Free chapter · Read without an account
THE COMFORT OF HOME
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER 106*
*THE COMFORT OF HOME*
*JIDDAAH BARKUM*
—————
Seeyama ta kalli Safina ta gefen ido kafin ta yi magana, fuskarta a ɗan sake kamar wadda a ƙarshe ta gano abin da take nema, “Kin san me? Nayi tunanin wata mafita guda ɗaya wacce nake kyautata zaton za ta yi min aiki,” Safina ta juya da sauri ta fuskance ta, tana nazarin fuskarta, “Really? What is it?” Seeyama ta ɗan gyara zamanta a kan kujerar motar, sannan ta mayar da idanunta kan hanya, “A lissafina dai, yau zai dawo ɗakina, jiya kwananansa bakwai cif tare da waccan yarinyar,” ta yi ɗan murmushi, wani irin murmushi da ya nuna cewa akwai wani abu da take shiryawa a ranta, “So, I have something in mind, which I think can work out,” Safina ta zuba mata ido, tana jiran ta ji abin da take shirin yi, “Wanne abu ne kuma, Seeyama?” Amma maimakon ta ba ta amsa, Seeyama ta yi murmushi kawai, ta ci gaba da driving ɗinta ba tare da ta ƙara cewa komai ba, Safina ta ɗan buɗe baki, ta sake rufe shi, tana kallon Seeyama da mamaki, “Are you kidding me right now? Kin faɗa min kina da plan, amma ba za ki gaya min menene plan ɗin ba?” Seeyama ta yi ƙaramar dariya, “Just wait and see, Safina, you’ll find out soon enough,” ta ƙara matse steering wheel ɗin kaɗan, sannan ta mayar da hankalinta kan hanyar da take bi, yayin da zuciyarta ke cike da tunanin abin da take shirin aiwatarwa.
A can kuwa, a gidan, Maryam, Bintu da Raihana sun daɗe suna hira, sun ci abincinsu, sun yi dariya, har hankalin Raihana ya ɗan kwanta saboda kasancewar su a kusa da ita, bayan ɗan lokaci, sai Raihana ta kalli Maryam, ta ce cikin wata murya mai ɗan roƙo, “Dan Allah, ku zo ku rakani na kwashe duk kayan amfanin da ke ɗakina, zan maida ɗakin shi,” Maryam ta tsaya cak tana kallonta na wasu daƙiƙu, kafin ta fashe da dariya, “Ke, Rayy! Waton ke daɗin miji Meyasa sai kin kwashe kayan gabaki ɗaya kin maida ɗakinsa? Ke dai kai wasu can, saboda watarana canjin kayan zai same ki a ɗakinsa, amma ban taɓa jin inda mace ta kwashe kayanta rankatakaf ta kai ɗakin mijinta ba!” Raihana ta yi mata wani irin kallo, ta ɗan harare ta kafin ta yi magana, “Daɗina da ke, fassara ce miki aka yi Daɗi ne zai sa na bar ɗakina na koma nasa? Toh, maciji na gani a toilet ɗin, ni kuma wallahi ba zan iya sake zama a ɗakin ba, gwara na koma nasa duk runtsi!” Ta ɗan tsaya, sannan ta ƙara da wani irin yanayi na shagwaɓa, “Kuma idan ma na maida kayana can, me ruwanki? Mijinki ko nawa?” Maryam ta sake fashewa da dariya, “Hehehehe! Ah, mijinki ne wallahi, Uwargida! Ran gidan nan!” Bintu kuwa ta tabe baki kawai, tana kallonsu, ba ta ce komai ba, amma daga yanayin fuskarta za a iya gane cewa lalura ke zaune da ita a wajen, “Ku tashi mu je,” Raihana ta faɗa tana miƙewa, kamar ba ta son a ƙara bata lokaci da maganar, Maryam ta miƙe tana dariya, Bintu ma ta biyo su, haka suka rankaya zuwa ɗakin Raihana.
Da suka shiga, Raihana ta fara nuna musu abubuwan da take son ɗauka, tana zaɓar kayan da za ta buƙata a ɗakin Zayd, wannan karon kuwa, kasancewar Maryam da Bintu suna tare da ita ya sa ta ɗan manta da tsoron da take ji game da macijin, Maryam ta taimaka mata wajen tattara kayan, har da kayan wankanta da sauran abubuwan amfani, ta shiga bathroom ɗin ta ɗauko kayan da suke ciki, sannan ta haɗa su da kayan shafanta, bayan sun gama tattara komai, sai suka fito daga ɗakin Raihana, suka nufi ɗakin Zayd, amma da suka zo ƙofar ɗakin, Raihana ta tsaya cak, ta juya ta kalli Maryam da Bintu, sannan ta ɗaga hannu ta tare ƙofar kamar mai tsaron shiga wani wuri mai tsarki, “Bani ku juya!” Maryam ta zaro ido, “Mu juya ina kuma?” Raihana ta ɗan gyara tsayuwarta, ta ɗora hannu a ƙugunta, tana ƙoƙarin yin serious face duk da yadda dariya ta fara kokarin kamata, “Ba ku ji na ce ku juya ba? Me za ku yi min idan kun shigar min turakar miji?” Maryam ta sake fashewa da dariya, har sai da ta dafe cikinta, “Wayyo Allah na! Haj rayy fa tayi miji ba zata barmu ku sarara ba Ya Allah ka aurar damu! Tun da farko ai ke kika ce mu rakaki!” Bintu ta tabe baki, tana kallon su kawai, kafin ta girgiza kai a hankali, Raihana ta zuba wa Maryam harara, “Ku dai kawai ku juya tunda kun taimaka min na kwaso Allah ya Bada lada amma ba matar da zata shigar min dakin miji wallahi! Bare ku tsaya kuna karewa komai kallo,” Maryam ta ɗaga hannuwanta ya mikawa raihana Kayan hannunta, “Gashi, ranki ya daɗe! Mu dai za mu tsaya a nan, ki shiga ki yi abin da za ki yi,” ta sake dariya, sannan ta kalli Bintu, “Zo mu je, mu bar amaryar ta shiga turakar mijinta ita kaɗai,” Raihana ta yi saurin kallonta, “Amarya ko uwargida? !” “Na’am, Uwargida!” Maryam ta amsa da dariya, kafin ta ja Bintu suka koma ɗakin Raihana, Raihana kuwa ta girgiza kai, tana jin kunya da haushin yadda Maryam ta mayar da komai abin tsokana, daga nan ta shiga ɗakin Zayd.
Da ta shiga, sai ta nufi wardrobe ɗinsa kai tsaye, ta buɗe ƙofar wardrobe ɗin, ta fara matsar da wasu daga cikin kayan Zayd gefe, tana neman gurbin da za ta jera nata, ta fara jera kayan da suka fito da su, har da kayan safe da ta riga ta ɗauko tun farko, waɗanda suke ajiye a kan sofa, ta kwaso su gaba ɗaya, ta saka su cikin wardrobe ɗin, tana gyara su yadda za su zauna cikin tsari, bayan ta gama, sai ta matsa zuwa dressing mirror ɗin, a hankali ta fara matsar da wasu daga cikin kayan Zayd da ke saman mirror ɗin gefe, sannan ta baza nata a hankali, tana ajiye su yadda za ta iya samun su cikin sauƙi, ta ɗan ja baya, ta kalli yadda komai ya kasance, sannan ta ɗan gyara wasu daga cikin kayan da take ganin ba su zauna yadda ya kamata ba, ta cike wajen tsafff da Kayan ta tamkar dai dakinta bana aro ba, “Hmm,” ta furta a hankali, tana kallon yadda ta samu gurbin kayanta a cikin ɗakin, daga nan ta nufi bathroom ɗin da kayanta na wanka, ta shiga, ta buɗe shelf ɗin da ke ciki, sannan ta fara jera kayan wankanta a tsari, ta ajiye sabulunta, kayan wankanta da sauran abubuwan da take amfani da su, har sai da komai ya zauna yadda take so, ta kalli shelf ɗin na ɗan lokaci, ta gyara ƙaramin abu da bai zauna daidai ba, sannan ta juya ta nufi hanyar fita, amma tana gab da fita ne sai ta tuna da wani abu, shanyarta! Nan take ta tsaya.
Ta juya da sauri, ta koma wajen rack ɗin da take tsammanin ta yi shanyar, amma da ta duba, sai ta tsaya cak, babu komai, ta zaro ido, ta sake kallon rack ɗin kamar ba ta yarda da abin da take gani ba, “Subhanallah! Ina kuma ya tafi?” Ta matso kusa, ta fara duba wajen da kyau, tana ganin ko ta rataye ne a wani gefen, ta duba ƙofar bathroom ɗin, ta duba shelf ɗin, har ta sake leƙa bayan ƙofar, amma babu, ta dafe ƙugunta, tana kallon wajen cikin mamaki, “Wai, shanyata ta ina ta ɓace? Ai na san na kawo nan!” Ta sake bincike, amma ba ta komai ba, a ƙarshe ta tsaya a tsakiyar bathroom ɗin, tana kallon komai da mamaki, “İkon Allah…” Ta kasa ƙarasa maganar, ta sake duba rack ɗin a karo na ƙarshe, amma har yanzu babu komai, cikin mamaki da tambayoyi a ranta, ta fito daga bathroom ɗin, ta rufe ƙofar a hankali, sannan ta tsaya a cikin ɗakin Zayd, zuciyarta cike da mamakin inda shanya ta shiga.
A ƙarshe dai, bayan ta gama ɗuk tunaninta ba tare da ta gano inda shanya ta shiga ba, Raihana ta fito daga ɗakin Zayd ta koma ɗakinta, inda ta tarar da Maryam da Bintu suna zaune, da ta shiga, ta nufi gefen wardrobe ɗinta, ta buɗe akwatinan lefenta da ke gefe, sannan ta juya ta kalle su da murmushi, “Toh, ku zo, kowa ya ɗauki abin da yake so, ku duba, idan akwai abin da kuka gani ya burge ku, ku ɗauka,” Maryam ta ɗan buɗe baki tana kallonta, “Really? Kina nufin za mu iya ɗaukar duk abin da muke so?” Raihana ta gyada kai a sauƙaƙe, “Eh mana! Me ya sa ba za ku ɗauka ba?” Ai kuwa, ba sai an sake faɗa wa Bintu ba, nan take ta matsa kusa da akwatinan, ta fara duba kayan da ke ciki da wani irin enthusiasm, kamar wadda ta daɗe tana jiran a ba ta wannan damar, “Ahhh! Raihana, wallahi kin iya zaɓar kaya!” ta faɗa tana ɗauko wata riga mai kyau, ta ɗaga ta tana kallonta daga gaba da baya, Raihana dai tana zaune a gefen sofa, tana kallonsu kawai ba tare da ta ce komai ba, Bintu ta ci gaba da cire abubuwa daga cikin akwatin, tana ajiye waɗanda suka burge ta a gefe, ta ɗauki wasu kaya, ta ɗauki takalma, sannan ta sake ɗauko wata jaka mai kyau, Maryam kuwa, wani takalmi ne Yayi mata kyau shi kadai ta dauka dan har saida raihana tayi da gaske snn ya dauki wata doguwar Riga mai mayafi, amma daga baya sai maryam ta lura da yadda Bintu ke ta tara abubuwa a gabanta, ta kalli kayan da ke gefen Bintu, sannan ta ɗaga gira, “Bintu! Wait a minute, kayan sun yi yawa fa!” Bintu ta juya ta kalleta, tana riƙe da wasu kaya a hannunta, “Kamar yaya suka yi yawa?” Maryam ta nuna abubuwan da ta riga ta tara, “Ki duba mana! Kusan abaya huɗu kika ɗauka, sannan ga sauran kayan, takalma, har da wannan Gucci bag ɗin, ke, ba fa wai za ki kwashe rabin lefen ba ne ko?” Bintu ta ɗan harare ta, sannan ta koma duba kayan da ke gabanta, “Tunda ba naki ba ne, sai ki ta kanki, ai ba ke kika ce na ɗauka ba!” Maryam ta buɗe baki tana kallonta, kamar ba ta yarda da abin da ta ji ba, “Wai Bintu, da gaske kike?” Bintu ta ɗaga kafaɗarta, “Of course! Ai Raihana ce ta ce mu ɗauki abin da muke so, ni kuma abin da nake so shi ne waɗannan,” ta sake ɗauko wata riga, tana dubanta da murmushi, “Besides, ba kullum ake samun wannan damar ba,” Maryam ta girgiza kai, tana kallon Bintu cikin rashin yarda, “Wallahi, ke kam kina da matsala!” Bintu kuwa ta yi mata banza, ta ci gaba da zaɓar kayanta kamar ba ta ji komai ba, Raihana da ke zaune a gefen sofa ta ɗan kalli Maryam, sannan ta girgiza mata kai a hankali, tana nuna mata cewa ta ƙyale Bintu ta ɗauki abin da take so, Maryam ta fahimci abin da Raihana ke nufi, amma hakan bai hana ta sake kwafa ba, “Fine! Ki ɗauka mana tunda ke baki San abinda yakamata ba, Bintu ta yi wata ƙaramar dariya, “Don’t worry about me, dear, I know exactly what I’m doing,” Raihana dai ta yi murmushi kawai, tana kallonsu suna ta saɓa baki, ba ta damu da yawan kayan da Bintu ke ɗauka ba, a wajenta, farin cikin ganin su a kusa da ita ya fi komai muhimmanci.
Sun ci gaba da zama tare, suna hira da dariya, har lokaci ya yi da Maryam da Bintu za su tafi, da suka gama haɗa kayan da suka zaɓa, sai suka tattara kayansu, suka shirya tafiya, Raihana ta raka su har bakin gate, fuskarta ɗauke da murmushi, duk da cewa a zuciyarta ba ta son su tafi da wuri, Maryam ta rungume ta sosai, “Ki kula da kanki, Rayy, and please, don’t forget us just because you’re now living with your handsome husband,” Raihana ta zaro ido, ta ɗan ture ta a hankali, “Maryam! Wallahi, ki daina shirmen nan,” Bintu kuwa ta na gefe kawai tace, “Za mu sake zuwa, little sister, nan ba da jimawa ba” Raihana ta gyada kai, tana ƙoƙarin murmushi duk da yadda zuciyarta ta fara nauyaya, “Allah ya kai ku gida lafiya,” “Ameen,” suka amsa a tare, daga nan suka juya suka nufi hanyar fita, Raihana ta tsaya tana kallonsu har suka yi nisa, sannan ta koma ciki a hankali, da ta shiga, sai ta tsaya a tsakiyar falon tana kallon wajen da suka zauna suna hira, nan take gidan ya yi mata shiru fiye da yadda ta saba, ta sauke numfashi a hankali, kafin su zo, gidan ya yi mata girma, amma da suka zo suka zauna da ita, ta ji kamar ta samu wani ɓangare na gidansu a cikin wannan katafaren gidan, yanzu da suka tafi, sai ta sake jin wannan kaɗaicin, a hankali ta koma cikin ɗakin Zayd, ta rufe ƙofar, ta nufi gado ta zauna, ta jingina da pillow, ta ɗauko wayarta daga gefenta, ta buɗe wayar, ta fara latsawa tana duba saƙonni, tana ƙoƙarin kawar da tunanin kewar da ta fara ji, amma duk da haka, gidan ya sake mata girma sosai, ta juya ta kalli ɗakin na ɗan lokaci, sannan ta sauke numfashi ta koma kallon wayarta, “Allah ya sa ya dawo da wuri,” ta furta a hankali, ba tare da ta ankara da abin da ta faɗa ba, sai da ta gama furucin ne ta ɗan tsaya kamar ta fahimci abinda tace, ta sake mai da hankalinta kan wayarta, ta shiga nan ta fita nan kamar babu abin da ya faru.
Da misalin ƙarfe huɗu na yamma, Zayd ya gama aikinsa a office, ba tare da ɓata lokaci ba, ya nufi Armaan Mansion kai tsaye, yana shiga lounge ɗin, ya tura ƙofar a hankali, yana sassauta tie ɗinsa, a falon, Ummie ce kaɗai zaune a kan doguwar sofa, yayin da wasu kayayyaki suke jibge a gefenta, kamar dai ta gama lissafinsu, Inno ma dama kwana biyu kenan da komawa Adamawa, jin motsin tura ƙofar ne ya sa Ummie ta ɗago kanta, a hankali, idanunta suka yi haske da farin ciki da ta ga tauraronta, habibinta, Zayd ya tako zuwa gabanta, kuma a tattare da shi akwai gajiyar da duk wanda ya kalle shi zai fahimta tun daga farko, duk da irin ƙarfin halinsa da yadda yake tafiyar da harkokinsa a office, akwai wani yanayi na musamman da yake shiga duk lokacin da yake tare da mahaifiyarsa, da ya iso gabanta, sai ya durƙusa, “Assalamu alaikum, Ummie,” muryarsa ta fito a hankali, kamar ba shi ba, “Wa alaikumussalam, habibi,” ta amsa da murya mai cike da ƙauna, fuskarta ɗauke da murmushi, kamar yadda ya saba, ya kama hannunta suka yi musabaha, sannan ya sumbaci bayan hannunta, Ummie ta ɗaga ɗayan hannunta ta shafa kansa, tana kallonsa da irin ƙaunar da ba ta taɓa raguwa ba, “Barakallahu feek, habibi,” “Wa feeki barakallah, Ummie,” ya amsa cikin ladabi, daga nan ya miƙe a hankali ya zauna a gefenta, ya jingina kansa a kafaɗarta, ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, kamar dai a wannan lokacin ne kawai ya samu damar sauke duk wani nauyi da ya ɗauko daga office, cikin muryar shagwaɓar da ya saba yi mata, ya ce, “Ummie, I am hungry,” Ummie ta yi wata ƙaramar dariya, tana kallon shi, “Haba, habibi! Matanka fa biyu, me ya sa za ka ji yunwa?” Zayd ya ɗan turo baki kamar ƙaramin yaro, ba tare da ya ɗago kansa daga kafaɗarta ba, “Ni dai naki nake so, I missed your food, Ummie,” “Really?” ta tambaya tana ɗan dariya, “So, your wives can’t feed you anymore?” A hankali Zayd ya buɗe idanunsa, ya ɗago kansa kaɗan ya kalleta, “Ummie, please, don’t start,” ta danyi dariya ganin yadda ya yi maganar, sannan ta girgiza kai a hankali, “Look at you! A grown man, a CEO, with two wives, yet you’re here behaving like a little boy just because you want your mother’s food,” Zayd ya sake jingina kansa a kafaɗarta, kamar ba shi da niyyar tashi daga wajen, “And what’s wrong with that? I’m still your baby, Ummie,” maganar tasa ta sa murmushin Ummie ya ƙara faɗaɗa, ta sauke idanunta a kansa, tana shafa kansa a hankali, “Yes, habibi, no matter how big you become, you’ll always be my little boy,” Zayd bai ce komai ba, sai dai ya ɗan murmusa, wannan ɗaya ne daga cikin lokutan da yake jin daɗin kasancewa kusa da ita, ba tare da wani ya zo da matsalar da zai warware masa ba, ko wani abu da zai buƙaci ya yanke hukunci a kai, Ummie ta ɗan matsa ta gyara zamanta, “It’s fine, bari na kawo maka abinci ka ci,” ta miƙe a hankali, ta nufi dining area, ta zuba masa wainar shinkafa tare da cow leg, ta hadi da jug din juice sai bottled water sannan ta dawo ta yi masa presenting ɗin abincin cikin kulawa, “Ga abincinka, habibi, ka ci sosai, kaji? You look tired,” Zayd ya ɗago kansa ya kalli abincin, sannan ya kalleta, “Thank you, Ummie,” daga nan ta ɗebo ruwa a bowl, Zayd ya miƙe da sauri ya karɓa daga hannunta, sannan ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa, ya yi Bismillah, sannan ya fara cin abincin a hankali, Ummie ta koma ta zauna a gefensa, tana kallonsa cike da ƙauna, a duk lokacin da ta kalli Zayd, tana ganin ƙaramin ɗanta da ya saba dawowa gare ta duk lokacin da yake buƙatar kulawa, duk da cewa yanzu ya zama babban mutum mai nauyin da ke rataye a kansa, ta ɗan karkatar da kanta, tana nazarin fuskarsa, “Habibi, how was your day?” Zayd ya ɗan dakata da cin abincin, ya ɗauki ruwan da ke gabansa ya sha kaɗan, “It was fine, Ummie, just a little hectic,” “Hmm,” ta furta, tana gyada kai, “You need to learn to rest, habibi, ba office kaɗai ne yake da muhimmanci ba, your health matters too,” Zayd ya ɗan ɗago gira, yana kallonta da wani irin kallo na mutum da ya riga ya san inda maganar za ta dosa, “Ummie, I’m fine,” “I know you,” ta katse shi a hankali, “You always say you’re fine, even when you’re exhausted, I can see it on your face,” ya ɗan yi murmushi, sannan ya koma cin abincinsa, “Okay, Ummie, I’ll rest,” ta kalleshi na ɗan lokaci, kamar tana son tabbatar da cewa ya faɗi maganar da gaske, kafin ta girgiza kai da murmushi, “That’s my boy,” Zayd ya ci gaba da cin abincinsa, yayin da Ummie take zaune kusa da shi, tana kallonsa cike da ƙauna, a fuskarta akwai irin wannan farin cikin da uwa ke ji a duk lokacin data kebe da ɗanta mafi soyuwa a gareta