki, zuciyarta tana ƙuna, kuma idan ta buɗe baki, tana jin za ta iya faɗa wa Abbah abin da bai kamata ba. Saboda haka ta yi shiru


Tun bayan fitowar Sultan daga gidan, ya kasa samun nutsuwa. Wani irin discomfort yake ji, amma ya kasa gano dalilin hakan


A ƙarshe sai ya yanke shawarar komawa gida, ko da zai samu ɗan hutu. Maybe stress ne kawai, tunda bai daɗe da dawowa daga ƙasar ba


Ya juya motarsa zuwa gida


Da isowarsa, ya yi parking, sannan ya shiga gidan. Yana kallon an bar ƙofar parlour a buɗe, sai ya ja tsaki ya nufi stairs


Amma da ya shiga parlour ɗin, sai wani irin bugawa zuciyarsa tayi


Jini ne ya malale a ƙasan tiles ɗin


Nan take tunanin abin da ya faru dazu ya fara dawowa masa. If he could remember correctly, ya ture Amrah a wajen stairs, kawai yayi assuming cewa maybe miscarriage ta yi


Ya ɗaga kafaɗunsa cikin ko-in-kula

“I don’t care. Dama cikin ne plan ɗinsu” Ya faɗi haka sannan ya nufi stairs


A wannan lokacin kuwa, su Abbah suka iso da gawar Amrah


Suka shigo da ita cikin gidan, Mummy da sauran mutanen suna biye da su a baya. Umar ya ɗan tsaya a wajen ƙofar, kamar yana tunanin ko zai shiga ko a’a, amma daga baya shi ma ya bi su


Ammi ce ta buɗe musu ƙofar parlour. Ta yi musu alamar su shigo, sannan suka shiga tare


Sultan, wanda ya fara hawa stairs, ya ji ƙarar buɗe ƙofar. Hakan ya sa ya juya kansa


Sai kawai ya tsaya cak, kamar gunki, yana kallon mutanen da suka shigo


Mufidarh ta nuna wajen da jinin Amrah yake “Abbah, Mummy, ku kalli inda Sultan ya kashe min ’yar uwa, kuma duk laifinku ne!!!”


Anty Badiyya ta yi saurin dakatar da ita “Mufidarh, ki yi shiru kawai”


Abbah, Ammi, Mummy, Khadijah, da Daddy wanda ya iso daga baya, duk suka tsaya suna kallon jinin da ke ƙasa. Jinin ya fara bushewa, amma har yanzu ana iya ganin fresh blood din


Sultan kuwa ya kasa motsi. Kalmomin Mufidarh suna ta maimaituwa a cikin kunnuwansa


Ammi ce ta fara kallonsa Sultan, so you’re here? Ba ka zo asibiti ba?”


Anty Badiyya ta yi dariyar takaici “Toh, damuwarsa ce da zai zo?”


Ammi ta juya gare ta “Look, ya kamata ku daina ɗora wa Sultan alhakin mutuwar Amrah saboda kawai an yi musu auren dole, shi ke nan?”


Daddy ya ɗaga hannu, yana son dakatar da gardamar


“Please, we’re not all here for this. Mutuwa aka yi mana, amma duk muna ta ce-ce-ku-ce. Ga Amrah nan, abin da take buƙata a yanzu shi ne addu’a”


Ya juya ya kalli Sultan “Kai kuma Son, ba za ka ƙaraso ba ne?”


Sultan ya kasa fahimtar abun da suke fadi, ya de daure ya karaso falon ya zauna kusa da Daddy sbd yadda zuciyarsa ke bugawa


Abbah ya kalli Mufidarh “Mufidarh, kin ce tana da wasiyya ko? To, ki kawo mu duba. Maybe ana bin ta bashi ne, ba mu sani ba”


Mufidarh ta miƙe ta fara hawa stairs, ta afiyarta ta yi mata nauyi, kamar an cire mata ƙarfinta, har yanzu tana jin kamar mafarki take yi, ba gaskiya ba


Ta shiga ɗakin Amrah, ta ɗauko diary ɗin daga inda ta ajiye shi, sannan ta dawo parlour ɗin


Ta miƙa wa Abbah diary ɗin, amma ya girgiza kai “No, buɗe kawai”


Mufidarh ta buɗe diary ɗin. Sai ta ga cewa Amrah ta rubuta sunayen waɗanda ta rubuta musu bcos ko wani page tana indicating sunaye, a first page ɗin ma ta yi bayani cewa a karanta saƙonnin da ƙarfi


Mufidarh ta ɗago kai ta sanar da Abbah, Abbah ya gyada kai “It’s okay, ki yi yadda take so”


Mufidarh ta kalli Sultan “Da Sultan ta fara”


Sultan ya yi mata wani irin kallo, amma ta kawar da kanta ta fara karantawa “Ni, Hauwa Aliyu (Amrah), na san duk da cewa kana matsayin mijina, ba na buƙatar yafiyarka a kaina, domin na san ban taɓa cutar da kai kamar yadda ka cutar da ni ba. Aurenka da na yi, ka san cewa dole aka yi min, amma ka zaɓi azabtar da ni, sannan ka raba ni da iyayena


“Amma ni, ina da pure heart, ba kamar kai ba. Duk wani abu da ka yi min, na yafe maka duniya da Lahira. Sai dai ba na fatan ’yata ta taso a hannunka. Kai ma ka yafe min idan na yi maka wani abu bisa kuskure. Bissalaam”


Shiru ya mamaye parlour ɗin


Duk idanu suka koma kan Sultan, wanda ya kasa ɗago kai. Hawaye suka fara zubo daga idanun Mummy.


