Free chapter · Read without an account
A Mother’s Trail
by NorthernAngel · His Rose
Ko da ta iso part ɗin Yemma, a foyer ta hango pram ɗin Jasmine a ajiye. Fuskarta a ɗaure ta shiga ciki, ko kallon Fadma da ke zaune a living room ɗin ba ta yi ba ta wuce abinta. Da wata ƴar dasasshiyan sallama da ita kaɗai ta ji abinta ta tura ƙofar ta shiga. Yemma da ƙawayenta na zaune sai hayaniya suke suna hirarsu, sai kawai ga Zara ta bayyana a gabansu kamar an jefo ta, exuding an intense, frosty aura. Abun mamakin shi ne, idon Jasmine biyu tana hannun Yemma ta ɗaga ta sama tana mata wasa, looking bright-eyed and alert. Da alama ba ta daɗe da farkawa ba, ɗan lokacin da Zafar ya fita da ita bacci ta fara ko kuma tada ita Yemman tayi, Zara ta faɗa a ranta rana sake haɗe fuska. Zara na kallonsu gaba ɗaya, kamar yadda suma duk suka ɗakata da maganar da suke yi suna kare mata kallo tun daga ƙafa har kai. Tuni fuskar Hajiyar Sudan da ta Yemma ta sauya gaba ɗaya, hardening into deep resentment. Waccan ƙawar Yemma da ake kira Malika da ta zo daga Algeria, ta gyara zamanta tana jefa wa Zara wani irin kallo. Matan abokan Baffa kuwa, biyu daga ciki ne kawai suka gane Zara saboda sun je Warri wurin bikin ta, sauran biyun kuwa, ba su gane ta ba. Ba yabo ba fallasa, Zara ta gaishe su a jam’u cikin sanyi, keeping her distance.“Ina wuni.” Waɗannan matan biyu da ba su santa ba ne kawai suka amsa mata cikin sakin fuska, sai dai tuni suka fara reading room ɗin—seeing how only the two of them responded yayin da sauran circle ɗin suka zama froze with visible disdain. Hajiyar Sudan ce ta fara magana cikin ƙasaita da zallar faɗa, “Da ba mu wuni ba ƙya gan mu? Haka ake gaida manya a gidan iyayenki? Kin shigo kawai ba sallama kin ce mana wani 'ina wuni', to wai wa kika gaisar a cikin mu?” Zara dai kallonta kawai take yi ba tare da ta ce mata uffan ba. Har Hajiyar Sudan ta gama wannan masifar tata, ba a samu wata alama ta cewa Zara za ta tanka mata ba. She just stood there motionless, idonta na kan ƴarta da ke lulluɓe cikin knit blanket ɗinta, rungume a ƙirjin Yemma da pacifier ɗinta a baki. Ba tare da ɓata lokaci ba, Zara ta tsare idon Yemma kyar, her tone firm and completely unbothered: “I came to pick up my daughter.” Wani gigitaccen salati ɗaya daga cikin matan abokan Baffa—wadda ake kira Hajiya Hauwa Shettima—ta doka tana cewa, “Wai ni Hajiya Aziza ya aka yi wannan yarinyar take gidan ɗanki har yanzu? Ni wallahi na zata ta zama tarihi! Duk na sha wannan ƴar uwar tasa da ya aura farko ita ce ta haihu!” Daga haka ta maida kallonta kan Zara tana sake wani salatin da haɗe fuska, “Yanzu ƙe yar nan, saboda rashin ta ido, kin san daga inda mu ke kuwa? Wasu ba ma a ƙasar nan suke ba! Ni kuwa tun daga Abuja na taso na zo nan ɗan in yi barka, amma ba kunya ba tsoron Allah ki ce mana wai kin zo ɗaukar ƴarki? Toh ba za a ba da ita ɗin ba! Yar iska mara kunya wadda ba ta san kara ba.” Wata mata daga cikinsu ta karɓe da hanzari, “Kara ai ta yi gabas ita ta yi yamma! Wannan tsantsar rashin tarbiya ne ƙarara ta nuna, ta kuma nuna mana irin gidan da ta fito da irin tarbiyar da ta samu!” Ɗaya ma daga cikinsu ta yi saurin ƙara wa da, “Ɗiyar marigayiya Maryam ce fa. Wa ya kai Maryam sangarta ƴaƴa?” Hajiyar Sudan ta karɓe zancen tana wani taɓe baki, “Ai kuwa kanta ta cuta, ɗan yanzu ina amfanin irin wannan?” Duk suka amsa a tare cikin haɗin baki, “Wallahi babu!” Hajiyar Sudan ta sake kallon Zara tana cewa, “Ƙin ɓace mun daga gani ne ko sai na tashi na sassaɓa miki?” Hajiya Hauwa Shettima tace, “Ta ɓace ina? Kina ganin yanda take kallon mutane cikin ido ko alamar kunya ko shakka babu. Ai wannan yar iskar babu alamar tsoro ko kunya a tattare da ita.” Yemma, dake tayi wa ƙawarta Malika bayani cikin yarensu na Algeria—explaining the intense situation to her—sai alokacin ta maida hankalinta kan abin da ke faruwa. Ta ɗago ta kalli Zara coldly, her voice laced with absolute command, “Fitar min a gida kafin in sa a fitar da ke.” Banza Zara ta yi mata. Ta ɗan turo bakinta gaba, instantly folding her arms across her chest while adjusting her stance into an immovable posture. Ɗaya daga cikin matan mai suna Hajiya Atine Galadanci, tuni ta saki baki tana kallon Zara cikin al’ajabi da tsantsar mamaki—is this really the same bride whose Warri wedding they attended, showing such unyielding defiance? Amma ba ta yi wani dogon mamaki ba, knowing the family history. “Tabdijam! Ikon Allah. Ai ni gaskiya ta min yawa,” ta faɗa tana riƙe haɓa, staring at Zara in sheer disbelief. Cikin wata gigitacciyar tsawa Yemma tace, “Ba za ki fita ba? Are you out of your mind?” Zara ta saki turo baki kamar za ta yi kuka, her voice trembling slightly yet resolute: “I’m not going anywhere without my daughter.” Is she intimidated? Yes, absolutely! Coupled with that overwhelming wave of helplessness data fara ji, ganin tana tsaye trapped in an environment where raw power and collective hostility are being weaponized against her. Tuni idonta ya ciko taf da ƙwallah, amma haka ta riƙa ɗaga kanta sama forcing the tears back, while they ruthlessly bombarded her da insults and verbal abuse—suna dragging late mother ɗinta into the mud. Musamman Hajiyar Sudan da Hajiya Hauwa Shettima—wadda kana ganin yadda take komai cikin izza da masifa za ka gane she’s naturally aggressive and disrespectful. Har da attempting ɗin marin Zara, amma Hajiya Atine Galadanci quickly held her back. Zara, tani tayi reaching limit ɗinta na tsayuwa da taking relentless insults ɗinsu, kawai ta fara tafiya. Ignoring the venomous glares in the room, ta nufi straight inda Yemma ke zaune to physically claim her daughter. Da tsananin mamaki Yemma ke kallonta, feeling completely stunned and waiting for her to step closer yanda zata samu tayi slapping the absolute disrespect out of her face. Bata tama tunanin insolence ɗin Zara ya kai wannan level ɗin ba, yau take tabbatarwa duk wannan built-up hatred ɗin da warnings ɗinda takewa ɗan ta about Zara’s lack of upbringing were spot on. Kafin Zara ta ƙaraso, Hajiyar Sudan ta miƙe tasha gabanta, blocking her path while locking eyes with her. Cikin kakkausar murya dake nuna tsananin ɓacin rai, ta nuna wa Zara ƙofa tana cewa, “Wuce… fita a gidan nan kafin in sa miki hannu.” Da mamakin rashin sa mata hannun da ba a yi ba har yanzu, Hauwa Shettima tace, “Wai ni kuna bani mamaki! Aziza ina Zafar ne? Wallahi wannan yarinyar in surukata ce ba za ta kwana a gidan nan ba. Wallahi da tuni wani zancen ake ba wannan ba.” Zara, wadda ta riga rayi broken down into bitter tears zuwa lojacin, tsaye take frozen a gaban Hajiyar Sudan. Fighting back the lump in her throat, ta kalli Yemma tana cewa, “Just hand over my daughter, please. I’m not here to start a scene; I only want my child.” A wani irin zuciye Yemma ta miƙe tana nufar Zara. Cikin sauri Atine Galadanci da ɗayar suka miƙe, physically stepping between them before Atine turned to Zara, tana faɗin: “Ke kuma Zara, ki tafi mana! Me yasa ba ki jin magana ne? Ba surukarki ba ce? Za ta cutar da ɗiyar ɗanta ne? Ita fa ta haifi uban yarinyar nan.” Cikin tsantsar taurin kai, Zara tace, “Ni ma ni na haifi ƴata. Ta bani ita in tafi abuna.” Duk suka yi shiru suna kallonta, completely shocked saboda it was only now Zara ta musu rashin kunya ɓaro ɓaro da baki without holding back. Atine tare da wata daga cikinsu har haɗa baki suka yi gurin cewa, “Aziza, ɗan Allah ba ta ƴarta ta tafi.” Wata ma ta ƙara da, “Ai shi ne. Tun kafin ta fara zagin mu, Aziza miƙa mata ƴarta ta tafi. Idan mu ne wallahi mun yafe, Allah ya raya Jasmine. Amma wannan kam sai kin tashi tsaye, ɗan jikarki ba ta da uwa, haka zalika ɗanki bai da mata, sam.” Hauwa Shettima, still seated with an unreachable aura, sneered, “Ai Aziza, kar ki sake ki yi kuskuren barin wannan tsinanniyar yarinyar ko kwana ta sake a gidan ɗanki! Dan wallahi ta ci bulus wannan ƙunyata kin da ta yi, shikenan ta ga hanya. Ni mamaki ma nake da tun ɗazu ba ki kira Zafar ɗin ya zo ya ga rashin arzikin da take yi da idonsa ba. Kuma wallahi kar ki ba ta ƴar nan. Idan da mai ƙwatar mata ita a duniya, ta je ta kira a ƙwatar mata. In ma Maryam za ta taso daga ƙabarinta ta ƙwatar mata ƴar a hannunki, to ta daɗe ba ta je ta taso ta ba.” Hajiyar Sudan na gyaɗa kai cikin gamsuwa ta ƙara da, “Yauwa. Ni ma dai abun da na gani ke nan. Ita har wace da za ta shigo har nan ta ce a ba ta ɗiya a ba ta? Wallahi ko Maryam ta yi kaɗan! Ki je ki kira duk wanda za ki kira. In ba ki yi wasa ba ma, ƙarshen ganinki da ƴar ke nan da kika yi wannan ɗiban albarkan. Yar iska da bata gaji musulunci da kunya ba.” Cikin kuka Zara ta kalli Yemma, her entire frame trembling visibly, muryarta na breaking yayin da takr forcing words ɗin out: “For the last time Yemma, hand me my daughter.” Ita wkuwa Yemma, the sheer humiliation da takaici kept her completely silent. Amma ta ƙulla a ranta cewa yau Jasmine sai ta kwana a ɓangarenta ta ga yadda Zara za ta yi. After all, she had already watched Jasmine drink every last drop of the formula from the bottle. Bata ma kula Zaran ba ta koma ta zauna, dan dai tasan Zafar na tare da abokan Baffa ne, ga kuma masu kawo kudin auren Aisha, shiyasa bata kirasa ba. Kuma deep down, she was secretly terrified that Zafar zai iya cewa ta ba Zara yarta back—he was completely capable of doing so, especially inya shigo ya ga Zara in tears ko kuma yaji harsh insults ɗin da friends ɗinta ke spewing. Bayan ta zauna, Zara ta sake cewa, “I want my daughter, Yemma.” Hauwa Shettima ce tayi magana cikin mamaki, “Anya wannan tsinanniyar Amadi girl din basu da maita a jininsu?” Wata daga cikinsu ta ce, “Meye ne ma basu da shi? Ai ba abun mamaki bane dan kin gano mayu ne.” Zara, wadda ke staring right at them, ta gyaɗa kanta slowly while wiping her tears. Cikin tsantsar zafin kai, ta kalli Yemma while still nodding, sannan tayi snapping fingers ɗinta da wani sharp precision. In a low, dangerous voice, ta ce wa Yemma, “Just watch me.” Daga haka ta juya a zuciye kamar zata tashi sama, rushing out of the parlour with pure resolve. Cikin mamaki Hauwa Shettima ta ce, “Aziza? Kece kuwa? Haka kikayi sanyi?” Wani soft, calculating laugh ne yayi escaping Yemma’s lips, tana girgiza kanta—ita kaɗai tasan kalan revenge and chaos she was quietly brewing in her mind. Zara na fitowa daga parlourn ta ci karo da Fadma tsaye bakin ƙofar—da alama laɓe take tana sauraren komai. Ba ta yi wata-wata ba ta sa ƙafa ta kwarfe ta, ta faɗi ƙasa tana sakin wani gigitaccen ihu. Zara kuwa, ba tare da ta tsaya ba, ta ci gaba da tafiyarta tana goge hawayenta da ya ƙi tsayawa. Tafiya take kamar za ta tashi sama, idonta ya rufe tsabar ɓacin rai. Babu abun da ke yawo a kanta sai mahaifiyarta da suka riƙa sakowa cikin zage-zagensu. Gyaɗa kai kawai take tana tafiya har ta iso wing ɗin Baffa. Har da tuntuɓenta garin shiga cikin foyer ɗinsa bayan ta buɗe ƙofar. Tun kafin ta ƙarasa cikin parlourn take jin maganar mutane sama-sama. Baffa na zaune shi da su Abbah da kuma abokansa su kusan huɗu, sai kuma iyayen saurayin Aisha, Galado, da ke zaune kusan su biyar su ma, sai kuma yayyinsa maza su biyu. Tattaunawa suke mai mahimmanci game da auren, inda mahaifin yaron ya bada shawarar su ɗaura kawai a masallaci bayan sun yi Magrib, illa yaso daga baya komai sai ya biyo baya. Kamar daga sama suka ga Zara ta shigo cikin parlourn—ko sallama babu—fuskarta jiƙe jagab da hawaye. Muazzam da Zafar a tare suka miƙe suna tambayar lafiya, me ya faru? Kafin Ahmad shi ma ya hau faɗin, “Subhanallah, me ya faru Rose?” Sai dai ko kallonsu ba ta yi ba gaba ɗayansu. Kai tsaye ta riƙa wuce mutane ta tsakiyar parlourn, her tear-filled eyes scanning the room intently har saida gaze ɗinta yayi landing on the exact person she was looking for. Ƙara saurinta ta yi ta isa inda yake zaune a kan wata royal oversized sofa. Tana zuwa ta ɗuka dai-dai kunnensa ta yi masa raɗa—wadda daga shi sai amininsa da ke kusa da shi ne kawai suke ji. Magana take masa mai tsawo a kunnensa, whispering a flood of details in his ear, yayin da rest of the room could only hear the soft, ragged sound of her muffled sobs. Tuni hankalin kowa a parlourn ya tashi, everyone frozen in suspense and assuming something terrible had happened. Zafar tuni ya matso inda take ɗuƙe ɗin tana wa Baffa raɗar yana kallonta. Har ya kira sunanta, amma Baffa ya ɗaga masa hannu—a sharp, silent command to hold back. Zara na cikin yi masa raɗar, farat ɗaya aka ga Baffa ya miƙe tsaye kamar an tsakure sa. Ba tare da ya kalli kowa ba ko ya cewa kowa wani abu ba, ya fara tafiya yana nufar hanyar da za ta fitar da shi ta garden ɗinsa. Zara ta fara bin bayansa nan take ita ma, tana sauke ajiyar zuciya tare da goge hawayen fuskarta. Cikin tsantsar tashin hankali, Zafar, Muazzam, da Ahmad suka hau bin bayansu to figure out abun da ke faruwa...