Mufidarh ta juya zuwa saƙo na gaba


“Dear parents, ni Amrah ina neman yafiyarku. Na san ban yi muku biyayya a lokacin da aka yi min aure ba, amma na yi biyayyar zama da shi, duk da na san wahala kawai nake sha. Na yi hakan ne just bcos of you


“Na roƙe ku, ba don halina ba, ku yafe min. Kuma kada ku ce ba ku nemi yafiyar ‘yarku ba. A’a, ba ku taɓa yi min komai ba, sannan ban taɓa riƙe ku a raina ba. So, you’re free with me


“Ku kula da abin da na bari tamkar ni ce yarinyar. Nagode muku, and da soyayyarku na mutu, Bissalaam”


Mummy ta kasa riƙe kukan da take yi. Ta rufe fuskarta da tafin hannayenta, kuka take kamar zata shide


Anty Badiyya ta kawar da kai, ba ta ji tausayin Mummy ba, domin a ganinta, duk abin da ya faru, su suka jawo


Parlour ɗin ya cika da kukan Mummy yayin da Mufidarh ta ci gaba da karantawa


“Dear best friend!


“I wish kina da aure, da kin fahimci yadda nake ji, amma nasan ba sai na roƙe ki ba, za ki ɗauki abin da na bari tamkar naki ne. Na san irin zuciyarki.


“Ina roƙonki, kada ki shigar da ƙara ko ki ɗauki fansa a kan Sultan. Ko da yake duniya ma kalilan ne, ki ba Farouq haƙuri. Please.


“Sannan ina neman alfarmarki, ki daure ki auri Faro…”


Gabanta ya buga da ƙarfi, ta kasa karasa karatun, sai ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta juya zuwa ɗayan shafin, tana share wayan daya ki tsaya mata


A saman takardar an rubuta:

Mufidarh, take this to Farouq. Ba sai kin karanta ba.


Mufidarh ta runtse idanunta na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin danne kanta


Daddy ya kalli Sultan

“Sultan, dama irin zaman da ka yi da Amrah kenan?”


Ammi ta girgiza kai cikin takaici

“Hmm! Ban san dalilin da ya sa wasu mutane ba sa sanin halacci ba. Laifin Sultan kawai kuke ta nema, kamar Amrah ba zata iya masa sharri ba”


Anty Badiyya ta miƙe “Ina zuwa”


Ta fita daga parlour ɗin, ba a daɗe ba sai ta dawo da system a hannunta

“Za ku iya kallon wannan, please?”


Ta kunna system ɗin, ta nuna musu CCTV footage ɗin da ya ɗauki abin da ya faru


Dukkansu suka yi shiru yayin da suke kallon yadda Sultan ya ture Amrah, har ta faɗi, ta fara kuka, sannan ta fara bleeding


Anty Badiyya ta kashe system ɗin

“Idan kuna son kallon abin da ya faru kafin wannan ma, za ku iya, tunda wasu shaidar kuke buƙata, but not now da muke cikin alhiki”


Ta kashe system ɗin gaba ɗaya, sannan ta ɗauke shi ta haura sama


Idon Abbah ya yi mugun ja. Mummy kuwa tana kuka kamar za ta tsuma. Mufidarh tana ƙoƙarin danne nata kukan, amma ta kasa. Ammi ta yi shiru tana kallon Daddy, wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa kawai sabar kunya


Da ƙyar Abbah ya kai hannu ya shafi fuskar Amrah “Amrah ki yafe mana. Tun daga ranar da muka haife ki, kina mana biyayya, amma mun kasa faranta miki rai. Mun cutar da ke tabbas, Allah Ya karɓi shahadarki”


Ya share hawayensa, sannan ya miƙe

“Ku yi mata sutura. Za mu jira ku a waje”


Ya gagara riƙe hawayensa, ya fita daga parlour ɗin. Daddy ma ya bi shi a baya, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa


Khadijah ta rungume Mufidarh, ita ma ta fashe da kuka. Ta san cewa Amrah ta yi mutuwar wahala, kuma wannan tunanin yana ƙara karya zuciyarta


Sun gama yi wa Amrah komai, sun shirya ta yadda ya kamata. A lokacin ne ’yan uwa da abokan arziki suka fara isowa. Maƙwabtansu ma sun shigo, har da Mami


An ɗauko gawar Amrah aka fitar. Abin mamaki, jama’ar da suka halarta sun yi yawa fiye da yadda kowa ya yi tsammani, ba maza balle mata


Bayan an yi mata sallah, aka shirya ɗaukarta domin a kai ta makwancinta na gaskiya


Mummy ta ƙaraso da sauri ta riƙe gawar ‘yarta, sannan ta fashe da kuka. Da ƙyar take iya furta kalmomi yayin da take yi wa Amrah addu’ar samun rahamar Ubangiji.


Daga nan aka ɗauke ta aka fita da ita, zuwa gidanta na gaskiya


Farouq da Abbah ne kawai suka rage a baya. Bayan an binne Amrah, sun ɗan jima suna yi mata addu’a kafin su tashi daga wajen


Allah Ya sa mu cika da imani😭💔


Sorry, darlings 😫🙏


naga ruwan comments da following mana🥹 if not nayi tafiyata sai ranan da kuma na sake wuntsulowa😒

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol